← Book details Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 52

Sashe 18

Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tabe baki tayi tare da fadin"zeeee! Mezan gani haka, taly ta fadi hakan tana zama agefenta. zee bata kulataba seda takai karshen aya,rufe kur'anin tayi,ta ajiyeshi akan mudubi. tare da matsowa fuskarta dauke da murmushi,tace"oyoyo my taly,har kin dawo nayi kewarki. Rungumeta taly tayi tace"nima nayi kewarki my zee,ya gida ya joeboy,sakinta zee tayi cikin kalar tausayi tace "Hmmm,taly kenan joeboy yaje Dubai tun jiya amma bekiraniba,har yanzu.hankalina gaba daya a tashe yake. "ayya my zee shiyasa naganki cikin damuwa,may be zekiraki kila wani abunbe yarikesa. Kawar da kai zee tayi tare da fadin " Allah yasa,ya maganarmu na binkice akan joeboy,kuwa taly najiki shiru. Gyara zama taly tayi tace" hmm,zee,kinsandai,bazan miki karyaba,to wlh joeboy ya shahara a wajen bin mata,karya ya miki yace miki ya dena,yanzuma kila da wata yarinyar yayi tafiya ya barki a gida shabau.dafe kirji zee tayi tace" kam bura'uba,amma za'ayi bala'i a garinnan, wlh duk randa na kama joeboy da wata 'ya sena kusa kasheta.amma yanzu mene mafita taly,"mafita kawai kema kikama sabgar gabanki,kikoma zeenki kawai."kai taly bazan iya ba,nariga na bar wannan rayuwar. Dafa kafadarta taly tayi tace"kawata kada kice haka, da kuriciyarki zaki cuci kanki,haka zakiyi ta zama,kicire tunanin komai babu abunda ze faru kawai ki shigo acigaba da fantamawa dake.akan wani danamiji zaki hana kanji jin dadin rayuwa,nandai taly ta hau tsara zee,tabi ta kalailayeta harta samu zee ta amince.zata fara Hulda da wasu mazan.number wani gaye sameer ta bata,akan zata hadasu.ta nunawa zee hotonsa,ba karya gayen ya hadu,abunka da zee datake cikin tsananin bukatar namiji,nandanan ta amince.batare da tunanin komaiba.zuciyar taly cike da murna tabar gidan.

Tana fita ta kira sameer,ta sanar masa zata sashi wani aiki,akan wata yarinya.tana sone Yakama musu hotel ya kuma San yanda yayi yasa camera,yanda komai sukayi zatayi recording. hoton zee tatura masa ta WhatsApp,aiko nandanan ya rude yaga yarinya ga kayan aiki.ga kuma kudi da taly zata biyashi.ba jinkirin komai ya amince,ya tabbatar mata da gobema ze kaddamar da komai.godiya taly ta masa tare da kara jaddada masa yanunawa zee soyayya. Domin ita macece meson a sota.

Se sukan 10 joeboy ya shigo gidan,zee tana kwance tana chat da sabon saurayinta sameer,sameer ya matukar kwanta mata arai,ya tura mata pictures dinsa kala_kala,har video call sukayi,yanda ya iya tsara zance da kalamai hakan ya kara burge zee.shikam sameer harga Allah zee tamasa,100%.ya matsu Gobe tayi ya lashi zumarta.

Tsayawa yayi Daga bakin kofa ya kura mata ido yana kallonta,kamshi turarensane yasanar mata da zuwansa,sallama tayiwa sameer,tace masa ta gaji bacci takeji.ta kashe wayar gaba daya.duk yanda ta kudirci yiwa joeboy rashin mutunci seta kasa,gani takeyi tamkar karyane abunda taly ta fada mata,gani takeyi tamkar joeboy bazeci amanartaba.ware hannunsa yayi alamun tazo garesa,soyayya ba karyaba,wata irin kewar joeboy ce ta bijiro mata.a hankali tatashi ta fara tako tamkar me tausayin kasa ta karasa garesa.fadawa jikinsa tayi tare da sakin kuka,domin zee duk zafin zuciyarta tana da rauni.hannunsa yasa ya rungumeta tsam ajikinsa,wani irin tausayinta ne ya fara bijiro masa,shikansa yasan be kyauta mataba,bubbuga bayanta ya farayi alamun rarrashi. Ahankali yafara mata magana"am sorry,my love.nasan nayi miki babban lefi amma kimun afuwa bazan kumaba.sakinsa tayi ta fada kan gado tana cigaba da kukanta.binta yayi yakara janyota jikinsa,kwace kanta tayi ta matsa Daga kusa dashi cikin kuka ta fara magana."kada ka kara tabani,joeboy babu abunda zakacemun,kanacan kana bin 'yan matanka ni ka ajiye a gida,na killace kaina bana kula kowa sekai,amma kai kananan kana cin amanata,to ko mekakeyi ana zuwa ana sanarmun.marairaicewa joeboy yayi ya fara tsara zee,harda hawayensa wai anaso arabasune kawai,yay ta mata rantse rantse akan shi baya kula kowa.abunka da zuciyar mace,da saurin yarda musamman ma ga Wanda takeso.nandanan zee ta sakko suka koma normal tamkar da.

