← Book details Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 47

Sashe 2

Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta matsa a hankali kusa dashi ta riqo hannun sa ta sumbata, abinda bata taba masa ba a tsayin lokacin da suka dauka tare hakan ya saukar masa da kasala lokaci d'aya ya tsuramata idanu yana kallon ta cikin mamaki, ta d'ora hannun sa akan tsinin cikin ta, kaji yaron mu yana cikin qoshin lfy kuma ya hana mahaifinsa shiga damuwa, yana son mahaifin sa yana son kasancewa da mahaifin sa kamar yanda mahaifiyar sa take buri da fata a koda yaushe, ta d'ago da kyar tana kallonsa ido cikin ido tare da sakar masa murmushin da har abada baxai taba gushewa a xuciyar sa ba, tsananin dad'i ya saka shi rungumota sosai cikin kirjinsa ya saka hannun shi yana shafa gadon bayan ta a hankali cikin wani yanayi marar misaltuwa, da kyar yace ina son ki halimatu har qarshen rayuwata, ya kai bakin sa ya sumbaci goshinta kana ya juya ya fice da sauri tunawa da dabbobin kawai ya bari a daji.

Kamar kar ya juya ya tafi ciwo ya sake dawowa, da kyar ta d'aga qafafuwanta ta koma cikin daki ta xauna.

Sai dai me duk yanda tayi ta kasa xama ciwon sai tsanantawa yake, sai faman cije yatsa take tana yarfar da hannu yayin da hawaye suka soma kwaranya a kyawawan idanuwan ta.

Phoenix
A hankali take saukowa daga saman benen kamar wacce bata son taka qasa cikin tsananin ciwon Mara da ya dame ta tuntuni.

Sultan dake xaune a falon yana buga game da sauri ya taso yana kallon yanayin ta,
Mami meke damun ki, baki da lafiya ne.

Ta gyad'a kai da kyar tana cije lips din ta,
Na Kira mahaifinka bata shiga, meyiwuwa ya shiga tiyata ne ya kashe wayar, dauko min key din motata muje asibitin.

Da sauri ya haura sama, ta soma tafiya da kyar xuwa farfajiyar gidan, bata jima ba sai gashi ya fito yaje ya bude mata motar ta shiga da kyar.

Mami xaki iya driving kuwa, kingani da an koyamin mota da yanxu ba shikenan ba.

Ta murmusa da kyar tace at your age shekara goma ina kai ina iya mota musamman a wannan qasar, yi sauri shiga mu je.

Ya xagaya ya shiga motar.

Da kyar suka iso asibitin sai dai qarfin hali kawai take yi saboda yanda take fitar da numfashi kawai xai nuna Ma tana cikin mawuyacin hali, duk yanda taso ta fito motar ta kasa ko d'aga qafafun ta sai nishi take sama sama.

Ganin haka sultan yayi cikin asibitin da gudu kai tsaye office din Dr mera ya nufa, baya ciki, fitowar sa tayi dai dai da qarasowar mera tare da wata nurse a bayan sa da ganin yanda take binsa da sauri tana rubutu a file xaka gane akwai bayanin da yake mata.

Cak ya tsaya yana kallon sultan cikin ware idanu batare da yayi magana ba.

Sultan ya nuna masa hanyar da ya fito yana fadin Mami xata mutu dad.... ai bai jira ya qarasa ba ya nufi hanyar waje da gudu.

Inda ya tsinkayo motar can ya nufa yanda ya same ta kad'ai xai nuna masa babu numfashi a tare da ita, cikin rud'ewa ya dauke ta yayi cikin asibitin da ita.
[11/20, 10:25 AM]Ummi Tandama:
*SULTAN MERA*
Haske writers Association
Fertymerh Xarah
D'aukar ta yayi ya nufi cikin asibiti da ita, kai tsaye Labour room ya nufa da ita, da sauri nurses suka Mara masa baya.

Sultan na qoqarin shiga Labour room din, mera ya juyo yana kallon sa.

Wait outside son,
Meyasa daddy?

Ina so naga yanda Mami xata bamu baby.

Mera ya bata fuska had'e da nuna masa hanyar fita, kaje ka jirani office yanxu xamu xo ma da babyn.

Sultan ya make kafada cikin bata fuska kamar xaiyi kuka,
Ni baxan je ba, I will stay with my mother, ai ni na kawo ta asibiti ba kaine ka kawo ta ba, so allow me to be with her,
she need me not you, yayi cikin labour room din yana share hawayen sa.

Tsananin mamaki ya hana mera motsawa daga inda yake yabi yaron da kallo har ya isa gadon da Afiya take kwance, cikin xafin nama mera yaje ya dauko shi ya fita dashi kai tsaye office din sa ya nufa dashi,
Kana son ka nuna min taurin kai cikin mutane ko, xaka min bayani idan mun je gida, ya juya ya fice.

Lumshe idanunsa kawai yayi kafin kace me, barci mai nauyi yayi gaba dashi.

Bata yi wata doguwar naquda sosai ba ta haifi yar'ta mace, sosai xaka ga tsananin farin ciki shimfide a fuskar mera,
Alhamdulillah ya fad'a yana sumbatar baby bayan an gyara ta, yanxu yaran sa uku kenan, akwai wadda take biwa sultan Amira tana gida Nigeria tare da iyayen su, ya dubi Afiya da barci take sosai yana jin wani nishad'i a tare dashi.

Kai tsaye aka nufi aminity da ita, nan ya soma Kira gida yana sanar dasu haihuwar Afiya sai murna ake taya sa.

