Sashe 46
Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
..........Tadau tsawon wasu mintuna tana dariyar sannan ta tsagaita,tana kallona tace. "Nacutar dake,ninan nina miki asirin da ciki baya zama ajikinki,nice nayi wa diyarki asiri akahadata da muggan aljanu tashiga yawon duniya,yanzu haka tanacan ta zama shahararriyar karuwa,sedai kashh,wasu sun batamin shirina,sun rabata da aljanun dake jikinta a yanzu_yanzu, kuma nice nasa acusa muku tsanarta acikin zukatanku kukaji ko ambaton sunanta bakwason ayi,sannan nasa akarufe bakin duk me magana akanta. Kisani Aisha banasonki banakaunarki,bani da makiyiya kamarki,duk kaunar danake nuna miki ta ganin idoce, bayan wannanma nabiki da wasu sharrukan kala_kala amma basa kamaki,saboda addu'ar ki,kuma bakya wasa da sallah. Wadancan yaranma dakika haifa naso kashesu amma....sekuma ta fashe da wani irin kuka Mara dadin sauti, daga baya kuma ta koma dariya. Innalillahi,kawai nake maimaitawa afili cikin razani da mamakin mommy,daddy kam suman tsaye yayi, amma bece komaiba,dashi mutum ne da idan ransa ya baci kokuma wani Abu ya firgitashi baya magana. Dakyar nasamu kuka yatahomun nafara rerashi,jikina se rawa yakeyi. Babban abunda yafi tayarmum da ahankali shine datace kinacan kinzama shahararriyar karuwa,bazan iya misaltamiki bakin cikin daya ziyarceniba a lokacin, daga bayama senadena gane komai se farkawa nayi naganni agadon asibiti, ansamu drip. Gwaggota nagani agefena,yunkurin tashi nayi,hakan ya ankarar da gwaggo na tashi, dasauri yanufoni tana zubamun sannu, hawaye nabin fuskata nace, "gwaggo ina alh,dan Allah kice masa yanemomun yata aduk inda take" sharemun hawaye gwaggo tahauyi tana fadin, "kiyi hakuri zainab zata dawo gareki da yardar Allah,(dayake daddy yamusu bayani atakaice) nifa dama nasan tafiyar yarinyarnan tawuce karatu,wanne karatune za'ayita yinsa batsayawa" nidai shiru namata ina sauke ajiyar zuciya, nikadai nasan menake ji araina. Kwanana daya aka sallameni,saboda matsawar danayi asallameni,muka dawo gida. A lokacin haukan mommy ya ta'azzara,tsirara take zaune, ko'ansiturce mata jiki,seta cire suturar tayar, tadinga ihu kenan tana fadar abubuwan data aikata. Lallai sharri dan'ankene,idan kika mommy a lokacin bazakice itamabace,mata yargayu da ita,hamshakiya amma takoma bakyan gani,abun tsoro, gaskiyar duniyarnan abun tsoroce Allah yasa mudace kawai,kwananta biyu anata magani damata rokiyya amma basauki,sema kara gaba da haukan Yakeyi,shine aka dauketa aka kaita gidan mahaukata. Yan'uwa da mutan gari,kowa yasan halin da'ake ciki da kuma abunda mommy ta aikata,domin duk Wanda yazo dubata,haka zataita sakar masa zantuka,tana tonawa kanta asiri.kowa se Allah wadai,yake da halin mommy, masu jajanyawa nayi masu dariya nayi,masu kukan tausayinta nayi,domin dukda ita tajawo wakanta amma abun akwai tausayi. Mahaifinki yasa malamai sumasa rokon Allah akan Allah karkato da hankalinki gida, yakuma bazama gari_gari nemanki,gidajen karuwai, ko Allah zesa adace,amma shiru ba'asamekiba. Nayi kuka nayi addu'a harna hakura, amma akullum senayi addu'ar idan kina raye Allah yakarkatomun da hankalinki zuwa gida,idan kuma kin mutune Allah yajikanji. Twins kullum sudameni da kuka,nakaisu gurin mommynsu,sedai na rarrashesu nacemusu sabuwar auntynsu takusa dawowa kekenan." Shiru ummi tayi,tana sauke numfashi, kuka kawai zee takeyi ba kakkautawa,cikin kuka nace, "yanzu duk soyayyar da mommy ta nunamun ta karyace, ada nake ganin kamarma tafini sonki,meyasa mutane suke hakane, son zukatanmu yamana,yawa. Mutum yadinga shirka akan duniya,ita yanzu mommy mene ribarta nayin haka,gashi ta batamun rayuwa tariga tahadi da bakin tabon dabaze taba warkewaba,arayuwata. Ya Allah kakaremu da sharrin masu sharri." Kawar dakai ummi,tayi tana kokarin maida kwallar data tararmata a ido. Cikin sanyin murya ummi tace, kibani labarin abunda yafaru dake tundaga tafiyarki zainab,naga kindawo gida cikin shigar kamala, bakamar yanda mukayi tunaniba, yanzu kinbar yawan barikin kokuma yaya?" Ajiyar zuciya nasauke, zuciyata namun zafi,bansan tuno rayuwata ta baya, amma ummi mahaifiyatace,dole