Sashe 50
Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Hankalinsa a matukar tashe yakarasa gidan mami,gudu yake zubawa bana wasaba acikin motarsa,iko da kuma kariyar Allah ne kawai yakaishi lafiya. Mommy na kitchen taga mutum yafado mata tamkar ancilloshi, ko sallama babu. Zubamasa ido tayi kawai tana kallon ikon Allah,tsantsar tashin hankalin data hango atattare dashi shiya tabbatar mata ba lafiyaba. "Lafiya kuwa Mahmud,meyafaru?" Mami ta jehomasa tambayar cikin dan razani. Bebata amsaba,se tsugunnawa dayayi akan gwiwoyinsa, yakama kafar mami, cikin muryar tashin hankali yace, mami dan girman Allah,badanniba mami kifadamun inda zainab take,wlh ina azabtuwa da rashinta kuma ayau Allah yabayyana gaskiya,zainab bata da masaniya akan abunda yafaru,sharri ne kawai da makirci aka kullamata." Wani gwauron numfashi mami taja, tana hamdala ga ubangiji aranta da gaskiyar ta bayyana,,amma a fili batace komai,se dafa kafadunsa da tayi ta masa alama daya tashi daga tsugunnon dayayi. Girgiza mata kai yayi idonsa yaciko da kwalla,sakin kafadartasa tayi tayi gaba zuwa falo,cike da tsananin tausayinsa. Kana ganinshi kasan baya cikin kwanciyar hankali,duk yabi yarame. Shima Dr,mikewa yayi yabiyo bayan mami. "Ka kwantar da hankalinka Mahmud,da izinin Allah yauzakaga zainab, kazauna muyi magana" cewar mami tana zama akan kujera. Shima zaman yayi, a gefen mami yana sauke numfashi. gyara zama mami tayi ta bawa Dr,labarin zee atakaice. Kafe mami yayi da ido tamkar itace zee din,kwalla na diga daga idonsa. "Mami dama haka zainab tayi rayuwa amma bansaniba,shiyasa lokuta dadama nake mamakinta yanda lokaci guda ta sauya daga me tsiwa zuwa shiru_shiru, ashe da dinma bayin kanta bane. Kuma dama alh,dan gaske shine mahaifinta amma koda wasa bata taba fadamunba,datuni banje har abujan na nemotaba,tunda" "yanzudai komai yawuce Mahmud,seka shirya yanzu kayi haramar zuwa garin Abuja nasan insha Allahu tanacan.,kuma gidan mahaifinta baze boyuba,tunda babban mutum ne." Mikewa Dr,yayi yana fadin,"ashirye nake mami, babu wani bata lokaci,yanzu zan tafi." Addu'a mami tashiga jero masa na fatan dacewa, da kuma kariya da tsarewar Allah atafiyar,amsamata yayi ya fice. Yabar mami da tagumi, dukda Dr, bewani yimata bayaniba akan yanda gaskiya ta bayyana, amma tasan baze wuce makircin su Rasheedah bane,dantasan halin mahaifiyarta farin sani..........
*_________*
*ABUJA*
*_________*
Kwanakinnan nayisune cikin farin ciki,saboda kulawa da kauna da tarairayar da iyaye da yan'uwa suke nunamun. Sosai zaman Abuja ya karbeni, jikina yayi bul_bul fatata banda sheki da kyalli babu abunda takeyi. Ammafa duk abunda nakeyi tunanin Dr,na manne azuciyata,kewarsa tacikamun ruhina,dauriya kawai nakeyi ina al'amurana. Yau tunda natashi banajin dadin jikina,tun ina daurewa har ummi ta gane. data tambayi meke damuna nace mata ciwon Kaine,maganin ciwon kai ta bani nasha tace na kwanta,na huta. Dama ciwonkanma nadamuna, inashan maganin se bacci ya kwasheni. Tun wajen 11 na kwanta amma seda 2 ta wuce na farka, shima yunwace ta farkar dani. Dasauri na tashi nashiga toilet seda nafara watsa ruwa na dauro alwala nafito nayi sallah,sannan na fita zuwa kitchen. Hadadden kuskus dayaji kayan hadi naga andafa,amma ni Sam senaji be burgeniba,dubawa nayi kozansamu wani abunda zanci amma komai na kitchen din bemunba. Cikin fara galabaita da yunwa naje nasanar da ummi, tace to menakeson ci,nace mata taliya da manja da yaji. Dakanta ta shiga kitchen din ta dafomun, ta kawomun hardaki...