Washegari, zee tun da safe take tunanin karyar dazatayiwa joeboy akan fitarta da sameer.seda kyar ta samo solution tace masa zataje wajen mamar taly.batare da tunanin komaiba ya amince mata.da rana sukayi zata hadu dashi, hakan yasa tun kafin 2 ta gama shirinta tsaf,kiransa tayi a waya ta sanar mata.address din hotel din dazasu hadu ya bata tare da number dakin.taly kam a time din tana tare da joeboy,ta kirasane akan yazo yarakata wata 'yar unguwa.seta kaisa hotel din dasu zee suke.ya kamata da idanuwansa.

Duk da tana danjin tsoro Wanda batasan kona meneba amma haka ta daure,rufe kofar part dinta tayi ta bufi motarta ta bata wuta se G.R.A inda anan hotel din,dazata yake.ammafa tanajin zuciyarta na 'dan bugawa.

Tayi kusan 5 minutes da fara tafiya wayarta ta fara ringing,bata Daga waya idan tana driving,amma se kiranta akeyi. a tunaninta sameer ne,janyo wayar tayi zuciyarta tanata bugawa,Wanda batasan daliliba.wata bakuwar number tagani,dagawa tayi tare da karawa a kunnanta."hello zee"aka fada Daga Daga bangaren. "Yess wake magana ta amsa cikin sanyin muryarta." Baki da bukatar sanin kowacece amma nakirakine intaimakeki,kada kikarasa inda kike kokarin zuwa,domin ananan ana shirya miki gadar zarene,kuma da zarar kin rufta shikenan. Ai sitiyarin wayarne ya kusa kwace mata dakyar ta samu tayi control din kanta ta faka motar agefen titi.dafe kanta tayi tana sauke numfashi."meyake damunane,me yake shirin faruwa da rayuwatane,komai ya canzamun,na koma tamkar baniba.wacece take kirana awaya tana sanar dani abubuwa,wanene yake kullamun wani Abu,tabbas babu tantama akwai wani Abu dayake faruwa dani.akwai wani boyayyen al'amari.ya Allah kakawomun dauki arayuwata.zee take fadar haka afili.kusan 15 minutes ta dauka tana sakawa da kwancewa.kiran wayarta aka karayi akaro na biyu.wannan karan sameer ne,kamar bazata dagaba,sekuma ta Daga. "Sugar baby inata jirankifa,ya fadi hakan cikin nuna zakuwa. " I'm sorry sameer harna fito kuma senaji wata kasala ta lullubeni,yanzuma ina kwance na kasa tabuka komai.ta samu kanta da basa amsar hakan.ai sameer jiyayi tamkar an kwada masa guduma,saboda bakin ciki,ya tama se kwashi dadi kuma anzo anbata masa budget.cikin bacin rai yace"ohk Allah ya kara sauki,Daga haka ya kashe wayar.kifa kanta tayi akan sitiyarin motar tare da lumshe idonta.

Taly dake ta jiran kiran sameer amma taji shiru, domin tace masa zee tana zuwa yakirata.ta dakko wayarta kenan zata kirashi kiransa ya shigo wayarta, wani farin cikine ya lullubeta,har wata ajiyar zuciya ta sauke,tashi tayi daga kusa da joeboy ta koma gefe.tana Daga wayar kafin yayi magana ta rigashi,"sameer tazo ko,Ku fara abunda zakuyi nanda 30 minutes zamu karaso. "Ai bazatazoba takirani wai batajin dadi.ya fadi hakan cikin wata marainiyar murya tamkar Wanda yarasa iyayensa.saboda takaicin zee ta fasa zuwa.kutmar ubannan,taly ta furta,masifa ta fara masa tamkar zata cinyesa." Haba sameer! Haka mukayi dakai,aikinnanfa ba kyauta zaka munba,kudi zan biyaka,tayaya zakacemun taki zuwa,kaifa namijine kasan yanda zakayi ka jawo hankalinta. "Kinga taly nayi,se'anjima kibarni da abun dayake damuna.yana gama fadin wayar ya kashe wayarsa.bin wayar taly tayi da kallo,bakin ciki tamkar ya kasheta.to meke,damun zee,meyasa zataki zuwa.alhalin itama tana bukatar namijin.

Ta kwashe mintuna ahaka,zuciyarta tana fada mata kawai taje gurin sameer,koma meze faru ya faru,taji muryar sameer da bacin rai tsantsa,kamar bata masa adalciba.to amma kuma batasan meze faruba.wayarta ta dakko takira number da'aka kirata amma hartayi ringing ta gama ba'adagaba........

