← Book details Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 52

Sashe 35

Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

.............Tafi gurin yakara dauka da dariyar mutane,kunyace ta kamani, sakin fuskartasa nayi ina boye kaina akirjinsa. Kiss yasakarmun agoshina yasa hannayensa yana shafa bayana. Rasheedakam takai karshe a kuluwa,se hararar zee take aranta tana cewa, "dama ansaba karuwanci ai dole." Karasowar su mami gurin yasashi sakina. Hotuna muka shigayi da su mami da shukura,itama yan gidansu sunzo anyi dasu, harda mamanta daduk dagowar dazayi semun hada ido,amma umma batazoba. Hakadai akacigaba da shagali har wajen karfe goma. Goma saura aka tashi saboda aranarne za'akai Rasheedah gidanta, kuma daga gurin dinner za'awuce. Nidai ina makale dashi yaki sakina,mami tace inzo mutafi gida amma yahana yace mata shize kawoni. Itama Rasheedah tana nane dashi itama,tace tunda be dakkotaba toshi zemaidata gida. Murmushi Dr,Mahmud yayi ganin yanda Rasheedah take cika tana batsewa,kuma tunda sukazo babu wadda tayiwa yar'uwarta magana,se dan dole da m.c yasasu gaisawa. Aransa yace, "duka zan iya daku ai,kowacce nasan tayanda zan iya da ita." Munzo zamushiga mota ganin tayi sauri ta shige se nace masa, "yaya ni bari naje yaya kabeer yamaida ni gida" wata uwar harara ya zabgamun yashige mota, tsayawa nayi abakin motar naki shiga, leko da kansa yayi yace mun, "zaki shigo kosena fito nashigo dake,kina batamun lokani ni." Cikin kakkausar murya yayi maganar. Hakan yasa na shiga ina turo baki gaba,ina kunkuni. Yanzu babu shukura tabi yan'uwanta sun tafi gida. Wanda yakawomu dazu yanzuma shize maidamu gida. Tunda muka fara tafiya, Rasheedah take ta masa zance kasa_kasa tana wani mammanne masa, shikuma sebiyemata yakeyi. Wani abune yazo yatokaremun akirji, nifa Dama shiyasa nace bazantafi tare dasuba,saboda na lura bazamu shirya da itaba danko.....dariyar danaji tasakice kamar ba maceba tadawo dani daga duniyar dana tafi, tsaki naja Wanda bansan sanda yafitoba. Ahankali yaji yakamo hannuna acikin hannunsa,cikin jin haushin dabansan dalilinsaba nasa hannuna na muntsinni hannunnasa,dasauri yajanye hannunsa daga nawa,amma bejuyo ya kalleniba. Iya kuluwa kam yau na kulu a tafiyarnan saboda nikaina nasan inada matsanancin kishi dukda banasonsa amma ai mijinane dole naji kishinsa. Har cikin gidansu mukashiga muka sauketa, dakyar ta sauka tanata zuba karairaya kamar ba yanzu za'akaita gidansaba,ko kunyar abokinsa bataji.

Juyawa mukayi muka fice daga gidan bayan tasauka,jingina bayana nayi ajikin kujera tare da lumshe idona,bacci nakeji sosai,ga tarin gajiya ajikina.Ahankali naji yajanyo jikinsa,ya rungumenu, luf nayi ina shakar kamshinsa,cikin mintuna kalilan bacci yadaukeni. Murmushi yayi jin saukar numfashinta alamun bacci yadauketa. Yasan Dama dagajiya, shikansa daze samu Dama baccin zeyi. Gyaramata kwanciya yayi ajikinsa yanda zataji dadin barcin. Jinayi kawai ana girgizani da sauri na bude idona, dake cike da bacci. "Muje naraki ciki,karki fadi ahanya garin magagi,sarkin bacci kawai." Lumshe idona nayi,kawai bance komaiba. Da kansa ya bude mun murfin motar kama hannuna yayi har bakin kofar,falo yakaini,sannan yatasaya yanamun sallama. Harna juya zantafi sekuma natsaya cak,saboda tunawa danayi yanzufa gurin wata zashi,dama ga takaicinsu dasuka kunsamun ahanya. Juyowa nayi ina kallonsa,naga shima niyake kallo betafiba. Hannu kawai nadaga masa alamar bye_bye nashige ciki,saboda baccin dake cina. Yau gidan ba mutane sosai,duk an watse, se yan'uwan mami najiki. Dakina nashiga,daurewa nayi na watsa ruwa,tare da dauro alwala. Inayin sallar isha'i nabi lafiyar gado.......

