Sashe 32
Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_________________________________________
▪️▪️▪️ *ABUJA*▪️▪️▪️

"Ummi, kinga hanif ko ya kwacemun choculate dina da daddy ya bani,ya shanyemun". "Allah ummi batasa bace, tawace nima ai daddyn yabani." Kyakkyawar dattijuwar data dafe kanta da hannuwanta duka biyu,saboda sarawar dayake mata. ta dago tana duban kyawawan yayannata (twins). Yau sam batajin dadin gari, wani irin yanayi me wuyar fassaruwa ta tsinci kanta aciki tanajin tamkar wani Abu datayi rashi arayuwarta zedawo gareta, ko kuma wani abun zesameta. Ahankali ta bude baki tace, "kyaleshi munib, zanbaka wata kaima bari naje gurin daddy na karbo maka." Tsalle munib yafarayi ummi zata karbo masa chocolate yanayiwa hanif gwalo. Shagwabe fuska hanif yayi kamar zeyi kuka yace, "ummi nibandani" hannunta takai ta janyoshi jikinta tana shafa kansa tace, "harda kai my boy dukanku zankarbo muku kaji" barin jikinta yayi,shima Yakama tsallen murna. Mikewa tayi ta fice daga hadadden bedroom dinnata, ta barsu sunata wasansu. Part din mijinta ta nufa Wanda taji shigowarsa tun dazu, zuciyarta na tsananta bugu, baya falonnasa hakan yasata nufar dakin baccinsa. Yana kwance akan gado, idanunsa a lumshe tamkar me bacci,amma tasan ba bacci yakeyiba. Kan gadon ta karasa ta zauna agefensa bayan tayi sallama cike da mamakin dawowarsa gida yau da wuri,saboda besaba dawowa a wannan lokacin ba. ahankali takai hannu ta fara shafa sumar kansa batare datace masa komaiba. Bude idonsa yayi yasauke akan kyakkyawar matar tasa dabata tsufa, janyota yayi ta fado jikinsa, cikin wata kasalalliyar murya yace, "mata ta gari, meke damunki naganki sukuku haka?" Gwauron numfashi, ummi taja tace, "bansaniba mijina amma gabadaya yau banajin dadin jikina,kaina namun ciwo sosai ga wani, bugu da zuciyata takemun." Kwantar da kanta yayi akirjinsa yana shafa bayanta, lumshe idonta tayi tana shakar kamshin mijinnata. Yanayin data tsinci kanta aciki, shima haka ya tsinci kansa yau, hakan yasa ana idar da sallar juma'a yadawo gida, ko zaman dayakeyi a masallaci yau beyiba. Shiru sukayi na wasu yan mintuna kowa da tunanin dayakeyi aransa. Dago da fuskarta yayi suna kallon juna cikin ido yace, "matar! inaji ajikina princess dita, ta kusa dawowa gareni" dammm zuciyar ummi ta buga da karfi, saboda jin ambaton yarta, mafi soyuwa agareta kuma gudan jininta da mijinta yayi. Ta bude baki zatayi magana sukaji wata kara da wani uban ihu, sun karade gidan alokaci guda. Dasauri ummi tatashi zaune cikin kidima tana fadin, "Alh. Kaji abunda nakeji kuwa?" Mikewa zaune daddy yayi yana sauketa daga jikinsa yace, "naji mana matar, kuma Kamar agidannane" "babu kama alh. Acikin gidan......ihun da'aka kara saki ne yasa ummi yin shiru bata karasa zancentaba, atare suka mike tsaye batare dajiran komaiba daddy yayi hanyar fita itama ummi Mara masa baya tayi. A part din matannasa yakejin ihunnatashi hakan yasa yanufi can da saurinsa. Hasashensa yazama gaskiya anandinne, kuma daga dakin uwargidansa. Masu aikin gidan duk sun fito sunyi curko_curko, a falo. Ga twins din ummima sun sakko kasa daga sama, sun kankakame laraba me kula dasu, cikin tsorata da firgici. Cikin karfin zuciya daddy ya shige dakin mommy, ummi na biye dashi abaya. Mommy ce take kwarara wannan uban ihun tana zagaye dakinta cikin fitar hayyaci. Dasauri daddy yayi kanta yarike ajikinsa yana kiran sunanta. Dif tadena ihun,tayi shiru, se kallonsa kawai takeyi,tana muzurai, zaunar da ita yayi agefen gadonta yana fadin. "Subhanallah,Hajiya lafiya meyafaru, meyafaru dake?" Ummi dake kallonsu cikin matukar mamaki, ta karaso garesu,domin tunda take da abokiyar zamanta tsawon shekaru kusan talatin bata taba ganinta acikin irin wannan yanayinba. Kallon daddy mommy tayi tace,Nashiga uku, Alh. Wlh sungama dani,sun cuceni duk wahalar danasha akan aikinnan,duk makudan kudin dana kashe, amma sun lalatamun, Alh. karshena yazooooo" takarashe zancen dajan maganar cikin karaji da ihu. Cikin rashin fahimta suke kallonta, daddy ne yakara mata magana akaro na uku. "Hajiya suwaye kike magana akansu, kuma wanne aikinne suka lalata miki,kiyi mana bayani kinsamu a duhu?"........
