Sashe 31
Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
..........Da sauri mami ta karasa gareta ganin zata fadi ta tallafota ajikinta,wani mugun nauyi taji zee ta kara, mutanen dake falone suka shigo dakin a gaggauce saboda jin karar da zee ta kwalla, wasu mata 2 ne suka taimakawa mami ta kwantar da zee,wadda ta zama tamkar gawa babu inda yake motsi ajikinta. Ruwa mami tasa akawo mata ta tofa addu'a ta fara shafawa zee, amma shiru babu motsin komai. Hankalin mamifa yatashi, gaba daya ta rude ga suturun mutane kowa yazo da abunda yake cewa, amma babu tantama wannan sharrin jinnune. Dakyar mami,tasamu tunanin kiran malam yafado mata, malam yana cikin jama'a hakan yasa tayita kiransa begaba, number Mahmud ta kira shima bedagaba, bata hakuraba ta kara kiran kawu, shima a kiran farko bedagaba se'a na biyu. Duk da taji yana cikin hayaniya amma haka ta masa bayanin abunda yake faruwa cikin hanzari, sallallami yahauyi yace mata gashinan zuwa gidan, kuma insha Allah zeyi kokarin ganin sun zo da malam. Zama mami tayi agefen zee ta rafka tagumi, tausayin zee yacika mata zuciya ganin yanda jinnu suke takura mata, dan adan zamannan datayi da ita taga yanda take fama da matsalar ciwon kai kokuma su rike mata kafa. Sauke tagumin data rafka tayi tafara tofawa zee addu'a. Mutane se shigowa sukeyi ganin ikon Allah, se daga bayane wata kawar mami ta rufe kofar dakin ta hana kowa shiga.
Dr, anata gaisawa da jama'a kawai yaji gabansa yayanke yayi wata muguwar faduwa, dama tun dazu kansa ke masa ciwo yayi tunanin hatsaniyace, yanzu kuma seyaji ciwon kannasa yafara tsananta, lumshe idonsa yayi cikin dauriya dan bayasan agane meke damunsa, hannun Dr kabeer ya kama yana fadin yazo suje gidansu Rasheedah kar lokaci ya kure.( Kamar yadda al',adar kano take idan aka daura aure,ango da abokanansa sesunje gidan su amarya). Mota suka nufa suda sauran abokanansu. Mota biyu sukayi, sewasu a Babur. Seda yasamu yazauna a mota yadakko wayarsa, missed call yagani dayawa be dubaba yaga wani message ya shigo, Rasheedah ce taturo masa text din, budewa yayi yafara karantawa. _mijina na kiraka baka dagaba, nasan kana cikin jama'ane. Nagodewa Allah dayanunamun wannan ranar ta aurenmu, farin cikin danake ciki baze misaltuba, sedai idan ankaini gidanka ingwada maka soyayya kala_kala. I LOVE YOU ANGONA_ lumshe fitinannun idanunsa yayi yanajin aransa dama zee ce, ta masa wannan text din. Hankalinsane yaji gaba daya yayi kanta, haka kawai yaji yanason jin muryarta. Bude idonsa yayi wadanda harsun fara sauya kala, su kabeer dasuketa hirarsu yaji sun tuntsire da dariya, bebi ta kansuba danbemasan hirar dasukeba. Missed call din mami ya gani har uku, dasauri yabi bayan kiran, saboda kawai jikinshi yabashi Kamar ba lafiyaba, amma itama mami bata dagaba, har 2 missed call. Haka yahakura,yasan may be mami tana cikin hayaniyane,duk da zuciyarsa na masa wasi_wasi akan hakan. Mintuna goma suka karasa gidansu Rasheedah, tundaga kofar gida yakeshan guda da tsokana, murmushi n yake kawai yakeyi, danshi kadai yasan halin dayake ciki, haka suka shiga cikin gidan abokanan wasa nata tsokanarsa, sundan jima agidan danseda sukayi hotuna sannna suka baro gidan. Suna shiga mota Dr,kabeer ya dubeshi yace, "mutumin saura gidan mami fa" harara ya zabga masa amma bece komaiba, dariya wani abokonsa dake gaba yayi Wanda shiyake driving yace, "kyaleshi k.b duk abunsa dai semunga wannan matar tasa da'aketa boye mana ita" shidai shiru ya musu,saboda Sam bayajin dadin jikinsa. Gidan Dr,kabeer suka nufa, acan zasu baje kolin angwancin.......