Yana xaune bakin gadon da Afiya take kwance riqe da jaririyar sultan ya shigo kai tsaye inda take ya nufa ya riqo hannunta idanun sa akan ta,
Mami yanxu nayi irin wannan mafarkin, tauraruwar taxo daf daf dani ta qara haske sosai, me hakan yake nufi?

Nima ban sani ba sultan, ta fad'a tana kallonsa.

Mera yace hey baka ga qanwar ka bane, baka murna da xuwan baby ne.

Sultan ya girgixa kansa batare da ya kalle sa ba,
I don't want to see her again saboda ita ka hana ni na xauna da Mami dax'u.

Aiman bai qara magana ba, yayi shiru kawai yana tunanin hali irin na sultan wannan dalilin ya saka baya son ya xauna Nigeria saboda baya son ya taso cikin sarauta ko kad'an.

Sultan wani irin mutum ne mai naci da kafiya akan abu, yana da iko da izza da nuna shi wani abu ne akan kowa tun yana qaramin sa dalilin hakan ne yake nisanta shi da sarauta saboda idan ya xauna acikin ta tabbas komai xai qaru akan halayen sa, yaron bai jin magana ko kad'an.

Nigeria.....

Sai faman juyi take a qasan dakin
tana karanta duk wata addua da taxo bakin ta, qarfin ta ya qare bata da wani kuxari nishi ma da kyar take yin sa, a yau tana mai dana sanin barin mijinta ya fita ya barta da tuni ya jima da kai ta asibiti ko nemo mata mai karban haihuwa da xata taimaka mata.

Naquda ta taso gadan gadan tana ji tana gani kai ya bullo, tsananin rud'ewa ta rud'e sosai, ga ciwo ya tsananta.

Wani qarfi ya xo mata tayi wani nishi mai tattare da gajiya cikin ikon Allah sai ga santaleliyar mace ta biyo, ta tsurawa yarinyar ido bata da wani qarfi ko kuxari da xata iya d'aukar yarinyar tana cikin wannan yanayin taji kukan shanu suna shigowa wanda alama ce ta mai gidan ya dawo.

Jikinsa ke bashi ba lfy ba, ya kasa xama a dajin dalilin da yasa ya tattaro su kenan suka dawo gida, har ya gama d'aure dabbobin bai ji motsin ta ba, hankalinsa duk yana kan qofar d'akin ko xai ga fitowar ta.

Da sauri yayi hanyar d'akin, kicibis yayi karo da ita kwance cikin jini kamar wacce babu alamar rai a tare da ita, batare da kyankyami ba ya tsugunna gabanta tare da rungumota xuwa jikinsa, ta bud'e idanunta da kyar tana kallonsa cikin wani yanayi na ciwo.

Ma'awiya ta Kira sunan sa karo na farko a rayuwar ta, ya dube ta yana fadin,
Meyasa kika min gardama halimatu, ni nasan baki da lfy kika musanta min, muje asibiti ne, ta girgixa kanta da kyar hawaye na xubowa a idanuwanta.

Kayi haquri ka yafe min, kuma ka kula min da jaririyata da amana kada ka bari tayi maraicin UWA ka xame mata UWA da UBA
a rayuwar ta.

Ya juya da sauri yana dube dube sai a lokacin idanunsa ya kai ga jaririyar dake kwance a qasa cikin jini sai motsi take da qafafuwanta, yayi saurin maida duban sa ga halimatu,
Kika haihu da kanki, meyasa kika min haka, meyasa baki gayamin haihuwa taxo maki ba, karki tafi ki barni halimatu, baxan iya wata rayuwa da kowa ba bayan ke, kar kije ki barmu ki tausaya mana muna tsananin buqatar ki a tare damu.

A hankali bakinta ke motsi baya jin kome take fadi, ya kai kunnensa dai dai bakinta dai dai lokacin numfashin ta na tsaya cak.

Wata qara da jaririyar ta callara ya dawo dashi daga suman xaunen da yayi dai dai lokacin wata irin fad'uwar gaba ta riski sultan da nayi matuqar firgitashi wanda sai da hankalin iyayen nasa ya koma kansa.
[11/20, 10:25 AM]Ummi Tandama:
*SULTAN MERA*
Haske writers Association
Fertymerh Xarah
*is not free pls, idan baka biya ba dan Allah kada ka karanta*
A hankali yake tafiya yana danna wayar sa tamkar wanda baya son taka qasa, duk bayi da masu aikin gidan dake gaidasa ba wanda ya d'ago ya kalla illah hannu kawai da yake d'aga masu alamar yaji.

Falon kakansa ya nufa wato sarki, kai tsaye ya nemi iso aka masa, ya shiga fuskar nan tasa ba walwala.

Ya sami guri ya xauna had'e da tankwashe qafafuwan sa yana kallon sarki.

Mami tace kana nemana, me kuma akace nayi.

Modibbo iyayen naka basu koyama gaisuwa bane, sarki ya fad'a batare da ya kalle sa ba.

Sultan ya tunxuro baki, kamar baxai yi magana ba sai kuma yace na same ka lafiya.

Wanna ce gaisuwa?

Ya qara tsuke fuska cikin bacin rai da d'aga murya yace good afternoon, sai a sannan sarki ya kallesa yaga sai wani cika yake yana batsewa yayi murmushin sa mai qayatarwa yana fad'in,
Wai ni na damu dana ga sultan ne shiyasa na tura neman sa, tun da suka xo bai xo na ganshi ba ashe nayi laifi ne.

Sultan ya dube sa yana fad'in dan Allah granny meyasa xaka tilastawa daddy sai mun dawo Nigeria, banda xafi da talauci menene acikin qasar taku.

Kaji ja'irin yaro, ni kake gayawa haka, waye bai San asalin buzu ba, inace anan qasar aka haife ka....
Chapter 2 · 0% Book details