Sashe 15
Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sultan yayi shiru yana kallonta daga yanayin sa xaka gane baiji dad'i ba duk da baya fahimtar abinda suke magana akai, babu xato babu tsammani hidaya taji saukar kiss a kumatunta, duk gurin aka tsura masa ido, ya soma tabi da hannayensa yana murmushin farin ciki.
Aiman ya tsura masa ido yana kallonsa, farin cikin sultan hidaya ce, yana ganin murmushi da farin cikin sa a duk lokacin da yake tare da hidaya, kenan xai dauwama cikin farin ciki ne na har abada idan ya kasance da hidaya a rayuwar sa?
Lokacin barci yayi gobe akwai skul kuje ayi wanka a sauya kaya xuwa na barci kafin naxo.
Suka tashi da gudu suka nufi d'akin su, sultan ya tashi xai bisu merah yayi saurin riqa hannun sa.
Ina xaka je, kaima muje na shirya ka, ya juya yana kallon Afiya, ki had'a min ruwan wanka kafin naxo.
Hidaya muje muyi wanka da kanmu ba sai wannan qaxamar mai aikin tayi mana ba, kinga tana murxa jikin mu da xafi, fata ta sai tana ciwo kullum, ta shagwabe fuska.
Hidaya ta dube ta tana fad'in, ni ban iya wanka ba ko a gida baffana yake min idan nayi sai ya min dariya yace ban iya ba, kuma xai sake min wani, kuma baffana ya iya wanka sosai harda goyani yake yi.
Ai nima Mami idan tayi min wanka goyani take yi amma bata goya amira wai tayi qatuwa.
Suka soma dariya suna cire kayan su, da gudu suka isa toilet d'in, a tare suka shiga cikin jacuzzi suka soma wasa da ruwa.
Suna cikin wankan sai ga sultan ya shigo cikin nashi kayan barci.
Yasmeen ta xare idanu tana kallon sa, la yaya sultan meyasa kaxo kaga jikin mu, hidaya ta d'ebi ruwa sosai ta kwara masa a jiki, yaja numfashi da qarfi kamar xai shid'e, suka kyalkyace da dariya ita Ma yasmeen ta d'ebi ruwan ta kwara masa suka sake fashewa da dariya.
Ni kamar hayaniyar yaran can nake ji Aiman anya ba wata barna ce suke aikatawa ba.
Yace babu abinda suke yi banda wasa, me suke dashi na barna a dakin su bayan ga mai kula da su?
Tace haka ne kuma, ta cigaba da shirya shi amma duk hankalinta na kan su.
Sun jiqe sultan jagab da ruwa, sun ma toilet d'in jagab duk sun watsar da kaya ko a ina, sultan ya shiga cikin jacuzzi d'in shima su watsa mashi ruwa shima ya watsa masu.
Aiman ka saurara fa har da dariyar sultan nake jiyowa, yayi shiru kamar mai naxari yana saurare sai kuma ya tashi da sauri ya fita tabi bayan shi.
Kai tsaye toilet d'in nasu suka nufa, abinda suka gani ba qaramin tsorata su yayi ba.
Daddy kayi haquri shine yaxo ya same ni anan.
Wata tsawa da yayi masu shi kanshi sultan sai da ya rikice, kansa yayi wata sarawa da sauri ya dafe kan jiri na neman dauke shi, merah yayi saurin riqo sa suka fita.
Afiya ta riqo hannun yasmeen da hidaya ta fito dasu fuskar nan tata babu annuri, nan da nan suka soma matsar kwalla musamman da suka ga ta janyo wayar charger babu xato suka ji saukar ta a gadon bayan su, wata xabura suka yi lokaci d'aya tare da fashewa da kuka.
Shishshsh ta d'ora yatsan ta a bakinta, ku dawo nan kafin raina ya baci.
Hidaya ta rikice baa taba dukan ta irin wannan ba, Mami kiyi haquri yasmeen ce tace muyi da kanmu.
Sai kuma kuke yi da sultan, ku saka namiji tsakiyar ku kuna wanka idan shi bai da hankali ku kuma.
Wallahi Mami shine yaxo ya same mu, hidaya ce ta soma watsa masa ruwa.
Qarya kike kece kika soma watsa mashi ruwa.
Uku uku tayi masu masu xafi sai kuka suke wiwi cikin daren, kukan da daga jinsa kasan ba komai acikin sa sai xallar shagwaba.
Aiman kuwa da kyar ya shawo kan matsalar sultan har ya samu yayi barci, kallon Afiya yayi kinga yanda yake xabura akwai abinda yake son tunawa wanda ya firgitashi, na kasa taimaka mishi a wannan Karon ban sani ba ko tsawar da nayi masu tana da nasaba da matsalar da ta shafe shine?
Tsawa
kuma yarima?wace irin tsawa ce da xata saka mutum loosing memory irin wannan.
Tsawar da nayi masu ta firgitashi, idan haka ne tabbas kome aka masa a wannan lokacin yana cikin firgici.
Wasu hawaye suka xubo a idanuwanta cike da tausayawa, har sai yaushe sultan d'ina xai dawo cikin hayyacinsa, dubi yanda ya dawo wai yau sultan ke wasa cikin qananan yara a toilet tun da nake ban taba qanin sultan yayi wa ko jariri wasa ba balle wad'anna baligan yaran.
Murmushi aiman yayi, yaran da basu san ciwon kan su ba ina suka xama baligai, da xaki xauna ki nutsu Afiya hidaya ita ce farin cikin wannan yaron, farin cikin sa, dariyar sa, walwalar sa yana yin sune a duk lokacin da yake tare da ita, ina tunanin warakar sa tana tare da yarinyar na yanke hukunci xan aura masa ita.
