← Book details Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 47

Sashe 28

Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga lokacin suka d'auki gaba babu mai kula wani acikin su abinda basu taba yi ba tun tasowar su kuwa.
*littafina na kud'i ne, idan baka biya ba kada ka karanta, xaka biya haqqi inda baka da iko, mai buqata yayi mgn 08169334980*
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*
Haske writers Association
Fertymerh Xarah
Kwanan su uku basa magana da juna, duk sun jigata saboda basu saba ba sai suka kasa jurewa dole suka shirya kowane yana da laifi a cewar su.

Amira da salwa basa gidan suna qasar Cairo acan suke karatun su yanxu na gaba da secondary, tun bayan shekaru uku da suka wuce aka sanya su, acan suka had'u da Aryan da Arham (El'mustapha) sanin suna da alaqa ta jini da juna ya saka su sakin jiki dasu inda suka yi matuqar sabo da juna, a taqaice sun manta da soyayyar yayyun su biyu da suke so sun bud'e sabon shafin soyayya da twins d'in Jiddatulmusty.

Fitowar ta wanka tana tsaye bakin mirror tana tsane gashin kanta da qaramin towel, ta cikin mirror d'in ta tsurawa yasmeen ido dake kwance akan gado tana chatting kamar ba fita xasu yi ba, ta girgixa kanta tana jan qaramin tsaki.

Yasmeen ta d'an dube ta tana fad'in, ke kuma wannan tsakin haka ke da wa?

Hidaya bata kula ta ba, ta cigaba da shirin da take yi, yasmeen kuwa gyara kwanciyar ta tayi batare da ta damu da xasu fita ba.

Cikin qanqanin lokaci ta shirya cikin Riga da skirt na lace marar nauyi bata bi ta kan yasmeen ba ta d'auki qaramar jakarta ta rataya tare da d'aukar key na mota ta juya xata fice.

Wai har kin shirya ne, shine baxaki jirani ba yasmeen ta fad'a tana qoqarin saukowa daga kan bed d'in bayan ta jefar da iPhone dake hannun ta.

Kinsan haifa ta kika yi dole na jira ki har ki gama abinda kike, mtsew ta sa kai ta fice, yasmeen ta biyo bayan ta da sauri, a falo suka ci karo da Afiya da fu'ad xaune.

Mami kiyiwa hidaya magana ta jirani dan Allah, yanxu xan shirya fa.

Afiya ta dube ta tana fad'in meyasa xakuyi tafiyar daban daban ne, ki jira ta batare kuka saba fita ba.

Baxan jira ta ba mami, tun d'axu nake mata magana tayi wanka ta shirya kafin nagama gyara d'akin daddy amma sai tayi kwanciyar ta tana chatting, har na gama naje nayi wanka tana nan a kwance, ni baxan jira ta ba.

Afiya ta dubi yasmeen tana fad'in dama nasan ayi haka game dake da wannan wayar, xan saka daddy ya karbe ta a huta.

Yasmeen ta shagwabe fuska tana kallon ta sorry mamee daga yau na daina, kice hidaya ta jirani.

Hidaya ta nufi hanyar fita falon tana fad'in idan na jiraki na xama shashasha kamar ke kenan marar aikin yi, kije kiyi ta kwanciya akan gadon mana.

Wait ma idan kinje ni dame kike son na tafi inaji mota d'aya muke amfani ni da ke dan haka ki jirani yanxu xan shirya I promise.

Hidaya ta jefa mata key d'in motar tana fad'in na riga na fad'a baxan jira ki ba, ta dubi fu'ad da tun da suke rigimar bai tanka ba tace yaya fu'ad dan Allah xo ka sauke ni gidan su Aneesa yau ake bikin ta, ina ta so ma na gayama, ta fad'a da qaramin murmushi akan fuskarta.

Yace ki jirani a mota ina xuwa, ta gyad'a kai kafin ta dubi Afiya tana fad'in Mamee na tafi sai na dawo.

Tace a dawo lafiya, ko kallon inda yasmeen take batayi ba ta fice, yasmeen ta tunxuro baki tana kallon Afiya.

Amma mami sai kace ke baki isa ki hanata taji ba, shikenan ita idan ta kafe akan abu sai a bar ta.

Afiya ta tashi tana fad'in ke kuma da kika kafe akan waya akwai wanda ya hana ki ne, ai hidaya ce maganin ki gidannan kuma game da wannan wayar sai mun sami matsala dake, har raba maku aiki nayi saboda ba abinda kuke yi a gidannan nace idan wannan ya gyara d'akin daddy yau wannan ya gyara gobe, nan kika dawo falo kika kira sultan kina qorafi mami ta saka ki aiki bayan ga bayi a gida, ke baki iya komai ba, ina ji sultan d'in na fad'in menene a gyaran d'akin da har sai an saka ki duk masu aikin dake gidan, kullum hidaya ce take gyarawa ko sau d'aya bata taba qorafin bakiyi ba,
ko uban wa xai je yayi maki gyaran d'akin mijin ki, girki ma baki iya komai ba kina ganin ko yaushe idan ina kitchen hidaya na shiga ta tayani, ke kuma jikar sarki kina kwance kina chatting, xaki gane kuskuren kine akwai lokacin da kud'in uban ki ko sarautar gidan ku baxasu hana namiji wulaqantaki ba idan kika kasance ballagaxa marar moruwa a gidan ki auren ki, Afiya ta sa kai ta fice tana jan qaramin tsaki.

Yasmeen ranta ya baci sosai, mamee ta disgata gaban wanda take so, ta xubar mata qima a gurin sa ko ya yake kallon ta a yanxu, ta soma bubbuga qafafuwan ta cikin shagwaba kamar xatayi kuka.

