← Book details Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 52

Sashe 33

Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tunda yatura kofar dakin yashiga kamshin jikinta daya gauraye dakin gaba daya yadaki hancinsa, karasawa yayi gaban gadon ya tsaya akanta yana kare mata kallo. Bacci takeyi amma kana gani Kasan batajin dadinsa,saboda yanda ta takure jikinta guri guda. Hawa gadon yayi ya zauna daf da ita, haryana gogar jikinta. Kyakkyawar fuskarta ya kurawa ido, ahankali ya matso da fuskarsa daf da tata, kamshinta gaba daya yacikasa. Farincikin daya tsinci kansa a wannan lokacin baze misaltuba, godiya kawai yakewa ubangiji daya azurtashi dasamun wacce yake matukar so da kauna. Tabbas soyayya gaskiyace, seyanzu yakara tabbawartawa dayake kan shaukinta,sabanin da dayake ganinta kamar shirme. Karan hancinsa yadora akan nata yana gogawa,lumshe idonsa yayi yana shakar kamshinta,dayake kokarin hargitsashi.ahankali ya dora labbansa akannata, yanajin saukar numgashinta akan fuskarsa,wani yammm yaji ajikinsa tsigar jikinsa ta fara mikewa,bugun zuciyarsane ya sauya ta fara bugawa da sauri_sauri,ahankali yafara lasar lips dinta da harshensa. mutsu_mutsu zee tafarayi jin iskan numfashi ta mata karanci.Ahankali yajanye fuskarsa daga kantata,yana sauke numfashi akai_akai. Wani dogon numfashi taja tare dayin juyi taci gaba da baccinta,murmushi yayi ganin yadda taturo dankaramin bakinta abun sha'awa. Hannunsa yakai yana shafa gashin kanta,dayasha gyara. kirjinta ya kurawa ido,saboda babu bra ajikinta, ahankali yakai hannu yana shafa tudun kirjinnata.Yadau tsawon mintuna ahaka sannan yadauke hannunsa daga jikinta. gyara mata kwanciya yayi tare daja mata bargo ya lullubeta. Jiyake tamkar karya tafi ya barta,wani shaukin sonta ne da sha'awarta yake fuzgarsa.badan yasoba haka yahakuraYa mike ya fice,saboda idan yacigaba da zama yana ganinta ahaka komai ze iya faruwa, dan tsaf setafka abun kunya🤔.............

