← Book details A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 46

Sashe 36

A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sallamar mahaifinta da ta jiyo tare da wasu mazan yasa gabanta bugawa, wannan fargaba ta zama jiki na kowacce amarya.
Humaira ce ta shigo fuska ɗaure tace “Aunty Mabruka su Alhaji na jiran ki a parlour”
“Ban gane ba” ta tambaya
Kamar ba za ta amsa mata ba amma tunawa da mai faruwa ta faru yasa ta ce
“Ki fita ki ji mana” daga haka ta wuce nata Bedroom ɗin ta saki kukan baƙin cikin rasa nagartaccen miji irin Yaya Sadauki.

Hijabi ta saka tana mai barin iya idanuwanta waje har ta isa parlourn. Tsugunnawa tayi ta sunkuyar da kanta ƙasa. Alhaji Uthman ne ya fara buɗe zaman da addu'a sannan ya ɗaura da nasiha ga amaryar tuni kukan da take haɗiyewa ya kufce mata, sosai yayi mata nasiha daga ƙarshe ya damƙa mata sadakinta a hannunta.
Alhaji Baba ya ɗaura da faɗin
“Ki yi shiru haka nan, duk wani abu da ya kamata a faɗa Papanku ya faɗa, a matsayi na na mahaifin ki kuma babu abun da zance illa iyaka ki kasance mace mai haƙuri a gidan aurenki tunda dama ibada ce ta kai ki, kul naji ko na gani kin yi rashin ɗa'a ga mijinki, ki bi shi sau da ƙafa shi ne kaɗai abun da zan roƙa a wurin ki. Kin gane?”
Kai ta gyaɗa ta ci gaba da kukanta.

Bayan su Alhaji Babba sun fita Aunty Na'eema tazo ta ɗaga ta suka shiga ciki, wanka ta sa ta gaba tayi bayan ruwan ƙamshin da ta haɗa mata a toilet. Bayan ta fito ma wasu turaruka ta ƙara bata ta shafe jikinta da su sannan ta ɗaura wani mai mai Masifar kamshi. Atamfa ta fitar mata ta saka su Raudha sai yaba kyau suke suna santi, ita dai amarya zuciyarta ce ke wani irin bugu kamar zata fasa ƙirjinta ta fito. Bayan ta saka aka ɗaura mata alkyabba a kai sai ta fito kamar wata gimbiya, kai tsaye ɗakin Hajiya Babba suka nufa, nan iyaye mata ma suka mata nasiha, Hajiya Babba dai addu'a kawai take mata cikin ranta kan Allah ya basu zaman lafiya. Daga nan suka wuce Part ɗin Hajjaty bisa umarnin Alhaji Baba, daga nan kuma za a wuce da ita ɗakin mijinta.

A can Part ɗin Hajjaty ma ta sha nasiha sosai, Aunty Madina dai da ido ta bi ƙanwar Tata ƙasan ranta tana mata addu'ar Allah ya daidaita tsakaninta da mijinta su yi rayuwa mai inganci, daga nan kuma Papa ya sa ta a Mota bai tsaya da ita ko'ina ba sai gidan mijinta wanda Daddynsa ya masa kyautarsa. Ma sha Allah, nan ya kara jan kunnenta kafin ya fito. Yana tafiya sai ga su Aunty Na'eema, Raudha, Ma'eesha, Aunty Madina sun iso.

Aure dai ya riga ya ɗauru, masu farin ciki suna yi, ƴan baƙin ciki ma ana nan ana ƙulla ya za a yi a warware aure, sai dai ta Allah ba tasu ba, abunda Ubangiji ya tsara babu mai iya ja da shi.

*ZAHRAH*

Sosai wannan biki ya mata daɗi ko ba komai ta ƙara sanin wasu ahalinta kuma alaƙa mai kyau ta ƙullu tsakaninsu, Musamman Aunty Madina, tun da aka ce mai sunan Mama ce ta ji tana ƙaunarta ita da yaronta Aamir, Yaya Haidar ma sosai ya nuna kulawarsa gareta har yake cewa in sun gama WAEC& NECO za ta zo musu hutu don tuni sabo ya shiga tsakanin ta da su, Aunty Salma matarsa ma Babu kaifi tana da kirki ga kyakkyawar babynsu mai shekaru huɗu Nihal, yarinyar ba dai shiga rai ba shiyasa Zahrah ta tattare su ita da Aamir da baby Aryan. Tun su Nasreen na mita har suka gaji. Sosai yaran suka ɗebe mata kewa.

*Mommah*

Duk da cewa she can say now she's stable Amma ta rasa yaya za ta yi ta dakatar da auren nan, ganin dai ba riba za ta ci ba tunda an ɗaura yasa ta ajiye makaman yaƙin ta gefe tunda dama can zuga ce ta rufe mata ido har zuciyarta ta makance ta yanke wa kanta wannan mummunan hukunci, yanzu ya za ta yi? Tana buƙatar gidan mijinta a yanzu amma ba ta da kwarin gwiwar tunkararsa.

Ya Junaid ma da yaje Hajja ta feɗe masa komai, sosai yaji zafin hali irin na mahaifiyarsa tasa, nan Hajja ta ja kunnensa kan kada ya kuskura yace zai kashe mata kuɗi, ya bar ta sai ta yi hankali. Bai so hakan ba amma babu yadda ya iya sai ya nema mata waya ƴar keypad yace kafin a gama bikin zai san yadda zai yi da ita.

