← Book details Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 52

Sashe 26

Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bana fita ko'ina daga falo se daki,sedai inyi kallo,amma ninake mana girki. Kawayen aunty sameera dadama sunnuna suna sona da less, amma aunty sameera ta tsawatarmusu. tace ni na kalar haka bace. Aunty sameera duk da takasance karuwace amma macece me ibada,hakan yasa Nima ibadata batayi rauniba. Wata rana kwatsam aunty sameera tazomun da wani mummunan labari akan zatabi wani alh,saudiyya amma batasan inda zata barniba,kuma baza ta tafi daniba,saboda hakan bazeyiyuba. Hankalina ya tashi na shiga damuwa kwarai,saboda na shaku da ita matuka, inajinta tamkar jininace. Itama kuma ta damu sosai, kuma tacemun dazata iya fasa tafiyar data fasa kodanni,amma tanaso ta cika wani buri na rayuwartane shiyasa zata bishi. A lokacin na sanar mata,Nifa karuwanci kawai nakeso nayi burina na zama shahararriyar karuwa wadda za'a dinga kwatance dani.

Aunty sameera taso hanani karuwanci tare da son nunamun illar karuwanci amma na kafe nise nayi,haka ta hakura tace zata badani ga uwar dakinsu,wadda suma ita ta rainesu zata koyamun salon karuwanci kala_kala kuma zanzama shahararriya kamar yadda nakeso ta dalilinta musammanma yanda nake kyakkyawa. Murna kamar ta kasheni. Haka aunty sameera ta kaini gidan barikin *aunty boss* Wanda ananne nayi kazamin barikanci.

Gidan barikin aunty boss,gidane na shahararrun kuma cikakkun yan duniya. Wanda yasamu daurewar gindin manyan kasarnan. Katon gidane kuma dayake dauke da part_part kala_kala rukunin yan iska kala kala. Akwai masu bin maza,da masu bin mata da yan daudu da yan luwadi. Aunty boss itace magajiyar gidan kuma kowa akarkashinta yake,karkashin ikonta. Macece masifaffiya me masifar son kanta,ga tsinannen son kudi. Kowacce yarinya idan taje tayi karuwancinta ita zaki bawa kudin, ita kuma zata sai miki komai na bukatar rayuwa ta baki kudin kashewa. Idan kika Dade kina mata aiki zata sallameki,shine ta yantaki kenan,kigama gidanki kici gashin kanki kamar su aunty sameera kenan. Rayuwata agidan aunty boss,itace sanadiyyar dana zama cikakkiyar karuwa ta bugawa a jarida....

Numfasawa zee tayi tana duban mami da shukura tace, naji anfara kiran sallar la'asar kuje kuyi sallah sena karasa muku labarinnawa,amma zantakaita mukune saboda idannace komai zan fada muku semu kwana nawa bamu gamaba.

Jinjina kai mami tayi tace gaskiya labarinki akwai abun tausayi da rudani,amma bari muyi sallar seki karasa mana. Shukura dake rike da haba taja gwauron numfashi tace, gaskiya aunty zainab daga jin labarinki kamar akwai lauje cikin Nadi. Murmushin takaici kawai zee tayi batace komaiba. Mikewa mami tayi tana cewa shukura "kitashi muje muyi sallah ta karasa mana na matsu naji karshen labarin zainab. Mikewa shukura tayi tabi bayanta suka shige daki.

Lumshe ido zee tayi tare da kwantar da kanta ajikin kujera,zuciyarta na mata zafi haryanzu tana jin radadi a zuciyarta na abunda joeboy da taly sukayimata, takasa mantawa da abun kokadan. Wani hawayen bakin cikine ya zubo mata, daidai lokacin Dr Mahmud ya shigo falon da sallamarsa........

Wai ina labarin joeboy da taly ne?......✍️

*By*
*zeey kumurya&real farhana*

.........Wuraren karfe goma sha daya na safe taly ta farka,Tashi tayi a firgice, tana fadin "Niiii....!Niii zee zatawa haka....?,niiii tally,zee zatamun hakan....!?,wlhy sena rama...!wlhyy sena rama abunda kikamun senayi sanadiyan ajalinkii zee,wlhyy zakisan ni kika aikatawa haka....inban ramaba uwata bata haifenii Talatu ba...!!!(kaiii tally wanan cika baki haka keda kika wage Iya wuya aka makamiki miki karfee😂😂🤣).

