← Book details Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 47

Sashe 7

Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace idan xaka fahimce ni ina so ka gane wannan kud'in aikin bani kad'ai keda alhaki akan su ba, akwai likitoci na kwararrin idanu da xamu gayyato a had'a ayi mata wannan aikin, domin yana da matuqar hatsari, dole ne kowane likita a bashi haqqinsa bayan kud'in da xaa biya na kayan asibiti da jinya amma na tausaya Ma xan rage Ma wani abu aciki ka bada miliyan d'aya da dubu d'ari takwas.

A hankali baffa ya share wasu hawaye da suka xubo masa koda xai siyar da komai nasa daya mallaka a duniya ya xauna tsirara ne sai ya nemawa hidaya lafiyar idanunta sai ya bata wannan farin ciki koda kuwa shine damar shi ta qarshe.

Likita yaushe xaa xo ayi aikin.

Yace xan rubuta maku magani kuje ku siya wanda xata fara sha daga yau, nan da kwana goma idan kun had'a kud'in kuxo ayi mata aikin.

Baffa yace naji kace aikin yana da hatsari koda baxan kasance a gurin ba, ka kula min da hidaya na baka amanar ta, ita kad'ai nake so da qauna a duniyar nan bayan mahaifina dake raye, ita kad'ai ce nake kallo naji sanyi a cikin xuciya ta cikin kowane hali, haka duk duniyar nan bata da kowa wanda ya fiye mata ni a rayuwarta, ni kad'ai ne gatan ta likita.

Mera yayi murmushi yana fad'in kada ka damu insha Allah xamuyi nasara akai xaka rayu da yar'ka cikin farin ciki kamar kowane UBA.
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*
Haske writers Association
Fertymerh Xarah
Dr.

Fulani sai kallon su take da murmushi ganin yanda suke ta murna sun kasa boye farin cikin nasu, ta dubi kyakkyawar yarinya,
Tace Noi inde ma?

Cikin murmushi hidaya ta bata amsa da Inde am hidaya.

Fulani ta jinjina kanta tana fad'in suna mai dad'i ya dace da mai shi.

Dr mera yana sauraren su duk da ba ji yake ba, ya gama rubuta masu maganin duka ya bawa baffa yana fad'in fulani taimaka ki nuna masu pharmacy su siye duka xasu samu maganin anan asibitin.

Baffa ya tashi hannunsa riqe dana hidaya yace likita mun gode sosai Allah ya taimake ka kamar yanda ka taimake mu,
Dr mera yace amin,
Kawu mun gode sosai...

Suka ji ta fad'a cikin sanyin murya, baffa da fulani sai kallon ta suke da murmushi, mera kuwa tsura mata idanu yayi yana kallonta kafin daga bisani ya Saki murmushin da ya fito har cikin xuciyarsa ya riqo hannunta yana fad'in.

Kada ki damu hidaya ba sai kin min godiya ba nima baffan kine, ina da yarinya sa'ar ki sunan ta yasmeen idan kin soma gani xan had'a ku qawance amma ita tana son boko sosai kuma tana xuwa ke kuma dax'u naji kincewa baffan ki bakya so.

Tayi shiru dan bata fahimci komai acikin maganar tasa ba, lura da hakan ya saka mera tunawa da taborar da yake ashe yarinyar bata jin komai acikin hausa gwanda baffanta kenan.

Fulani tayi mata bayanin duk abinda mera yace, aikuwa da sauri ta soma tsalle Miyi di, miyi di (ina so, ina so)
Basu jima a asibitin ba suka siye maganin suka kama hanyar garin nasu.

Yaya sultan wai kaxo inji umma,
Yau kuma ni umma ke nema, me akayi ne?

Ta yatsina fuska kafin tace nima ban sani, ta juya tana qoqarin ficewa ya kira ta,
Xo nan Amira..., ba musu taxo tana kallon sa,
Daga yau koma ince daga yanxu idan ina magana dake kika sake juyawa xaki tafi batare da ixini na ba sai nayi maganin ki gidannan, yaushe kika fara raina ni ne haka.

Kayi haquri yaya ta fad'a cikin shagwaba sanin halin sa tsab xai iya marin ta a gurin.

Kije kice baki same ni ba, ko kuma kice kawai ina barci, saura naji wata magana ta fito bayan wadda na fad'a yanxu, get out naughty girl, ta juya da sauri ta fice.

Wannan tsohuwa da jaraba take ko kiran me take min yanxu da sanyin safiya haka, hmm nan bada jimawa ba xan gudu na bar maku qasar ku kwanaki kad'an ne suka rage, ya xauna yana dafe kansa da hannuwansa duka biyu cikin damuwa.

Kwana kinnan ya rasa gane kansa game da yawan mafarkin da yake, ga wannan tauraruwar tasa tun daga ranar daya soma ganin ta dishe ta daina kusanto shi dalilin haka yake jin kansa wani iri, ya riga yayi sabo da wannan tauraruwar tun yana qarami, yana jin dad'in barcin sa a duk lokacin da yayi mafarki da ita, ta riga ta xame masa wani bangare na xuciyarsa duk da har yanxu ya kasa gane dalilin wannan tauraruwar a mafarkin sa.

Haka kwanaki suka riqa tafiya duk wani shirye shirye baffa na tayi ya siyar da dabbobin sa duka da duk wata qaddara tasa ya had'a kud'in harma fiye da abinda aka buqata, farin cikin sa dana hidaya baxai misaltu ba, ranar kawai suke jira.

Ya salam hidaya ashe maganin nan baxai maki kwana goma ba gashi saura kwana hud'u aikin ki dole gobe naje birni a siyo maki wani kada a tsallake kowane rana a sami matsala.

