← Book details Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 52

Sashe 51

Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

cikin farin ciki, ummi tadawo part dinta, dakin zee tashiga. Ina zaune ummi tashigo dakina,tana fadin,"Zainab!, kindade dayin wankane.?" "A'a ummi, yanzu dana tashi nayi." "Ohk tashi kiyi sallah kisauya kayan jikinki, kidakko wannan dinkin da'aka kawo miki jiya kizaba aciki kisaka. Da mamaki nake kallon ummi, "ummi, unguwa zamujene"?"Bansan yawan tambaya ki shirya kawai" ummi ta fadi haka tare da juyawa ta fice daga dakin. Bani da zabi banda bin umarnin ummi, toilet na shiga nadauro alwala. Ina idar da sallah na shirya cikin Wata atamfa super dinkin Riga da zani.hijabi na dora Wanda yashiga da atamfar na fita zuwa dakin ummi, bayan nafeshe jikina da dadadan turaruka,masu sanyin kamshi. Afalo muka hadu da ummi, ta sanarmun inje part din baki inada bako. "Ni kuma ummi, wanne bako, bayan da aurena" na tambayi ummi cikin mamaki. hararata ummi tayi tace, kiwuce kijeni, ainafiki sanin kina da auran" zankara magana ummi ta katseni ta nuna kofa kawai, alamun na fice. Cikin sanyi jiki nafara tafiya zuciyata nata tararrabin,wanne bako kuma nayi alhalin da aurena, to me ummi take shirinyine. Ahanya naci karo da idi, tare da twins,wadda ummi tatura adakkosu,domin subawa su Dr,guri. Bugun zuciyatane ya tsananta sanda na karaso part din. Cikin dauriya nabude kofar falon na shiga bakina dauke da sallama,kamshin danaji a falonne yasani dago kaina da sauri,ina kallon inda amon sautin daddadar muryarsa ke amsamun sallamata. Gabanane yayanke yafadi,dan banyi tunanin ganinsa nankusaba,saboda yanda na baroshi yadau zafi sosai akan lamarina. Murza idona nahauyi ganin yanufoni zuciyata na bugawa, atunanina mafarkan dana sabayi dashine. Bude idona nayi nagadai shidinne agabana, jikinane yadauki rawa nayi baya luuu zanfadi, dasauri Dr, yataroni nafada faffadan kirjinsa. Atare muka saki wasu tagwayen ajiyar zuciya,kamshin jikinsa dana shaka yasaukarmun wata nutsuwa, kallon cikin ido mukewa juna, kallon me cike da kauna, da dumbin sakonnin masoya. Amma bakunanmu sungaza furta komai saboda nauyin da harshikanmu suka mana. "Ashe dama zezo gareni nankusa, alokacin dabanyi tsammaniba, tabbas soyayya gaskiyace, kuma nasan shima kwanakinnan cikin tashin hankali yayi su,saboda yadda naga duk ya rame. gabadayanmu jikinmu yayi lakwas barinmani da kallonsa ya kashemun jiki gaba daya, kwallace ta cikomum idona,lumshe idannayi,ina dan fesar da numfashi,daga bakina,inajin yanda zuciyarsa ke bugawa. Rabani yayi daga jikinsa, Yakama hannuna muka zauna akan kujera. Cikin raunin murya yace, "Princes am sorry,na hukuntaki akan lefin dabaki da masaniya akai, na cutar dake,kiyafemun plsssss! Yanda yaja maganar seda tsigar jikina tatashi, tausayinsa yacikamun zuciya ganin hawaye na zuba daga cikin idonsa. Hannuna nakai nima ina hawayen,nafara goge masa nasa nace, "babu komai mijinah, namaka uzuri,komawaye yaga abunda kagani irin hukuncin daze dauka kenan" lumshe idonsa yayi cikin jin dadin kalamanta, ahankali yayi kasa da kansa, yasumbaci cikinta tare da fadin, "sorry twins dina,abbanku yamuku lefi, amma nayi kewarku sosai dafatan bakuyi fushiba,kun wahalarmun da love dita." Nidariyama yabani yanda yadage yana magana sekace da wani babban yake maganar. Shafa lallausan gashin kansa nahauyi, ina lumshe idona cikin tsananin farin cikin, ganinsa. Gaskiya farincikin danake ciki ahalin yanzu baze misaltuba. Jikawai nayi mutum yajanyoni jikinsa, ahankali na bude idona ina kallonsa, shima kallonnawa yakeyi. "Love nagake,korama bakiyiba hankalinki kwance,sema kyau da kika kara,nikadai nayi kewarki kenan." Banbashi amsaba,sebakina dana hade da nasa,danyanda yake magana bakaramin tsumani yakeba. Abunnema yasamu dama ankwana biyu ba'ahaduba, nanfa Dr, yahau yamutsata, cikin salonsa me tsayawa mutum,arai. Itama zee yau salon datake masa kokarin zautar dashi yake. Seda zee taga yana kokarin wuce gona da iri, sannan kwace kanta tana maida numfashi. Dr,bece mata komaiba domin shima yasan gurin dasuke bedace suyi sex ba. Kusan 3 minutes suna maida numfashi, kafin zee tayi karfin halin kama hannunsa,zuwa dinning. Dantasan halinsa dakyar inyaci abinci. Dakanta tayi serving dinsa, takuma bashi abincin abaki cikin salon soyyarta. Yanaci yana bata labarin abunda yafaru bayan barinta gidansa, sosai zee tayi mamaki da sunan taly yafito, tarasa meta tsarewa taly arayuwa, tayi auranma amma bazata barta ta hutaba. Hirarsu suka cigaba dayi cikin tsananin farinciki da annashuwa,walwala da jindadi.......

