← Book details Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 52

Sashe 44

Zee Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daddy ne dakansa yataso ya buge kofar, kaina na kasa naji kamshin da bazan taba mantawa dashiba arayuwata, ahankali nadago kaina ina dubansa, wata zabura daddy yayi lokacin dayayi ido hudu da princess dinsa, wadda ko barci yake yaganta seya ganeta. yarda jakar hannuna nayi dagudu na karasa garesa na rungumesa ina sakin kuka meban tausayi. Kasa aiwatar da komai daddy yayi,saboda farincikin ganin tilon yarsa,wadda yake matukarso da kauna. Kukan mace da ummi taji yasata tashi dasauri tabiyo bayan mijinnata zuciyarta natsansnta bugu, mamaki da al'ajabine yakamata ganin mace kwance akirjin mijinta to wacece ita? cikin razani tace, "Daddy me...... Dasauri zee tabar jikin mahaifinta jin muryar mahaifiyarta tanufe dagudu, nuna zee ummi tayi da hannu tanason tayi magana amma takasa jikintane yadauki rawa,kawai gani sukayi tayi baya luuu tafadi kasa sumammiya..........

Dr,yatsinci kansa acikin wani irin mawuyacin hali, yana kwance shiba bacciba shiba ido biyuba,karfin addu'ane yadawo dashi cikin nutsuwatsa. Se la'asar yasamu nutsuwa hankalinsa yafara dawowa jikinsa, ahankali ya mike yashiga toilet yasakarwa kansa ruwan sanyi, yadade a toilet din sannan yafito daure da alwala, sallar azhar yarama yakuma kawo la'asar. Duk yanda yaso tunanin zee yabar zuciyarsa amma yakasa tamkarma kara masa tunaninnata akeyi, ga wani son ganinta da zuciyarsa ta kwadaito dayi. Mikewa yayi cikin azalzalar zuciyarsa yanufi dakinta, dammm zuciyarsa ta buga saboda begantaba, dasauri yanufi toilet yana addu'ar Allah yasa bata tafiba,nanma wayam yaganshi,sip dinta yabuda yaga ga kayantanan babu abunda aka taba,kitchen yanufa cikin nanma begantaba. Afilii ya furta Kalmar "innalillahi, meyake shirin faruwa dashine, dagaske zee dinsa yakora daga gidansa da kansa" shiyasa bayason yanke hukunci cikin fushi,duk da koma meyafaru zee dince tajawowa kanta, zama yayi akan kujera yana cizon lebe, yanaji idan begantaba tamkar ze iya mutuwane, wata wutar sontace take ruruwa aransa. afili ya fara magana. "Meyasa zakimun haka zainab, meyasa zaki cutardani,mene ribarki na aikata haka,gashi kinriga kinyiwa zuciyata illah, kinzama jinin jikina,sedake sannan zan iya rayuwa."

Kamar an tsikaresa ya mike yadauki makullin mota ya fice daga gidan gabadaya yanufi gidan mami domin yasan bata da gurin zuwa dayawuce nan, amma yana zuwa seyatarar mamin batanan se megadi, kuma megadi yatabbatar masa da tunsafe mami ta fita, yayi tunanin kiranta yayi, sekuma yafasa, yace yadawo anjima. zuciyarsa cike da zullumi da firgici,addu'a yakeyi Allan yasa mami tana tare da zee, yatambayi megadi ko zee tazo yace masa batazoba. "To ina tatafi, kodai kiran mami tayi tasanarmata mami kuma tafada mata inda taje tabita?" ........

