← Book details Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 52

Sashe 27

Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shukura data matsu taji karshen labarin zee har ta dawo falo suna dan taba hira jefi_jefi da zee. Fitowarsu Dr ta katse musu hirarsu. "Laa yayana yaushe kashigo.?" Shukura ta tambayesa tana murmushi. "Yanzu nashigo kanwata yanzuma gida zankoma dawowata kenan daga office. "Ayya yaya sannu,kagaida gida. Kagaishemun da hajiya kaka kace nayi missing dinta. Kallon zee yayi datunda yashigo falon tayi kasa da idanunta, saboda indai ta ganshi zuciyarta setaita bugawa,ga kuma bala'in kunyarsa da tsoronsa datakeji. Ita kanta mamakin kanta takeyi dama zataji irin haka akan wani mutum,jinta takeyi tamkar ba itaba. Allah yakiyaye din da mami da shukura suke masa ya katse mata tunani. Dagowa da kanta tayi cikin sa'a suka hada ido saboda yanda ya kura mata ido. Kai wannan mutumin akwai kallo,ta fadi haka aranta. Harara ya wullamata yace, "ke baki iya a adawo lafiya bane. "Da sauri mami ta tari numfashinsa tace, "kaga malam wuce kayi tafiyarka daga zuwanka bazaka takuramun yarinyaba. Waro kyawawan idanuwansa yayi waje yace, "mami yau saboda kinyi sabuwar ya kike korata.? Shikenan na tafi sekinnemeni zaki kara ganina agidanki. "Eh din naji, yanzu bana ta kai. Murmushi kawai yayi ya fice daga falon. Dariya shukura take musu,cikin dariyar tace "yau dai munji kan da da uwa. "Ke kuma ina ruwanki, ai zamu shiryane." Murmushi zee tayi domin sun matukar burgeta,rayuwarsu gwanin sha'awa cikin wasa da dariya. Dama itama haka take danata a familyn, amma kaddara ta canza mata rayuwa. Kwallace ta ciko cikin idonta da sauri tayi kokarin mayar da ita,dan karsu mami sugani tasan yanzu sesu daga hankalinsu.

"Aunty zainab kikarasa mana labarinnaki kar magriba tayi" murmushin takaici zee tayi ta dubi shukura tace, "labarin da babu komai acikinsa se faduwa da asara, da tarin takaici. "Haba aunty zainab kidena cewa haka kinsan kowanne bawa da tasa kalar kaddarar. "Hakane sister bari na karasa muku." Mami kawai kallonta takeyi cike da tausayawa,lokaci daya taji yarinyar ta shiga ranta matuka,dama ita macece meson yaya kodan ita bata haihuwa bane shiyasa.

Gyara zama zee tayi ta cigaba da basu labarinta. "Tunda muka shiga gidan aunty boss muke cin karo da mata kala_kala wasu gasunan sunyi shiga tsirara_tsirara,wasu suna saida abubuwa a gidan,wasu kuma suna aikace aikace. Kallonsu kawai nakeyi kamar yadda suma suke kallona, aunty sameera tana gaisawa da wadanda ta sani. Wani part muka nufa,Wanda yafi kowanne part na gidan kyau da tsaruwa. Seda mukayi knocking sannan aka bamu izinin shiga. Wata katuwar matace hakimce akan kujera tana latsa wayarta, tana da tsayi da kiba. Gashi taci farin bleaching har daukar ido takeyi. Tana ganinmu naga ta ajiye wayar tataso da sauri tana kuramun ido. Kawai gani nayi ta rungumeni ajikinta, "welcome fyn baby" murmushi na mata nace, "welcome ma" kallon aunty sameera tayi tace, "zauna mana sameera sannunku da zuwa. Kai gaskiya sameera kin matukar burgeni yau, wannan irin kyakkyawar yarinya haka, wanke hannu ka taba ina kika samota.?" Ta fadi haka tana zaunar dani akan kujera. Gabadaya ta rude da ganina, aunty sameera dai murmushi kawai take mata. "Aunty ai wannan itace yarinyar dana miki magana jiya akanta." "Wow sameera amma fa naji dadi don wannan bakaramin arziki zanyi da itaba, yarinya ga kyau ga diri kamar ita tayi kanta." Nidai kawai binta nake kallo ina jinjina halittar da ubangiji ya mata, na tsayi da kiba, tamkar mutanen farko tabbas wannan taci sunanta aunty boss.......

