← Book details Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 52

Sashe 36

Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Se wajen goma da yanmintuna mami tashigo dakina gaisawa mukayi tanata tsokata, daga baya kuma tashiga samun albarka,da godiyar girkin danayi. murmushi kawai nake mata. "Zainab kin karya kuwa?" "A'a mami" "kai zainab kina wasa da cikinki kiyi girkin amma kiki cin abincin,?" "Banayin yunwane mami shiyasa" "mekikaci dazakice bakyajin yunwa bari nakawo kayan ki karya dama akwai wani hadin kaza dazan baki kici." Tafadi haka tana mikewa. Bayan wasu mintuna segata tadawo hannunta dauke da katon tire, Wanda tajera food flaks guda biyu aciki, sekaramin tea flaks da bread. Dariya nayi bayan ta'ajiye tiren nace, "kai mami ina zankai wannan abincin har flaks biyu?" "Aiwannan ba abinci bane" takarashe zancen da budemun flaks din, naman kazane dafaffe amma yayi wata kala kamar ansa masa magani. "Wannan sekin gama karyawa sannan zakici" bata fuska nayi nace, "mami ina zankai wannan gaskiya bazan iyaciba kingafa ta janza kala." Hararata tayi tace, "karkici kiga yanda zamu kare dake a gidannan" kawar da zancen nayi da fadin, "mami inason naje gida dan Allah yaushe zani." Duk da inajin tsoro nafada mata amma naga kozancen zuwa gidan batamun shiyasa natambayeta. Gyara zama tayi tace, "zakije gida zainab, amma bayanzuba kibari kitare ko bayan wata ukune seki shirya kije." "Saboda me mami,wlh nayi kewarsu yanzu inason nagansu naga halin dasuke ciki" nakarashe zancen kwalla na cikamun ido. "Saboda nafison suganki da aurenki da mijinki, se sunfi jindadin hakan." Zanyi magana mami ta katseni tana fadin, "kici abincinki nariga nagama magana,kuma karkimun kukannannaki" cikin sanyin jiki na sakko,ina hadiye kukana, dankalin nazuba nafara ci. Cike da tausayawa mami take kallonta, jitakeyi tamkar tacanza ra'ayinta saboda tasan kewar iyaye akwai taba zuciya, amma tafiso se zee tatare sannan taje gida. Dantasan yanzu idan tatafi bazata dawo da wuriba. Mikewa tayi ta fice daga dakin.

Dr,yau yasha raki da tabara a gurin Rasheedah. Lallabata yakeyi saboda kobakomai takawo masa budurcinta. ita kuma se jindadi take,aganinta yafara sonta ne, shikuwa yana mata komaine saboda bayason ubangiji yakamasa da rashin adalci atsakanin matannasa. Se wajen karfe goma yasamu tayi bacci,bayan sun karya da abincin da umma ta aiko musu. Wanka yayi yashirya cikin wani milk din yadi,Wanda ya matukar yimasa kyau. Gidan mami yanufa domin yaga sahibarsa,dan da kewarta yatashi yau.

Tura abincin kawai nakeyi,inaci ina hawaye. kadanma naci na ture. Kusan minti goma Inata juya kazarnan amma nakasaci dakyar nasamu na gutsira nakai bakina. Yamutsa fuska nayi nadaure na tauna. Na kara gutsurowa kenan zanci naji kamshin da agun mutum daya nake jinsa. Mamakine yakamani, kodai hancinane yakemun gizo domin wannan Tabb....muryarsa najiyo a falo yana gaisawa da jama'a. Dasauri na rufe flaks din kazar, dankarya gani,nasan dole seyashigo dakina. Ture tiren nayi gefe na koma kan gado na kwanta tamkar me bacci.

