← Book details A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 46

Sashe 31

A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“Eh Lilyn Yaya, idan ban takura ki ba please lazy creatures ɗin nan su taimaka miki ku yi mana girki Ni da baƙi na.”
Amsa ta bashi da “To Yaya, In an gama zan sanar da Hajjaty cewa ta ƙira ka, Bye Ango..”

Maganarta ta ƙarshe ta so ta bugi zuciyarsa wai ango? Da gaske wai angon zai zama? Ya tambayi kansa.
Murmushin takaici yayi yana mai ƙara tausayawa ƙanwarsa Mabruka, kamar wanda aka zare masa laka ya fara laluɓen Numbern da jiya ta ƙira shi tana masa magiyar ya ce ya fasa auren don Allah.
Bai ɓata lokaci wurin shawara da zuciyarsa ba ya danna mata kira, ringing ɗin farko ta ɗaga kiran.
Shiru yayi sai da ta yi sallama ya amsa mata. Shirun ne ya ƙara kasancewa tsakanin su kafin tace
“Yaya Sadauki ina jin ka”
Ƙuƙƙifta ido ya fara yi kamar wani maras gaskiya yace
“Akwai abun da kuke buƙata na hidimar biki, kuyi listing sai ki tura min ko?”
Amsa ta bashi da “To Yaya, na gode” daga haka ta cire wayar a kunnen ta tana mai fashewa da kuka.

A nasa ɓangaren katse kiran yayi yana mai ƙara kallon sararin samaniya na tsawon daƙiƙu kafin ya koma cikin ƙawayen nasu.

Can ɓangaren Zahrah tuni ta tattaro Aminanta suka nufi kitchen don cika umarni mai martaba sarkin da ke mulkar zuciyarta. Nan kuma suka hau aiki.

*GRA, Bauchin Yakubu*

“Yanzu shi ke nan Mom, na rasa Zahrah! Na rasa ta kenan har abada?”
Ya Ishaq ya faɗa yana share ƙwalla. Kan sa Mom ta kwantar bisa cinyarta tana share masa hawayen da ke zuba, bangare guda zuciyarta na tsananta bugun yadda tilon ɗan ta ke wahaltuwa kan soyayya.
Lallashin sa ta fara tana ƙara kwantar masa da hankali.
“Is ok son, ya isa kukan haka, jarumi kamar ka bai kyautu a ce yana kuka ba idan matsala ta tunkare shi, ina so ka ƙara samun ƙarfin zuciya, In Sha Allah in dai Zahrah rabon ka ce za ka same ta duk daren daɗewa.”

Idanuwansa da suka gama yin ja ya buɗe a hankali kana yace
“Mom In babu ita ba zan rayu ba! Ban san ta ina zan fara neman ta ba, ko da numfashi na ƙarshe zai kasance to ina so ya kasance na haɗu da Zahrah, na so angel da zuciya ta da kuma gangar jiki na, ta ya za a ce na rasa ta? Nooo ba zai yiwu ba Mom, Idan ban same ta mutuwa zan yi” sai kuma ya fashe da wani irin kuka mai ban tausayi.

Tapping bayansa Mom ke yi tana faɗin
“Ya isa son, be brave man Mana, na maka alƙawarin zan taya ka neman ta only on one condition”
Kamar ba shi bane mai kuka ba nan take yayi shiru tare da miƙewa zaune yana mai zubawa Mom ɗin ido.
“Ina jin ki Mom, ai ko meye sharaɗin na yadda da shi”
Kamar za ta yi dariya ganin yadda ya sauya lokaci ɗaya, hakan yasa ta ƙuduri taimakon sa wurin dawo masa da farin cikin da ya rasa tsawon wasu shekaru dalilinsu ita da mahaifinsa tana kuma tirr da hakan.

“Kana ji ko Son?” Kai ya gyada kamar wani ƙaramin yaro
“In har kana so na taya ka neman Zahrah to dole za ka zama mai ƙarfin zuciya, wannan kukan da kake kamar wani baby boy duk za ka daina shi, be strong and pray, Allah zai ji ƙan ka ya tausaya maka sannan ya samar maka da mafita, ok?”
Kai ya gyaɗa yana murmusawa amma kallo ɗaya mai karatu zai masa ya san cewa murmushin nan ne da ake kira Yaƙe.
“Oya now, tashi ka ci wani abun, zama da tunda ba na jarumin ɗa na bane!” babu yadda ya iya haka ya miƙe gudun kada ta samfo har yanzu fa damuwar ba raguwa tayi ba.

*ABATCHA ESTATE*

Aunty Mabruka ce tare da wasu ƙawayen ta guda biyu sun sa ta tsakiya sai rarrashinta suke akan ta cire damuwar komai ta fuskanci zahirin.
Ma'eesha ta ƙara dafa kafaɗarta tana faɗin
“Haƙuri za ki yi Barrister Mabruka, kowa da yadda ƙaddararsa take zuwa masa, karɓanta hannu bibbiyu sai kiga Ubangiji ya dube ki ya musanya miki da mafi alkhairin ta. So calm down.”

Kanta kawai ta jijjiga tana mai goge ƙwallar da ta zubo mata.
“Ba za ku taɓa gane raɗaɗin da nake ji a zuciya ta ba, ba wai ban karɓi ƙaddara ta bane ko wani abun makamancin haka, ina so ku fahimci matsaya ta ne, ina da wanda nake so, amma saboda wani dalili an katange Ni da shi.”

