Sashe 22
Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun kafin magriba zee take bacci har'akayi magriba bata tashiba.ahankali ta fara bude idonta tana karewa falonnata kallo,idanuwantane suka sauka akan fareeda dake zaune agefenta tana mata firfita. "Sannu zee kin tashi" dasauri zee ta mike zaune,abunda ya faru ya fara dawo mata cikin kwanyarta. Dafe kanta tajeyi saboda Sara matan dayayi.kallon fareeda tayi cikin marainiyar murya tace"fareedah,dan Allah kice mafarki nayi abunda nagani bagaskiya bane pls fareedah.!? Takarasa zancen hawaye na bin kuncinta. Kara rikicewa fareedah tayi,domin tunda take da zee bata taba ganin tana kukaba. "Banganeba zee,me kike magana akaine nifa yanzu naxo nasameki ahaka. Cikin kuka zee tafara magana. "dagaske ne,ba mafarki nayiba.taly taci amanata taci amanar kaunar danake mata,ta bani kunya da mamaki bantaba tunanin zatamun hakaba.
"Wai me talyn ta mikine,nifa kara rikitani kawai kikeyi zee,kifadamun mana. Kuka kawai zee ta cigaba dayi,me tsuma zuciya batare data cewa fareedah komaiba.rungumeta fareedah tayi ajikinta,duk da batasan meyafaruba amma zee ta bata tausayi sosai. Rarrashinta tafarayi, "Haba zee,kukan na menene,kiyi hakuri dan Allah, karkijawo wakanki wani ciwon,dama ke ba cikakkiyar lafiyaba. Dagowa zee tayi,tare da janye jikinta daga jikin fareedah,fuskarta sharkaf da hawaye da majina ta fara magana."dole inyi Kuka fareedah,kozanji sanyi araina,wadanda na yarda dasu na basu amanar rayuwata, nake zaune dasu,suna kama da idanuwa suna ha'intata.fareedah Ashe dama abunda kike fadamun gaskiyane,taly da joeboy suna cin aman......kukane yaci karfinta ta kasa karasawa. Kuka takeyi me ban tausayi.fareedah batayi yunkurin hanataba domin ta gano inda zancen yadosa.seda tayi me isarta sannan tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya akai_akai. Cikin tausayawa fareedah ta dubeta tace."to ke tayaya kika gansu,meyakaiki inda suke? Majina zee tasha,ta hadiye wani yawu me daci ta bawa fareedah labarin duka abunda yafaru.ta kara da cewa. "Bantaba jin tsanar rayuwar barikiba irinta yau,tabbas fareedah *bariki ba riba* kokadan acikinta sema faduwa.nayi kuskuren yarda da joeboy,bantaba zaton zemun hakaba arayuwata.cin amanarma yarasa da wanda zemun seda aminiyata.shiru zee tayi tana sauke numfashi,akai _akai. hawayenma yadena zubowa,ta koma kukan zuci. "Kiyi hakuri zee...."hakurin me zanyi fareedah,na tsani taly tsana me tsanani, na tsani joeboy.tsanarsu ta mamaye gurbin kaunar danake musu araina.yanda nakejin zafi da kuna araina,daza'abani bindiga wlh sena harbe taly da joeboy! Ta fadi hakan cikin karaji. Dasauri fareeda ta karasa jikinta tare da rufe mata baki. "Kidena anbaton kisa zee,ki kyalesu kawai kibarsu da halinsu. "Hmmm" kawai zee tace,saboda ita kadai tasan irin abunda takeji aranta. Se bayan isha'i fareedah tatafi daga gidan zee,bayan ta lallameta sosai tare da kwantar mata da hankali.........
*************
Dakyar likitocin hotel din suka yadda zasu duba taly,domin da cewa sukayi se'ankira jami'an tsaro,seda security suka saka baki sannan suka fara dubata. Likitoci sun rufu akanta,dakyar suka samu numfashinta yadawo dai_dai. Bandeji sukasa suka nade mata kanta gaba daya,bayan sunyi treatment din ciwukan dataki. Gabanta kuwa seda suka wanke mata shi,da ruwan magani,sannan suka barbada mata magani agurin danya kame.
Joeboy daketa kaikawo a harabar clinic din,ganin likitocin sun fito yasashi tunkararsu yana tambayarsu ta farfado,wani likitane yace masa yabiyosa office dinsa.bayan sun zauna yadubi joeboy yace"Agaskiya anbuga mata kanta sosai,Wanda idan ba'ayi wasaba zata iya loosing memory dinta,sannan kuma gabantama yayi rauni sosai,anbuga mata Abu kuma yatabo har ciki,shima zata iya yiyuwama se'anmata aiki. Amma dai yanzu munfi bukatar ta farfado semusan abunyi.Wata zuface ta fara yankowa joeboy duk da fankar dake kadawa a office din. "To..to..shi..kenan.do..ctor na..gode,yanzu ..zan iya ganinta. Ya fadi hakan cikin rawar murya saboda tsabar kaduwa. "Eh,zaka iya ganinta,amma mun mata allurar bacci. Mikewa yayi yace. "Bari naje naga jikintana Dr. "Ohk,to Allah ya kara sauki.