*BY*
*zeey kumurya & real farhana*

..........murmushi aunty samira ta karayi tace, "auntynmu kenan,maganin kukanmu,gatanandai nakawo miki ita, seki dorata akan layi ni zan tafi saboda ina sauri zanje na karasa shirina na tafiya. "A'a sameera kizauna kodan ruwa akawo miku mana, ganin yarinyar gaba daya ya rudar dani nama manta, bankawo mukuba." "Haba aunty, gidan sekace bakona bakomai wlh nizan wuce," aunty sameera ta fadi haka tana mikewa. Se alokacin naji wani tashin hankali da aunty sameera zata tafi ta barni, adan zaman danayi da ita na matukar sabawa da ita, jiki a sabule na tashi domin yimata rakiya a bakin get din gidan muka tsaya munayin sallama. Hannuna aunty sameera ta kama tace, "zee banso tafiya na barki a gidannanba, sedan kin dage kinaso. Amma fa kisani zaman gidannan ba wani dadi gareshiba, kinga wannan aunty boss din, shegen son kudi gareta baruwanta koda mutum ze cutu itadai kawai ta samu kudi. Duk Wanda yazo yace yana son mu'amala dake indai ze sakar mata kudi,bashi ke zatayi dan haka kisan irin mazan dazakiyi mu'amala dasu,sannan karki yarda kiyi less domin yanada illa babba. Nidai duk bayanin aunty sameera betadamun hankaliba kokadan, nidai burina kawai inzama karuwa kuma shahararriyar yar bariki, rabuwa da aunty sameera ne kawai damuwata a lokacin. Haka mukayi sallama da aunty sameera ina kuka tana kuka, kayan sawata ta fitomun dashi daga bayan motar ta na kinkima na koma cikin gidan.

