← Book details Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 47

Sashe 9

Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaji gabansa ya fad'i, kin kira rumaisa basu tare da fu'ad acan.

Na kira fu'ad yace tun dax'u suka rabu, wai sunje wani Party ne kuma ya dawo kafin shi, na kira ammi ma tace duk yau bai je ba, ga wayar sa tana ringing amma ba respond.

Yace gani nan xuwa yanxu, ya tsinke wayar da sauri cikin tashin hankali, komai bai tsaya d'auka ba ya fito office da sauri, a harabar asibitin yaci karo da baffa d'auke da hidaya yana tafiya kad'an kad'an numfashin sa na fita da kyar, cak mera ya tsaya yana kallonsa cikin sanyin jiki har ya qaraso, ya xubawa hidaya idanu jikinta duk jini ya d'ago da sauri yana kallon baffa.

Meya same ta haka ko hatsari ne,
Baffa ya girgixa kansa yana miqawa Dr mera ita, da sauri ya karbe ta kuwa ganin yana qoqarin fad'uwa kamar qarfinsa ya Gaza.
*FYAD'E* aka mata likita, ya cutar da rayuwar mu.

Wata irin fad'uwar gaba ta dirar wa mera lokaci d'aya har sai da yaja baya saboda firgita, baffa ya Ciro kud'i cikin jikinsa ya d'ora a saman jikin hidaya da kyar yace
Wannan kud'in aikin hidaya ne kamin alqawarin hidaya xata gani a rayuwar ta dan Allah ka cika mata wannan burin k....

Yayi shiru sakamakon wani tari da yaxo masa lokaci d'aya ya dafe xuciyarsa had'e da durqushewa gurin, mera ya soma kiran nurses gurin cikin gaggawa ganin yanda jini ke fita bakin baffa.

Kafin su iso tuni ya xube gurin, mera na ganin haka ya juya da sauri yayi cikin asibitin da hidaya ganin numfashin ta sai ya dawo kuma ya d'auke alamar tana neman taimakon gaggawa.

Cire xanin yayi yana kallon gurin, da sauri ya rumtse idanunsa yana ja da baya dai dai lokacin wayar sa ta d'auki qara, ya ciro ta cikin aljihunsa da sauri Afiya ce, wannan Karon kuka take,
Baka xo ba yarima, har yanxu baa ganshi ba, jikina yana bani sultan ba lafiya ba.

Da kyar cikin sanyin murya yace ina hanya yanxu xan qaraso.

Ya kashe wayar gaba ki d'aya, xuciyarsa tafi aminta akan ya taimakawa hidaya domin yasan sultan mutane da dama suna can suna neman sa a yanxu hidaya kuwa bata da wannan gatan sai Allah sai shi a yanxu.

Wannan aika aikar da akayi wa yarinyar ko waye ya je mata da qarfi batare da tausayi ko concern na kasancewar ta qanqanuwar yarinyar da bata san menene wannan abin ba, nan da nan ya shiga bata taimakon gaggawa ciki kuwa harda d'inki, ya d'auki fiye da awa d'aya kafin ya gama, ya cire kayan jikinta ya goge mata da qaramin towel kafin ya sauya mata kayan xuwa na majinyata, ya saka mata drip kana ya fita kiran nurse d'in da xata kula da ita.

Saboda tsananin rud'ewa bai qara bin halin da baffa yake ciki ba ya fice.

Har xuwa washe gari babu sultan babu alamar sa, shi kansa fu'ad da qaseem a rud'e suke musamman sauran abokan nasa babu inda baa tura cigiyar sa ba.

Kwatsam sai ga jami'an tsaro sunxo da sultan sun same sa acan qauyen a hanya mutanen garin sun xageye sa suna kallon sa.

Jikinsa da kansa duk jinine babu alamar numfashi a tare dashi, Afiya ta xube gurin a sume, mera yayi kanta da sauri.