Sallar azahar ce,kawai ta tsaidashi ahanya, sekuma maida dayasha a wani gidan mai.kafin la'asar yashigo garin abuja, gudu yake shararawa amma gani yake tamkar mortar bata gudu, wata doguwar ajiyar zuciya yasauke sanda yashigo garin abuja, yauko ruwa besawa cikinsaba,balle abinci. Faka motarsa yayi atasha yafara tambayar gidan alh dangaske, mutanen farko daya tambaya irin yan zaman bakin tasharnanne, dasauri wani matashi yace yasan gidan ze rakashi, godiya ya masa yashigo motar suka tafi yana nuna masa hanyar har gidan. Hannu yazira a aljihunsa yazaro 2k yabawa matashin,godiya matashin yahauyimasa. Shidai kawai Dr,tsayawa yayi yana karewa gidansu kallo, fadar tsaruwa da haduwar gidan bata lokaci agurinsa,amma gidan yakai karshe a haduwa. Fitowa yayi daga motar yataka har bakin wangalelen gate din gidan yafara knocking cikin sauri,kamar yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri. Megadine yataso ya bude masa,bayan sungaisa yake tambayarsa daga ina. Atakaice Dr,yace masa shi bakone daga kano, yakuma fada masa cikakken sunansa. Dayake malam sananne, se megadin yabawa Dr, izinin shigowa tare da hadashi da wani ma'aikacin gidan me suna idi, amintaccen yaron daddyne,dayake kular masa da harkar cikin gida.
Ummi tana falo azaune ita da twins da zee takoro matasu, daya daga cikinsu masu aikintace tashigo ta sanar mata tana da bako a waje. "wanene?" Ummi ta tambaya. "Banganshiba amma dai idi yacemun sunansa Mahmud Abubakar gezawa" dasauri ummi ta mike tsaye tana fadin, "zubaida kinji sunan kuwa daidai?" "Eh wlh hajiya haka yacemun" "ohk,maza yisauri kijekicewa idi,akaisa babban falon baki,kukuma kuhada masa abinci dasu drinks ganinan zuwa" amsawa zubaida tayi ta mike tafice. Hamdala ummi, takeyi domin tagane surukintane yazo, tana addu'ar Allah yasa yazo akan komawar zee dakintane. Amma bazata fadawa zee ba sedai ta mata surprise daga ita har daddy. Tsadadden mayafinta dake tashin sassanyen kamshi ta dakko ta yafa. Twins naganin ta haka suka rukunkumeta waise sunbita, dole ta kama hannuwansu suka tafi tare,dan'idan tace bazata dasuba sesu cika gidan da ihu. Iso idi yaje yay wa Dr, zuwa cikin gidan,tare da masa jagora har part din bakin.Dr,yana zaune a falon bakin yana karewa falon kallo,yana ganin irin dukiyar da'akakashewa falon,cikin mintuna kalilan ma'aikatan gidan suka cika masa kan dinning din falon,da kayan ciye_ciye. Shikam hankalinsa duk ba'akan wannan yakeba,yanaga sanin halin da matarsa take ciki. Jinginar da kansa yayi ajikin kujera idonsa a lumshe. Sallamar ummi cikin sassanyar muryata yasashi bude idonsa da sauri, tare da amsa mata sallamar,saboda jin muryar tamkar zee dinsa,saidai tafi ta zee manyance kawai. Koba'afada masaba yasan itace mahaifiyar zee saboda tsananin kamar dasukeyi. Karasowa ciki ummi tayi, tana satar kallonsa,ita kanta ta yaba kyawu da cikar zati,da Allah yayiwa surukinnata. zamowa Dr,yayi daga kan kujerar yahau gaishe da ummi,cikin kulawa da sakin fuska ta amsa masa,tana tambayarsa,iyali da mutanen gida. Shiru ummi tayi bayan sungama gaisawar, se twins dasuka karasa gurin Dr,sunata masa surutu, bayan sun gaishesa.harsuna fada masa sabuwar auntynsu tadawo. Wata sassanyar ajiyar zuciya Dr,yasauke domin yasan zee yaran suke nufi. Ummi dai mikewa tayi tabashi guri, yaci abinci kafin taturo masa zee, tayi_tayi su hanif su taho amma sukaki,waisu agurin new uncle dinsu me kyau zasu zauna. Kyalesu tayi, tafice abunta. Idi ne yashigo yasanar da Dr, idan yagama cin abincin ga dakinan akwai toilet yashiga ya watsa ruwa. Hankalin Dr, duk bayakan wannan shidai burinsa yaga matarsa. Dakin yashiga bayan yabar twince da wayarsa sunata game, yaran sunmasa kyau, kuma sun matukar burgesa,gasu da tarbiyya. Toilet din dakin yashiga ya watsa ruwa ,tare da dauro alwala. Kayan jikinsa ya mayar, man dayagani akan mudubun dakin yadan mutstsika sannan,yashimfida dadduma yatada sallar la'asar.....