← Book details Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 52

Sashe 24

Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

****************

Cikin Daren jiya taly ta farka,da ihu ta farka cikin dashashshiyar muryarta tana fadin. "Ku taimakeni,zata kasheni,zata kasheni wayyyooo!! Dasauri joeboy da gyangyadi ya fara daukarsa ya mike yafice ya nufi office din likita yana sanar musu ta farfado.Cikin sauri suka taho suka bata taimakon gaggawa,allurar bacci suka kara mata.ansamu ta farfado cikin hayyacinta,sedai fa ta zubar da jini da yawa dan haka yanzu za'a mata Karin jini.andauki jinin joeboy za'a gwada kozeyi daidai da nata.........

Da kansa Dr Mahmud yadawo gidan mami ya musu bayanin itace zee.mamaki da al'ajabine ya cika zukatansu.shukura aranta tace,"lallai dole yayanta ya rude akan wannan baiwar Allah domin takai kowanne namiji yasota,sedai kawai ace kyan haline babu,Wanda wannan kuma kaddarartace. Se kusan 12 zee ta farka,a lokacin Dr baya gidan yakara fita.bin dakin datake tafarayi da kallo, yunkurin mikewa tayi saboda batasan inane nanba,shukura dake gefenta se lokacin ta Ankara da farkawartata.da sauri ta riketa tana jera mata sannu,filo tasa mata abaya,ta jinginar da ita.kallo daya zee tamata, taji zucuyarta ta buga saboda tsananin kamar dataga sunayi ita da Dr.Mahmud.to mehadata dasu,meyakawota gurinsu? Tambayar datake yiwa kanta kenan.ficewa shukura tayi daga dakin,bin bayanta kawai tayi da kallo tana kara karewa dakin kallo.hannunta ta kalla taga abun karin ruwa a hannun,takasa tuno abunda ya faru da ita,tundaga lokacin data ganshi a gidanta.tare da wata kyakkyawar mata taga sun kara dawowa.sannu mami ta fara jerawa zee,dakai kawai ta amsa mata.kamata shukura tayi zuwa toilet,brush ta bata tayi da wani sabon brush.sannan ta kara taimaka mata ta dawo dakin,zama tayi a bakin gado tana maida numfashi.wani irin sukuku takeji ajikinta,tamkar ba itaba.tunanin gidansu da iyayenta ne ya cunkus acikin zuciyarta.tabbas akwai abunda yake faruwa da ita.tea me kauri shukura ta hada mata ta bata,batayi musuba ta karba,saboda azababbiyar yunwar datake ji,sosai tasha ruwan tea din.kadan ta rage.kallonta kawai sukeyi cike da tausayawa.ruwan wanka me dumi mami ta hada mata da kanta,tace taje tayi wanka.

*AFTER TWO HOURS*

Zee,tayi wankanta taci abinci Wanda shukura ta dafa.hakan yakara dawo da ita hayyacinta da nutsuwarta.mami ta bata wata doguwar Riga da hijabi irin karaminnan,Wanda yake tsayawa iya wuya.masha Allah kawai mami da shukura suka ce,saboda se alokacinne ainihin kyawun zee yakara fitowa.adan awanni da zee tayi dasu mami,sun matukar burgeta lokaci daya suka shiga ranta.saboda yanda taga suna kula da ita.da nan_nan da ita.alhalin yau ne kawai suka taba ganinta arayuwarsu.bata tambayesu meyakawota nanba,suma kuma basu fada mataba.suna zaune a falo dukansu,bayan su mami sunyi sallah, ta dubi zee tace, "zainab idan bazakidamuba dan Allah inason jin tarihin rayuwarki.rass gaban zee yayanke ya fadi,sunkuyar da kanta tayi kasa,kwalla na cika mata idanu,bazata iya kinbawa mami labarintaba,saboda matar ta mata, haka kawai taji ta shiga ranta.wani gwauron numfashi taja,batare data dago kantaba tace, *sunana zainab Ahmad dan gaske* dasauri mami da shukura suka kalli juna cike da tsantsar mamakin jin sunan da zainab ta ambata.(Alh.ahamad dan gaske,shahararren dan kasuwane,kuma babban me kudi.sanannene a kasarnan dama sauran kasashe,dalilin dayasa mami da shukura mamaki kenan) "Nasan tabbas dama zakuyi mamakin jin cewa ni yarsace,amma idan na Baku labarin komai yadda yake zaku gasgatani.dagowa zee tayi tana share kwallar data zubo mata,taci gaba da basu labarinta.....