Innalillahi wa inna ilaihir raji'un shine abinda Dr mera ke nanatawa bayan x-ray d'in sultan ya fito.

Gaba ki d'aya family d'in hankalin su ya tashi jin abinda ya sami sultan na loosing memory.

Saukar marin da suka ji a gurin ya saka hankalin kowa komawa gurin, rumaisa ce ke dukan fu'ad.

Da ixinin wa kuka je wani Party, me ka jawo wa d'an uwanka haka, you are to blame fu'ad sultan bai san ko ina nan garin ba kaine ka jasa.

Mommy wlhy....

Yayi shiru sakamakon saukar wani Mari da ta qara d'auke shi da shi, a gigice ya nufi gurin sarki ya fad'a jikinsa yana kuka, granny ka gayawa umma ta daina duka na ba laifina bane.

Aliyu (mahaifin fu'ad, yayan Afiya idan baku manta ba) ya d'ago jajjayen idanuwan sa yana kallon fu'ad da kyar yace ya akayi ka bari ya dawo shi kad'ai bayan kasan bai san gurin ba.

Abba sai dana ce ya jira mu dawo tare yaqi shi baya jin dad'in jikinsa baxai iya jira a gama ba.

Amma shine ka kasa biyo sa ku dawo bayan kaji yace bashi da lfy, wane irin yaro ne kai ai kaine babba, Afiya ta fad'a tana kallon sa cikin bacin rai, fu'ad xai yi magana Dr mera yayi saurin dakatar dashi yana kallon rumaisa.

Karki sake dukan sa idan ba haka ba ranki xai yi matuqar baci, kafin ya juya ga sauran yana fad'in meyasa kuke ganin laifin fu'ad ne, kun manta taurin kai irin na sultan, kun manta sultan idan yayi niyar abu ba wanda ya isa ya dakatar dashi, idan ke da kike mahaifiyar sa kin masa magana bai ji ba saboda me xai ji maganar fu'ad.

Sultan xinari ne ko gold?

Dubi yanda ku ka cika asibitin nan gabaki d'aya, yan'uwa, securities, fadawa duk papa (sarki) ya kwaso yaxo dasu, xaku bashi lafiya ne, Sultan ya wuce qaddarar ubangiji ne kome, kuna so ku nuna baku yarda da qaddarar ba har kuke d'orawa fu'ad laifi, loosing memory ba yana nufin rasa rayuwa ne ko kuma baxai dawo normal ba xai tabbata haka, results d'in sa basu gama fitowa ba ballantana muyi saurin yanke hukunci akan abinda bamu da masaniya akan sa.

Kafin case d'in sultan, yarinya aka kawo min sa'ar yasmeen she was raped by unknown person, she is just 10years, yarinyar har yanxu bata dawo hayyacinta ba, marainiya ce bata da uwa, makauniya ce kuma bata da idanu, a yau ta rasa mahaifinta ta rasa gatan ta dalilin abinda ya faru da ita a jiya, dukan ku anan should think and put yourselves on her shoes idan kune ita ya xaku d'auki rayuwa, da wane hannu xaku karbi sabuwar rayuwar da xaku fuskanta a yanxu, she have nothing else, to hakane a gurin sultan shima ya fuskanci sabuwar rayuwa babu abinda yake buqata a gurin ku yanxu kamar addu'a, sultan yaro nane baxan barshi haka ba, xan nema masa lafiyar sa ko a ina ne a duniyar nan, kowa yaje gida, papa kayi haquri kaje gida sultan xai sami sauqi.
*littafina na kud'i ne idan baka biya ba pls kada na karanta*
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*
Haske writers Association
Fertymerh Xarah
Duk gurin jikinsu yayi sanyi, wace yarinya ce wannan, waye wannan ya cutar da ita haka.

Sarki yace ba inda xanje sai naga farfad'owar jikana kuma sai na saka an hukunta duka mutanen wannan qauyen dalilin wannan abin da suka ma sultan.