Joeboy ne yatashi yanufeta rike kafadunta yayi cikin sanyi murya yafara fadin "My tally calm down pls...!ki kwantar da hankalinki kinji...kibari inkin samu lafiya kyayi duk wani abinda kikeson yii...!amma yanxuh samun lafiyarki itace tafi mahimmanci agurinmu....!,"haka joeboy yata kwantarwa da tally hankali Kafin yasamu tadan nutsu...tashi yayi yana fadin, "tunda kin farka bari nasanar da doctor" kai kawai ta daga masa batare datace komai ba,abubuwa kala-kala take kitsawa dazatawa zee tana cikin wannan tunanin ne joeboy yashigo doctor nabiye abayansa...sannu yayi mata tare da tambayarta ya jiki, Kafin yafara dube-dubensu irrin na doctors, bayan yakammalane ya umarci joeboy yabiyosa office..."ohk. bayan fitar doctor da 5minute ne shima yabi bayansa...Dan seda yatsaya ya lallashii tallynsa,duk dade duk wani movement dinshi zee ce ke fado masa,ji yike tamkar yaje ya sameta,tunaninta ya masa katutu aransa,so yake yaje ya ganta yaga halin datake ciki. amma de yasan zafin zuciya irin na tally, dole ya zauna ya kula da ita, amma anjima zeje yasanar da mama halin da'ake ciki.haka yanufi office din Doctor da sallama yashiga office din...kujera Doctor yamuna masa hade dacewa,"have a site pls!"zama yayi hade da fuskantar doctor, kallonsa doctor yayi hade dacewa "group din jinunku ba dayabane,hakan yasa bazamu kara maka jinintaba. amma munada irrin nata seka siya kawai mu dora mata." "Ohk doctor babu damuwa se'a siya. "Sannan Abu na biyu, maganar gabanta sedai mu turaku babban asibiti su bincikata dakyau, danmu nan kaga karamin clinic ne, idan kukaje can duk abunda yadace zasuyi mata." Ajiyar zuciya joeboy yasauke yayiwa Dr,godiya. Hannu ya mikawa doctor sukayi musabaha ya fice. Taly tana kwance,wani irin mugun jiri takeji duk da tana kwancen ga kanta dayake mugun Sara mata,ga wata muguwar aza ba da kasanta yake mata. Tsanar zee ce takara ninkuwa a zuciyarta,ta gudurce aranta matukar ta samu lafiya seta dauki mummunan mataki akan zee,wlh bataci bulus ba, bata daki banzaba. Sannan tasan zuwan zee duk shirin sahirane,yanda ta dauki saheera tamkar jininta amma ta mata haka,itama wlh setasa ankashe mata ita gabadayama. hawayen bakin cikine ya zubo mata, ahaka joeboy ya shigo ya sameta. "Oh my God, taly mene na kukan kidena damuwa zakiji sauki insha Allah, kiga kin koma kamar da." Fashewa taly tayi da kuka, cikin kukan tace, "haba joeboy kalli kainafa yanda yayi rundumeme, ga gabana wani shegen zugi yakemun tsoronama daya karnaje na rube." Kama hannunta Joeboy yayi cikin lallashi yace, "banason kina wannan maganganun, yanzu Dr yace zasu kara miki jini, zuwa dare idan jinin ya kare, zasu turamu babban asibiti akara dubaki sosai idanma aikine se'ayi miki. Yanzu zanje nakirawo mama tazo taga halin dakike ciki, dannasan yanzu tanacan hankakinta a tashe yake, ga wata nurse nan zata kula dake zata baki duk kulawar data dace." Kai taly ta daga masa alamar ta gamsu, ficewa yayi daga dakin, da kudirin seya fara zuwa gidan zee sannan yaje gidan mama..........

************

Zee tayi nisa a tunaninta hakan yasa bataji sallamarsaba. Shikanshi Dr seda gabansa ya fadi,zuciyarsa ta buga, dayaga ganta zaune. domin beyi tunanin ganintaba a halin yanzuba. Musammanma shida ya fice ya barta kwance babu lafiya. Tsayawa yayi kawai yana kallonta yanda hawaye yake kwaranya daga idonta. Wani tausayintane yakamasa,tun da yaje gidanta dazu ya lura akwai abunda yake damunta. Kana ganin fuskarta Kasan tana cikin tsananin damuwa. Fuskarta tayi fayau alamun bata da lafiya,Tayi masa kyau amma duk da haka. Sallama yasakeyi akaro na biyu amma zee bata jiba. Harde hannuwansa yayi a kirji kawai yana kallonta.