*****************

Ni kadaice,Allah ya'azurta mahaifina da mahaifiyata a duniyarnan.mahaifiyata itace mace ta biyu a gurin mahaifina.mahaifina ya Dade da auran uwargidansa haj.saratu wadda nake cemata mommy.sunfi shekara 10 da aure,amma Allah bebasu haihuwaba,sunyi Neman magani gari_gari,kasa_kasa Amma Allah bebasu haihuwaba.

Haka yan'uwan mahaifina suka takuramasa akan seya kara aure,koze samu haihuwa.amma yaki.tunda yace shi matarsa tana masa komai babu abunda tarageshi dashi.dakyar suka shawo kansa suka aura masa mahaifiyata,wadda takasance cousin dinsace.zaman lafiya ne yake gudana tsakanin mahaifiyata da mommy.sun hade Kansu zamansu gwanin sha'awa.cikin ikon Allah Sega mahaifiyata da ciki,murna agurin iyalan gidan kamar me.mommy jitakeyi da cikin kamar me,tamkar ita ta sameshi.ta hana mahaifiyata yin komai,ita takeyi.duk zigar da mutane data kawayenta amma mommy ta toshe kunnanta.

Haka suka cigaba da rainon cikin,cikin tattali da doki.amma Allah beyi cikin zezo duniyaba,befi wata uku ba ya bare.bakin cikin da su mahaifina suka shiga baze misaltuba.mommy kam harda kwanciya a asibiti.hakadai suka hakura suka fawwalawa Allah.bayan wasu watanni ta kara samun wani ciki,shima kamar wancan bewani jimaba ya kara zubewa.hakadai mahaifiyata tai tayi har sau biyar.nanfa hankalin mommy da dadddy na,yakara tashi.suka shiga nemarwa mahaifiyata magani,amma duk inda suka je,se'ace musu lafiya kalau take kawaidai daga Allah ne.haka suka hakura suka mikawa Allah komai.seda ta Dade dan takai shekara biyu sannan ta kara samun ciki. Da kanta ta gane ciki ne da ita,setaja bakinta tayi shiru ko mahaifina bata fadawaba,taita rainon abunta ita kadai.

Seda cikinta yakai wata hudu sannan,ya bayyana shima wani zazzabi tayi me zafi tamkar zata mutu. Da'akaita asibiti shine aka gane tana ciki ne.basuyi wani dokinsaba,Dan sunyi zaton shima zubewa zeyi.duk da dai mahaifina yasa ana masa rokon Allah,itama mahaifiyata haka ta dage da addu'a.cikin ikon Allah cikin be zubeba,ya tsaya har ya tsufa.farin ciki kamar me,daki guda mahaifina ya dinga cikawa da kayan babes kamar me. Komai yagani na jaririrai seya kawo ya jibge,saboda doki.

Cikin ikon Allah,mahaifiyata ta haifeni lafiya kalau.farin cikin da mahaifana suka yi baze misaltuba. Kowa yana tayasu murna da farin ciki. Haka mahaifina yayi ta rabon kudi saboda murnar samun zuri'a.a lokacin yake jinsa cikakken mutum.shima ya zama baba,a yanda yake bani labari har kuka yayi saboda murna. Tun a lokacin yamun huduba da suna zainab.........

Na taso cikin soyayya da kulawar iyaye,yar gatace ni ta gaban kwatance.iyayena suna nunamun soyayya sosai.amma hakan besa sun kasa bani kyakkyawar tarbiyyaba.mutane da yawa basa tantance wacece mahaifiyata tsakanin mommy da Ammina.kowacce acikinsu jitake dani.kuma daga kaina mahaifiyata bata kara samun cikiba.mahaifina kuwa yadda yake kaunata baze misaltuba. gani da farin jini,kowa kaunata yakeyi yan'uwa da abokan arziki. Bani da hayaniya sosai,hasalima ni cikakkiyar miskilace.gani da nutsuwa da hankali da kaifin tunani,da addini kamar yanda kowa yakefada.wata rana a lokacin ina da shekara goma sha shida.nadawo daga school.............