******************

Taly ce zaune a falon ta misalin goma dayan mintuna nadare, ta mike kafa joeboy yana mata tausa ita kuma se faman latsa waya takeyi,tana taunar cingum kas_kas. Knocking din kofar falon akayi, umarni ta bayar ashigo. Wata kawartace safna,ta shigo. Joeboy dake duke tamkar sabon bawa,yanawa taly tausa,yana ganin tashigo ya mike yayi ciki,dama yagaji. Yanzu taly tamaidashi tamkar wani yaronta, se'abunda tace yayi shiyakeyi kuma baya iya mata musu, ga kewar zee da tunaninta daya addabi rayuwarsa hakan yasa duk yabi ya lalace. "Safna kece agidannawa yau da darennan" zama safnah tayi tanabin taly da kallo tace, "hajiya taly manyan gari,manyan mata irin wannan daula haka dakike ciki,ga hadadden guy" murmusawa taly tayi tace, "toyaza'ayi safna ai ita rayuwarnan gwara kaji dadinka,kaci lokacinka ka wataya." "Gaskiyane babbar yarinya, dama wani abu nazo na nuna miki," safna tafadi haka tana dakko wayarta daga cikin jakarta." Cike da son Karin bayani,taly tace, "menene safnah?" Batare data bata amsaba ta mika mata wayartata. Karba taly tayi tana dubawa, murza idonta tayi danta kara tabbatar da'abun datagani. Videon su zee ne,lokacin dasuke shigowa gurin biki da kuma Wanda suke yanka cake sekuma hotunansu kala_kala. "Kutmar..........taly ta lailayo wani uban ashar tana mikewa tsaye, da sauri safna ta cabki wayarta da taly ta saki, Allah yasota batakai kasaba. "Safna dan Allah abunda idona yaganemun daidaine,ko nice bangani daidaiba.?" Girgiza mata kai kawai safna tayi. Cikin karaji zee tace, safnah ina kikasamo wannan picks din,?" Mikewa safna tayi tana fadin,"gashinan yanata yawo a social media nayi mamakima dabaki ganiba" "kaiii bazeyiyuba gaskiya wannan ba zee bace,sedai mekama da ita. Saboda nasan mijin, Dr, ne, A aminu kano babu tayadda za'ayi ya auri zee" tabe baki safnah tayi tace, "nidai zan wuce,amma tabbas kam babu tantama wannan zee ce" dafe kai taly tayi cike da takaici wani bakin ciki da hassana ya turnuke mata zuciya. Cikin hanzari ta dauki wayarta dake kan kujera ta kunna data,domin rabonta da online tun yamma tanata kallon BF dinta. Instagram ta shiga dayake tayi following din Dr,kabeer post dinshi nayau ta duba, taga beyi posting photo ko dayaba,na auran. Harzata fita sekuma taga wasu sunyi posting din hotunan, bata yardaba seda ta shiga face book tagani,ga hotunannan da video ga kuma sunayensu ansaka, tabbas babu shakka zee ce, tayi aure da wannan Dr, din Wanda taly tadade tana mafarkin yazamto mijinta. Cillar da wayartata tayi tafara zarya a falon se uban gumi take tamkar ansata a tanda. "Meyasa zee tafita sa'ane a duniya,meyasa komai tayi burin samunsa se zee tarigata samu, tayaya akayi zee ta auri wannan kyakkyawan guy din?" Cikin ranta take wannan maganar. A fili ta furta, "wlh bazeyiyuba bazeyiyu kiyi aure ki barniba zee!!! Wlh senayi sanadin tarwatsa wannan aurannaki, wlh bazaki shiryu kibarniba,ni wannan Dr yadace yaxama majina bakeba zee!" Cikin karaji da daga murya take magana. Wanda tasa joeboy datun dazu yake jin maganarta kamar afusace yafito daga daki da gudu jin kalamanta nayanzu dasuka kusa tarwatsa kwakwalwarsa..........

