Sashe 29
Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nan zee Ta cigaba da basu labarinta da abubuwan daya faru har zuwa yau. Ta kara da cewa. "Naso joeboy kamar hauka,hakama na kaunaci taly na bata yarda amma sukaci amanata. Wannna shine dalilin dayasa naji na tsani rayuwar bariki gaba dayanta, na kumayiwa kaina alkawarin bazan kara karuwanciba tunda babu amana a cikinsa. Taune lips dinta zee tayi tana sauke numfashi. Numfasawa mami tayi tace, "Gaskiya zainab kinyi rayuwa,gaki kyakkyawa amma kin bata wayonki amma kozaki iya fadamun meyaja ra'ayinki kika shiga karuwanci.?" Ajiyar zuciya zee ta sauke tace, "wlh mami bansaniba, nidai tun Daren dana baro gidanmu naji babu abunda nakeso sama danayi karuwanci, abunda banma sanshiba saboda ni agida daga school se islamiyyya se kuma gidan yan uwa idan naje ziyara amma ko fita banayi." Jinjina kai mami tayi tace" "To yanzu kinajin hanhalinki yayi gida?.". "Gaskiya banaji danni kozancen gidama banaso amun,amma dai bakamar daba. Domin da sena shekarama ban tuna da iyayenaba, idan kuwa na tuna dasu wani bakin ciki da kuncine yake ziyartata, jikina har wani zafi yakemun tamkar garwashi. Amma yanzu Alhamdulillah naji ina tunawa dasu, amma duk da haka gaskiya banason komawa. Dan harnayi karuwancina na gama ko hanyar abuja banayi, ko sunan garin naji an,ambata yanzu kaina ze juyamun naji tamkar numfashina zebar jikina." Gyada kai mami tayi tace, "Amma abun da mamaki sosai,kuma shima mahaifinki yanda yake babban mutum, nemenki baze masa wahalaba akasarnan amma kuma benemekiba kuma har garinnan yana zuwa." "Gaskiya dai kam mami abunda matukar mamaki, nima abun yadauremun kai, labarin aunty zainab kamar akwai sa hannun wani" "Nima haka nake tunani shukura, Allah dai ya kyauta, shukura ki shiga kitchen kidora girkin dare" "tom mami" shukura ta fadi haka tana mikewa. Nima mikewa nayi ina cewa, "muje na tayaki girkin," amma mami ta hanani. "Ina kuma zakije zainab keda baki da lafiya,ki zauna ki bari tayi ita kadai." "Dan Allah mami, kibarni na tayata naji saukifa, wlh gajiya nakeyi da zama nafison indinga dan motsa jikina. Mami badon tasoba ta barni na tayata, muna aikin muna hirarmu.......
*************
Horn yake dannawa megadi,akai_akai saboda yanda zuciyarsa ta kwadaitu da ganin zee. Megadi daya zagaya bayi, da sauri ya fito ya wangale masa get din. Yana masa sannu da zuwa. Hannu kawai joeboy yadaga masa, parking motar yayi ya fito, ko rufe murfin mortar beyiba, saboda yasan fushin zee, gashi kuma bata iya bacin raiba. A bude ya tarar da falon hakan yasa yasauke ajiyar zuciya saboda tananan kenan. Beganta a faloba, bedroom dinta ya nufa nanma wayam batanan,amma ga kayantanan data hada da wayarta data tarwatse akasa. Toilet ya leka nanma batanan, agigice ya fito daga dakin ya fara duba sauran dakunan gidan yana kwala mata kira, amma yaji shiru. Ko'ina seda ya duba amma bega zee ba. Nanfa hankalinsa yayi kololuwar tashi wani gumine yafara fetso masa, to ina zee tatafi. Yasandai bata da kowa a garinnan se kawaye amma dai bari ya tambayi megadi. A firgice ya fito yana kwaklwa me gadi kira, "malam inusa!, malam inusa!" Dasauri megadi ya taso ya karaso gabansa, "gani ranka ya da.." "Ina zee?" Joeboy ya katsesa da wannan tambayar cikin tashin hankali. Rarraba ido megadi ya farayi yasan yanda yaga yanayin ubangidannasa idan yace masa wanine ya dauketa, ai ze iya mangareshi hakan yasa yace, "ai ranka ya Dade ta fita tunda safe" "what? Ta fita kuma, ita dawa ta fita?" "Ita kadaice ranka ya Dade" dafa kai joeboy yayi bece komaiba. Be koma cikin gidanba ya nufi motarsa domin zuwa Neman zee gidan kawayenta.