**************
Ahankali nafara bude idona,da sauri na mayar na rufe saboda nauyin dayamun,kaina kuwa jinsa nakeyi tamkar andoramun dala da gwauran dutse,saboda nauyin danaji shima yamun. Jikina kuwa jinsa nakeyi tamkar banawaba, gaba daya gabobun jikina sun saki ga wata irin kasala da gajiya danakeji tamkar anmun duka. Wani yanayi na tsinci kaina dana kasa gane kansa,gadai ciwo jikina yanamun amma zuciyata fess, nake jinta.kirjina kuwa tamkar ansaukemun wani Abu me nauyi acikinsa, ahankali cikin dauriya na kara bude idona. Dakin danake nafara karewa kallo,dakyar na samu na gano inda nake, dakin kawune. Mamakine yakamani me kuma yakawoni dakin kawu, yunkurin mikewa nayi amma nakasa. Haka nahakura naci gaba da kwanciya,jina nake a wata duniyar daban,tamkar baniba tamkar ancanjani haka nake jina. Bude kofar dakin naji anyi, mamice ta shigo dakin. Ido na kura mata Kamar zanga wani Abu daga gareta. Dasauri ta karaso gareni, "zainab,Ashe kin farka, Alhamdulillah" binta kawai nake da ido,amma nakasa magana harshena yamun nauyi bakanba,na kasa sarrafashi. Goshina ta taba, tana fadin. "Dazu naji jikinki, da zafi amma yanzu naji zafin ya ragu, dama zuwa nayi naga ko kintashi saboda baccin ya isa haka,magriba tayi. Bari nahada miki ruwan dumi kiyi wanka ko kyaji dadin jikinki, sannun kinji." Bata jira amsataba ta mike ta nufi toilet din dake dakin, ruwan wanka mami ta hada mata ta fito. Taimakamun tayi na tashi ta kaini har toilet ta zaunar dani, wankanma seda tataimakamun saboda Sam jikina babu kwari, danayi wankan kuma naji dadi sosai ajikina. Zama nayi akan gado,ita kuma mami ta fita kwasomun kayan sawa. Jingina abaya nayi ajikin gado, wata matsananciyar kewar gida da tunanin iyayenace ta cikamun zuciya. "UMMINA,DA DADDYNA DA MOMMYNA, kuna ina, inason ganinku dan Allah kuzo gareni". na furta hakan a fili hawaye na zuba daga idona.......✍️
*yasin hannuna yagaji, ma hadu gobe,kowacce ta tanadi ankonta na zuwa dinner, saboda ankonki gate fass dinki,kuma za'a cashe,arakashe.💃😛*
*By*
*zeey kumurya & real farhana*
............Mamice ta dawo dakin da sallama, ajiye kayan hannunta tayi akan gadon,zama tayi agefena ta janyoni jikinta batare datacemun komaiba,kamar ta kara zugani nakara volume din kukana, bayana kawai take shafawa,alamun rarrashi. Kusan mintuna 5 muna haka, ahankali mami ta dagoni daga jikinta tana sharemun hawayen fuskata, cikin lallami ta fara magana. "Ya isa haka kukan kuyi shiru,karya saka miki ciwon kai dama jikinki da zazzabi Kinji d'iyata" gyada mata kai nayi ina hadiye sauran kukana,ajiyar zuciya nafara saukewa,akai_akai. Mamice ta taimakamun na shirya cikin wata doguwar Riga Mara nauyi, abinci ta fita ta kawomun, ni kuma k'ok'artawa nayi kafin ta dawo,natada sallah dama da alwala ta. Har na idar da sallolina mami bata dawoba, kan gadon na koma na kwanta jikina gaba daya babu kwari. Mintuna kadan da kwanciyata mami ta dawo dakin hannunta dauke da karamin flaks din shayi da kofina, ajiyewa tayi akasa tana cewa. "Tashi kisha tea zainab,kidena wannan kwanciyar, rashin kwarin jikinnannaki harda yunwama." Babu musu na mike na sakko daga kan gadon,domin nikaina nasan inajin yunwa dan rabona da abinci tun safe danaci kosan da aka yiwa baki, shima kadannaci danya bani sha'awanema. Tea me kauri mami ta hadamun nasha kuwa sosai, sannan ta bani maganin ciwon kai dana jiki. Hanani kwanciya tayi tace na bari ayi sallar isha'i sena kwanta gaba daya. Ai kuwa ana kira naje na kuskure bakina, nayi sallar na koma na kwanta, mintuna kadan bacci yadaukeni.........