****************

Murmushi Dr,yayi bayan zee tashige yanajin tamkar karya tafi ya barta, ga sonta dayake ninkuwa aransa. Ahankali ya juya yakoma mota. Ko gida bekoma direct gurin masu saida chicken yanufa yasai musu, tare da yuoghurt. Kiransa su Dr, kabeer sukaitayi akan zasuyi masa rakiyar ango, amma ya kanne idonsa yace baya bukatar rakiyar kowa. Seda 11 ta wuce yaje gidannasa. Danyasan zuwa lokacin ankai Rasheedah.

Rasheedah ce asama, zee kuma itace akasa hakan yasashi nufar saman,babu kowa duk an watse. Dakin Rasheedah yashiga da sallama. Rasheedah dake kwance ta mike zaune jin sallamarsa,fuskarta dauke da fara'a babu alamun kuka a idonta,ta amsa masa. Zama yayi akusa da ita cikin matsanananciyar gajiya. Kallon Rasheedah yayi tare da shafa kumatunta, yace, "Amarya" cikin tsananin jindadi tace, "na'am angona" "kinyi kyau sosai" murmushi tayi cikin jin dadi. mikewa yayi yana fadin "nagaji sosaifa yau bari nadan watsa ruwa kozanji dadin jikina." Toilet yashige yayi wanka da sauran uzurirrika, jallabiya yasaka yatada sallah. Rasheedah tana ganin yafito tashige toilet din itama domin yin wanka...

Bayan sun idar da sallah gaba dayansu, ya umarceta tatashi su kara raka'a biyu. Addu'a yayi musu sosai akan Allah yakade musu fitintinu a aurannasu. Kanta yadafa yayi mata addu'a kamar yadda addini ya koyar. Itama ya umarceta data masa, amma seta kasa. Karanta mata yashiga yi ita kuma tana maimaitawa. Tambayoyi yamata akan addini, wasu ta amsa daidai wasu kuma takasa. Jinjina kansa kawai yakeyi,aransa yana cewa lallai seya dage da karantar da Rasheedah saboda bata da wani ishashshen ilimin addini. Dakansa yaciyar da ita,kazar. Aikuwa taci sosai,dan dama yunwa takeji, hidima bata barta taci abinba. Gadon dakinnata yahaye idonsa cike da bacci, addu'ar bacci yakaranta ya kwanta. Rasheedah kuwa gaban mudubi aka tsaya anata shafe_shafen turaruka,wata shegiyar rigar bacci ce ajikinta. Kashe light din dakin tayi ta haye gadon, jikinsa ta fada batare da tunanin komaiba tafara masa salon datasan ze rikitar dashi, duk yanda yaso kin biye mata amma yakasa saboda gunduma gunduman salon datake masa tamkar ba budurwaba, dole duk namiji me lafiya seyaji sauyi ajikinsa. Aikuwa yasauke mata tuzurantakarshi adaren yau, tagane shayi ruwane, harda mugunta yahada mata tunda tahanashi bacci, kuma ita takawo kanta......

Tunda na kwanta banfarkaba seda asuba,shima dakyar natashi nayi sallah. Koda na idar da sallar bankoma bacciba alkur'ani megirma na dakko nafara karantawa. Seda gari yayi haske sannaya na tsaya. Dakina na gyara tare da wanke toilet. Falo na fita babu kowa duk suna daki, nikam gajiyar jikina gabadaya ta barni,tunda nayi bacci. Kitchen na nufa domin hada breakfast kamar kullum danasaba. Ruwan tea nafara dorawa sannan na hau ferayar Dankali. Harna gama hada komai babu Wanda yafito duk da naji kukan yara alamun suntashi. Dakina na koma nayi wanka,zama nayi a bakin gado Ina tunanin Dr, sosai naji Ina kewarsa, wani abune yatokaremun kirji dana tuna yanzu yanacan tare da wata,kilama ya manta dani..
Chapter 35 · 0% Book details