na zayyana mata,kodan tasan matsayina a yanzu. Labarin duka abunda yafaru nabata, har aurena da abunda yabaroni daga gidan Dr,banboyemataba. Jinjina kai kawai ummi takeyi,wani gurin tayi kuka alabarin zee,wani gurin kuma takaici, wani gurinma dariya yabata. Babu Wanda yafi burgeta takumaji kaunarshi tashiga ranta,kamar mami, tajita tanason matar kuma tanason ganinta kodan yadan ta rike mata yarta. Sekuma Dr, da malam,koba komai basu kyamaci yartaba, sunyi amfani da ilimin da Allah yabasu. "Gaskiya zainab,kinyi rayuwa Allah ubangiji yayafe miki lefin da kika aikta, sannan kuma maganarki ta karshe a labarinki,ki kwantar da hankalinki insha Allah,Allah ze bayyana gaskiyar al'amari,kuma tunda kince mijinki besakekiba,zaki koma gidanki da yardar Allah. kikwantar da hankalinki karkisaka damuwa aranki,kodan cikin dake jikinki. Ammafa naji dadi dajin wannan daddadar labarannaki na aurenki,tabbas zainab ko dawowarki gidannan bemun dadin labarin aurenkiba,saboda alokacin ina fargabar Dame kikadawomun. "Allah ubangiji,yasakawa mijinki da maminsa da mahaifinsa da gidan Aljannah,sungama mun komai arayuwa. Zainab kisani burin kowacce uwa aduniya,taga ta aurar da yarta,musammanma yanzu da zamani yalalace. Allah kashirya mana zuri'a." "Ameen ummi" nafurta haka ina sauke numfashi. Mikewa ummi tayi tana fadin, bari naje nayi sallah nasanar da mahaifinki wannan daddadan labarin, narasama ina zansaka kaina dan farinciki." Murmushi kawai nayiwa ummi,nima na mike nanufi toilet danyin alwala.
Kafin na idar da sallah har ankawomun kayan fruits cikin wani katon faranti,dariya nayi nasan wannan aikin ummine,dantaji ina da ciki yanzu zatayi ta dirkamun abinci. Janyo farantin nayi cikin,Tsinkewar yawu nafara sha,duk bugun zuciyata tana bugawa da tunanin yaya ne,da kuma begensa.....
Ummi tana idar da sallah tanufi part din daddy,yana zaune akan darduma ya tasa laptop agaba yana latsawa,sallama tayi ta karaso jikinsa ta rungumeshi tana fadin, "Albishirinka mijinah" daddy yana murmushi yace, "goro fari kal matar" "princess dinka,Ashe tayi aure yanzuma daga gidan mijin take" tattara hanjalinsa daddy yayi akan ummi yace, "dagaske kike Aisha koda wasa" "dagaske nake maka daddy,babu wasa,aikasan bazan maka wasa amaganar aureba" raba jikinsa daddy yayi dana mommy,yafuskanci alkibla yayi sujjada ga ubangiji,kafin yadago yada hannunsa sama yanawa Allah godiya. Murmushi kawai ummi take dokawa,fuskarta dauke da tsantasar farincikin dayakasa boyewa. "Kai amma gaskiya matata,dole inbaki tukuicin zancennan,Wanda zesaki farin ciki kamar yadda kikasani." "Bani yakamata kayiwa tukuci Wanda ya auri,yarka da kuma wadanda sukariketa kafin auranta,susuka cancanki tukuici." "To Aisha wanene mijinnata,suwaje kuma suka riketan?" Gyara zama ummi tayi,tabawa daddy labarin zee duka Wanda tabata.
Cikin jimantawa daddy yace, "yanzu yar cikinace tayi wannan rayuwar,kai amma baraka bata kyautamunba,kuma ta cutarmun da yarinya,amma taje indai duniyace zata gani akanta" haba alh,banason kanayin irin wannan maganar,abunda mommy tayi yariga ya wuce,sedai kawai muyi fatan Allah yakiyaye gaba, halin datake ciki yanzuma ya isheta ishara." Jinjina kai daddy yace, "inaga zanje kano gobe nahadu da malam Abubuwar gezawa" "amma,alh gobe kaman yayi kusa kabari mana nasan mijintah zenemeta da kansa insha Allah,daganan seku hadu" "A'a Aisha mutumin dayayi maka wannan abun bazakatsaya seya nemekaba,niyakamata nanemesa dakaina namasa godiya,har mijinnata" tausasa murya ummi tayi tace, "dan Allah kakara hakuri daddy,yarinyarnanfa korota yayi,yanzu idan kaje nasan malam ze bukaci ta koma,nikuma nafison seya gane gaskiya da kansa" murmushi daddy yayi yace, "shikenan Aisha, Allah ya bayyana gaskiyar da wuri, tunda Ku dole sukunja aji,karkuje ace kunzo biko ko,aina ganoki" dariya ummi tayi tace, "A'a fa nibahaka nake nufiba kawaidai......" Kawaidai me? Fadi gaskiya dai" dariya sukasa gaba dayansu..........
*KANO*
Dr,yanda yaga rana jiya haka yaga dare, daga baya tashi yayi yafara jero sallah. Har akayi kiran assalatu.
*SEYANZU NA SAMU CAJI NAMUKU,AMMA KO EDITING BABU🥺😢*