Tana kwance akan gadon tamkar gawa,karasawa yayi gaban gadon yana kallonta,gaba daya ta canza kamanni,fuskarta ta kumbura tayi suntum,gaba daya tayi muni.kasanta ya kalla,inda akasa wani Dan kyalle aka rufe,da sauri ya dauke kansa saboda gurin bakyan gani yayi jaga_jaga da jini kamar ta kone. Zama yayi ya rafka uban tagumi,zuciyarsa cike da zullumi......
**************
Numfashi Dr.Mahmud yaja yace. "Mami banajin Abba,ze ki amincewa Saidai hajiya kaka da umma sune nasan se'ankai ruwa rana.ballema umma dama fushi takeyi dani,akan nace banason Rasheeda. " Toh,Mahmud nidai Saidai natayaka da addu'a Allah yazaba abunda yafi alkhairi,amma wannan abunnaka akwai rikici . "Ameen mamina nagode,insha Allah komai zezo da sauki.anan yaci abincin,rana sunata tattaunawa akan maganar. Se bayan magriba yayi mata sallama ya koma gida.
Dukkansu suna zaune a falon kasa suna kallo,har umma.fuskarnan tasa a tsuke ya shigo falon.ciki_ciki yayi sallama.dasauri shukura ta mike tana masa sannu da zuwa,tare da karbar briefcase dinsa. Sannu da gida yayiwa hajiya da umma,hajiya kakace kadai ta amsa,bata tsaya iya amsawarba ta kara da cewa."kai kuwa likita kana duban kanka a mudubi kuwa dubi yadda kabi ka rame.sekace kazar matsiyata.wata uwar harara ya wurga mata,batare dayace komaiba.tabe baki tayi tana nuna umma. "Kaga wacce kayiwa amma baniba.bebi takantaba ya wurgawa Rasheedah da zulaihat wani mugun kallo,saboda ganin Kansu ko dankwali babu.sannu da zuwa suka kama masa cikin borin kunya. Cikin tsawa yace" dalla ni ba gaisuwarku nake bukataba,Ku wuce Ku daure kanku kafin na aske muku gashin kanku.sum_sum suka mike suna kunkuni kasa_kasa suka shige dakinsu.shukura ce tafito daga dakinsa,yaya na hada maka ruwan wanka.duk tsananin damuwar dayake ciki amma seda yayi murmushi. Hannunsa ya hade 👍 alamun Jinjina ya nufi dakinsa.yanaji aransa dama zee ce take da halin shukuransa.kafin yafito daga wanka harta kawo masa abinci da ruwa.......
***********
Tunda fareeda tatafi ta barta ko motsawa batayiba,jitake tamkar mafarki takeyi.tarasa wazata tunkara da damuwarta,dama taly ce abokiyar shawarar ita kuma taci amanarta.wani hawayene me zafi ya zubo mata. Afili ta fara magana."yanzu shikenan duk kaunar danakewa joeboy,mun rabu kenan.taly tayi nasarar rabamu.kanta ta buga akan kujera tana sunbatu tamkar wata sabon kamu.wayartace tayi kara alamar shigowar sako. Banza tayi da ita batabi ta kantaba.seda ta gaji da zama sannan ta mike ta koma dakinta,toilet ta nufa ta sakarwa kanta ruwa,kotaji sanyi aranta.pant kawai tasaka da pad ta zira rigar bacci ta kwanta.ko'abinci bata nemaba saboda matsanancin ciwon kan dayake damunta.kudunduna tayi da bargo saboda wani zazzabi daya lullubeta. Wayartace ta karayin kara alamar shigowar sako.kamar bazata dubaba,sekuma ta dauko ta duba.number da'ake turo mata da text ne.ko dubawa batayiba tayi cilli da wayar,wayar ta wargaje akasa. "Duk kalamanku dayane,maza dukanmu mayaudarane babu wani namiji dazan kara yarda dashi arayuwata" ta fadi hakan a fili,hawaye na zubowa daga idanunta. Ita kadai se huci takeyi,aranta Tana ayyana badan mama dase ta kashe taly! Itakadai tasan bakin cikin dayake nukurkusarta a zuciya.........
************
Badan yanajin yunwaba yaci abincin kadan,sedan kawai shukuransa taji dadi.kadan yaci ya tashi ya nufi masallaci.ka'idar mahaifinsa idan yayi sallah magriba,se'anyi isha'i yake dawowa gida.shima yau zama zama yayi yayita lazimi yana Neman taimakon ubangiji akan abunda yake gabansa,tare da Neman zabinsa.