Duk wadda yasan zee tana mu'amala da su seda yaje gurinsu nemanta amma batanan, fareeda kam itama hankalinta ya tashi lokacin dayake mata bayanin abunda yafaru. Gashi ta bar wayarta a gida balle su kirata. Tun kafin azhar yake yawon Neman zee Amma har yanzu be gantaba, gashi yamma ta farayi. Gidan saheera ne yafado masa tunda tare sukaje hotel may be yanzuma suna tare. Amma yana zuwa gidan saheera ya tarar a rufe. Tsaki yaja cikin takaici ya kwantar da kansa akan sitiyari, a fili ya fara furta. "Zee ina kika shiga, dan Allah karki gujeni wlh ba lefina bane, nima bansan ya'akayi na fara son taly ba. Zee kece rayuwata kidawo gareni idan babu ke bazan iya rayuwa ba." Idanunsa sunyi jajur saboda tashin hankali duk Wanda yaga joeboy a lokacin seya gane baya cikin nutsuwarsa. Saboda har wata yar rama yayi. Yana masifar son zee dan haka dole ne yanemota a duk inda take. Da wannan tunanin ya tada motarsa domin zuwa dakkowa taly mama.........
************
Bawani abinci mukayi me wahalaba shinkafa da miyace se hadin kayan salad. Ina zaune akan gadon dakin dana sauka inayin game a wayar shukura, mami ta shigo dakin da sallama tace muzo mu gaishe da megidanta yadawo. A falo muka tarar dashi yana zaune akan kujera. Durkusawa nayi har kasa ina gaishesa. Cikin sakin fuska shima ya amsamun, nasiha ya doramun da ita sosai me ratsa jiki wadda tasani yin kuka,tareda mun addu'oi dafatan shiriya arayuwata dani da masu hali irinnawa. cikin kuka nace, "nagode sosai kawu" (haka naji shukura tana kiransa). Daki na koma naci gaba dayin kuka, nasihar kawu ta ratsamun jiki sosai.tsoron Allah ya kara lullubeni,ni kaina se yanzu nake tunanin wanne rudin duniyane ya kaini yin sabon Allah mafi muni, wato zina. Bansan sanda tashigoba kawai jinayi ta rungume ni ajikinta, tana shafa bayana alamun rarrashi. "Kiyi hakuri zainab kidena kuka,kowanne bawa datasa irin kaddarar. Tunda Allah yasa kin gane gaskiya tun kafin lokaci ya kure miki, seki godewa Allah. Yanzu kawai abunda zakiyi guda dayane shine ki dage da addu'a da istigfari. Ubangiji gafururrahim, kuma yanason bayinsa masu tuba. Insha Allah idan kika dage da wannan zakiga dai_dai agaba, kinji yata share hawayen kidena kuka" mami ta karasa zancen tana dagoni daga jikinta, hawayen fuskata ta fara sharemun. Ajiyar zuciya na sauke, inajin kaunar mami da ahalinta masu halacci tana ratsa jikina. "Mami bani da bakin dazan miki godiya, sedai kawai nace Allah ya biyaki da aljannarsa." "Ameen, Karki damu,babu godiya a tsakaninmu kema yatace ai, yanzu zanje gurin surukinki mu tattauna,saboda bayan magriba kadai ake samunsa free. (😂😂😂mami zee fa batasan Dr yana sontaba,) shiru zee tayi tana maimaita Kalmar suruki aranta, waye kuma surukinta?. Murmushi mami tayi domin ita a tunaninta kunya zee taji. Rabani tayi da jikinta ta mike tana cemun seta dawo. Adawo lafiya na mata, ina kara mamakin abunda tacemun. Inason na tambayeta amma nakasa, harta fice daga dakin. Gwauron numfashi na sauke, mami ta tafi ta barni da tararrabi akan abunda tace, gefe guda kuma ina mamakin dalilin dayasa Dr ya daukoni ya kawoni gidansu,alhalin babu wata alaka atsakaninmu, ni da shi.......