*************

Rasheedah seda tagama gunjin kukanta,sannan ta kwashi kayanta a trolly tayi gida, tana kuka tasanar da mahaifiyarta abunda yafaru, kozama bata bari tayiba tatasa keyarta zuwa gidansu Mahmud,Allah yasoma malam befitaba, tijara tahauyi da bala'i,agidan wai ita Mahmud ze wulakanta yasakarmata ya, babu Wanda yace mata kanzil hartagama,har umma kuwa. Sedatagama malam.yadubi Rasheedah yace ta fada masa gaskiyar abunda yafaru, har Mahmud yasaketa. Rasheedah duk dan arangwanta mata ta fadi gaskiyar duk abunda ta kulla tana kuka. Salati kowa dake gurin yadauka,dansu seyanzuma sukasan zee bata gidan Mahmud.hajiya kaka tayo kanta da masifa da zagi. Dakyar malam.yasata tayi shiru, yakumace shi babu abunda zece game da wannan lamari se'abunda Mahmud yace, tunda shi tayiwa lefi kuma shi zezauna da ita. Kiran wayarsa malam yayi amma taki shiga. Sedaga baya dasukayi waya da mamine tasanarmasa inda Mahmud yatafi. Hakuri yabawa maman Rasheedah, akan su jira dawowar Mahmud se'asan abunyi. Itakam umma Allah wadai tayi da halin yar'uwarta dana rasheseedah, tayi datasanin hada auranta da Mahmud. Shukura kuwa har kukan tausayin zee tayi,dataji abunda ya faru.....

******************

Daddyma daya dawo yaji matukar dadin ganin Dr, kuma yayi farinciki. Sungaisa cikin girmamawa da farinciki, sunsha hira sosai, tun Dr, yana sunsunne kai hardai ya ware ya saki jikinsa. Sunkuma tattauna akan abunda yafaru cikin fahimtar juna. Fadar iri karramawa da girmamawar da akayiwa Dr agidansu zee bata bakine. Anan Dr, ya kwana a part din baki, zee harta kwanta adakinta ummi ta korata gurinsa. Ranar kam Dr, yadirjeta,sedatasa masa kuka wiwi sannan ya barta ta sarara. Tarairayarta yake tamkar kwai, soyayya yake nunamata zallarta tare da tsantsar kauna me tsayawa mutum arai, me wuyar mantawa a zuciyar dan'adam.

Washegari gari Daddy yace dole su shirya su tafi zuwa kano, ummi taso su kara kwana 2 amma daddy yace,jiranme zasiyi, su tafi gidansu kawai. Tare suka tafi dukansu,a gidan malam,sukayada zango. Anmusu tarba irin ta bangirma,kowa se girmama juna akeyi, hajiya kaka kamar tayiwa daddy sujjada, saboda girmamawa. Itakam ummi, burinta kawai taga mami ta mata godiyar abunda ta mata. Seyamma sukaje gidan mami, nanma sunsamu tarba taban girma, dama mami tasan da zuwansu. Sosai ummi da daddy sukayiwa kawu da mami godiya,akan rikon dasukayiwa zee. Se dare suka koma gidan malam. Zee kuwa tana gidan mami se'angyara mata gidanta gobe zata koma. A washegari daddy yagabatar musu, da kyaututtukan dayayi niyyar basu, ya bawa Dr, wani katoton gidansa dake nan kano, a unguwar tarauni, tare da alkawarin gina masa clinic, da kyautar kujerar hajji da makudan kudi. Su malam ma, dasu mami,hajiya kaka,umma,kawu harsu shukura ba'abarsu abayaba, duk yahada yabiya musu hajji da umra, hatta da dr,kabeer datasa kyautar shima. ummi ma tayiwa kowa kyauta ta bajinta musammanma mami. Godiyakam sunshata ba'adadi hajiya kaka harda kuka,kamar bata taba zuwa makkaba. Gidan da daddy yabawa Dr, agyare yake damutanema aciki suna haya, wani gidan yasauyamusu,aka kara yiwa gidan kwaskwarima,su zee suka koma. Kyawun gidan da tsaruwar gidan baze faduba,ku kiyasta kawai da kanku. Komai najindadin rayuwa akwaishi agidan, lokacin dasuka koma cikin zee yashiga Wata na hudu.
Chapter 51 · 0% Book details