Kusan 40 minutes, malam da kawu suka sauka agidan mami,duk da tarin jama'ar dake jiransa wadanda sukazo dominsa,amma da kawu yamasa bayanin halinda surukartasa take ciki, cikin hanzari yace sutaho domin ceto rayuwarta. Gaisawa sukayi da jama'ar dake gidan aka nuna musu dakin da su zee suke ciki, knocking sukayi cikin sanyin jiki mami ta tashi,ta bude kofar, tana musu sannu da zuwa. Amsawa sukayi malam yanemi guri a gefen zee yazauna, kallonta yakeyi cikin nazari. Tambayar mami yayi akan abunda yafaru ta masa Karin bayanin halin datazo tarar da zee.
Shiru malam yayi na wasu yan mintuna yana nazari, numfashi ya sauke ya dubi mami yace, "Rahma wannan sharrin jinnune kije waje ga bakinan kuma duk danke sukazo, kidena damuwa insha Allah zata wartsake, zan mata rokiyya yanzu duk taurin kan aljanin dake kanta da izinin Allah seyayi magana. Jinjina kai mami tayi cikin gamsuwa ta mike ta fita. Gyaran murya malam yayi yayi Bismillah yafara karanto ayoyin rokiyya cikin daddadar kira'arsa. Mintuna biyar da farawarsa wani gumi yafara karyowa zee, tamkar ana yayyafamata ruwa, amma ko motsi batayiba. Fahimta malam yayi aljanun jikinta masu taurin Kaine, danda wasune da tuni sunyi magana. Kara kaimi yayi wajen karanta ayoyin rokiyyar, nandanan jikin zee yafara wata irin kyarma, tana sakin wani gurnani ahankali_ahankali. Wata zabura tayi ta mike zaune, da sauri kawu dake gefe ya taso yariketa. Fusge_fusge tafarayi cikin wata kakkausar murya ta fara magana idonta arufe, "Ku cikamu! Kuma kudena wahalar da kanku kuna konamu domin baxamu taba barintaba har'abada,kuma baxamubarta tayi rayuwar mutunciba, wannan alkawarine mukayiwa uban gidanmu,kuma bazamu karyabaaa!!. Tsaida karatun malam yayi yafara musu magana. "Kukuwa bayin Allah meyasa kuka zabi yimata haka metayi muku.?" "Bata mana komaiba, kawai samu akayi, kuma tunda muke aiki da ubangidanmu betaba bamu garar dayabamu akan aikin wannan bil'adaman dan haka kadena wahalar dakanka bazamu bartabaa!" Cikin fushi malam yace, "karya kuke mushirikan Allah, yanzunnan zanfitar daku daga jikinta da ayar Allah" wata mahaukaciyar dariya suka sheke da ita, wadda tasa kawu sakinta da sauri yayi baya, seda suka gama dariyar sannan sukace. "Munsha jinin dabamu tabashaba akan wannan bil'adama dan haka zamu jure duk wata azabarka,harkayi kagama" ran malam yafara baci, saboda sunfara bata masa lokaci. Cikin daga murya yacigaba da karatunsa bayan yadauresu da ayar Allah yanda basu iya guduwaba, befe minti uku da farawaba suka fara ihu suna malam yayi musu rai sun tuba. Tsayawa malam yayi da karatun yana kallon zee, gyara zama yaga tayi ta tankwashe kafa irinna na sarakai, yatsun hannunta ya tankwashe Kamar na kutare. Bude idonta tayi tana dan zazzarosu. Cikin wata murya wadda ba itace ta dazuba aka fara magana. "Malam wanene kai dazakazo kana konamun yara?" Shima malam fuskarsa ba wasa yace "kai wanene?." "Nine irham,sarkin kutare na kafiran, aljanun yankin kudu" "mekakeyi ajikin wannan baiwar Allah?" Malam yakara jefomasa tambaya, "nine Wanda nake jagorantar wadanda mukeyin aiki akanta" "wanne irin aikine wannan?" "Aikine, aka bamu akanta tunshekara bakwai da suka wuce, akan mu korata ta shiga duniya kuma mumantar da ita gida, mu gurbata rayuwarta tazama abarki ga kowa, kuma duk namijin daya tunkarota da nufin aure mu kawar dashi, amma lokacin dana shiga jikinta senaji ina sonta tamun, hakan yasa na hana yarana cutar da ita, Kamar yadda ubangidanmu ya umarcemu, nadai cika masa aikinsa munbarota daga gida, mun mantar da ita kowa nata. Aduk lokacin data tuna gida,ko'aka tuna mata muna cusa mata