← Book details Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 47

Sashe 4

Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jeji da ita yake xuwa, wani xubin ya kan goyata ne yayi yawo da ita acikin jejin tare da dabbobin sa, mutane tun suna masa dariya har suka xo suka daina saboda bai taba kulawa dasu ba,
Kullum xai dafa madarar shanu ya bata, baya son kukan ta ko kad'an duk da bata da fitina, idan tana rashin lafiya tamkar shine ba lafiya komai qanqantar ciwo dole sai ya dage an bashi gado a qaramin
asibitin su dake garin.

Kowa yasan hidaya yar gidan ma'awiya, kowa yasan soyayya da kulawa dake tsakanin yarinyar da mahaifinta.

Lokacin da ta soma rarrafe a lokacin mahaifinta ya fuskanci bata gani, bai yarda da xargin sa akanta ba har sai da ya kaita asibiti aka duba ta aka qara tabbatar masa tabbas makauniya ce.

Fadin irin halin da ma'awiya ya shiga a ranar baxai fadu ba, yayi kuka har ya gode Allah, dalilin haka wata soyayya da shaquwa ta qara shiga tsakanin shi da ita, ya dauki lokacin sa da rayuwarsa kacokan ya damqa wurin kula da ita, tun da ta fara bud'e baki tayi magana ya koya mata da ta kira sa baffa.

Wasa wasa rayuwa ta soma ja, yau gashi hidaya tana shekara goma cif a duniya.

Yarinya ce mai haquri sosai, bata da yawan magana ko neman fitina gurin abokannin wasan ta idan sun xo gidan, tana yin komai nata a natse, idan ka ganta xaka rantse idanunta basu da matsalar komai domin a bud'e suke farare qal dasu, xaka ga dariyar tane idan tana xaune da mahaifin ta bayan shi sai dai murmushi ya had'a ka da ita kawai.
ita wata irin miskilar yarinyace da wuya ka fahimci inda tasa gaba domin fuskarta bata nuna abinda ke xuciyarta komi girmansa da muhimmancinsa koda xata cutu.

An haifeta a gidan, ta taso cikin gidan tayi rayuwa acikin gidan tun tana koyon xama, rarrafe, har tafiya shiyasa lungu da saqo na gidan ba inda bata sani ba, ba inda baxata shiga ba kai tsaye batare da sandar ta, ta dogarawa ba, idan ka ganta da sanda a hannu tana tafiya tabbas ta fito waje ne, a hakan take taimakawa mahaifinta ta tsar nonon shanu ko madara, wani lokacin ma ta kan taimaka masa gurin d'aure dabbobin idan sun dawo jeji.

Xakuyi mamaki idan nace maku a wannan shekarun nata tayi kusa hardar qur'ani saboda yanda baban ta ke xaunar da ita a koda yaushe yana koya mata tun tana qanqanuwar ta, tabbas bata gani amma babu ayar da xaka janyo mata a qur'ani bata karanta ta ba sai kuwa wadda bata kai ba.

Bata San wani harshe ba a rayuwar ta bayan nasu na fulani, duk ruggar basu da bahaushe ko mai yare da hausa, manyan ne kawai ke hausa sama sama saboda suna shiga gari tallar nono amma mafi yawan yaran d'if suke.

Baffa yau xan bika jeji, na jima banje ba yau ka barni naje.

Kiyi haquri har xuwa wani lokaci Hidaya bana son kina fita ko kad'an, sannan gasu Asiya duk xasu xo su taya ki xama kuyi wasa anan ko bakya farin ciki da xuwan da suke yi na dakatar dasu.

Ina yi baffana, ina kuma jin dad'in kasancewa dasu shiyasa nake da burin fita dasu tallar nono a rugar Ard'o, yaushe ne xan fara baffa?

Xan kaiki rugar ard'o amma ba dan ki siyar da nono ba, rugar kakan ki ce ai na gayamaki mahaifin maman ki.

Aa baffa ni nafi so naje tare dasu Asiya, ina so naje tare dasu muna wasa a rafi kullum suna bani labari.

Su idanun su masu lfy ne sabanin naki kada ki biye masu.

Baffa ni sai yaushe xan fara gani?

Yayi shiru yana kallonta kafin yace duk ranar da Allah ya sauke ikon sa akanki, bani da wannan burin a yanxu kamar na ganki da idanun ki kina gani kamar kowa a wannan rugar, xan iya salwantar da duk abinda na mallaka domin na sama maki lafiyar idanun ki idan har aka tabbatar min da cewa xaki gani.

Tayi murmushi a hankali tare da riqo hannunsa tace baffa ni babban burina a rayuwa shine naga wannan baffana mai sona, nabi baffana duk inda xai je ina biye dashi sannan kuma na ganni tare da qawaye na muna xuwa rafi wasa.

Da yardar Allah idan ina numfashi a rayuwar nan burin ki xai cika Hidaya, ta tashi tana tsalle kafin ta lalaba ta haye bayansa tana fadin baffa yau duk baka goya ni ba, ni baxan sauka ba.

Ya tashi da ita yana murmushi yana juyawa da ita cike da farin ciki.

Kyakkyawa ne matuka, dogo fari amma farin nasa ba mai irin hasken nan bane, fari ne daya cakud'e da gogayya cikin jin dad'i
hutu da wayewa irin ta yan boko, ma'abocin fad'in qirji da alamun qarfi ta ko ina, abin alfaharin kowacce mace, har maxa yan'uwan sa suna yaba shi.
*SULTAN AIMAN MERA* kenan mai shekaru 20 kacal a duniya, kasancewar sa d'an wasar buga ball ya saka jikinsa wani irin girma da qarfi da xakayi tunanin ya wuce shekarunsa.