Da sallama ya shigo dakin, amsa masa nayi azuciyata ina kara lumshe idona. Ahankali ya taka har gaban gadon murmushi yayi danyagane ba bacci takeba,jinsane yasata yin haka. Zama yayi akusa da ita yakai hannunsa jikinta yafara mata cakulkuli, duk yanda naso daurewa amma nakasa seda nayi dariya amma naki bude idona. Fuskarsa ya matso da ita daf da tawa,kawai jin saukar numfashinsa nayi akan fuskata ga kamshinsa daya kara baibaye hancina. Dasauri na bude idona jin idonsa nayawo ajikina. Ya wani tsareni da ido yana kallona. Turo bakina nayi gaba ina kunkuni ina cewa, "nifa banason yawan kallo" lumshe idonsa naga yayi ya kwanta agefena, hannunsa yakai yashafo kirjina cikin wata kasalalliyar murya tamkar mejin bacci yace, "meyasa bakyason saka bra,kinfiso kibarsu haka suyita tsonemun ido." Waro idona nayi waje, hannunsa na ture daga kirjina bance komaiba. Dandaga jiya na lura shima jarababbene yasin, gashinan sewani annuri yakeyi,alamun ya angwance. Hannuna Yakama yarige,dayan hannunsa kuma yamayar kan kirjina yana fadin,"meyafaru dake naga idonki kamar kinyi kuka?" Bata fuska nayi ina shirin yin wani kukan nace" gidanmu nakeson zuwa kuma mami tahanani" harara ya gallamun yace, "dakinsan kinason gidan amma kika baroshi. Hawayene yazubo daga idona cikin kukan dayatahomun nace, "ni wlh bansan natahoba,dan Allah karoki mami tabarni naje, daddyna bashida kowa seni nasan yanzu yanacan hankalinsa atashe." Kuka nafashe dashi dama jiran kadannake. Rungumeta yayi tsam ajikinsa yana shafa bayanta cikin rarrashi. Tausayintane ya lullubeshi, shima yanason taje gida taga iyayenta suma suganta, amma tun sanda yakawota dayayiwa mami zancen zuwan, setace se'anyi auransu sannan zata je. Kuka sosai nakeyi Ina kara shigewa jikinsa. Dago kaina yayi yana lashe hawayen fuskata,cikin daddadar muryarsa me sanyi yace mun, "ya isa haka kukan kinji babyta, zanroki mami tabarki kije ko'asatinnanne,amma sekinyi shiru kindena kuka,banason ganin hawayenki, yana tabamun zuciya." Hadiye kukana nayi ina jan majina, nace "tonadena yaya,insha Allah" "yawwa amaryata,dakainama zankai gida yar gidan daddy" yafadi haka yanajan karan hancina. Murmushi nayi cikin jindadi, nama manta a inda muke, kuma akowanne lokaci mami zata iya shigowa. "Kaikuma dan gidan mami,amma yanzu mami tazama tawa na kwace maka" nakarasa zancen dayi masa gwalo. Bata fuska yayi, yace, "shine haddamun gwalo ko? Aikin kusa barin mamin kidawo gurina, senaga dama ma zanbarkima kizo kiganta" marairaicewa nayi cikin shagwaba nace, "to kayi hakuri badakai nake gwalonba dakainafa nake." Make kafada yayi kamar yaro yace, "um'um sekin bani wannan nasha yanzu" yakarasa zancen yana nuna kirjina da hannunsa..........✍️

*By*
*zeey kumurya & real farhana*
............waro idona nayi waje cike da mamakinsa kallonsa nayi naga yadagemun gira yana wani kashemun ido,mikewa zaune nayi ina fadin, "katashi dan Allah kar mami ta shigo ta ganmu ahaka." "To mene idan ta ganmu?" Ya tambaya yana tashi zaune. Kawar da zancen nayi nace, "ina auntynah,dafatan dai tananan lafiya kalau" sosai zee ta burgeshi data tambayi Rasheedah dan beyi tunanin zata tambayeta. Murmushi yayi yace,"tananan kalau tamace ingaisheki" "shine baka fadamunba seda natambaya" "aiduk ke kika mantar dani da wannan idanunnaki." "Hmmm" kawai nace ina kokarin sakkowa daga kan gadon. Janyoni jikinya yayi yace, "ina kuma zaki aibaki bani abunda nace kibani,zaki wani gudu nizakiyiwa wayo?" Marairaice fuska nayi nace, "bafa guduwa zanyiba fitsari nakeji" sakina yayi yana fadin "muje inrakaki,kiyi fitsarin" sauka nayi daga kan gadon nashige toilet da gudu na rufe kofar. Murmushi yayi kawai,yarinyar tana matukar burgesa komai nata mekyaune, gata daga gani akwaita da tsafta,lumshe idonsa yayi yanajin kamshinta daya game dakin. Fitowa nayi daga toilet din, naganshi zaune abakin gado,nina daukama yatafi. Zama nayi agefensa,dagowa yayi yana kallona,nuna kansa yayi da hannu,yace. "Nikikaiwa wayo ko,zankamakine zakizo hannuna." Dariya nayi kawai bance komaiba. Kallon agogon dake hannunsa yayi, dasauri ya mike danyasan zuwa yanzu kila Rasheedah tatashi. "Har 12, gaskiya nadade anan,bari na wuce gida." Mikewa nayi jikina a sanyaye,banason yatafi saboda yana matukar debemun kewa,yanzu idan yatafi tunane_tunane kawai zantayi. "Bakyaso intafi naga kincanza lokaci daya?" Kaina nadaga masa idona yacicciko da kwalla. "Yasalam! Mene na kuka kuma?" Bejira amsataba yajanyoni jikinsa yarungumeni tsam akirjinsa. Lumshe idona nayi ina kara manne masa, ahankali yakai hannu yanashafa gaban kaina dayafito waje. Kusan mintuna 3 munahaka, daga baya yarabani da jikinsa yana fadin, "kitakurawa mami da kuka zatakawomunke anjima" bata fuska nayi nace, "to aini banason binka,kawaidai banason katafine." Murmushi yayi kawai becemun komaiba, kissing lips dina yayi ya fice yanamun bye_bye. Wata doguwar ajiyar zuciya nasauke bayan ficewarsa, se kamshinsa kawai dayabarmun adakin....