*By*
*zeey kumurya&real farhana*

_*ZEE 'YAR BARIKI*_

*FARIN JINI WRITER'S ASSO....📚*

*96_100*

*Bismillahirrahmanirrahim*

..............dafe kanta tayi tana sauke numfashi ahankali_ahankali.tunaninta gaba daya ya gudu, gwagwalwarta ta dena aiki,ta rasama tunanin me zatayi,wani gwauran numfashi ta sauke tare da kunna motarta ta fara driven a hankali,gidan maman taly ta yanke shawarar zuwa,kamar yadda tacewa joeboy......

Saheera,bayan ta gama waya da zee ta kama kaikawo a falonta tana rokon Allah yasa kada zee taki daukar shawararta,Allah yasa kada taje hotel dinnan.kiran da zee tamata ne ya katse mata tunaninta,dauko wayar tayi taga Ashe zee ce,kamar ta Daga sekuma taki dagawa domin tasan dole zee zataso sanin wacece ita,ita kuma bayanzu takeson bayyana mata kantaba........

Cikin sanyin jiki ta koma kusa da joeboy ranta a matukar bace,juyowa yayi yana dubanta,ganin se fesar da numfashi takeyi,tamkar wadda tayi tseran gudu.janyota yayi jikinsa yana shafa gefen fuskarta yace "yadai masoyiyar,na ganki haka kamar ranki a bace. Tashi tayi Daga jikinsa cikin bacin rai ta fara magana."seda nagama shirina,nagama komai kawai ina kiran wadda nace maka zaka kaini gurinta,shine take cemun wai batanan.tunda nace mata zanzo batacemun batananba seda nagama shiryawata sann....kara janyota jikinsa yayi," calm dawn my taly,shine abun damuwa daze bata miki rai haka,just forget her,kizo muji dadinmu.ya karashe zancen yana shashshafa jikinta tare da shinshinata.shiru tayi tana karbar sakonsa duk da ranta a matukar bace yake. da wargajewar plan dinta........

Mama tana daki a kwance zee tayi sallama,da sauri mama ta mike Daga kwancen datake.fuskarta dauke da fara'a bakinta yaki rufuwa.saboda ganin zee.itama zee yake ta farayi. gaishe da mama ta farayi bayan ta zauna agefen gadon da mama take. "zee! Yau kece agidannawa,haba zee harnayi fushi kwana da yawa kin buya kinyi wuyar gani.dariya zee tayi tace"tuba nakeyi mamana ayi hakuri wlh bana fita sosai yanzu kwata_kwata Daga gida,sekuma idan zansiyo wani abun a kasuwa."Ayya shiyasa najiki dif. "Am,mama ina taly kuwa kota fita.nandanan fuskar mama ta sauya fara'ar dake fuskarta gaba daya ta dauke,rike haba tayi tace" hmm,zee yanzu senayi kwana 3 bansa talatu a idonaba,gwarama da kullum tana dan lekoni amma yanzu setaga dama,zatazo ta bani kudi ta wuce. "Subhanallah mama, taly abunnata harya kai haka,ita kuwa meyayi zafi haka,mama? "Dana mata magana akan haka,setacemun wai wani saurayi tayi sabon kamu,shiyasa. ni kuma gashi na rasa meyasa bana iya tsawatarwa da taly akan duk abunda zatayi.hawaye ya fara zuba Daga idanuwan mama,wlh zee nikadai nasan bakin cikin danakeji akan wannan rayuwar da kukeyi,gashi taly ita kadai gareni ita kadai Allah ya bani.memakon tayi aure ta haifamun jikoki nima insamu zuri'a amma ta gwammace taje tayi ta yawon gararinta.wani irin tausayin mama ne ya tsirgawa zee,kenan itama datana gaban mahaifiyarta haka zataji,haka zataji bakin ciki kamar mama,haka zubar da hawayenta akanta.kwantarwada mama hankali ta farayi,da dadadan kalamai ta kuma tabbatarwa da mama zasuyi magana da taly akan rashinta zuwa duba maman.ta dade suna hira da mama,inda mama tayi mata nasiha tare da fada me ratsa zuciya, zee har kuka tayi,domin ita kanta tasan abunda takeyi badaidai bane amma kotayi niyyar barin rayuwar bariki,setaji ta kasa.kamar janta akeyi haka takeji. seda ta cika mama da alkhairi sanna sukayi sallama mama tanatasa mata albarka tare da mata fatan shiriya.jikinta a matukar sanyaye ta bar gidan mama,zuciyarta cike da tunanin wanene Wanda taly take tare dashi,Wanda yasa har bata zuwa duba mama.......
Chapter 18 · 0% Book details