Da yamma kawai sai ga Ammie da Mamie sun kai mata ziyara, a maimakon da ta gano kuskurenta ta yanke alakar ta sa su sai ma ƙara ɗinkewa da suka yi, yanayin da suka ganta yasa suka fahimci akwai saura fa, hakan yasa suka koma bayan zigin da suka mata amma kafin su fita Hajja sai da ta tare su ta buga musu warning na su fita daga rayuwar ƴarta. Abun ku da ƴan duniya sai Ammie tace
“Ki raba mu da ita tunda ke kika haɗa mu da ita, ka ji tsohuwa da iya shege” daga haka suka cika bujensu da iska.

*9:00pm*

Yaran Zahrah da Zakiyya suka kai wurin Hajjaty saboda su samu su shirya, da ƙyar Ya Aufa yace zai kai su da sharaɗin suka wuce time ɗin da ya sa ba zai kai su ba, nan suka wuce suka fara shiri a gaggauce.

Waɗanda ke gidan amarya tuni aka fara haramar tafiya Dinner, kowa sai kece ado yake kamar ba shi ba. Takanas make-up artist ɗin tazo ta sheƙawa amarya kwalliya, idan ba sanin cewa Aunty Mabruka ba ce ba lallai ka iya gane ta ba, ta yi kyau sosai abunta kamar ka jefa a aljihu ka gudu da ita.

Horn ɗin da suka ji ya tabbatar musu da cewa ango ne ya zo ɗaukar amaryarsa. Yaya Khalil ne ya rako shi har parlourn kana ya maka sallama, hakan yasa su Raudha fitowa suka ba su waje, shi kaɗai ya shiga ciki, “Tabarakallahu Rabbul khalikin” ya samu iya gurtawa can ƙasan maƙoshi yana yaba yadda tayi kyau. Tsinin idanuwansa da ke yawo kanta yasa ta ƙara sunkuyar da kanta, hakan yasa ya ɗan kauda fuska ya nufe ta tare da mika mata hannunsa
“Amarya, Are we good to go?”
Ba ta amsa masa ba sai ta miƙa masa nata hannun a kan nasa. Gaban su ne ya buga a tare.

Ganin za su ɓata musu lokaci yasa Yaya Khalil yin gyaran murya, da sauri ya ɗago ta tsaye har suna iya jin numfashin junansu.
“Mu je” ya faɗa a hankali. Suna fitowa su Raudha suka rangaɗa guɗa, murmushin da iyakacin sa kan fuska ta saki har suka bar parlourn, nan masu hoto suka fara kashe musu aiki. Net ɗin da aka makala mata a ka ta take ta ƙasa sai tayi tagal-tagal kamar za ta faɗi, caraf ya riƙe ta sai ta ɗan kwanto jikinsa. Habaaaa ai pictures da videos ɗin da aka yi ba a magana a lokacin.
“Ki kula da hanya” kai ta gyaɗa masa, nan suka wuce, shi ya buɗe mata motar ta fara shiga sannan ya rufe mata, ya zagayo ya shiga ɗaya side ɗin. Nan Prince Bello ya ja motar zuwa event center ɗin.

Lokacin da motarsu ta tsaya shi ya fara fitowa ya buɗe mata, bayan ta fito ya riƙe hannunta suka shige hall ɗin, daidai isowar su Zahrah da squad ɗin ta. Ma sha Allah, the growing ƴanmata kenan! Sun sha kyau abun su duk da cewa ba kwalliyar da suka yi, ɗinkin ya amshi jikinsu kamar dai an gwada su aka yi.
Tare da Ya Aufa suka shige yana gaba suna bayansa. Cikin mintuna uku aka fara shagali.

Nan aka ƙira amarya da ango stage, kamar dai kowanne masoya haka suka fito suka ɗan taka, zo ku ga yadda ake watsa kuɗi kamar na tsugunna na kwashe amma babu dama, bayan sun koma aka ba wa ƙawayen amarya dama da su fito su ma, Raudha, Ma'eesha sai Aunty Na'eema suka fito, sosai su ma aka watsa musu kuɗi, me zan ga, daf da za su koma Yaya Junaid ma yazo ya gwangwaje amaryarsa da dollars, Ni ko nace har yanzu dama ana watsa dollars?.

Dangin miji aka fara kira, shiru kowa yaƙi fita sai ga su Jidda, Hibba an fito, kafin kace me sai ga su Zahrah an fito fili. Aka sa musu sauti su gwangwaje ai kuwa nan aka san an zo Dinner, bayin Allah rawa suke kamar an aiko su, nan fa hankalin jama'a ya dawo kan su, ashe tun fitowarsu Prince Bello ya ƙyalla idonsa kan Zahrah, hohoho abun da ake kira da love at first sight shi ya faru, yadda take rawa ana mata liƙi yasa yaji wani iri, da sauri ya fita, within a minute Sai ga shi ya dawo, dollars ya shiga liƙawa Zahrah wacce bata ma san yana yi ba.

Babu zato babu tsammani taji an ja hannunta da ƙarfi, ɗagowar da za ta yi idon ta ya sauƙa akan Yaya Sadauki. Gwalo idanuwa tayi ta ma kasa magana saboda yadda taga fuskarsa a ɗaure. Bai tsaya ko ina da ita ba sai da suka bar hall ɗin, a jikin wata bishiya ya tsaya yana aika mata wani mugun kallo, kanta ƙasa taji yace
“Are You out of your senses Lily? Za ki shiga fili kina rawa ana miki liƙi saboda ba ki da kunya?”
Mamakinsa ne ya kama ta, ko ina ruwan sa da rawar ta?
Murya shagwaɓe tace
“Haba Yaya, bikin ka fa ake yi kuma sai kar nayi farin ciki? Naga...”
“Shut up!” ya dakatar da ita
“Don ana biki na baki ga maza ne cike a hall ɗin ba?”
Caraf Zahrah tace “To ai ƴan uwana ne”
Chapter 36 · 0% Book details