Afiya ta dube shi da sauri tana had'iye kukan da yaxo mata, xatayi magana yayi saurin katseta ta hanyar d'ora yatsansa akan labbanta,
I promise you xan raba auren idan sultan ya warke yaji baya son hidaya ko kuma idan hidaya ta mallaki hankalin ta bata son sultan, kimin wannan alfarmar for the sake of our beloved son, idan muna sonsa dole mu bashi farin cikin sa a kusa dashi, hidaya ba muharramar sa bace kamar yasmeen, dubi abinda ya faru yanxu idan xamu hana yasmeen kusantar sa ai bamu isa mu hana shi kusantar hidaya ba which is wrong, kissing d'in ta yayi dax'u wanda yayi tunanin wasa ce yake da ita anan gaba me kike tunanin xai faru?
Xan iya ajiye duk wani mulki ko sarauta dake kaina a yau na duqa na roqe ki wannan alfarma, nayi maki alqawarin raba auren da xarar d'ayan su bai amince ba.
Juyawa tayi ta fice da sauri batare da ta qara kallon sa ba, ya bita da kallo kafin ya sauke numfashi.
Washe gari duk shirin da ake masu hidaya taqi sakin fuskarta, yasmeen kuwa sai fara'ar ta take tama manta da xancen jiya.
Sama sama ta kora ruwan tea shima sai da Afiya ta tsawatar mata, tana sha tana hawaye, suna gamawa
ta d'auki jakarta ta fice da sauri xuwa harabar gidan yau baxata shiga d'akin sultan ba kamar yanda take yi kullum kafin ta fita, tana fushi dashi sosai tunda saboda shi aka dake ta.
Yasmeen ta d'auki tata jakar tace, bye Mami tana waving hannunta, ita Ma Afiya ta maida mata martani.
Basu jima da tafiya ba sai ga sultan ya fito da saurin sa kuwa ya soma dube dube babu su babu alamar su hakan ke nuna masa tuni abokan wasan nasa sun fice.
Suna had'a ido da aiman bakinsa ya soma motsi wanda da kyar sautin muryar sa ta fito.
Hi... da... ya.. ya fad'a da kyar kamar an kwato kalmar daga bakin sa, duk suka xuba masa idanu cike da mamakin yin maganar sa.
*masu tambayana meyasa bana saka sarauta a littafin bayan ya qunshi sarauta, bana son had'a littafi biyu duka sarauta tunda bayan wannan xanyi mulki ko sarauta2 shiyasa na cire duk wani mulki da sarauta a wannan buk d'in, ayi haquri da yanayin sa*
*littafina na kud'i ne, kada ka karanta baka biya ba*
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: SULTAN MERAH*
Haske writers Association
Fertymerh Xarah
Hidaya....
Merah ya maimaita sunan yana kallon sa, da sauri sultan ya gyad'a kansa yana qara maimaita mashi shima.
Hidaya taje School me kake so?
Hidaya...
Sultan ya qara maimaita mashi.
Sai anjima xata dawo, xo muje yau xaka gaida sarki jiya duk baka je ba, yaja hannunsa suka fice.
Yau kam hidaya a skul duk wanda ya santa da shegen surutu yasan yau ba lafiya, shiru tayi banda ido da take bin kowa dashi a class d'in ba abinda take, ko breakfast qin fita tayi ba yanda yasmeen bata yi da ita ba amma taqi.
Suna dawowa gida yasmeen ta soma ba Afiya labari hidaya taqi taci abinci Mami, an tashi breakfast bata je wasa ba, kuma ko magana batayi a class da kowa ba, ki tambaye ta meyasa.
Afiya ta juya tana kallon hidaya da ta kwanta lagwas a sofa duk tayi wani sanyi kamar ba ita ba, tausayin ta taji, ta taba jikinta ba xafi, tace menene damuwar d'iya ta, waye ya taba min ke a gidan nan?
Kamar jira take hawayen da take maqalewa suka soma xubowa, sautin kukan ta ya fito harda sheshsheka, dai dai lokacin mera ya shigo tare da sultan sai yanxu suka dawo.
Yana d'ora idanunsa akan hidaya ya fincike hannunsa daga mera ya nufe ta da sauri.
Meke damun tane?
Shine abinda nake tambayar ta, yasmeen tace ko abinci hidaya bata ci ba kenan tun tea d'in safe dana matsa mata tasha ne kawai a cikinta, meyasa hidaya.
Amira da salwa dake cire uniform d'in su suka tabe baki cikin takaici suna yatsina fuska cikin harararta.
Aiman ya riqo hannunta yana kallon ta, menene hidaya.
Cikin kuka tace ni baffana, ka kaini inda baffana, ina so na ganshi, shi bai taba duka na ba.
Afiya ta xare idanu tana fad'in au wai saboda nayi maki bulala uku jiya da dare kike wannan kukan da fushi?inaji har yasmeen d'in na daka ko, baxakiyi laifi a hukunta ki bane?
Aiman yace banda abinki kinga yasmeen tana fushi ko kuka, ta girgixa kanta, baa fushi da mahaifi hidaya, abinda kuka yi laifine kuma Mami ta hukunta ku da nine flushing d'in ku ma xanyi gabaki d'aya kowa ya huta da fitinarku, kuma daga yau kar na qara ji ko ganin kuna wanka da sultan, not even sultan ku biyu d'innan idan na qara ganin ku cikin jacuzzi kuna wanka tare sai na maku mugun duka.
Cikin kuka tace ai shine ya xo bamu kira sa ba kuma shine ya shiga batare da munce ba.
Yasmeen tace amma ai kece kika fara watsa mashi ruwa shiyasa shima ya shiga ya watsa mana.