Ba miskili bane dan bashi da shariya ko rashin qin magana idan aka masa,
sai dai shi mutum ne da baya son wasa ko dariya da yara musamman da baya son raini ko kad'an
, abu kadan yana amusing din sultan, a very jovial and loving personality.

Xaune yake gaban mahaifin nasa fuskarsa a cunkud'e da alama baya cikin walwala daga yanayin fuskarsa,
Dad kayi haquri ka barni anan, na fi son kasancewa ta anan qasar akan Nigeria please.

Na riga na gama magana gobe Nigeria xamu je, almost 2years an a half rabon da muje qasar mu, kuma ba wai nace baxa mu dawo bane ai xamu dawo inaji hutu kuke yi ai a skul ko kana da wasar da xaka buga ne mu jira ka.

Ya girgixa kansa a sanyaye, tamkar ya fasa ihu yake jinsa.

Asibitina tana buqatata sosai bayan wannan Ma mai martaba ya nemi da mu koma na d'an wani lokaci idan kunyi resuming school xaka iya dawowa ba wai ina nufin xamu koma gida Nigeria da xama baki d'aya bane na canxa ma makaranta.

Sai a sannan ya sauke numfashi kad'an kafin ya tashi yayi hanyar dakin sa.
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERA*
Haske writers Association
Fertymerh Xarah
Yanda yake sharara gudu a titi sai kayi tsammanin tashi sama xaiyi, fu'ad kallon sa kawai yake kafin ya girgixa kansa a ransa yana fad'in Allah ya kyauta.

Dai dai gate din gidan su fu'ad yayi parking batare da yayi yunqurin shiga gidan ba, fu'ad bai kula sa ba ya fita daga cikin motar yana Jan tsaki, a fusacce ya qara Jan motar da qarfi ya bar unguwar.

Yanda ya shigo gidan xai tabbatar maka ba lafiya ba, cikin gidan ya nufa, akayi sa'a kowa na babban falon ya shigo ba sallama, duk suka xuba idanu suna kallon sa cikin mamaki yanayin shigowar sa.

Tafiya yake da sauri batare da ya d'aga kai ya kalli kowa a falon ba, ya saka hannuwansa da qarfi yaja rigar dake jikinsa nan take ta rabe gida biyu, yana qoqarin hawa step, Afiya tayi saurin dakatar dashi.

Kai mahaukacin ina ne xaka shigowa mutane falo haka ba sallama ballantana gaisuwa, me ya hau kanka ne haka?

Yayi shiru batare da ya tanka ba,
Ba magana nake maka ba? ta fad'a cikin tsawa tana kallonsa, ya juyo yana kallonta idanunsa sunyi jawur,
Meya same ka haka, xaka min magana ne ko sai na d'auke ka da Mari yanxu.

Ya bud'e idanunsa sosai yana kallonta da kyar ya bud'a baki
Yace Mami gaban yaran can kike min ihu haka salon su raina ni.... bata bari ya qarasa ba ta sauke masa lafiyayyun yatsun ta a kuncin sa,
Wannan ce tambayar da nake maka, xaka amsa min ne ko sai na qara ma.

Ya shafi kuncin sa yana haqiye wasu yawu da kyar cikin bacin rai, ya motsa bakin sa a hankali wanda ita kad'ai ke jiyo abinda yake fad'a,
Yace ba abinda ke damuna,
Saboda wane dalili xaka shigo mana falo ba sallama, ba gaisuwa, don't you have respect for that?

Cike da bacin rai ya juya yana kallon mutanen dake falon, ina wuni ya fad'a da karfi kafin ya haura sama batare da ya qara kallonta ba cikin sauri dan kar ta samu damar dakatar dashi.

Afiya tayi shiru, ta rasa wane irin yaro ne sultan, ta juya ta qarasa cikin falon, ina ma Aiman na nan da qila xai mata maganin sa,
Yana shiga sashen sa ya sakawa qofar falon key, kana ya nufi d'akin sa, kai tsaye toilet ya shiga acan ya cire komai nasa ya wurgar, shower ya sakar wa kansa tare da lumshe idanuwansa, wannan toxarcin da Mami ta masa yayi mugun bata masa rai fiye da abinda d'an fulani yayi masa, a gaban su yasmeen da Amira xata mare sa, yanxu ya xasu riqa kallon sa?

Baffa naji dad'in da ka sauya min slippers d'innan, amma kaine xaka riqa min kwalliya da wadannan kayan saboda ni ban iya amfani da su ba.

Jin yayi shiru tun dax'u da take ta faman surutu ya saka ta riqo hannunsa,
Jikina ya bani akwai abinda ke damun baffa, ta matsa a hankali had'e da xama a saman qafafun sa,
Baffa meya same ka, ka gayamin naji.

Batare da tunanin komai ba ya kwashe duk abinda ya faru ya sanar da ita.

Tayi shiru tana sauraren sa, abinda ke xuciyarta tabbas baxaka iya karantashi a fuskarta ba, saboda ita wata irin yarinyace da baka gane inda ta dosa, a shekarunta tabbas ta gane ko waye wannan yaci xarafin mahaifinta, meyasa ya mare sa,
Baffa kayi haquri, ka daina tunanin sa kaji, kace idan mutum na saka damuwa a xuciyarsa xai kamu da wata cuta, ni bana son wani abu ya same ka har ka barni, ta qanqamesa sosai tana hawaye.

Qamshin turaren dake jikinsa ta shaqa a hankali ta d'ago kamar wadda ke kallon sa,
Baffa wannan turaren na jikin ka fa, a ina ka samu.

Cikin son kauda damuwar dake xuciyarsa yace inaji turaren wannan marar mutuncin ne dana had'a jiki dashi, tun dax'u turaren ke damuna nima.
Chapter 4 · 0% Book details