Fu'ad ya d'ago yana kallon ta, wata qaramar riga ce a jikinta iya gwiwa, ba qaramin fito da shape d'in ta rigar tayi ba, suna had'a ido gaban su ya fad'i lokaci d'aya take nutsuwa taxo mata lokaci d'aya da kyar ta wayance tana fad'in,
Please yaya fu'ad ka hana hidaya tafiya ta jirani yanxu xan shirya, wallahi bana jin dad'in tafiya ni kad'ai bada ita ba.

Tun da ta soma magana yake kallon siraran labbanta dake motsi a hankali kamar basu ke furta maganar ba, tare da sauraren muryarta dake fita cikin nutsuwa da taushin kalami, akwai wani abu a tare da ita wanda babu a gurin amira, yau ne ya fara tsayuwa ya qare mata kallo sosai, ya tashi batare da yayi magana ba yasa kai ya fice saboda wata kasala da ta saukar masa lokaci d'aya, tabi bayan shi da kallo kafin ta tabe baki tasa kai ta fice.

Hhhhhhh da gaske yaya sultan, amma shine sai yanxu kake gayamin....

Yasmeen dake shigowa falon Umma (maman aiman) ta fad'a idanun ta akan waya da alama video call ne take yi.

Hidaya dake xaune a qasan traditional carpet na sarauta
ta tabe bakin ta tana cigaba da sakawa d'inkin da ta karbo wasu irin beats masu kyau,
Umma tace hidaya yaushe kika gama saka wad'annan duwatsu haka naga abin da yawa.

Yanxu xan gama, telan ya nuna min iya inda xan saka ai,
kuma fa umma ya raina ni dana bashi kud'in d'inki har dana saka beat amma dana je karba wai bai sami lokacin sakawa bane nayi haquri.

Masu d'inkin nan haka suke hidaya bama kamar Mohd naga haka yake wa su amira dan yaga suna son d'inkin sa kuma da yake su fitinannu ne ba kamar ke ba sai suke yin dai dai da shi.

Hidaya tayi murmushi batare da tayi magana ba dai dai lokacin yasmeen ta gama wayar da take ta dubi hidaya tana fad'in wannan qaseemu friend d'in yaya sultan yana waje yana jiran ki, tun ranar dana saka pic namu a status ya takura min, kije ki same shi yana jiran ki.

Hidaya ta tunxuro baki tana fad'in ba inda xanje, kice bana nan baki ganni ba.

Umma kuwa kallon su take sanin abinda ke kan hidaya wanda su basu sani ba ya saka ta fad'in, shi kuma qaseemu yaushe ya fara xuwa gidan batare da yaxo mun gaisa ba, ke yasmeen hidaya aiki take yanxu kuma kin gani jeki fad'a masa ni na saka ta aiki.

Yasmeen ta juya tana fad'in an gama ranki shi dad'e, our latest granny mai ran qarfe ke da wancan mijin naki, hidaya tayi dariya tana kallon umma,
Gaskiya umma yasmeen ta gama raina ki, ya kamata kiyi maganin ta.

Yasmeen ta fice tana dariya, bata jima ba sai gata ta dawo ta xauna
tana fad'in umma yau fa d'an bisa ranki yaya sultan xaa bashi Award nasa na ball da suka buga, nasan yau a gindin TV xaki tare.

Hidaya ta kaimata duka cikin wasa tana fad'in wannan bakin naki baxai fad'i kalma mai dad'in sauraro ba, idan yaya sultan d'an bisa ranta ne to waye acikin ran?

Sarki mana, yasmeen ta fad'a tana ware idanun ta, umma ta soma dariya.

Tun da ta koma sashen su, lokacin kallon yayi ta soma tunani tana son ganin wanne irin ci gaba ya samu a shekarun da tayi bata ganshi ba? ta tuna sura da kyau irin nasa, yana da wasu ilhamomi da bata taba ganin kowa da irin su ba wanda take addu'ar mijinta ya kasance dasu amma na gari kuma ba mai kyamatar mutane da wulaqanci ba.

Ta tashi ta fita daga d'akin ta nufi falo, su uku ne xaune a falon sun tsurawa TV idanu, daddy, mamee da yasmeen.

Wannan ne Karo na farko da ta soma fitowa ayi kallon da ita, duk sun yi mamakin haka, yasmeen xata yi magana Aiman yayi mata alama da hannu akan tayi shiru, hidaya ta nemi d'aya daga cikin sofa ta xauna idanun ta akan TV dai dai lokacin kuwa aka hasko sa da qaton cup na silver a hannun sa, mai matuqar kyau da tsada, tayi turus ganin kyakkyawar xuciyar sultan ma'abociyar kwarjini ta CIA fuskar d'irkekiyar akwatin TV d'in jikin bango plasma dake falon,
Cikakken matashi d'an shekara ashirin da biyar, ya xama qaton gaske
kamar mai shekara talatin, yana da wata irin halitta da kalar fata mai d'aukar hankali da fizgo xuciya xuwa gare sa.

Girman da ya qara ya bata mamaki matuqa, dogo sosai mai ginannen jikin da babu qiba babu rama a jikinsa, ba kamar yanda yake a da ba, ko dan ta jima bata ganshi ba, taga kamar dukkansu babu mai mamakin sauyawar shi.

A yanxu idan ka kalle shi mayuwaci ne ka banbance nationality d'insa ya xama kamar wani d'an qasar Egyptian.

Ita kanta da ta kalle shi taji yayi mata kwarjini ainun ya kuma burge ta, burgewa ba kad'an ba, tace a ranta irin wad'annan maxan tsiraru ne a cikin al'umma, ashe haka yaya sultan ya ke da kyau?
Chapter 28 · 0% Book details