← Book details Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 52

Sashe 52

Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Rasheedah kam yanzu tayi lakwas,tayi nacin Dr, yamaidata amma yaki. Tayi kuka tayi nadamar biyewa sharrin zuciya,har gida taje tanemi gafarar zee. Uwartama tayi nagama,tunda duniya ta juya musu baya. Wani wan mahaifin Rasheedah,irin me zuciyarnanne,dama tarata yakeyi dayaji abunda yafaru yabata kwanaki,bayan gama iddarta ta fito da miji,ita tunda tafitoma babu Wanda yace yana sonta, balle tafito da mijin,kwanakin daya dibarta na cika, aikuwa wan mahaifinnata yabada ita sadaka ga wani abokinsa, yana da mata daya da yaya shida. Mamanta tatubure yarta bazata gidan tsohoba,shikuma yace aure babu fashi, mahaifinta kam bece komaiba akan lamarin.batasan sanda aka dauro aureba,se zuwa kawai yayi yace Rasheedah ta shirya su tafi, dama yagama sai mata komai na amfanin gida dazata bukata. Rasheedah na kuka,itama mamanta na kuka haka ya tasa keyarta yakaita gidanta da kansa,dole Rasheedah tahakura ta zauna agidan mijinta tunda bata da zabin daya wuce haka,shima mijinnata ba lefi yanada rufin asirinsa,kuma suna zaune lafiya da matarsa. joeboy kam duniya ta juya masa baya,al'amura duk sun tsaya masa cak, dama ita duniya komai lokacine. Har gidan zee yanema, yaje kafa_kafa ya nemi gafararta akan abunda ha mata,yana kuka wiwi. Ita zee tamadade da mantashima a rayuwar ta, dayazo dinma tausayi yabata tace ita dama bata rikeshiba ta yafemasa. Godiya yayta mata sannan yatafi. Cikin zee yashiga watan haihuwa, gashi cikinnata katone,kowa yagani seya tankata. Malam kullum seya aika mata da rubutu. Ranar wata lahadi zee tatashi da nakuda, babata lokaci Dr,yadauketa zuwa asibi. Zee taci bakar wahala,dan har anamata shirin aiki ta santalo yayanta daya bayan daya har uku. Maza biyu mace daya. Zokuga murna agurin Dr,rasa inda zesa kansa yayi dan dadi da murna. Dangima kowa murna dason barka yakeyi Gidan mami aka wuce da ita, daga asibiti. Ranar suna yara sukaci sunan, malam da daddy,macen kuma sunan mami. (Ahmad,abubakar,Rahma) Amma ana kiransu da, noor,sadiq da nana. Watan zee biyu da haihuwa ta koma gidanta bayan tazaga yan'uwa da abokan arziki. Har gidan maman taly taje,amma dakyar Dr ya barta. Batayi zaton ganin taly agidanba. Amma kuma abun mamaki taly tana gidan, dafarkoma zee bata ganetaba, saboda tayi baki ta rame, wasu kuraje duk sun feso mata, ga wani ruwa medoyi datake fitarwa daga gabanta. Taly na kuka,tasanar da zee abunda joeboy yamata, kuma yafice yabarta a mummunan yanayi bayan ya kwashe takardun duk wata kadara daya mallaka mata, dakuma kudadenta. Baba megadinema ya taimaketa,yakaita asibin gwamnati saboda babu kudi, yan kudin hannun mama ta tattare aka saimata magani, amma gabanta kam sunce ya rube, ga cutar kanjamau datake da ita, haka suka dawo gida ita na kuka mama na kuka, rayuwa tayiwa taly baki,abincin dazasucima se mama tayi bara suke samu. Gidan data zauna da motarta duk joeboy yasiyar, Itama zee seda ta zubarwada taly da hawayen tausayi, kudi me tsoka tabawa mama,takuma ce zata dinga ziyartarsu akai_akai insha Allah. Taly se kalkon kyawawan yayan zee takeyi, cike da sha'awa. Tana kuka tana neman gafarar zee, Lallai ta yadda duniga, duk ABUNDA KASHUKA SHIZAKA GIRBA, duk hanyoyin databi wajen ganin zee ta wulakanta,amma gashi se gaba takeyi,ita kuma ga sakamakon abunda yasameta nan. Agurin taly zee takejin labarin saheera da fareedah suma duk sun tuba sunyi aure, bayan bariki ta juya musu baya. Bayan wasu watanni akayi taron bude sabon clinic din Dr. dake gaban gidansu zee din,ma'aikata basuyi wahakar samuwaba duba ga halin da kasarmu take ciki na wahalar aiki. A wannan kwanakinne kuma aka saka ranar, auransu shukura da zulaihat, Wanda a yanzu ta sakko suke mutunci da zee sosai. Wata rana, zee sunfita shopping ita da Dr, suka hadu da aunty sameera. Itama tayi auranta tarema da mijinta suke, aikuwa sunyi murnar ganin juna, aunty sameera dama tanemi zee,amma batasamu address dintaba seyanzu da Allah yahadasu. Bawa juna address din junansu sukayi, aikuwa suna zumunci sosai. Agurin aunty sameera, zee taji labarin aunty boss tayi gobara agidanta, suna cikin gudanar da bikinsu na shedananci wuta ta kama,bakuma asan dalilin daya haddasa gobararba, wasu sun mutu, wasu kuma sunsamu muggan raunuka ajikinsu,irinsu aunty boss, Wanda da rayuwar azabar ciwon dasukeyi gwara mutuwa. Kayan gidan kuwa da dukiyoyin ciki,duk sun kone kurmus. Dama haka rayuwatake, kayi daidai sekaga daidai. Ya Allah kasa mudace, ameen.🙏😭.

