← Book details Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 52

Sashe 23

Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ke! Fatsima kinsan me kike fadamun kuwa,jikinnawane yakeson karuwa.Mahmud din yafara shaye_shaye ne bamu saniba.ko kuma kansa ya kuncene,muje insamu malam din,wannan wanne irin zancene. Mikewa tayi ta fito falo.tanata mita.dai_dai lokacin Mahmud ya fito,shan gabansa tayi. "Kai Mahmud me nakeji mahaifiyar ka tazo tana fadamun,wai yar tasha rainon titi,ragowar kwararo zaka aura,a matsayinka na dan gidan babban malami agarinnan.wata uwar harara,yazabga mata,yanda ta hakikance kamar wadda ta kamashi yayi kisa,se wani daga murya takeyi,har tasa kannensa sun fito daga daki,ga munanan kalaman data jefi zee dinshi dasu,sunfi komai bata mata rai. Kaucewa yayi ya fara tafiya. Rigarsa ta cakumo,ina maka magana kana karayin gaba,fizge rigarsa yayi bece mata komaiba,yayi gaba.yayi gaba abunsa.kuka hajiya kaka ta saka tana sallami."shikenan angama dashi wlh ta shanyeshi asiri ta masa,wannan aikin asirine.zulaihat da Rasheeda ne suka karaso gurinta ganin ya fita,bakinsu har rawa yakeyi wajen tambayarta abunda ya faru.bayani ta fara rattaba musu har da Karin gishiri da maggi. Sakaro Rasheedah tayi tana kallon hajiya kaka,aranta tana cewa.kutmar lallai za'ayi bala'i.yanzu duk zaman jiran ya,Mahmud danakeyi haka zemun,wlh be isaba yayi kadan be'isa ya wulakantataba.dakin umma ta nufa fuuuu,ita kuwa hajiya kaka dakin malam tayi.

Umma kaiwa da komowa kawai tajeyi adakinta,bakin ciki tamkar ya kasheta. Ita yaronnan ze kunyata,bayan yaki auran yar,yar'uwarta sannan yanzu kuma,yazo mata da wani zance da hankali bazai daukaba.auran karuwa,ita kuwa wacca irin kunya zataji acikin yan'uwanta da kawayenta.auran danta na fari,amma ace da karuwa.kai abunma da bazeyiyuba kenan.shikuma malam harda kara yarjemasa,saboda ya masa dadin baki.Rasheedah ce ta shigo dakin tana kuka,ta fada jikin umma."Umma gidanmu zantafi,domin zamana bashi da amfani,kuma yanzu umma kina gani ze'auri wata baniba.shafa bayanta umma ta hauyi cikin rarrashi. "Ki kwantar da hankalinki,yata.wlh wlh wlh kinji na rantse Mahmud bashida da wata mata a duniya seke. Koyanaso kobayaso dolene ya aureki,ki share hawayenki kidena kuka.zakiga mezanyi a gidannan,indai ina numfashi bazeyi aurannanba.....

Ita kuwa shukura tana daki bata Masan me akeba,saboda tasa earpiece a kunnanta tana jin karatun alkur'ani,tanabi ahankali. Zulaihat ce ta shigo tana daka mata duka. Dasauri ta mike tana bata rai,haba aunty zulaihat se kawai ki shigo kina dakamun duka.saboda mugunta.ta fadin bayan ta kashe akaratun. "Ke dalla can,kinanan bakisan me yayanki yake shirin aikatawaba. "Yaya kuma,me yayi? "Eh mana yana shirin kawo mana masifa, baragurbi, cikin zuri'a wai karuwa yakeso ze'aura. Da sauri shukura ta mike,karuwa kuma aunty zulaihat anya kuwa kinji daidai.yayan da mata basa gabansa,mekuma ze hadashi da wata karuwa. Harara zulaihat ta cilla mata,tace "sekije ki tambayayesa ai,tunda ni na saba karya.Kallonta kawai shukura takeyi tamkar itace yayannata,tome yake shirin faruwa a gidansu. Dafe kanta tayi,bata dame bata amsar tambayarta,kokuma ya tabbatar mata da'abunda zulaihat ta fada mata.seshi yayan,shikuma bata isa ta tunkaresaba,amma dai zata jarraba.......

Hajiya kaka,kuwa dataje malam yana lazimunsa,kuma tasan bayason tsayawa idan yanayi.fitowa tayi daga dakin tana cewa. "Kiran Allah ba wasabane,yagama lazimun zata dawo ta sameshi.kwafa tayi ta koma dakinta....

Ransa a matukar bace ya koma Dakinsa,yasan halin hajiya kaka da rikici yanzu seta dawo masa da hannun agogo baya.wanka yayi ya kwanta yau ko bi takan laptop dinsa beyiba,ballema yayi wani aiki. Kwata_kwata zuciyarsa babu dadi,yasan fushin mahaifiya akan danta,shi kuwa bazeso yayi aure batare da saka albarka taba,dolene ya sameta ya mata bayani yanda zata fahimta,kafin afara zugata domin yasan halin mata,da zuzuta Abu. Ya kuma yanke shawarar gobe ze dakko zee,yadawo da ita gidan maminsa,da yardar Allah. Kafin kuma ya maidata gidan iyayenta da kanta,domin yanayin dayake ciki kwanannan ya matsu yayi aure,dan yana gab da hallaka.....