*****************

Ummice kwance akan gado,bayan ta farfado,mungama murna da koke_koken ganin juna. nikuma ina kwance akan cinyarta tana shafa kaina, idanunta na zubar da hawayen farinciki. Daddy kuma kallona yakeyi tamkar yanason gano wani Abu atattare dani,cikin sanyin murya ummi tafara magana. "Tabbas Allah shine abun godiya, daya dawomun dake alokacin dabanyi zatoba, harna fiddarai da ganinki sekuma gaki kinzo gareni" dago da kaina nayi ina duban ummi nace, "umminah wai ina mommy nane tunda nazo bangantaba, kobatananne?" Kallon ummi daddy yayi da sauri yana girgiza masa kai. "Kama hannunta nayi cikin rudewa nace, " ummi dan Allah kusanar mini ina mommytah kota mutune" numfashi ummi taja tace, ''bata mutuba zainab amma labarine metsaho kibari kihuta kiyi wanka sena baki labarin,amma yanzudai mommy bata cikin gidannan" badonnasoba na hakura amma seda nakara jehowa ummi wata tambayar. "Ummi naga wasu yara guda 2 masu kama da daddy sukuma yaran waye?" Kallon juna ummi da daddy sukayi naga sunyi murmushi atare.har daddy zeyi magana ummi takatseshi da fadin "y',ay'an auntynkine da daddynki ya aura bakyanan" kallon daddy nayi fuskata dauke da murmushi nace,"amma najidadi sosai,Ashe nima inada rabon samun wasu yan'uwan a duniya ina auntyn tawa take itama naga bangantaba, bari naje nakara ganin kannena na rungumesu ajikina inji duminsu.nafadi haka ina mikewa, "A'a zainab,kije kiyi wanka dan wadannan yaran surutunsu baze barki ki hutaba, idan kika fito nakira miki su. Zuciyata cike da murnar kasancewata da ahalina nanufi toilet, farin cikin danake ciki baze misaltuba amma duk wannan abun dake faruwa Dr, na makale acikin zuciyata,inajin ummi da daddy na dariya dabansan kota meneba, waya ummi ta dakko tafara kiran y'an uwa da abokanen arziki,tana sanar musu dawowar zee gida.......✍️

*kuyi manage da wannan pls, yau ko editing babu*

*By*
*zeey kumurya & real farhana*

..........Bayan nafito daga wanka na shirya cikin jallabiya ta mata da ummi takawomun,kozama banyiba ummi tajani dinning,dayake dama nayi sallah ta. anhadamun kayan ciye_ciye akai na alfarma,ai tundaga jin kamshi yawuna ya tsinke dama rabona da abinci tun safe,ummi dakanta take bani abincin abaki,daddy kuwa yana gefena, gani yake kamar idan tayi nesa dashi zata iya kara barinsa. Seda naci nayi nak,sannan muka koma kan kujera,se'alokacin masu aikin gidan suka shigo sunamun sannu da zuwa. Twins din mommy ne suka shigo falon da sallama kamar yadda aka horesu, tare da me kula dasu. Turus suka tsaya suna kallon zee, cikin mamaki sunga me kama da umminsu. "Hanif da munif ga auntynkufa tazo wadda nake Baku labarinta" ummi tafadi haka tana murmushi. Mikewa nayi nakarasa garesu na rungumesu domin bazan iya jira sukarasoba, idonane yacika da kwallar farin ciki, yau nice rungume da yan uwana, abunda naketa kulafuci tun shekarun baya, seyanzu allah yabani, dan'uwa komai kankantarsa dan'uwand,domin wata rana idan babu iyayenka,sune zasu, zama abokin shawararka. Suma luf sukayi ajikina se kuramun ido dasukayi suna kallona. Shafa Kansu nakeyi kaunarsu naratsa dukkan gabbaina,da jinin jikina. Kallon ummi nayi nace, "ummi ina mamantasune Haryanzu bangantaba" murmusawa daddy yayi yace, "zonan diyar albarka kiji inda mamansu take" hannunsu na kama muka zauna a inda daddy yanunamun,ina kallonsa. "Wasa umminki take miki babu wani aure dana kara, ita tahaifesu shekara 5 dasuka wuce." Aibansan sanda naje narungume umminaba,cikin tsananin farin ciki, cikin kukan murna nace, "umminah Ashe dama kekika haifamun yan'uwa, nagodewa Allah,Allah yaraya manasu. "Ameen,ya Allah, kukan ya'isa haka, Ashe haryanzu kinanan da kukannannaki" ummi tafadi haka tana sharemun hawaye. Murmushi nayi nace, "ummi kinki kifadamun inda mommy nah,take. Nayi missing dintafa sosai" kafin ummi tabani amsa wasu kannenta sukayi sallama, da gudu nabar jikinta naje na rungumesu, susu ukune, dayake duka both familyn ummi dana daddynah abuja suke,kadanne suka fita wasu garuruwan. Zama mukayi suka sani atsakiyarsu kowa yana murnar ganina,anata hirar yaushe gamo,abunda yake bani mamaki babuwanda yatambayeni inanaje,Saidai kawai murnar ganina suketayi. Sallar isha'ice tatayardamu. Muna idarwa muka Dora, kafin karfen goman dare wasu yan'uwan sunkara zuwa domin acewarsu bazasu iya hakura zuwa safiyaba. Harda maza kannen daddy, da kuma mata sa'annina Wanda wasunsu duk sunyi aure. Hira akeyi cikin nishadi,farin ciki idan yana kisa toyau ze kasheni, saboda ganina cikin dangina. Gaskiya kasancewa da dangi akwai dadi, Allah kahada mana kan zuri'a. Har karfen biyun dare muka kai anata hira,dakyar daddy yakatse hirar yakora kowa daki yace gobe a dora,gasu twins ma ba'abarsu abayaba sewasa suke suna danemun cinya. Part din saukar baki daddy yarakasu da kansa, nikuwa ummi tace yau tare zamu kwana,yau ta'ajiye kunyar yar farin setarairayata takeyi. Bayan nagama komai nashirin bacci na kwanta a gefen ummi, tunanin Dr,yafadomun arai wata balayayyiyar kewarsace ta baibayeni. Jinake tamkar nadakko wayata nakirasa,yanzu kome yakeyi koyayi bacci kokuma yana me oho? kwallace tacikamun ido nasan bazan iya sabo darashinsaba, "ya Allah kawaiwayo da hankalin mijina agareni" nafadi haka araina,hannu nakai nashafa cikina,shima nasan yayi missing jagwalgwalon abbbansa. Lumshe idona nayi na matsa jikin ummi,rungumeni tayi ajikinta atare muka saki ajiyar zuciya,bajimawa bacci yayi awon gaba dani dama yau bamugamuba.........

