← Book details Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 52

Sashe 40

Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Se wajen biyu saura muka tashi,ninafara tashi sannan na tasheshi sallah mukayi. Ina kokarin Dora girki shukura tazo tare da wata kawarta, naji dadin ganinsu sosai, narasa inda zan ajiyezu dan murna. Girkin dabanyi kenan saboda umma ta'aiko shukura da abinci. Shikuwa wanka yayi yafice bayan yaci abinci. Munsha hira da shukura sosai se kusan magriba suka tafi, bayan sunje gurin Rasheedah sungaisa. Inayin sallar magriba nayi wanka, zama nayi agaban madubi ina tsara kwalliya wadda nasan zata burge mijinah. Cikin wata gawn maroon colour nashirya, robace rigar hakan yasa takama jikina sosai,shape dina yafito sosai acikin rigar. Ana kiran sallar isha'i natashi nakawo tawa. Tunanin abunda zamuci da daddare nahauyi, bansaniba kozeci guntun abincin da umma takawo danda saura sosai, tun lokacin da'aka kawo namasa maganar nakaiwa Rasheedah ne, yayimun banza, kuma ina kayan garama da'aka kawoni dasu kotabasu banyiba. Ina cikin wannan tunanin ya shigo gidan. Sannu da zuwa na masa tare da karbar ledar dayashigo da ita. Zama yayi a falo yana bina da kallo. Dawowa nayi nazauna akusa dashi ina fadin, "yaya meza'a girka makane bansaniba kozakaci guntun abincin da umma takawo?" "Yanzu ai lokacin girki ya wuce, bakikaiwa megadi abinci bane?" Kama habata nayi nace, "wlh yaya namanta sha'af kuma tun rana nake tunanin yazanyi da abincin can, gashi banji almajiriba kodaya" "jeki duba kigani idan beyi sanyiba kikawo nakai masa" "toh" mikewa nayi naje naduba, har yanzu abincin da duminsa saboda acikin kula yake, juye masa nayi acikin food flaks, nakawo masa yafita yakai masa yadawo. Ledar danakai masa daki yace na dakko masa. Dakko masa nayi nakawo masa. Kayan fruits ne sekuma wata ledar daban daya mikomun yace nabude nagani. Rungumeshi nayi cikin tsananin murna ina zuba masa godiya bayan na bude. Wayar hannuncece kirar kamfanin Samsung sabuwa dal akwalinta me kyau. Godiya namasa sosai tare da jerin addu'oi. Kayan fruit din dayazo dashi mukasha tare da kayan gara, seda mukasha hirarmu medadi cikin nishadi ta masoya sannan muka kwanta bacci......

Rasheedah kam yau wunin bakin ciki tayi, tundaga ganin zee setaga takara mata kyau, lallai seta tashi tsaye akan zee musamman yanda taga tafita komai. Koda su shukura sukazo mata bata wani sakar musu fuskaba, saboda ita damacan basa shiri da shukura sosai.......

Washegari, bayan mungama duk abunda zamuyi wajen shadaya na safe yadaukeni a mota, mukaje kamfanin mtn yasaimun sabon sim,akamun register muka dawo gida. Muna dawowa bajira, nabude chat, saboda wararana idan baya gurina zata debemun kewa, seda natambayesa kuma da izininsa sannan nabude. Aranar da yamma wasu yanmata sukazomun wai makotanmune,sundade sannan suka tafi.........

**************

Yau kwanana 3 da tarewa soyayya kawai mukesha da Dr, cikin tattali da kulawar juna tamkar babu gobe. Kodayaushe muna manne da juna, sallah ce kawai take fitar dashi. Tare muke wanka mukecin abinci, har aikin gida tayani yakeyi. Dr,kwata_kwata baya sakarwa Rasheedah fuska, kullum dai ze shiga bangarenta da safe da daddare domin yaga lafiyarta amatsayinta na matarsa. Ita kuwa Rasheedah duk tabi tadamu hankalinta akan yanda yake nuna mata, Wanda hakan yakara mata haushi da tsanar zee azuciyarta atunaninta duk saboda ita yake mata haka. Amma ta kudirce matukar yadawo hannunta da girki, zee ko ganinsa bazata dingayiba.

