← Book details Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 52

Sashe 25

Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin dare naji ana kwalamun kira,a matukar firgice na tashi.jikina namun wani irin zafi tamkar ana gasamun garwashi.zuciyata se tafarfasa takeyi.wani irin juyi kaina yakemun.matsanancin kunci da bacin Raine ya ziyarceni,a lokaci guda.jinayi tamkar ana fizgata na tashi da gudu na fice daga dakina,part dinma gabadaya na fice. Farfajiyar gidan mu babu kowa,hakan yasa na nufi kofar get.abun mamaki kofar get din gidanmu a bude take.dasauri na bude na fice daga gidan da gudu. Inajin araina banaso ko'amafarki nakara komawa gidan har'abada.gudu nakeyi sosai a cikin dare,bansan inda nake nufaba,tafiyar fiye da sa'a guda nayi,amma ko gezau banyiba,kuma babu alamar gajiya a tattare dani.gashi kafata ko takalmi babu.jikina kuma doguwar rigar bacci,se hijabin dana kwanta dashi ajikina.ban hadu da kowa a tafiyata se karnuka dasuketa haushi.ni macece me tsananin tsoro amma a wannan daren babu tsoro kokadan araina,burina kawai inyi nesa da gidanmu. Saboda jinakeyi tamkar ana yankar naman jikina agidan.intakaice muku zance,gaba dayama na bar arearmu,ina tafiya ahanya aka fara kiraye_kirayen sallar asuba.

Sedanaga mutane sunfara fita zuwa masallaci sannan na samu gefen wani gida na rabe.ai kuwa ana idar da sallah megadin gidan yakoreni.haka na tashi nacigaba da tafiya.tunanin gidanmu dana iyayena gaba daya yaficemun daga rai.har gari ya fara haske Inata gararanba a garin abuja.dakyar nasamu wani bawan Allah ya fito a motarsa.nace masa Dan Allah tasha nakeson zuwa,amma bansan a ina takeba.tambayata yayi nikuma ina zanje yar yarinya dani,ko irin yarannane mu wadanda muke zuwa karuwanci. Karya na masa nace,wata matace ta kawoni,tanaso tasani a hanyar banza. ni kuma yanzu nakeso nagudu na koma gida yanzuma batasan na gudoba.Kataimakeni dan Allah.tsayawa yayi yana karemun kallo,yagadai tabbas banyi kama da karuwaba,kome zaman kanta.duk da dai basu da kama.amma yanayin nutsuwar mutum yanasa a fahimcesa. Motarsa yace na shiga,muka dauki hanya har tasha. Har anfara lodin sassafe,tambayata yayi inane garinmu.kawai jinayi bakina yace kadauna,alhalinma ni bantaba zuwantaba.seda yasani a mota ya bani kudin mota.godiya na masa.na matsu motar tatashi mubar garin abuja,saboda naji natsani garin na tsani komai nasa.

Cikin ikon Allah mukazo kaduna lafiya,tundaga lokacin naji namanta da komai nawa,namanta iyayena da yan'uwana.ko sunan garinmu ka tambayeni bazan baka amsaba.wata daban najini,ga wani azababben zafin da zuciyata takemun.haka nayita yawo agarin k.d bansan kowaba,bansan inda zannufaba.tun a tasha nasai takalmi nasakawa kafadata,da guntun kudin da mutuminnan ya bani.har magriba ta kawo kai banhutaba.ga yunwa da kishirwa. Gefen wani layi na samu na zauna ina maida numfashi na rasa meyakemun dadi a duniyarnan duniyar gaba daya ta canzamun. Wata motace tazo ta wuce ta gabana,har ta wuceni sekuma aka dawowa baya.tsayawa yayi tare da zuge glass din mortar. "Yanmata ya fada yanamun wani kallo, tare da sakarmun wani munafukin murmushi. Nima tsaresa nayi da idanuwa cikin rashin kunyar da'ada bani da ita nace, "malam lafiya kuwa.ina zabga masa harara. Kara kasa yayi da murya, "haba yanmata ki saurareni mana. "To ina jinka na fada adakile. Tsarani ya hau da kalamansa,koya fuskanci ina bukatar taimako shine yabiyomun ta wannan hanyar. Gashi ni koda ina gida bantaba saurayiba,bana kulasu hakan yasa kalamansa sukayi tasiri akaina na yarda na shiga motarsa. Da zummar ze kaini gida wajen matarsa.