Tare suka koma gida da malam,bayan anyi sallar isha'in.kallo daya malam ya masa yasan da magana abakinsa.seda ya bari yaci abincin dare sannan ya samu mahaifinnasa adakinsa. Sunkuayar da kansa yayi kasa batare dayace komaiba. "Mahmud lafiya kuwa,daga ganinka da magana abakinka,kafadamun ko menene.shiru yayi yana Sosa kansa. Daurewa yayi cikin dakiyarsa ya fara magana cikin nutsuwa."Abba dama akan maganar da mukayi kwanakine,akan innemo mata.to nasamo. "Kai,Alhamdulillah masha Allah.Mahmud kai da bakinka yau kakecemun kasamo matar aure,naji dadi sosai Allah ya maka albarka. Yarinyar dakake so din yar inace.?
.Shiru yayi yana juya maganar aransa,yama rasa ta ina zefarawa mahaifinsa bayani.umma ce ta shigo dakin da sallama, ta nemi guri ta zauna,bayan sun amsa mata.akaro na biyu malam yakara magana inajinka Mahmud kayi shiru. Satar kallon umma yayi zuciyarsa na bugawa,beso zuwantaba a wannan lokacin. Ita kuwa tabe baki tayi ta dauke kanta daga garesa. "Abba bansan itadin diyar wayeba. Yafadi hakan cikin dakiya. "Mahmud! Bangane me kake nufiba,kana Neman auran yarinya amma bakasan diyar wayeba to'a ina kasanta.dasauri umma tadubesa Tana jifansa da wani kallo,se lokacin ta fuskanci inda zancen yadosa.kenan dagaske yaronnan baze auri Rasheedah ba,toh ita kuwa matukar ita haifesa bashi da mata se Rasheedah.........
*BY*
*zeey kumurya & real farhana*
*116_120*
*Bismillahirrahmanirrahim*
............shiru yayi kansa yana kasa ya kasa magana,Mahmud kai nake sauraro.numfashi ya sauke yace"Abba,ita kadai take zaune agidanta,kuma bansan wani nataba. "Banganeba Mahmud bazawarace,ko kuma.... "Wacce irin bazawara malam,me zaman kanta yake nufi Nina gane ai inda zancen ya dosa.umma ta katse malam cikin daga murya. "Haba fateemah,wacce irin me zaman kanta kuma,maida kallonsa yayi ga Mahmud. "Mahmud kayi shiru kanajin abunda mahaifiyar ka tace,Wanda nasan ba gaskiya bane,karamun tunaninsune na mata. Gyada kansa yayi,Abba abunda umma tace hakane,yarinyar zaman kanta takeyi. Salati umma ta rafka,tana tafa hannuwa,malam kuwa kawai sakar baki yayi yana kallonsa.
Shiko, ko ajikinsa,domin tunda yariga ya furta duk wani tsoro ya kau daga zuciyarsa. Malam kam yarasa mezece,tsawon wasu yan mintuna kowa da tunanin dayajeyi aransa. Malam ne yakatse shirun da cewa. "Al'amarinnanka gaba daya ya dauremun kai Mahmud.nama rasa mezance. Ita yarinyar a ina take,kuma meyaja hankalinka akan ta, duk yan matan dake cike agarin kano amma se ita ka hango.kansa na kasa yafarawa mahaifinsa bayani. "Abba,kawaidai inason yarinyarne kuma ina son nafitar da ita daga gurbatacciyar rayuwar datakeyi. Saboda yarinyar tani nisa,amma inasaran insha Allah nine sanadin dawowarta kan madaidaiciyar rayuwa.Abba dan Allah,karka hanani addu'arka kawai nake bukata.na maka alkawari,insha Allah babu matsalar dazata faru.shiru malam yayi yana nazari,tare da auna maganar Mahmud a mizanin hankali,tabbas ba'asan abunda ubangiji ya boyeba,kila sanadin Mahmud din yarinyar ta shiryu.umma kam zuciyarta tamkar tafaso saboda bakin ciki da takaici.wani mugun kallo kawai take jifansa dashi."shikenan Mahmud na yarje maka ka'aureta,kaje Allah ya bada sa'a. Allah yasa haka shiyafi alkhairi.bazan hanaka aurantaba,domin ba haramun bane,idan kayi sanadin shiryuwarta kaima kana da lada.Dasauri ya dago yana duban mahaifinsa cikin tsananin mamaki,da al'ajabi.domin beyi tunanin samun kansa da sauki hakaba.duk da yasan mahaifinsa mutum ne me fahimta,da kuma amfani da iliminsa.mutum ne shi,me tawakkali,tare da mikawa Allah dukkan al'amuransa.Mikewa tsaye umma tayi tana huci. "Haba malam me kake nu....daga mata hannu malam yayi batare dayace mata komaiba. Tasan halinsa baya magana 2,kuma bayasan musu hakan yasata ficewa daga dakin ta nufi sanar da wadda ta isa dashi. Da kallo suka bita,ganin tamkar zata tashi sama. "Abba,nagode sosai Allah yakara ilimi da girma. "ba saurin godiyarba,Mahmud,inada sharadi. bazan bari ka auri wannan yarinyarba harse ta koma gaban iyayenta.batare da tunanin komaiba yace ya amince.mikewa yayi ya fice zuciyarsa fal da farin cikin amincewar mahaifinsa.