Yana zaune akan kujera yana kallon labaran dare, sadaf_sadaf nazo ta bayanshi na rufe masa ido. Ina dariya, cire hannunnawa yayi yana murmushi, zagayowa nayi nazauna akan cinyarsa ina fadin"sorry mijin nabarka kai kadai ko azaune" kansa yadora akan kafata yace, "ehh mana tundazu kinje kinata waya mekuke cewane?" "Inaruwanka ba mamita bace" "nidin baxaki fadamunba, dan fadamun naji kinji amaryata" "nidai bazan fada makaba" "shikenan nahakura toni bari nafada miki wani Abu" akunnena yaradamun wata magana, cusa kaina nayi acikin kirjinsa ina dariya. Knocking kofar falon aka farayi da karfi tamkar za'a balla. "Waye wannan haka kamar ze ballamun kofa?" "Kaje kagani mana yaya" saukeni yayi ya mike ya nufi kofar, gani nayi yatsaya yana kallon waje bayan ya bude kofar, daga baya kuma yajuyo batare daya rufe kofarba. Wacce banyi zatoba ko tsammani itace tashigo wato Rasheedah. Da mamaki nake kallonta, meyakuma yakawota gurina a darennan?" Tsayawa tayi tana karewa falo kallo, hannunta tarike kugu tana jijjiga jiki. Shikuwa guri yanema yazauna bece mata komaiba. "Yaya Mahmud gurinka nazofa, naga aka'ida yau yakamata na karbi girki, amma naga shiru har yanzu shine nabiyo bayanka inga lafiya?" Da mamaki nake kallonta, "awacce ruwayar?" Ya tambayeta cikin rashin fahimta,domin shi bemagane inda zancennata ya dosaba. Tsokalo daurinta takarayi gaban goshi tace, "to ainaga ita bazawace" "ke Rasheedah banason hauka, ke wacce irin fitinanniyar yarinyace me neman magana, matar tawace bazawara?" Yafadi haka cikin fushi. Nikuwa tuni na fuskanci inda zancennata yadosa, kwallace tacikomun idona. Kara gyara tsaiwarta tayi tace, "kamanta matartaka ba budurwa bace, ragowar titice ragowar wasu, kaga kuwa ai kwana uku, zakayi mata domin itama bata da maraba da bazawar......a matukar fusace Dr, yamike cikin tsananin bacin rai, idanunsa harsun kada sunyi jaa, jijiyoyin kansa duk sun fito rudu_rudu. Ai Rasheedah tana ganin ya mike a cikin wannan yanayin tahadiye maganarta tajuya da nufin guduwa,amma taku biyu yayi yadamkota, ya wanka mata mari. "Rashida matar tawa kike kira raguwar titi agabana?" Yatambayeta cikin tsananin kunar zuci, muryarsa har rawa takeyi saboda bacin rai da kishi. Bejira mezataceba ya kara wanka mata mari, gani yayi hakan bemasaba yarufeta da duka. Da sauri na mike ina kuka nafara bashi hakuri ganin yanda yake dukanta cikin fitar hayyaci. karasawa nayi gabansa na rikesa ina rokonsa dan Allah yayi hakuri ya kyaleta, wata uwar tsawa yadokamun tare da fadin, "in matsa in basa guri karya hada dani." Bayanayi da sauri ganin yanayinsa, na matukar tsorata domin bantaba ganinsa cikin makamancin wannan yanayinba. Kuka nakeyi itama tana kuka, amma yaki kyaleta seda yagaji dankansa yakyaleta ficewa yayi daga part din gaba daya yana fesar da numfashi, itama kanta zee din haushinta yakeji domin dabataje tayi karuwancinba aibaza amata goriba. Abunda yariga ya manta dashi arayuwarsa bayason atuna masa,saboda yasan yanada masifar kishin daze iya tarwatsa masa zuciya. Ficewa yayi daga gidan gaba daya saboda idan yacigaba da zama ze iya hallaka Rasheedah, har zee dinma ze iya hadawa da ita. Karasawa nayi nakamata bayan fitarsa ina mata sannu, tabbas naji zafin maganganunta amma koma metacemun ninajawowa kaina, dabanyiba dabazata fadaba. Har samanta nakaita duk da uwar hararar datake jifana da ita,babu bakin magana sedai a tsaya a hararar. dawowa part dina nayi nazube akan kujera ina kuka me tsuma zuciyata, ina zancen zuci. "yanzu duk abunda mutum yayi arayuwarsa baya wucewa, yanzu haka za'ayitamun gori har yaya da jikoki, agefe guda kuma ga fitar dayayi cikin fushi,karyaje wani abun yasameshi" kukana nacigaba dayi babu me lallashina.

Rasheedah kuwa, zee tana fita ta lallaba ta kira mahaifiyarta,domin kuwa ta daku ba karya, sanarmata da duk abunda yafaru tayi, takara da gishiri da maggi. Nan uwar tahau tadinga bala'i tace bari ta kira uwartasa tasanar mata,bazata yardaba se'anbiyata hakkin yarta. Tun takwas da yan mintuna ya fita amma har karfe goma bedawoba, naci kukana na koshi wayata na dauka nakirashi naji wayartasa na ringing agida, gashi sekiransama akeyi. Hankalinafa yatashi nafara addu'ar Allah yadawomun dashi gida lafiya.