Tun muna tafiya ina ganin gidaje,harna dawo se filaye nake gani gashi kuma dare yayi.inaso na tambayesa amma tamkar yadauremun baki.tafiya mukayi me Nisan gaske, a wani guri yayi parking motar yace na fito.fitowa nayi daga motar ina karewa gurin kallo,babu shakka gurinnan jejine. Saboda babu gida gaba babu gida baya. Se wani makeken gida guda daya tak. Wanda a kofar gidan yayi parking motar. Gaba yashige yace na biyosa,kallonsa nayi cike da matsanancin tsoro nace malam ina kakawoni nanne gidannaka. Bemun maganaba ya matso kusa dani da niyyar ya kamo hannuna,jaa baya na farayi.kawai gani nayi ya dakko wani Abu daga aljihunsa ya shakamun,daganan bankara sanin inda kaina yakeba. Se farkawa nayi na ganni acikin wani gida me kamar kango, ga mutane nan mata da maza a zaune sunata aikin kuka,abun tausayinma harda yara. Binsu kawai nakeyi da kallo daya bayan daya cike da tsananin mamaki,wata tsohuwa na gani tanata lazimi ita bata kukan,tashi nayi na karasa kusa da ita nace, "dan Allah baaba inane nan aka kawoni. Girgiza kanta ta hauyi hawaye yana zubowa daga idanunta, tace. "Yarinya nima yanda aka kawoki gidannan haka aka kawoni,amma dai tabbas gidannan gidan masu shan jinine,kuma matsafa.............

*BY*
*zeey kumurya&real farhana*

........Cikin matukar rudewa nace, "innalillahi wa'inna ilaihirra'ji'un yanzu gidan yan yankan kai kenan baaba aka kawomu,gyadamun kai kawai tayi. tunani nayi ta yanda akaima na shigo gidannan,dasauri na mike bayan nagama tuno abunda ya faru tsakanina da mutuminnan. Ficewa nayi daga dakin da muke nafara zagaye gidan,harna samu nazo bakin get din gidan. Wani Dan tsoho nagani alamun shine megadin gidan,yana zaune akan kujera. Da matukar mamaki yataso yana kallona. "Yarinya ya'akayi kika iya fitowa. Cike da mamaki nima nake kallonsa,amma banmasa maganaba,sedai kalar tausayi dana koma ina rarraba ido. Sassauta murya yayi yace, "yarinya nima nan dakika ganni satoni akayi suka tsafaceni nake musu gadi,amma ba'ason raina bane.kuma duk Wanda suka kawoshi gidannan sesun tsafaceshi,kinga dakin da suka ajiyeki,sunansa dakin duhu, ko bakin kofa bazaka iya fitaba idan suka kaika dakin kuma sun tsafaceka kenan,kuma ko magana mutum baya iyayi,Saidai kayita kuka. amma ke tunda naga kin iya fitowa to basu tsafecekiba. Cikin matukar tsoro nace "Baba dan Allah kataimakeni infice daga gidannan,wlh ni marainiyace bani da kowa. Shiru yayi nawasu yan sakanni kafin yace, "yanzu idanna fitar dake idan akazo niza'a hukunta kuma yanzu suna gab da dawowa. Marairaicewa nayi na fara matso hawaye. "Baba dan Allah tunda na fito daga dakin duhu,kataimakeni insamu nabar gidannan,kamar yadda nafada maka ni marainiyace kuma ina da kanne,kuma nice mekula dasu. "To shikenan yarinya zanfitar dake kofan darajar maraicinki,konima Allah zesa sanadiyyarki na samu na bar gidannan. Cikin azarbabi nace, "yawwa baba nagode Allah ya fitar dakai kaima,akawai wata tsohuwa a ciki da alama itama ba'a tsafacetaba kozan iya zuwa inkirakata kafitar damu tare.

Girgiza kansa yayi,alamun a'a kafin yace, "yanzu kafin ma kije kikirata zasu iya dawowa,kuma idan nafitar daku Ku biyu da matsala.dan haka kekadai kawai zan iya fitarwa. juyawa yayi ya bude mun get din tare da cemun nayi sauri na fice. Jikina na rawa saboda razana na fice, "kiyita tafiya karki sake ki juyo duk abunda zaki gani karki tsaya kawai kiyita tafiya harkije titi,kina juyowa zaki kara ganinki acikin gidannan.batare dana juyoba nadaga masa hannu,alamun sallama.

Shikanshi dajin abun tsorone rasama ina zan dosa, saboda ko'ina sarkakiyace. Daure zuciyata nayi na fuskanci gabas na falfala da gudu. Gudu nakeyi iyakar karfina,ina karanto addu'a azuciyata. Nagamu da abubuwa dayawa na ban tsoro,se ina cikin tafiya se inga katon kogi,haka nake daurewa in cigaba da guduna sekuma inga Ashe ba kogi bane tsabar tsafine.