Kamshin turaren data jine me dadin gaske yasata kara bude kofofin hancinta tana shaka,tana kara lumshe idanuwa. Ahankali kuma taji kamshin yana kara mamaye kofofin hancinta,bude idanuwanta tayi taga mutum tsaye kikam a gabanta, Damm zuciyarta ta buga da karfi,"kamar aljani,yazo ya wani tsaya akaina ni tsoroma ya bani yaseen" ta furta hakan aranta. Kasa tayi da idonta batasan daliliba kawai setaji hawaye yana kara kwaranyo mata,tayi kokarin tsayar da kukannata amma ta kasa. Runtse idonsa yayi,tare da taune lips dinsa na kasa, cikin jin zafin zubar hawayenta yanajin tamkar tana watsa masa garwashi a sassan jikinsane,kukanta yana taba masa zuciya sosai.

Ahankali ya fara takowa zuwa gabanta hannunsa ya zira yazaro handkerchief dinsa dayaketa tashin daddadan kamshinsa. Kawai jitayi yafara share mata hawaye dashi. Lumshe idonta tayi tana shakar kamshinnasa, batasan daliliba kawai jitayi wata matsananciyar kunyarsa ta rufeta, wadda ta hanata dago ido ta kallesa.ga luguden da zuciyarta take mata tun sanda yashigo falon. Tambayar kanta takeyi meyasa ya shigo rayuwarta,da har ya dakkota yakawota gidansu. Domin tunaninta betaba bata sonta yakeba,saboda mutum kamar wannan me kamala da kyau da kwarjini mezeyi karuwa irint..... "Meyasaki kuka haka?" Ya katsemata tunani da wannan tambayar,girgiza masa kai tayi alamar babu komai. "Banason zancen kurame tunda ke bakurma bace,dan haka kidago kanki ki kalleni. Ya fadi haka yana babbata rai, Ya Allahu,zee ta furta hakan aranta. Handkerchief dinsa dayasakar mata tana share hawayenta tafara wasa dashi. Ahankali kuma ta dago idanta tana kallonsa,kallon cikin ido yake mata,hakan yasa da sauri tayi kasa da nata idon domin bazata iya jurar hada ido dashiba. Murmushin gefen baki yayi bekara cemata komaiba ya mika mata hannunsa alamun ta bashi handkerchief dinsa. Kara kamkeshi tayi a hannunta batare da tayi yunkurin bashiba,amma ta dago fuskarta ta zuba masa daradaran idanunta. Murmushinsa me tsada ya mata Wanda yakusan zautar da zee yace, "ki wankemun abuna zankarba,saboda kinbatashi da wannan kazamin hawayennaki. Yana gama fadar hakan ya wuce zuwa dakin mami.baki sake zee ta bishi da kallo,murmushine kawai taji ya subce mata, Wanda batasan kona meneba.Handkerchief din, ta Dora akan fuskarta tana shakar kamshinsa, Afili ta furta "inason kamshinnan,tun ranar dana fara jinsa, saboda yana sanyamun nutsuwa,gashi da dadin gaske."

Da sallama Dr ya shiga dakin mami, zama yayi a bakin gadonta yana jiran ta idar da sallar datake. Ita kadaice a dakin shukura tana dakin da'a sauki zee. Bayan mami ta idar tayi laziminta ta juyo tana kallonsa. "Mahmud sannunka har andawo daga asibitin.?" "Eh mamina nadawo ko gidama bankarasaba nace bari nazo naga jikinnata." Murmushi mami tayi tace ja'iri,wato yau badanni kazoba dan ajiyarka kazo. Shafa kansa yayi yana murmushi yace, "haba mamina kawaidai na barta a mawuyacin haline shiyasa nazo nakara dubata,kuma naga jikinnatama yayi sauki sosai. "Jikinta kam yayi sauki sosai, nima nayi mamaki, gata yarinyar akwai ladabi ga saurin sabo. "Dama mami,Ku mata ai kunada saurin sabo bari nakarasa gida na watsa ruwa na huta. Ya fadin hakan yana mikewa. "Mahmud ka tsaya mana kaci abinci, duk da dai tunna dazune da shukura da girka bamu sake sabon girkiba. "nagode mamina a koshema nake.
Chapter 26 · 0% Book details