Hajiya kakace zaune gaban malam tanata zuba masa mita akan abunda Mahmud yake shirinyi, shidai malam yayi mata shiru kawai yana jinta. Ana haka mami ta karaso gidan. Falon malam ta nufa saboda bata gansu a falon kasaba.(Rasheedah da zulaihat suma basanan,sun tafi gidan su rasheedan) Da sallama ta shiga tare da gaishesu. "Yawwa Ramatu gwara da Allah ya kawoki,nasan kema kinji labarin tabargazar da yaronnan ze mana" hajiya ta fadi haka tana fiki_fiki da idanuwa,batare data amsa gaisuwar mamiba. Umma ce ta shigo falon saboda taji sanda mami take sallama,dama tana daki tana jin duk fadan da hajiya kaka takeyi. Gaisawa sukayi da mami. Gyaran murya malam yayi yace, "Alhamdulillah dama sonake Ku hadu gaba daya na tunatar dako abunda kuka manta. Itafa rayuwarnan kowa da irin tasa jarrabawar, ita wannan yarinyar da'ake magana akanta bansantaba bantaba ganintaba, amma kuma bazan iya hana Mahmud aurantaba. Saboda kasancewarta musulma,kai koma da kafirace zanyarda Mahmud ya aureta. Saboda hakan ba haramun bane a musulunce, abunema me kyau saboda ta sanadiyyarka wani ze shiryu kaga kana babban lada kenan" "hakane malam,amma bantari numfashinkaba amma ance idan zaka nemi mata kanemawa yayanka uwa tagari, kuma me asali. Wannan kuma yarinyar dagaji bata da tarbiyya." Cewar umma tana bata rai. "Zancenki gaskiyane fateema kema, to amma ai idan tayi auren shine zata shiryu ta koma me tarbiyyar dakike cewa, sannan kuma maganar asali dama nacewa Mahmud bazan yarda da auransa da itaba harse ta koma gaban iyayenta. Dan Allah kubar wadannan maganganun Ku mata akwai Ku da rikici akan Abu,karamin Abu seku maidashi babba. Meyasa bazamu mikawa Allah al'amarinsaba meyasa a komai bazamu dinga Neman zabin Allah da alkhairin abuba. Sedai kawai abunda ranmu yakeso shizamuyi. Nasiha sosai malam ya zarce dayi musu tare da ja musu aya da hadisi. Sosai jikin hajiya kaka yayi sanyi harda kukanta.( 😂😂😂 tsohuwa anji wa'azi) Ummama ta yarda Mahmud ya auri zee,saboda kalaman malam sun shigeta. Amma fa da sharadin sedai ya hada da Rasheeda ya auresu duka biyun. Mamice tace sunji sun yarda Allah yasa haka shiyafi alkahairi,Allah ya hada Kansu ya basu zaman lafiya. dama su addu'ar su kawai suke bukata a auran. Gyara zama mami tayi tana fuskantar malam tace, "dama yaya zuwan danayi nazo mu tattauna akan yarinyarne, domin yanzu haka yarinyar tana gidana Mahmud ya kawota tunsafe, kuma ta bamu labarin rayuwarta gaba daya. Mahaifintama sanannen mutum ne, ALH. AHMAD DAN GASKE........✍️
*By*
*zeey kumurya*
......"Wanne alh. Dangasken, kee Rahma banason karya,wannan ai zancen banzane, tayaya ta zama yartasa?" hajiya kaka ta katse mami da wannan tambayar tana zaro ido waje cikin mamaki. Umma kuwa haba ta rike tana kallon mami cike da tararrabi tama kasa magana. Jinjina kai malam yayi yace, "Rahama wanne dangasken kike nufi, badai Wanda nasaniba. Murmushi mami tayi ganin yanda duk sukayi daga jin furucinta tace, "dama nasan dole zakuyi mamaki koma kuce karya nakeyi,nima lokacin data fadamun nayi mamaki sosai,amma idan na Baku labarinta kamar yadda ta bani nasan zaku yarda. Labarin zee duka mami ta basu.