*BY*
*zeey kumurya &real farhana*

.......mommy,da ummina duka suna zaune a falo.harma da daddy.cikin murna na karasa jikinsu ina hugging dinsu daya bayan daya. "Princess dinta yau kin dadefa a school,dafatan dai lafiya. Daddy ya jehomun tambaya,bayan na zauna akusa dashi. Dan karamin hijabin jikina na cire nace. "Daddy senior class dinmune yau sukayi candy, shine muka tsaya,sunyi celebrated ne. "Gashi ke kuma zainab da son harkar casu ko? Ummina tafadi haka tana murmushi. Nima murmushin nayi. Mommy ce,tace. "Aida gaskiyarta gwara ta cashe abunta. "Yawwa mommy nah,fada matadai. Maida hankalina nayi ga daddy nace, "Daddy,kaga muma next year zamuyi candy, pls daddy idan nayi candy, zaka kaini waje nayi karatu. Shiru daddy yayi,na wasu sakanni kafin daga baya ya numfasa yace. "Princess meyasa kikeson karatu a waje. "Daddy kawai,ni tun ina karama burina kenan,kuma kaga karatun can yafi nanan kasar qualities sosai. Shafa kaina daddy yayi yace. "Hakane princess.amma gaskiya ni bazan kaiki karatu wajeba,saboda ke kadaice dani.bazanso naga kinyi nesa daniba,saboda kekadai nake gani naji sanyi araina.kizabi duka school din da kikesu a fadin garin abuja,zankaiki amma banda kasar waje. Turo bakina nayi cikin fushi na dauki hang bag dina,na shige dakina. "Haba Alh. yazakayi mata haka,kasanfa ita yarinyace abunda takeso kawai tasani,Mommy ta fadi haka cikin rashin jin dadi. "Haba hajiya yakamata kigane meyasa na hana princess zuwa kasar waje karatu,kinsanfa ita kadai Allah ya bani,banason tayi nesa dani kokuma wani Abu ya gurbata rayuwarta. "Da gaskiyarka alh.nima banga lefinkaba.gwara tayi zamanta akusa damu.ummina ta fadi haka.

Tunda na koma daki na cillar da jakata,nafada kan gado nafara kuka.yanzu duk burin danaci akan nayi karatu a waje.Ashe bazanyiba,kawayena duk zasu tafi su barni.wata zuciyarce tacemun,haba zainab kiyiwa mahaifinki adalci mana,komai kika nema yana miki,komai wahalarsa,tunda kikaga be mikiba yanada kwakkwarar hujja. Share hawayena nayi na fawwala Allah, araina nace haka Allah yayi bazaniba na hakura.mikewa nayi na cire uniform dina na daura towel na shiga wanka.nariga na hakura da maganar wani karatu a waje,nama cire zancen daga raina.amma mommy ta shiga ta fita,tayita zugani,ai daddy yana da kudin daze kaini waje,kawai begadama bane.tun bana daukar zugarta harna ta dawomun da ra'ayin abun araina.nannaita bori ina tada hankali akannifa yabarni naje waje karatu.ummi kuwa banda fada babu abunda takemun.abunda bata taba yiba hardukana tayi.abunka da yarinta sena dinga cewa ummi,bata sona mommy ce kawai take kaunata. Ganin yanda natada hankalina,haka daddy badan yasoba ya yarda ze turani waje karatu.ranar daya fadamun tamkar na zuba ruwa akasa don murna. Ummi tayita fada,mommy kuwa tare mukayita murna.tundaga time din mommy tafaramun siyayyar kayan tafiya muna Tarawa.ummi dai sedai ta kallemu tatabe baki. Wani Abu mommy take bani kullum,kamar rubutu wai maganin tsarine da kariya akan tafiyar dazanyi.batare da tunanin komaiba nakesha,saboda mommy tamkar ruwa take agareni.ita da ummi duk kallon matsayi daya nake musu.

Lokacin danayi candy,har dan karamin party daddy na yahadamun,kuma naji dadinsa sosai.saboda suprise yamun.Tundaga time din nafara shirye_shiryen tafiya waje karatu.se yawon zaga yan uwa ina musu sallama. Har zuwa lokacin da WAEC dinmu ta fito.Alhamdulillah result dina yayi kyau sosai.nanfa shirin tafiya ya kara bada himma.anmun visa anmun komai tafiya kawai nake jira. Ana washegarin zantafi kawai na tsinci kaina a wani irin yanayi,gabana ya dinga faduwa.kuka kawai na zauna inayi,saboda nayi tunanin kewace take damuna.mommy ma haka tayita kuka,daddy ma kamar zeyi kuka jikinsa duka a sanyaye. Ummina kuwa macece me dauriya amma kana kallonta Kasan itama tana cikin damuwa.gaba daya ranar gidan babu dadi,kamar an mana mutuwa.jinakeyi dama na fasa tafiyar. Hakadai muka wuni jigum_jigum. Harna samu mommy ina kuka nace mata na fasa,amma mommy tacemun dama haka zanci amma daga baya zan ware na saba. Dadaddare wajen 11 harna fara bacci, mommy ta shigo ta tasheni. Wani Abu ta bani acikin Kofi,Wanda saboda baccin dayake kaina bazance gashiba.nidai nasan nasha na koma bacci.
Chapter 24 · 0% Book details