*************
Batayi wani baccin kirkiba,adaren jiya.daga ta fara take farkawa.wani mummunan mafarki tayi,wai gata zata fada wani katon rami,me matukar zurfi da duhu,se ihu take kwararawa tana Neman taimako,tazo zata fada ramin taji wani hannu ya riketa,can kuma daga cikin ramin wata mata tanata kwala mata kira,itama tana janta zuwa cikin ramin. A matukar firgice zee ta farka,ta jike sharkaf da gumi.wani irin Abu takeji ajikinta,tamkar ana zuke mata jini.tsorene ne tsanani ya lullubeta,tanason tuno muryar mata dataji tana kiranta amma ta kasa,acikin mafarkin kuma tabbas tasan muryar. Addu'a tafara karantowa tare da dunkulewa waje daya. agefe guda ga takaicin abunda su joeboy suka mata. ta yanke shawarar gobe zata tattara kayanta ta bar gidan joeboy, zata bawa ne gadi Makullin gidansa ya basa,zata tattara duk wani Abu daze dunga tuna mata dashi arayuwarta, ta rabu dashi.Amma ta tabbatarwa da kanta,shima joeboy beci bulus ba,zesan yayi da ita,zata dauki mummunan n mataki akansa.tanaji ana kiraye_kirayen sallah,amma ko motsawa batayiba danma ba sallar takeyiba.wani azababben ciwon Kaine yake damunta,jikinta yayi zafi zau,zazzabine ajikinta.amma gari na fara haske,ta mike tana yamutsa fuska tayi wanka,wata doguwar Riga ta zira,ko bra bata sakaba ta fara hada kayanta,duk da azabar datakeji ajikinta,amma haka ta daure domin ta kudiri niyyar barin gidannan ayau saboda ta tsani mamallakinsa.

Karfe 7 ya shirya,zuwa office amma azahiri ba office din zejeba dakko zee zeje,domin ya matsu ya dakkota saboda munanan mafarkan dayayi akanta.be hadu da kowaba a falo,hakan yasashi ficewa batare da sunyi sallama da yan gidanba.malam kam dama sungaisa a amasallaci da asuba.text yayiwa shukura akan taje gidan maminsa ta jirasa yanzu.direct gidan Dr kabeer,ya nufa.a kofar gidansa yayi parking kiransa yayi akan yana jiransa a waje. Bayan kamar 15 minutes Dr kabeer ya fito,front seat ya bude ya shiga."Haba malam,dankai baka da iyali bakasan dadin bacci tar...."kaga malam ba dogon zancene ya kawoniba,zanje gidan yarinyarnanne zan dakkota shiyasa nazo na fada maka. "Haba Mahmud,ai yanzu yayi wuri,karfa ka manta zainab fa batasanka,kana tunanin zata biyoka ne? Bata rai yayi,yace. "Zaka gani,nagama fada maka abunda ya kawoni semunyi waya,nizan wuce ina saurine. Girgiza kai Dr kabeer yayi yafice daga motar,yana shiga ya dakko wayarsa,yakira layin zee Amma seyaji wayar akashe......

Shukura tana wanke_wanke taga text din yayannata,sauri _sauri ta karasa aikinta dama tana son ta tattauna da yayannata.shap_shap tayi wanka ta shirya, harta gama kimtsawa babu wadda tatashi agidan,se umma. Fada mata tayi zataje gidan mami ta kira tace tana son ganinta.batare da tunanin komaiba,umma ta barta,tadaiyi tunanin ko itama taji zancen,abunda Mahmud yake shirin aikatawa,shiyasa tayiwa shukuran kiran sassafe.driven malam tayiwa magana ya kaita gidan mamin......

Tsayawa yayi kawai yana kallon gidan bayan yayi parking akofar gidan,seda yagama karewa gidan kallo sannan yakara tada motarsa yafara danna horn, megadi yayi zaton joeboy ne, dasauri ya fito ya wage masa get din,dannan hancin motarsa yayi cikin gidan. Seda yayi parking sannan yafito suka gaisa da megadi.kallon rashin sani megadi yake binsa dashi,domin betaba ganinsaba,yaso ya tambayesa waneshi amma yakasa saboda kwarjinin mahmud ya masa,gashi ya tamke fuska tamau.part din zee ya nufa,bayan me gadi ya tabbatar masa da tananan.dukda wata zuciyar tana fada masa kamar hakan bedaceba,kamarshi agidan mace,amma babu yanda zeyi hakan shine kawai mafita agaresa.