Tunda na dawo gidan aunty boss da zama take nan_nan dani, tamkar kwai haka ta maidani nima nasaki jiki da ita sosai. Salo_salo na karuwanci da duk wata hanya da zanbi indauki hankalin maza aunty boss bawanda bata koyamunba. Kananun kaya ta bani bingil_bingil tace su zandinga sakawa. Kalaman batsa kuwa na rashin kunya da badala duk cikin kwanaki kadan suka zauna abakina. Ga Rashin kunya da rashin tsoro. Wanda yasanni abaya idan akacemasa nice zainab din dayasani, wlh baze yardaba,nazama tifikal cikakkiyar yar bariki abunda ya ragemun kawai na fara Hulda da maza. Haka aunty boss tayita yabona tana kozantani,ni kuma ina jin dadi. Duk ranar lahadi shine ranar baje kolin gidan aunty boss, ranar maza manyan alhazawa suke zuwa su zabi mata son ransu, hakama manyan hamshakan yan less suma suke zuwa su dauki nasu rabon. Ranar tunsafe za'a fara kide_kide ana gasar rawa. Wannanene karo na biyu da'akayi bikin agabana. Kuma yaune nima zanfara fita domin adama dani. Kaya na alfarma aunty boss ta bani nasaka takanas ta kirawo me kwalliya akan t cancaramun, ga uban turaruka data bani na saka. Kai ranar naga Abu yanda Kasan sarauyiua haka na koma. Tare muka fito gurin bikin da aunty boss, aikuwa kallo yadawo kaina wadanda basu sannibama agidan yau sunganni. Haka muka zauna akan kujera anata faman biki, abun ya matukar burgeni yanda suke rawar tuburan ta tantiran yan iska, anata juya duwaiwaka da nonuwa, senaji dama nima na iya rawar dana shiga nayi. Haka akacigaba da shagali agidan har zuwa dare. Lokacinne manya_manyan motoci suka fara fakawa a kofar gidan domin daukar mata. Duk Wanda yashigo ya ganni seyacewa aunty boss ze daukeni, se'anyi ciniki sekuma naga ba'abashiba wai basu daidaitaba ni wlh abunma dariya ya fara bani,sekace wata kayan siyarwa nifa na matsu inganni na fara harkarnan. Wani matashi ne yazo gurin aunty boss, tunda yashigo yaketa faman kallona nikuma se fari nakeyi ina zuba rangwada, aunty boss sekirari take zuba masa. Intakaice muku zance matashinnan wai shi outhman shine Wanda aunty boss tabawani. Outhman cikakken dan duniyane gashi yana da bala'in kudi, kowacce mace a gidan aunty boss burinta idan outhman yazo ya dauketa saboda bacin kudin dayake biyan aunty boss idan kika gama abunda zakuyi seya kara maka. Haka nabi outhman acikin wata rantatstsiyar motarsa. Wani
Hadadden hotel outhman ya kaini, Wanda shine zuwana hotel na farko a duniya, ranar dabazan taba mantawa da itaba kenan arayuwata,saboda aranar outhman yayi nasarar rabani da martabata da mutuncina. Wato budurcina. Duk da dasanina kuma da yardata,amma seda naji badadi a zuciyata. Gashi naci bakar azaba tunda usman ba sauki. Tundaga ranar yazamana cewa outhman kusan kullum seyazo ya daukeni, tun ina jin zafi da radadi harnazo na saba na ware tamkar kowa nima nazama yar hannu. Dafarko Inajin dadin zama da aunty boss amma saga baya se al'amari ya zauya, domin kuwa son kanta yayi yawa, kowa yazo yace yanason mu'amala dani setace inje, nikuma gaskiya banason tarkacen kowa, da outhman kawai nasaba, kuma Inajin dadinsa sosai. Hakan yasa muka fara batawa da aunty boss, tace indai ina gidanta dolene in kula duk Wanda taso, ita kasuwanci take damu dan haka duk Wanda yazo dole ta bada mu. Nikuma gaskiya Inajin tsoro, musamman gargadin da aunty sameera. tamun akan karna kula kowanne namiji, saboda gudun karna kwashi ciwon kanjamau. Wani alhaji, shine mutum biyu danayi mu'amala dashi bisa takurawar aunty boss. Tunda ina kula maza 1,2 harna ware nafara mu'amala da maza da yawa. Cikin kankanin lokaci na zama cikakkiyar yar bariki, fiyema da yadda nake zato. Sunana ya fita a garin Kaduna *zee y'ar bariki* harma da wasu garuruwan. Zuwa akeyi adaukeni. Nayi rayuwar bariki amma gaskiya ba kowanne gaja nake kulawaba, kuma ni kudi baya gabana aharkar bariki kawai burina nayi iskanci, nikaina mamakin kaina nakeyi yanda nakasance mabukaciyar maza, jarababbiya sabanin da dako wani Abu feeling bansaniba. Duk inda kake Neman cikakkiyar karuwa tantiriya Mara kunya da ganin mutuncin kowa to nakai. Shiga ta fitsara na kware wajen yinta, rawa kuwa kala_kala ta yan iska na iyata.

Amma fa duk da haka banajin dadin zaman gidan bariki, saboda bariki babu amana, babu riba. Rayuwace Mara yanci Wanda mutane suke mana kallon tamkar wasu dabbobi. Rayuwace ta zallar fin karfi, da nuna isa. Babu tausayawa juna kokadan acikinta. Ga jefe_jefe na asiri idan kikaga wata ta Fiki. Nidai nasan gaskiya kafin na baro gida bani da aljanu, amma a yawon barikina suka shigeni. Wanda mutum yana batamun rai yanzu zasu tashi suci ubansa, hakan yasa kowa yake shayin taboni.
Chapter 27 · 0% Book details