Merah yace a'a papa kada kayi haka idan basu bane fa, idan kuma acikin mutanen da suka je party tare ne fa, ko kuma idan wasu mutane daga wani wuri ne daban suka masa haka ba, meyiwuwa akwai abinda sultan d'in yayi har aka masa wannan hukunci dan Allah kayi haquri ka miqa lamarin ga ubangijin mu yafi kowa sanin dalilin wannan abin.

Shigowar Dr mera yayi dai dai da farfad'owar ta cikin qara mai raxanarwa wadda ke nuna a tsorace take, sai matse qafafunta take tana qoqarin sauka daga gadon, da sauri ya qarasa gurin ta ya riqeta gam, wannan riqon da yayi mata ya qara tsorata ta, ta Saki wata qara mai firgitar wa tana qoqarin barin jikin shi.

Hidaya......

Hidaya....

Ya soma kiran ta da kakkausar murya, tayi shiru tana sauraren muryar kamar ta taba jinta.

Tace baffana... ni baffana.

Dr fulani ta shigo dakin da sauri tana kallon merah, ihun ta na jiyo dama nayi tunanin ta farka.

Ta qarasa tana kiran hidaya menene cikin pullo
Tace Toi baffa am (ina baffana)
Fulani tace Baffa yahi wartime (baffa yaje ya dawo)
Tace Yaram e mako ( a kaini gurin sa)
Fulani xatayi magana mera ya katse ta is better kina yi kina koya mata hausa duk abinda xaki ce kina nuna mata shi da hausa, duk sanda bakya nan ban san ya xamuyi da ita ba.

Kaima kaso xancen likitan, inaji kaima d'in bafillace ne amma kace baka ji.

Yayi murmushi kad'an yace kad'an nake ji kuma ban iya mayarwa ba so kinga akwai gyara.

Hidaya ta riqo hannunta tana fad'in likita ki kaini inda baffana, baffana ya tafi ya barni tun jiya ban ganshi ba, yaje birni xai siyamin magani, ni ban ganshi ya dawo ba kuma dare yayi sosai sai naje neman sa, wani ne ya d'auke ni ya kwantar dani a hanya ya cire min xani ya saka min wani abu cikin fitsari na, akwai ciwo har yanxu akwai ciwo, ta fashe da kuka tana qoqarin nuna mata.

Kwalla ta taru idanun fulani cike da tausayin yarinyar, ta riqe hannunta tana girgixa kai kamar tana ganin ta, ba sai kin nuna min ba hidaya ai nagani ma Allah xai saka miki ko waye yayi maki wannan abin.

Ta juya tana kallon mera tayi masa bayanin komai da hidaya ta fad'a, ya xauna a hankali kusa da hidaya yana riqo hannunta, ta fisge da sauri cikin yanayin tsoro tana matsawa a hankali.

Likita waye shi wannan, kice yayi haquri kada ya qara sakamin.

Wannan likita ne wanda yayi magana da baffa har yace xai gyara miki idanu.

Hidaya ta qarasa gurin sa da sauri tana kuka, likita wani ya samin wani abu anan duba kagani tayi qoqarin bud'e masa ya hana ta duk da bai fahimci maganar ta ba amma ya lura tana fad'a masa ne, ya shafa kanta tare da rungumeta sosai a jikinsa, yana jin tausayinta ta ko ina ajikinsa, xai karbe ta hannu biyu ya riqeta amana, yayi alqawarin xame mata gata da farin ciki a rayuwarta kamar yanda xai riqe amira da yasmeen.

Haka hidaya ta tsinci kanta cikin nutsuwa bata san dalili ba amma xuciyarta na kwadaituwa da son jin muryar baffanta da d'umin jikin sa kamar ko yaushe.

A ranar Dr fulani ta xauna tare da ita, tana koya mata yaren hausa kad'an kad'an wanda xata iya ganewa.
Chapter 9 · 0% Book details