Duk da zuciyarsa tana bugawa,saboda shikanshi yasan ya taro dala ba gammo.yasan fin karfi kawai zeyi,amma banda haka rana tsaka mace bata sanshiba yazo ya dauketa,macenma irin zee me shegen tsiwa.baya tunanin zata amince masa ta dadin rai seya mata wuta_wuta. Danma da kyakkyawar niyya yazo mata,Allah yaga zuciyarsa.yana rokon Allah yabashi nasara.(Kai Dr,fin karfin yayi yawa,Anya bakaso kanka dayawaba😂😂). Murda handle din falon yayi,cike da kwarin gwiwa da jarumta ya shiga falon,da karfi ya buga kofar wajen rufewa,domin tasan da zuwansa,idan kuma barcima takeyi zejirata harta tashi.

Seda ta gama hada kayanta Tass,acikin trolly dinta,zama tayi abakin gado tana dafe kanta,tare da sauke numfashin gajiya.
Kamar a mafarki taji motsin bude kofa afalonta,to waye wannan yazo mata da sassafiyarnan,ko me gadine,to ai idan megadine knocking yake mata,kafin ya shigo.tunawa tayi bata sawa kofarta key ba,tun jiya saboda bamata da nutsuwar wannan tunanin. Sallama yayi a falon duk da yaga babu kowa,mazauni yayiwa kansa akan daya daga kujerun falon yana karewa falon kallo, .ahankali zee ta mike ta fito falon,jin motsi zuciyarta na bugawa. Wani daddadan kamshine ya ziyarci hancinta,duk da yanayin damuwar datake ciki amma lumshe idanta tayi cikin San tuno,inda tasan wannan daddadan kamshin. Kujerar dayake zaune,ta bawa kofarta bayane,hakan yasa bayan mutum kawai ta hango. Cike da tsananin kaduwa da mamakin wane kuma wannan,ta karaso gabansa,motsinta dayaji yasashi dago kansa yana kallon gefen datake. 4 eyes, sukayi da juna.............

*sis,farhana bata da lafiya tana bukatar addu'arku😢😭🙏🙏*

*BY*
*Zeey kumurya*

..........dasauri tayi kasa da idanunta saboda yanda yatsareta da rikitattun idanunsa,ga kuma wani kwarjini da yayi mata. to, meyakawoshi gidanta da wannan farar safiyar, mezeyi mata,ina yasan gidanta.ta bude baki da niyyar zata masa magana ta kasa.saboda wani jiri_jiri ta faraji,ga yunwa na nukurkusarta ga zazzabi ajikinta,ahankali duhu ya mamaye ganinta.kanta yafara juya mata,jikinta ya kama wani irin rawa. Shikuwa ido ya kura mata ganin kamar bata cikin nutsuwarta, kawai gani yayi ta tafi luuuuuu zata fadi,da sauri ya mike cikin zafin nama yay azamar tarota,tafado jikinsa,daganan zee bata kara sanin inda kanta yakeba.kura mata ido yayi yana kallon yanda fuskarta ta kumbura,saboda kukan datasha.idanuwansane suka sauka akan kirjinta Wanda har kan nipples dinta ana ganin shatinsa,saboda babu bra ajikinta.runtse idonsa yayi sabowa wani Abu dayaji ya tsirgamata,batare da jiran komaiba ya kinkimeta se motarsa. abayan motar ya kwantar da ita tamkar gawa.se a lokacin wani tashin hankali ya ziyarcesa.dakarfi yafara dannawa me gadi horn,bude masa get din yayi,yafice daga gidan da mugun gudu. Baze iya kaita asibiti da wannan banzar shigar tataba,direct gidan maminsa ya nufa da ita.yasan bazerasa kayan aikin daze duba zee ba. (Saboda mami itama likitace) mami suna zaune a falo ita da shukura da zuwanta kenan,kawai gani sukayi mutum yashigo da mace a hannunsa tamkar gawa.batare daya musu bayanin komaiba yashige daki da ita,ya shimfideta akan gado.cike da tsantsar mamaki mami da shukura suka bi bayansa,suna tambayarsa ba'asi.a gaggauce yacewa mami takawo masa kayan aiki ze dubata,batare daya basu amsar tambayarsuba.da kansa ya dubata,inda ya gano tsananin damuwace ta haddasa mata ciwon kai,da zazzabi.seda yafita ya samo ledar ruwa yasakamata,su dai su mami kallonsa kawai sukeyi da ido,ganin yanda duk ya rude,kokadan basuyi tunanin itace wadda yake soba,su a tunaninsuma bugeta yayi da mota.

Seda yamata duk abunda yadace sannnan ya fice yana kara jaddada musu da zarar tatashi su bata tea,domin acikin abunda yake damunta harda yunwa.dakin datake suka shiga,suna kare mata kallo.shukurace ta dubi mami tace, "mami anya kuwa wannan lafiyarta kalau,kinga kanta ko dankwali babu, kalli kuma yanayin shigarta.gata kyakkyawa ga gashi. "Nimadai abunda nake tunani kenan shukura,amma dai mujira farfadowarta......
Chapter 23 · 0% Book details