Baffa idan kaje gobe asibitin xaka je.

Eh mana can xanje na siya maki, can kad'ai na sani.

Shikenan baffa ka dawo da wuri.

Sultan ya maganar birthday qaseem xaka je?

Yaushe ne birthday d'in,
Gobe ne mana, ka tuna wannan gidan gonar mahaifin sa dake wani qauye na fulani haka, ina ji mun taba xuwa da kai fa, acan xaa yi.

Fu'ad baxan tuna ba gaskiya, Anya xan iya xuwa wani qauye yanxu.

Miye aciki, ina ruwan ka da qauyen ko mutanen dake cikin qauyen, idan baka je ba qaseem ba xai ji dad'i ba.

Sultan yace hakane naga ya saka buri a wannan ranar tuntuni yake wannan plan d'in, xan je amma in secret saboda wannan tsohon yanxu ya saka min ido duk inda xanje ya riqa tambayana kenan sai kace dad ya basa ajiyata ne, sai kaxo da motar ka, ka dauke ni muje acewar xamu je inda Ammi ne.

Fu'ad ya bata fuska yana fad'in chab, waye xai d'auke ka a mota, man sai dai kaje a taka motar danni a tawa holewa xanyi, wata beb xan nema hadaddiya mu shiga ciki ta bani kiss, ko na biya ne xan biya.

Mtsew Allah ya shiryeka ya kuma tsare zuri'ar mu daga abin kunya, ni Sam wannan abin baya burgeni cos ba macen da xata burgeni har na bata lips d'ina.

A juri xuwa rafi dai, kar gobe na ganka rungume da wata kaxo kana cika baki.

Sultan ya masa wani kallo yana fad'in baka da hankali I see har ka manta waye sultan merah, ka taba ganin ina magana da mace, ko ka taba ganin na tsaya da wata mace apart from family, ni fa wlhy a school ko a class ban taba xama da mace seat d'aya ba, anyi ta case dani akan wannan fa sai da dad yaje da kansa skul d'in sanin halina, nifa ko xaka kashe ni a yanxu baxan gayama sunan wata mace a class d'in namu ba, yanxu ne ma na had'u da wata marar kamun kai data nace min, yar qasar Sudan ce ina ji.

Fu'ad ya tabe bakin sa yana fad'in ya rage naka ai mata abin sone, abin jin dad'i ne alfaharin kowane namiji....

Sultan yayi saurin katse sa banda ni malam, ya fice ya barshi gurin.

Washe garin ranar bayan la'asar suka shirya suka nufi qauyen.

An qayata gurin yayi matuqar kyau sosai, Kallo d'aya xaka masu ka gane ya'yan manya ne kowane yana ji da kansa da kud'i, kowane yana ganin ya isa yafi wani gata a gurin, isowar sultan gurin kallo ya koma kansa tun daga kan motar da ya hau yaxo gurin abin kallo ce.

Kyakkyawa ne na qarshe, ma'abocin ado, zankad'ed'en saurayi mai ingarman jikin dake boye shekarunsa, fari Sol dashi, ma'abocin gargasa ta gashi a ido, sumar kai da gefen fuskarsa, haka kuma suka bi duk wata gaba ta jikinsa suka kwanta linkif a fatar jikinsa.

Yana da wasu irin idanuwa masu matuqar d'aukar hankali farare fes kamar madara, boye cikin baqin gilashin Prada, sosai ya tafi da xuciyar yan matan dake gurin, bai damu da irin kallon da ake masa a gurin ba cos idan da sabo ya saba da hakan wannan yana d'aya daga cikin dalilin da yasa yake qara d'aukar mutanen qasar nigeria da rashin waye wa.

Yau da ta sake d'ora idanun akan sa ta qara jin xuciyarta ta Lula akan sa tabbas idan bata sami sultan ba komai xai iya faruwa da ita, ziyada kenan, daga inda take xaune ta tsurawa lips d'in sa idanuwa tana imagining yanda xata sarrafasu acikin bakin ta, ta lura ma gabaki d'aya matan dake wurin ba wacce ta isheshi kallo maxan kawai yake kulawa su d'in ma fuskar sa a d'aure.

Lallai yau ba abinda xai hanani samun ka, ta tashi da sauri tunowa da wani tablet a jakarta, yanda na dad'e ina kwadayin ka yau xan d'and'ani xumar ka kota halin qaqa.

Baffa ya dube ta yana fad'in xanje yanxu na siyo maki maganin kada ki fita ko ina kinji.

Ba inda xanje baffa xan jiraka har ka dawo,
Yace yauwa yar albarka bari nayi sauri kinji.

Tace baffa ka kula kada ka had'u da wannan mutumin da ya wulaqanta min kai ya qara yi ma hakan, ni idan aka min aiki baxan dawo qauyen nan ba har sai na nemo shi na rama maka marin da yayi ma.

Murmushi baffa yayi ya shafa kanta yana fad'in 'Hakkilin horema (ki kula da kanki)
Itama murmushi tayi tana fad'in Jaumirawo hokke sa'a wartire jam (Allah ya baka sa'a ya dawo da kai lafiya).

Wasa wasa har magrib babu alamar baffa shi kuma a lokacin yana gurin neman maganin babu a asibiti ya shiga cikin gari nema.

Sai bayan magrib kafin ya sami magani duk hankalinsa a tashe tunanin sa yana kan hidaya bai taba kai magrib a waje batare da ita ba, sai da yaxo gurin shiga mota babu motar da xata je garin nasu a wannan daren, hankalin sa yayi matuqar tashi sosai kuwa.
Chapter 7 · 0% Book details