Galala su Raudha suka yi suna kallon ta, ko yaushe rai ta fara kula samarin bare har ta ce akwai wanda take so, dey play.

“To ke Mabruka ina ce dai ko samarin dama ba ki kulawa, ƙarewarta ɗan'uwa na dake mutuwar ƙaunarki ma haka fir kika ƙi saboda wani ra'ayin ki, yanzu ga shi Allah ya baki namiji son kowa ƙin wanda ya rasa amma kina neman butulce masa.” Raudha ta faɗa tana hararar Mabruka.

“Rabu da ita Raudha, wai ma uban waye take cewa tana so ɗin, ina ce duk cikin masu son nata ma iya Captain Hisham ne ya samu arziƙin kallo, shi kuwa har yau ba ta amsa soyayyar sa ba, and see her wai akwai wanda take so, na rantse da Allah Mabruka in kika yi sake mijin nan ya kuɓuce miki ba za ki samu ya shi ba.”

Caraf Raudha tace “Wallahi ko Ni aka haɗa da guy ɗin nan da gudu zan yadda, wallahi maza irin su wuya suke Mabruka, kin sani ko cikin ƴan matan familyn ku ba za a rasa waɗanda ke son shi ba, in za ki kama abun ki ki riƙe Tom, In ba Haka ba za ki ji ana labari.”

Ba ta ce komai ba saboda ta san duk abun da suka faɗa gaskiya ne, ya za a yi su fahimci cewa mahaifiyarsa ba ta son ta bare kuma auren? Meye makomar auren bayan duk su biyun ba su son juna? Ga shi kuma ƴar'uwarta uwa ɗaya uba ɗaya ta mace a son mijin? Da a ce tana da wata dama da ba shakka za ta yi wa ƴar'uwarta wannan ƙoƙarin ko don yadda ta kasance mai iya ɓoye damuwarta. Da haka dai suka ci nasarar shawo kanta har ta saki ana hira, zuwan wasu gang ɗin friends ɗinta yasa ta sake kamar ba komai, fatan ta Allah ya sa zaɓin ya zama alkhairi.

*Zahrah's POV*

Ba su daɗe ba suka kammala haɗa girkin ko don suna da yawa ne oho, sai da ta tabbatar ta jera komai cikin basket kafin ta sanar da Hajjaty. Daga nan suka koma Bedroom ɗin Zahrah suka ci gaba da gwada ɗinkin da suka karɓo, su saka wannan su cire su saka wancan gashi duk ba wanka suka yi ba.

Rumaysa da ke gefe tana kallon su tace
“ku ci gaba da saka kayan ba wanka idan kula gumama su da tsami kwa yi bayani ai” ta idasa tana hararar su
Nainarh tace “Kut! Rumaysa mu ne za mu gumama kayan da wari? Me kike nufi?”
“Abun da kika fahimta” ta bata amsa a taƙaice.

Zahrah tace “kin dai san ba mu kai matakin gumama kaya da wari ba don mun shiga kitchen tun da duk cikin mu kin fi kowa kitse, look at you, wata tiƙeƙiya da ke” ta idasa tana aikawa Rumaysar gwalo.

A hasale Rumaysa ta miƙe ta yo kan Zahrah, ai ba shiri Zahrah ta daka tsalle ta haye Bed, Nasreen sai dariyar mugunta take
“Tab! Yau Zahrah sai ɗan buzun ki”

“Na rantse da Allah kika taɓa Ni sai na faɗawa Hajjaty, kawai daga faɗan gaskiya! Naga kema kin gasa mana maganar mun ƙyale ki.” Zahrah ta faɗa tana sauƙe ajiyar zuciya, daidai nan Hajjaty ta shigo da wayarta tana faɗin
“Ungo Yayan ku zai yi magana da ke”
Amsa tayi ta kara a kunnenta tana faɗin
“Assalamu Alaikum”

*React please, sannan a taimaki baiwar Allah a taya ta sharing.*

[1/13, 8:15 PM] Diamond Bhatool:

*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*

*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_

_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow

*PAGE* 2️⃣4️⃣

                      ﷽

Amsawa yayi yana faɗin
“Out of those girls wata ta rako ki ki kawo min abincin garden ɗina”
Daga haka ya katse kiran, miƙawa Hajjaty wayar ta yi ta diro daga saman Bed ɗin,
“My people, a Zo a min rakiya Please”

Kallon ta suke alamar they no gerrit, ganin hakan yasa ta kau da kanta gefe tace
“I'll be taking the food to him”
Nainarh tace “To who? Ba da Ni ba wallahi, naje ya kakkauɗe Ni da slap, rufa min asiri”
Dariya dukkansu suka yi kowa sai zamewa yake shi ba ya zuwa. Daga ƙarshe dai zuciya tayi tace
“Kar Allah yasa ku je, kuma wallahi In naje sai na ce duk ƙin raka Ni kuka yi” a fusace ta ja hijab ɗin ta ta bar musu ɗakin wannan na faɗin “Wallahi ba zan je ba, ai sai na bari mun haɗu da shi ko?”
Nasreen ce tayi ƙarfin halin bin bayanta suka wuce su kuma suka yi ƙirmisisi suka baje sai mita suke.
Chapter 31 · 0% Book details