*_____________________*
*AFTER 5 YEARS*
*_____________________*

Rayuwa me cike dajin dadi da farinciki ce kawai take agudana atsakanin zee da dr. Hankalin kowa a kwance yake yanzu babu wani tashin hankali ko fargaba, se godiyar ubangiji kawai. Zee ta kara haifar mace baby girl, wadda taci sunan umma wato fateema suna kiranta da zahra,yanzu shekararta biyu aduniya.

Dr,ne kwance akan akan doguwar kujera, dayake yau Sunday befita aikiba,yakara kyau,haiba da cikar zati gamida kamala, yaransa 4 gaba daya suna jikinsa sunata tumurmusheshi. Zee na hango tana sakkowa daga kan step, taci kwalliya se baza kamshi takeyi, ta kara kyau da cika, da kamala. Yaran suna ganinta duka suka taso sukayo kanta, daga tayi daya bayan daya tadagasu tana shillasu. Dr, kawai tsayawa yayi yana kallonsu cike da farinciki. Chocolate din dake hannunta, ta babbasu,tace su shiga daki ta kunna musu game a laptop, domin tasamu damar kula megidanta yanda yakamata. Daki sukashige suna murna da gudunsu. Karasawa zee tayi kujerar da Dr, yake tana murmushi. Cikin takunta najan hankali. Zama tayi ahannun kujerar dayake, ta rankwafar da kanta tabusa masa iskar bakinta, sannan tace. "Wannan kallonfa mininah!?" Wata sassanyar ajiyar zuciya Dr, yasauke tare da lumshe ido, yana shakar daddadan kamshin dake tashi daga jikin zee. Ahankali ya tashi zaune, yana bin zee dawani fitinannen kallo, yace. "Badole in kallekiba,irin wannan kyau haka" yakarasa zancen dajanyo ta jikinsa. Murmusawa zee tayi tace, "tabbas nikam nayi dacen miji nagari, abin alfaharin kowacce mace,gwarzo kuma jajirtacce daya tamkar da dubu. A kullum ina kara godiya ga ubangiji daya azurtamun kai amatsayin miji." Karan hancinta Dr, yaja yace, "kamar yadda nima nayi dace da mace tagariba, inajin tamkar duk duniya babu Wanda yakaini dace da mace, saboda kinhada komai da kowanne namiji yake burin samu ga matarsa, gaki da kyau,nutsuwa kamala,hankali, biyayya, kunya,iya kula da miji,iya kwalliya iya girki, tsafta, tarbiyya yara, girmama iyayena, ga uwa uba hakuri." Kallonsa takeyi kamar yadda shima yake kallonta, cikin jindadin yabon dayayi mata. "Nagode sosai,kaunata da wannan yabonnaka" Kanne mata ido daya yayi yace, "na fadi komai naki amma banda Abu daya, kuma naji baki tunamunba" "ai ka fadi komai mijina, babu abunda yarage." murmushi Dr yayi yace, "banfadi zakinkiba me kamar.... Rufe masa baki zee tayi da hannunta tana dariya, tare da boye kanta acikin kirjinsa. Hannayensa duka biyu Dr, yasa yarungumeta akirjinsa cikin tsananin farinciki Mara misaltuba. Yanajin kaunarta, da sonta nakara ninkuwa aransa. A fili ya furta, "ya Allah kabarni da matata har abada,anan gidan duniya da lahira, Allah ka kauda da shedan da fitina azamanmu." "Ameen ya Allah"..........✍️.Tammat.

_*Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah. Godiya tatabbata ga ubangiji madaukakin sarki,daya bani ikon kammala wannan book dinnawa ZEE Y'AR BARIKI,kuskuren danayi aciki Allah yayafemini,abunda nakaita daidai Allah yabani ladansa. Thank you so much ZEE Y'AR BARIKI PAYMENT GROUP, for your contributions. Dahaka nake cewa ma'assalam🙏🥰.*_

```littafin zee Y'AR BARIKI nakudine,kar/ki karanta batare da ka/kin biyaba,ki/ka sauke hakkin dake kanka/ki. 200 naira kacal, ta wannan number 09066710753,ka/ki biya kisauke nauyin dake kanka/ki,kafin ki/ka karanta```

*BY*
*ZEE KUMURYA*
Chapter 52 · 0% Book details