************

Dr,bayan yabar gidan mami gidansu yawuce ko zee taje can dataga mami batanan. amma yana zuwa yatarar batanan,se tambayarsama dasu umma sukayi yasuke. Daurewa yayi cikin danne abunda ke damunsa dan karsu gane yace sunan klu. Amma tsakanin d'a da uwa,seda umma ta fuskanci kamar wani Abu yana damunsa harta tambayesa yace mata babukomai, tasan halinsa da shegen muskilanci da zurfin ciki koda'akwaima wani Abu bafada mata zeyiba,addu'a kawai ta masa aransa. Yanayin sallar magriba yakara komawa gidan mami, wata nannauyar ajiyar zuciya yasauke lokacin dayaga kofar part din abude alamun mami ta dawo. Dasauri yanufi cikin gidan,mami da dawowarta kenan taji sallamar sa, a falo. Fitowa tayi tana amsa masa sallamar tare da masa sannu da zuwa. kamar yadda tasaba tarbarsa haka ta tarbesa,suka fara hira. Se baza kunne yake yaji ta inda mami zata sako masa zancen zee, seyaji shiru,sema tambayarsa datayi yasuke da kuma jiki_jikin zee, dantunranda zee tazo tagane tana dauke da juna biyu. Amsa mata yayi,atunaninsa ummi tanason wajigashine,shima ya waske, ganinyai dagaske mami bazata masa zancen zee ba. Mikewa yayi ya leka dakin da zee tasauka agidan yaga batanan,dakin mami ya leka nanma wayam. Mami dai binsa kawai takeyi da ido. Kasa boye tashin hankalinsa yayi,yazo yatsunna gaban mami yana rokonta tafito masa da zee. Sororo mami tayi tana kallonsa cikin rashin fahimta,tace. "Mahmud mekedamukane, meyasamu zainab dinne, dazan boyeta kotace maka tazo nanne. Cikin tashin hankali yasanarwa mami abunda ke faruwa. Mikewa tsaye mami tayi tana sallallami cikin razani. "Amma Mahmud,kayi gaggawar yanke hukunci, kasan yarinyarnan bata da kowa agarinnan amma ka kama kakoreta daga gidanka,wlh ni batazomun nanba, shiyasa ashe naketa kiran wayarta tun rana taki shiga, haba Mahmud da hankalinka da tunaninka ka aikata haka,nidai a gaskiya asanin danaiwa zainab bazata kawo wani gidankaba, kodan shegen tsoronta." wani yawu medaci dr,yahadiye zuciyarsa na bugawa da sauri dasauri,tamkar zata faso kirjinsa ta fito saboda tashin hankali yace, "mami bacin Raine kawai, mami baza kigane yanda najiba alokacin,lokacin dana shigo nagansu jinayi tamkar ana zaremun numfashina saboda bacin ciki" komawa mami tayi ta zauna tana sauke numfashi tace, "amma Mahmud baka tunanin wani ze iya hada mata wani tuggun,bakayi binkiceba kawai kayanke hukunci nidai gaskiya zuciyata ta kasa amincewa zainab ta kawo kwarto gidanka,alhalin da auranka akanta,gaskiya wannan Abu akwai lauje cikin nadi"
Chapter 44 · 0% Book details