Washegari da asuba mami tatasheni,alhamdulillah naji saukin jikina sosai duk ciwon danakeji agabobin jikina da ciwon kaina duk babu. Amma fa nasha mafarkai kala_kala abaccin danayi,masu kan gado da marasa kan gado. Ga tunanin gida daya yawaita acikin zuciyata, har abun yabani mamaki saboda ada Sam banayi. Bayan nayi sallah,nahau gyaran dakin kawu duk da babu wani datti amma haka na shareshi na gyara shi Tass. Kasa nasauka muka gaisa da baki
kowa se sannu da jiki yakemun,abun ya matukar dauremun kai da bani mamaki, saboda ni bansan nayi wani babban ciwoba,kwakwalwatama ta kulle nakasa tuno abunda yafaru dani. Amsawa kawai nakeyi,dakin mami nashiga nanma da baki suma gaishesu nayi nanemi guri na zauna,domin nan yafi saukin mutane akan falo da dakina. Gabadaya nazama wata silent,duniyar gabadaya ta juyamun komai cikin sanyin jiki nake yinsa. Seda gari yayi haske, mutane duk antafi gun aikin girki saboda yaune yini yaune mami take taronta,sannan muka samu kebewa da mami. Bayan tamun yajiki, tagyara zama tacemun, "zainab kisaurareni dakyau,kuma kijini da kunnan basira zanfada miki Abu me mahimmanci" gyada mata kai nayi dukda bugun da zuciyata takemun tun kafin ta sanarmun. "Ajiya juma'a aka daura aurenki da Mahmud, Wanda shine dalilin dayasakama Mahmud yakawoki gidannan." Ai numgashinane yadauke na wucen gadi, saboda abunda mami tace, tundaga sanda ta ambata andaura aurena da Mahmud bankara fuskantar metake cewaba, wani yanayi na tsinci kaina aciki me wuyar fassaruwa,tabani da mami tayi shiya dawo dani daga duniyar tunanin dana tafi, cigaba da magana mami tayi, "inafatan zainab bazaki bani kunyaba,zaki zauna lafiya da mijink....."amma mami ina ita dayar matartasa daze aura?" Nakatse mami da wannan tambayar. Murmushi mami tayi tace, "tananan tare aka aura masa Ku" "amma mami y..... "babu da lokacin magana yanzu kibari daga baya matattauna,tunda ke bayau za'akaiki gidankiba senan da sati biyu, yanzu kawai kisaki jikinki akarasa bikinnan." shiru nayi saboda harga Allah bansan mezanceba,kaina ya kulle. Mikewa mami tayi ta fice daga dakin bata kara cemun komaiba akan maganar auren,se wani rubutu databani tace nasha. mikewa tsaye nayi nafara zagaye dakin ina zancen zuci. Tabbas biri yayi kama da mutum,duk abubuwan da mami takemun a yan kwanakinnan irin Wanda akewa amarene,haka kawai mami bazata kira megyaran jikiba tayimunba dankawai zatayi bikin d'a,banda gyaran jiki akwai abubuwa dayawa makamantan haka. Dafa kaina nayi afili na furta, "meyasa tun abaya kwakwalwata ta kulle, meyasa nakasa gane nufin mami akaina. Kenan ta aurawa danta ni, tabbas mami takai mace me halarci da karamci. Amatsayina na wacca tayi karuwanci amma bata kyamaceniba ta hadani aure da jininta" Zama nayi a bakin hado, cikin mikawa ubangiji komai da kuma karbar duk kaddarar data sameni. Abunda yafi damuna guda dayane, nayanda zanyi zaman aure da Wanda bayasona,domin nasan umarnin mami yabi kawai ya aureni,sannan kuma da kishiya. Anya kuwa zan iya zamannan,? Niyanzu burina dayane a duniya inkoma ga ahalina ingansu,inga halindasuke ciki, amma kwatsam Sega mami tazomun da zancen tamun aure, gashi bazan iya bijirewa umarnintaba, saboda bata cancanci haka daga gareniba, ahalin yanzu bani da kamarta, ta sanadiyyarta rayuwata ta gyaru. Wani gwauron numfashi naja. Cikin rashin sanin mafita,amma na kudircewa raina insha Allahu bazanbawa mami kunyaba. Kwanciya nayi zuciyata cike da tunanika iri_iri, rayuwata ta baya kawai nake tunawa,ta bariki danayi amma cikin ikon Allah waiyau gani nice amatsayin matar aure.........

Nadade a kwance ina tunanika,ganin nayi tunanin baze fishsheniba,dole na hakura namikawa Allah komai. tashi nayi nadauro alwala natada sallah, domin itace kawai mafitata ahalin yanzu. Mami da kanta ta kawomun break naci, nasha ruwan rubutun data bani. sani tayi,nayi wanka. Wani hadadden Dubai less, ta bani nasaka. Maroon colour ne da adon milk,yasha kwalliyar duwasu. Banyi wata kwalliya meyawaba,powder kawai nasaka se lipstick. Wata kawar mamice datakeyin make up,takafamun dauri me kyau, yari masu matukar kyau mami tabani nasaka. Nikaina dana kalli kaina a madubi seda nace, *masha Allah* mayafi nayafa milk colour takalmin kafatama milk dinne. Turaruka masu sanyi da dadin kamshin na fesa. Duk Wanda yaganni yasan ni amaryace. Falo mami tasani nafito wai za'ayi pictures tunda jiya ba'ayi na daurin aureba. Nidai a kunyace na fito ina sunkuyar dakai kasa. Nanfa falon yakaure da gudar mata,ana ga amarya ga amarya. Nidai wata kunyace ta kara lallabani. Hotuna muka dinga dauka kala_kala,kowa seyace seyayi photo dani nidai harseda nagajima yasin.