Seda akayi sallar isha'i sannan yadawo gida, amatukar gajiye yake, gaisawa yayi da jama'ar gidan abokanan wasa nata tsokanarsa. Murmushi kawai yake musu,amma bakin mayarda martani.Yana shiga dakinsa yafara rage kayan jikinsa,toilet ya nufa domin watsa ruwa ajikinsa. Bayan yafitone ya dakko wayarsa da nufin yakira shukura ta kawo masa abinci, danyau beci wani abincin kirkiba,kiran malam ne yashigo wayartasa. Dasauri ya daga tare dayin sallama. Amsa masa sallamar malam yayi tare da fadin, "Mahmud kazo dakina yanzu idan kagama abunda kakeyi." "Toh Abba,ganinan" katse wayar yayi yazura jallabiyarsa fara kal ajikinsa, saboda kayan sawarsa gaba daya shukura ta hade masa su, acikin jaka, sedan abunda ba'arasaba ta bari. Seda yafesa turare sannan ya nufi kiran malam.
Wani rubutu,malam ya bashi ajarka yace yakaiwa mami,yanzu mantawa yayi tundazu bebayar ankai mataba,hidimar jama'a tasha masa kai seyanzu ya tuna,kuma sakon na gaggawane. Babu yanda ya iya,haka ya karba,amma shi kofitowa daga dakinsa beshirya yibama se gobe idan me duka yakaimu,saboda gajiyar data addabesa ga yunwa dake nukurkusarsa. Cikin abunda befi 15 minutes ya iso gidan mami, shimadai gidan balefi da jama'a kamar gidansu,gashi shikuma befiyason shiga taroba. Hakadai ya hakura ya shiga ciki, yana tafe yana gaisawa da mutane. Abokan wasa na tsokanarsa,kamardai na gida. Mami tana dakinta ita da wasu baki yayi sallama daga bakin kofa, amsa masa sukayi mami ta bashi izinin shiga. Gaisawa sukayi da matan dake dakin sannan suka fice suka basu guri. Ajiye rubutun hannunsa yayi akan loka, zama yayi agefen mami ya kwantar da kansa akan kafadarta, shagwabe fuska yayi kamar yaro yace, "mamina lefin me kuma nayi dabaza'akulaniba.?" harararsa mami tayi tace, "seyanzu kaga damar zuwarmun,kenan aiko kwalliyar angonci kazo ka nunamun kokuma kazo ka duba lafiyar matartaka." Murmushi yayi yace, "ayi hakuri mami na tuba bazan karaba" ya karasa zancen yana hade hannunsa guri guda alamar roko ya wani marairaice. Shafa sumar kansa mami tayi tana murmushi tace, "Kasan ai bazan iya dogon fushi dakai bane shiyasa kakemun abunda kaso, ya taron nagama dukka fada." Lumshe idonsa yayi yace, "mami sha'anin taro akwai wahala, gashi yau da ciwon kai na wuni, bama najin dadin jikina gaba daya." "Ayya sannu my son,dama sha'anin taro yagaji haka, se daga baya zaka warware." Mami ta karasa zancen tana mikewa ta dakko rubutun daya kawo mata, tace, "dama yanzu nake shirin kiran malam ince naji shiru sekuma gashi kakawomun" mikewa Dr,yayi yana fadin mami nizan koma saboda ina bukatar kwanciya, ina amaryar gidanne?" "Amarya tana dakin kawu batajin dadine" arazane yace, "subhanallah mekedamunta mami amma shine bakisanarmunba." "Ehh,bawani ciwo bane ciwon Kaine kawai yatakurata shima nasan hayaniyace" ( saboda duk abunda yake faruwa akan zee,Mahmud be saniba,ko labarinta mami catai kar'afada masa sebayan auransu. Yasandai kawai anboye mata zancen auransu shima besan dalilin hakanba.) Ajiyar zuciya ya sauke yana fadin, "bari na dubata mami tana ina?" "Tana sama dakin Abba,nabata magani tasha nasan kilama bacci ya dauketa.amma kaje kaga jikinnata." Kai kawai yadagawa mami ya fice daga dakin.