kunci da takaici acikin zuciyarta taji tamkar zata mutu. Kuma mune muke tunzurata ga harkar banzan datakeyi, tare da kiyayyar aure acikin ranta,Wanda ko zancen aure bataso a mata. Wannan auranma da'aka daura mata yau, nayi ina yina wajen ganin na hana, amma addu'ar dakuka bata tajeyi kullum, ita tahanamu cimma nasara, mijin data aurama munso ganin bayansa amma saboda karfin addu'arsa ko tunkararsa munkasayi, shiyasa yau da'aka daura auren, nasa yarana su kwantar da ita jinya,kuma sudinga tsoratata, kuma su cusa mata kin auren azuciyarta, ta bijire muku. yanda zaku gaji ku warware auren, saboda auranta shine makaryin sihirin dake jikinta,Wanda muke aiki akansa" "Duk wayasaku wannan aikin?" "Ubangidanmune, boka la'ananne na kan tudu"
Gyara zama malam yayi yace, "yanzu karku batamun lokaci inada uzuririrrika da dama, zaku fita ta dadin rai kosena kokkonamuku jiki" "malam kome zaka mana bazamu fitaba saboda alkawari mukayi kuma munajin dadin zama ajikinta" Bismillah malam yayi yacigaba da rokiyyarsa ya lura wadannan kafiran jinnun zasuyi taurin kai. Shidai kawu yana gefe yana kallon ikon Allah. Tunda malam yafara karatu, suke kuka ahankali, amma malam yaki bari, nandanan suka cika dakin da ihu da kararsu, suka fara rokon malam, amma malam yaki denawa, soyake sugama jigatuwa,sannan ya barsu.
Ihu sukeyi da zabura, Wanda har falo ana jiyowa. Zuwa lokacin kowa ya fuskanci abunda yake faruwa, mami jitayi tamkar ta shiga dakin,duk da tasan ba yartata keyin hakaba, addu'a takeyi Allah yasa aljanun subar jikin zee ayau, kota huta. Kusan minti 20,malam yayi yana karatu kafin ya tsagaita. Kuka zee takeyi harda hawaye jikinta ya jike sharkaf da gumi, aljanun se rokon malam suke akan suntuba,yayi musu rai. Cikin kakkausar murya malam yakara tambayarsu zasu fita ko yaya. Taurin kai suka kara nunawa, aiko yacigaba da karatu. Dakyar dai malam yasamu aljanun suka fice, daga jikin zee,tare da alkawarin sun barta kenan, saboda sunci azaba bakadanba,dan malam bemusu da wasaba. Kwanciya tayi sharaf akan gadon,bayan tayi atishawa ba'adadi. jikinta yashika tamkar ta suma. Doguwar ajiyar zuciya malam yasauke, shikansa yahada gumi. Duban kawu yayi yace, "Abdullahi kaga ikon Allah ko, ita kuma tata kaddarar kenan, amma da izinin Allah sunbarta kenan har'abada." "Allah yasa malam, mudama burinmu kenan da kuma fatanmu." Jinjina kai malam yayi yace, Allah ya kyauta ya kuma kare mana zuri'a ubangiji Allah yashiga tsakanin nagari da mugu, amma koma wane yayi mata wannan sihirin ya cutar da ita ba kadanba,kuma ubangiji baze barsaba, saboda wannan zalunci ne, Allah kuma yayi hani dashi. Allah dai yadade karemu daga sharrin mutum da aljan." "Ameen malam" "tashi muje muyi sallah tunda anyi tundazu, gashi tun dazu ake kiran wayata" mikewa sukayi suka fice daga dakin, suka bar zee kwance akan gado, wani nannauyan bacci ya dauketa. dakin mami suka shiga suka tarar da ita akan dadduma, tunda tayi sallar la'asar bata tashiba tanata rokon Allah, akan yayewa zee wannan lalurar. Kozama basuyiba malam yamata bayani, akagauce saboda saurin dasukeyi. Yakuma kara da cemata, anjima dadaddare ze kawo mata rubutu na kariyar jiki, tabawa zee tasha. Kawune yace da mami tadauki zee takaita dakinsa saboda maganar mutane. Godiya sosai mami tayiwa malam, tare da godewa ubangiji, dafatan insha Allah karshen abun yazo. Dakin zee ta nufa dasauri, hawa gadon tayi ta janyota jikinta ta rungume, tanajin kaunarta na ratsa ko'ina na jikinta. itadai zee baccinta kawai takeyi.wasu kawayenta tasaka suka kinkimi zee, suka kaita dakin kawu, suka kwantar kafin ta farfado.........