Yau gidan acike yake damkam da mutane, fiye da jiya,babu masaka tsinke. Nidai kawai dauriya nake,amma nikadai nasan halin danake ciki,sonake mu kebe da mami, in mata zancen inason zuwa gida amma bamu kebeba saboda jama'a. Nidai baxance ina farinciki ko bakin ciki da wannan auren danajishi lokaci dayaba,kawaidai ganin abunnake tamkar mafarki nakeyi zanfarka daga baya. Wajen karfe uku,nasakeyin wanka bisa umarnin mami, yanzu kam bani nashirya kainaba shiryani akayi,cikin wata atamfa. Dinkin Riga da zanice itama, zaninma flan. Kuma da irin atamfar akamun lullubi kamar mayafi. Yanzunmadai ba'amun kwalliyaba amma nayi matukar kyau. Rumfa akasaka a farfajiyar gidan mami aka Jere kujeru, malama ta musamman mami takira zatayi wa'azi akan aure. Kowa ya hallara jama'a duk sunnufi can, itakanta malamar ta karaso nikadai ake jira. Seda na tsaya nayi sallar la'asar,domin kafin agama shiryani har an idar. Mami dakanta ta kama hannuna har gurin taron. Aikuwa ido yamana caa,kafata harfara hardewa tayi saboda ido. Har gurin da'aka tanada domin zamana mami ta kaini ta zaunar dani. Bude taro malama tayi da addu'a tayi Bismillah ta fara jawabi akan aure damenene shikansa auranma. Jawabi malama tayi na kusan awa 2,jawabin daya ratsa mutane dadama, harda ni kaina. Wa'azinta ya karyarmun da zuciya. Musamman yanda take fadar ladan da mace take samu agidan auranta, amma da na gurbata rayuwata da harkar banza,wadda banda tarin zunubi da asara babu abunda zantsinta acikinta,amma dayake Allah gafururrurahimune,segashi ya datardani tun kafin lokaci ya kuremun. Wasu zafafan hawayene naji sunshiga kawaranyomun daidai lokacin tsoffi sukazo sunamun feshin turare wai kamu. Mayafin atamfar naja narufe fuskata,naci gaba da kukana kasa_kasa. Jinayi kawai anrungumeni daga mayafin nayi naga kowaye,shukurace da sauri nabude fuskata duka ina murmushi nace, "yaushe kikazo?" Murmushin tamun itama tasa hannu tana sharemun hawayen fuskata tace, "tundazu nazo aunty zainab, zama nayi naji wa'azin auren nima,kinga hajiya kaka can da itama mukazo." Zanyi magana kenan cousin's din shukura suka karaso gurinmu, gaisawa mukayi sunamun Allah yasanya alkhairi. Hotona suka fara daukata awayarsu kafin daga baya suka shigo aka mana tare,nanfa mutane suka fara matsowa ana daukarmu, mama dijee ce dataga abun bana kare bane,tajanyeni cikin gida saboda za'ashiryani zuwa wajen dinner. Abinci mama dijee,takawomun inci karnayi ta zama da yunwa, abincin kadan na tsakura naci na barshi. Kwanciya nayi akan gado nadan mike kafin ayi sallar magriba. Danna matukar gajiya bakadanba. Su shukurane da wasu yanmata suka shigo dakin da nake, kayayyakinsu suka fara sauya ankonsu na dinner, wasu kuma suka baje kayan make up, suka fara kwalliya. Nikam jinayi Dama mami tace,infasa zuwa gurin dinner, dan ahalin yanzu kwanciya kawai nake bukata. Kiran sallar magribane yatadani alwala na dauro natada sallah. Ina cikin yin sallarne mami ta shigo tana kwadamun kira, zama tayi ganin ina sallah. Ina idarwa kuwa tace nataso maza, zamuje gurin kwalliya saboda time din dinner yakusa. Ko hijab din jikina bancireba muka tafi nida shukura,direban mamine zekaimu. Seda mukaje naga shukura tana fito da ledodi kayansawarmune aciki da duk wani Abu dazamu bukata,nifa wlh gaba daya kaina ya kunce, komai sabo nake ganinsa, nazama tamkar ba wayayyiyaba,tamkar banice *ZEE Y'AR BARIKI* ba,me budadden ido. Gurin kwalliyar kam yahadu babu karya, ga mutanenan yan kwalliya,danma masu kwalliyar suna dayawa. Wata amarya da'ake yiwa aka karasawa sannan aka faramun. Dama already mami tayi mana bucking. Itama shukura watace ta kama yimata.
Chapter 33 · 0% Book details