Dakin mami Dr,yanufa danyi mata sallama da kuma batun zuwan zee gida. cike da mamaki mami take kallonsa bayan yashigo. "Mahmud,dama baka tafiba nadauka ai katafi tundazu. Zama yayi agefen gadon yana sosa kansa yace, "bantafiba mami se yanzu" "kai yaran zamani, ba kunya, ko kunyarta data mutanen falo bejiba yazo yashige gurin matarsa yazauna" mami ta fadi haka aranta. "Mami zainab tamun magana akan tanason zuwa gidan iyayenta,amma kinhanata meyasa?" Gyara zama mami tayi tace, "bahanata nayiba Mahmud,yanzu idan tatafi kasan sundade basuga junaba, riketa zasuyi seta Dade acan,amma idan tatare sukaji tana gidan mijinta zasu barta tadawo da wuri" "hakane mami,amma ai tare zamu tafi" "idan kuntafi taren,kabar Rasheedah a ina?" kawai ka bari Tatare din, kobayan wata biyu ne sekuje." "Shikenan mami,hakanma yayi amma ita wai inanema garinnasu?" Hararar wasa mami ta masa tace, "kaje katambayeta mana ai zata fada maka" murmushi yayi kawai ya mike, sallama yayiwa mami ya fice....

Seda yayi sallar azhar sannan ya koma gida, gidan yananan yanda ya barshi ko shara batayiba,ga kayan baccinsunan adaki ko kwashewa batayiba tana nade akan gado har lokacin,amma tatashi danse latse_latsen waya takeyi. Bece mata komaiba, ya kwashi kayannasu duk da yanajin tambayar datake masa akan ina yaje? Rigar yadin jikinsa yacire ya shige toilet, wanke kayan yayi tass sannan ya wanke toilet din. Dakansa yashare dakin dasuka kwana da falo,Dama bawani datti bane kawaidai shi bayason ganin datti kokadan. Amma yayiwa Rasheedah uzuri may be jikinnatane. Sedayagama komai sannan ya saurari Rasheedah, lallashinta yahauyi saboda karshe kuka tasamasa dontasan gurin zee yaje, dan abunda yakara tabbatar mata haka sauyin kamshin dataji ajikinsa. Wunin ranar babu abunda Rasheedah tayi, wankama se daf da la'asar tayi,bayan la'asar kuma yan'uwanta sukazo da kayanta da kuma gararta. Dama abincin rana mami ce ta'aiko musu dashi......

Hakadai rayuwa tayita tafiya,kullum se Dr,yazo munsha hirarmu me dadin gaske, duk da mitar dayake sha agurin mami akan zuwannasa. ayan kwanakin damukayi dashi nasaba dashi sosai. Yanda nake kallonsa Ashe bahaka yakeba. Miskikine shi nakarshe,amma idanyaso ya iya surutu. Gashi dabawa mutum abundariya,kuma idan kana zaune dashi zaka karu da abubuwa sosai.mami ta rarrasheni akan nahakura da zuwa gida harse na tare, haka nakura. Kullum se mami ta dirkamun abuwawa,amma ba masu cutarwaba masu amfani. Kayan fruits kuwa dama nadade kullum sune abincin darena. Gashi mami tahanani amfani da ruwan sanyi kokadan sedai na dumi, kuma safe da dana da dare, kullum senayi tsarki da tafasheshen ruwan lalle. Har lokacin mama dijee bata tafiba,tana cigaba da gyarani. Zuwa yanzu kam nikaina nasan na gyaru, dan har kasana nasan bakaramin matsewa nayiba. Tun washegarin dinner da daddare aka kawomun kayan lefena daga gidan yayar umma. Kayan sunyi kyau sosai,gasu kuma duk masu tsadane, takanas na karbi wayar mami nakirasa namasa godiya. Duk wani dabarun zaman aure mami tana koyamun, da yanda ake kula da gida, dayanda ake kula da miji da kishiya da yan'uwan miji. Gaskiya nikam bani davakin godiya ga wannan baiwar Allah,sedai namata fatan gamawa da duniya lafiya domin kuwa mami tagamamun komai a duniya, da uwa zatayiwa danta....
Chapter 36 · 0% Book details