Kokuma ina cikin tafiya inta gamuwa da muggan abubuwa agabana kamar su zaki kura,suma idanna danne tsorona naci gaba da tafiyata se inga babusu. Ina cikin guduna na hango fitilar mota, ko shakka banayi tasuce,saboda babu me iya zuwa gurinnan idan basuba. Wani mahaukacin tsorone yakamani zuciyata ta fara bugawa da sauri_da sauri.

Kuma a hanyar danake bi tanan suke tahowa,Allah ya taimakeni nasamu wata yar duhuwa na fake,aiko ta daf dani motar tasu ta huce,saboda tsabar tsoro har fitsari na saki.

Wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke bayan sun wuce,na mike nacigaba da tsala guduna,gudun ceton rai ko gajiya ma banaji .ina cikin tafiya naji kamar ana bina abaya, duk da haka na daure naki juyawa harna samu na fice daga jejin, na iso wani guri kamar bayan gari. Amma duk da haka ban tsayaba,takalmin kafata tuni Yakama gabansa. Seda na karaso titi naji wata uwar gajiya da kishirwa da yunwa ta bijiromun. Faduwa nayi a bakin titin ina maida numfashi. Motoci tsilli tsilli ne suke wucewa, da kyar na samu na yunkura ina layi na nufi tsallaka titi, domin ina gudun abunda ya faru dani yakara faruwa. horn naji kawai akaina ana dannamun. Rudewa nayi narasa ina zannufa, kaina gaba daya ya juye,numfashinane ya dauke,hankalina ya gushe.......

Farkawa kawai nayi na ganni akan gadon asibiti ansamun Karin ruwa a hannuna. Bin asibitin na farayi da kallo,ahankali abunda ya faru yafara dawomun kwanyata. Yunkurin mikewa zaune nayi, dasauri naga wata kyakkyawar matashiyar mace, tataso tana mun sannu. "Sannu yanmata,bari na kira likita tunda kin farfado kaina kawai nadaga mata ina bin bayanta da kallo. Tare suka shigo da wani kilita duddubani yayi ya tambayeni inda yakemun ciwo, kaina kawai na nuna masa. Tea me kauri ta hadamun bayan likitan ya fita,da kanta ta bani a baki, se jeramun sannu takeyi,cikin tausayawa.

Intakaice muku zance,matarnan ita ta taimakamun nayi wanka na rama salllolin da ake bina. Ita tayi jinyata harna tsawon kwana 3, sedai naga wasu kawayenta sunzo dubani. Bata tambayeni daga inda bakeba,kuma bata mun itama waceceba.

Da'aka sallamenima gidanta muka wuce,gidanta me kyau dan madaidaici. Wani daki ta nunamun tace inshiga in huta. Bayan na gama duk abunda ya dace ta shigo dakin danake da murmushi dauke akan fuskarta tace, " sannu zee ya jikin.(dayake tun a asibiti na fadamata sunana) "Dasauki aunty." na amsa mata. "Masha Allah, nidai sunana sameera ina zaune anan garin Kaduna,nan shine gidana amma bani da miji zaman kaina nakeyi. Da mamaki nake kallon aunty sameera, amma bance mata komaiba. Tambayata tayi inane garinmu seta maidani gida. Nandanan raina ya baci, karya na mata nace mata ni bani da kowa, se kakata ita kuma kakartawa Allah ya mata rasuwa. Batare da tunanin komaiba ta yarda kuma ta tabbatarmun zata kula dani tamkar ita ta haifeni.

Aunty sameera, ta soni ta kaunaceni tamun rikon mutunci da amana, tamkar wata jininta. Komai danakeso arayuwata tanamun. Taso maidani makaranta amma nace mata banaso. Aunty sameera cikakkiyar karuwace amma kokadan bata tabamun zancen na shiga karuwanciba. Ina gani dai za'azo a dauketa su fita,wataranma agidan suke harkarsu. Tasha fadamun cewa bataso nayi karuwanci,tafison nayi aure. idan na nuna mata bukatar hakan,saboda tacemun babu komai acikinsa se takaici suma kaddarace ta kaisu. Amma ni Sam naki hakura,rayuwarta kawai tana burgeni tunda na baro gidanmu naji babu abunda nake da muradin zama sama da cikakkiyar karuwa. Kuma senazo Allah yahadani da aunty sameera, hakan yakara samun kaunar rayuwar bariki.
Chapter 25 · 0% Book details