Seda 11 ta wuce yashigo gidan,ina dakina Inajin shigowarsa nasauke ajiyar zuciya,amma tsoro yahanani fita gurinsa. Shikuwa Dr, yanashigowa dakinsa ya wuce,wayarsa ya dauka yaga missed call dayawa, ummansace se zee da kuma maman Rasheedah. Ajiye wayar yayi yace dasafe yakirasu, amma se wani kiran yakara shigowa. Ummansace hakan yasashi dauka da sallama, amsa masa tayi takara da fadin, "ina kashigane tundazu Inata kiranka?" "Umma nafitane kuma nabar wayar agida" "Toh dama maman Rasheedah ce takirani tadagamin hankali wai kadaki Rasheedah, tananan kwance cikin jini, shine abun yabani mamaki domin nasan badabi'arka bane duka, danko kannenka baka duka balle matarka." Dogon numfashi yaja, yafadawa umma duk abunda yafaru. Numfasawa umma tayi tace, "Allah yakyauta, Rasheedah kam bata kyautaba, amma kaima kayi saurin hannu, dan Allah adinga hakuri ana kai zuciya nesa, yanzu katashi kaje kadubata kabata magani" "shikenan umma insha Allahu za'akiyaye nagode" "yawwa Allah yabamu alkhairi, Allah yabaku zaman lafiya,yakauda fitina adai dunga hakuri dan Allah" "ameen umma, nagode seda safen kigaida su malam da hajiya" "zasuji insha Allah" ajiye wayar yayi bayan umma takatse kiran, mikewa yayi yanufi part din Rasheedah, makulli yasa yabude yashiga tana kwance akan gado adakinta taci kukanta itama tagode Allah, mahaifiyarta taso zuwa amma mahaifinta yahana yace sedai gobe sazo tare. Fuskannan tasa ahade yadubata, itakuwa Rasheedah wani bala'in tsoronsane yashigeta harya gama dubata batace kalaba. Maganin ciwon jiki kawai yabata yakuma ce taje tagasa jikinta da ruwan zafi...

Inajin fitarsa da kuma dawowarsa amma nakasa tashi naje garesa, kusan 15 minutes dakara dawowartasa sannan na mike cikin karfin hali nanufi dakinnasa. Kwance nasamesa yana latsa waya fuskarsa a tsuke. Sallamar danayima ciki_ciki ya amsa. Dama mami tafadamun idan yayi fushi yanada wahalar sauka,amma kafin yayi ana dadewa. Durkusawa nayi agaban gadon cikin muryar kuka nace, "dan Allah yaya kayi hakuri" dago dakansa yayi yana kallonta, ta bashi tausayi sosai ba ita tamasa lefinba amma duk tabi tatada hankalinta, becemun komaiba,ya ajiye wayar hannunsa, waremun hannayensa yayi, dasauri natashi nafada kijinsa,ina fashewa da kuka. "Ya isa haka kukannamenene kuma?" Ya tambayeni cikin muryarsa datake nuna haryanzu yana cikin bacin rai. Bance masa komaiba se kukana danacigaba dayi. "Kimun shiru mana, kinsan banason kukannannaki na banza" cikin fada yayi maganar, hakan yasa bashiri na hadiye kukana ina sauke ajiyar zuciya. Kaina nacusa cikin kirjinsa, inajin yanda zuciyarsa take harbawa. Besan sanda murmushi ya subuce masaba,ganin yanda tayi, duk tabi ta tsorata. Seyaji tausayinta yakara kamasa, yasan itama dole zataji dacin kalaman Rasheedah akanta, gashi kuma yafice yabarta yasan hankalinta atashe yake. Hannunsa yasa yazagaye bayanta, dago da kanta yayi yace, "menene love dita?" satar kallonsa nayi naga yasaki fuskarsa bakamar dazuba. Kirjinsa nanuna da hannuna. "Sorry tawan, nine ko, nasaki kuka?" Yakarasa zancen yana shafa saman idona. Gyada masa kai nayi ina turo bakina gaba cikin shagwaba nace, "kuma katafi kabarni kasa hankalina duk ya tashi" "ganinan nadawo yanzu,kuma bazan kara tafiya inbarkiba mekika ajiyemun?" Kallonsa nayi na make kafada ina turo bakina gaba, murmushi yayi ganin yanda tayi,bakinsa yahade danata yafara kissing dinta.........✍️

*BY*
*Zeey kumurya & real farhana*
Chapter 40 · 0% Book details