← Book details Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 47

Sashe 22

Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da gabansa ya buga, ya tsura mata ido har ta qaraso gabansu tana huci shi mamaki ma take bashi yarinya sai liqe masa take.

Ke wai ni abokin wasan kine ko nine ubanki da kika nace min haka.

Cikin sauke numfashi tace aa kai ba baffana bane amma kai abokin wasa na ne.

Cikin xafin rai ya d'aga hannu xai mare ta fu'ad yayi saurin riqe masa hannu, hidaya kuwa baya ta ja cike da tsoron yanayin da take ganin sa dashi abinda bata taba gani ba.

Wane wawanci ne wannan, taya xaka mari yarinya qanqanuwa haka me tayi ma, ba gaskiya take gayama ba ko an gayama qarya take.

Ya nuna kansa yana fad'in nine abokin wasan nata dan ubanka, yarinya na neman ta raina ni kana min maganar banxa dalla cika min hannu, ya fisge hannunsa da qarfi yana dirowa daga saman motar, tana ganin haka tayi cikin gida a guje.

Fu'ad ma dirowa yayi yana buga qirjinsa yace ko kana so ko baka so dole a kira ka da abokin wasar yasmeen da hidaya, yarinyar nan ba qaramin taimakon ka tayi a rayuwa ba, bata cancanci wulaqanci ko toxartarwa a gurin ka ba.
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*
Haske writers Association
Fertymerh Xarah
Kai tsaye falon aiman ya nufa, baya nan sai ya nufi bedroom nasa yana xaune bakin gado sai danne danne yake a laptop ya shiga da sallama
Aiman ya amsa batare da ya dube sa ba.

Daddy shiru kwana biyu banji kayi mgnr phone d'ina ba.

Me kake so ayi, xuwa xanyi ina cigiyar wayar taka bayan watannin da bacewar ta?

Yace aa wata nake so ka siya min updated nagaji da xama haka olways lonely no friends to chat with.

Aiman ya kalle sa yana fad'in banda kud'in siyen wata waya yanxu mai tsada manage ka siye da kud'in ka.

Sultan ya shagwabe fuska tare da xama bakin gadon yana kallon sa.

Daddy baxan yarda ba wallahi kana da kud'i dan Allah ka siya min.

Serious banda kud'i yanxu sultan, baka ko tausayi na nawa na kashe wurin nema ma lafiya tsakanin nan qasar da Riyadh inda aka ma aiki, and again kasan adadin kud'in dana bada kafin su yarda su sake d'aukar ka ball kuwa, ka siya idan na sami kud'i xan siya ma wata is that ok.

Sultan ya girgixa kansa yana fad'in nima ba kud'i a wuri na,
Duk me kake yi da kud'i, ina duk kud'in dake account d'in ka?

Ya shafi sumar kanshi yana murmushi, aiman ya tsare sa da idanu yana fad'in, anko kake yiwa yan matan ka ko kuma waya kake siya masu?

Sultan ya bata fuska jin an ambaci mata, yace xanje papa ya siya min ni dai ko shi ko Abba (Aliyu).

Is better kaje gurin Aliyu dai, sultan ya tashi har xai fice ya juyo yana kallon sa, daddy na manta saura mota bana son waccan itama a canxa min naga ma fu'ad an canxa mashi mota balle ni da nake fresh yanxu with new life.

Aiman yace hakane amma ka manta na gayama banda kud'i ko sata xanje nayi saboda kai, wait ma ba within a week xaka bar qasar ba, me xaka yi da ita.

Oh yeah haka ne na tuna but kafin na dawo xaka canxa min wata promise.

Promised Aiman ya fad'a yana maida hankalin sa gun aikin da yake, sultan ya juya ya fice, yana fitowa yaci karo da ita akan sofa sai barci take abinta.

Yaja tsaki yana d'auke kansa duk da yana jin yarinyar a ransa bai san dalili ba, ya d'aga kafadun sa sama qila dan munyi wasa ne kamar yanda suke cewa, kai amma gidannan fa an cuce ni barin nayi wasa da wadannan yaran, tukunna wace irin wasa ce ya fad'a yana sake kallon ta.

Qato dani haka acikin su nake wasa, no baxan taba yarda ba nasan me nakeyi taya ma Mami xata yarda nayi wasa cikin wadannan yaran haba ai ko papa baxai yarda ba suna fad'in haka ne dan kawai na Saki jiki da yarinyar and I will not, mtsew yarinya kullum glass a idanu harda barcin ma ko miye dalili yasa kai ya fice abinsa.

Bayan kwana biyu.

Duk wani shirye shiryen tafiyar sa yana kan yi, farin cikin xuciyarsa baxai misaltu ba xai bar qasar kullum idan ya tuna haka tamkar yayi tsuntsu yake ji, yayi kewar friends nasa ba kad'an ba.

Sallama tayi ta shiga dakin nasa, kamar baxai amsa ba sai kuma ya amsa ciki ciki sanin muhimmancin sallamar batare da ya d'ago ya dubi mai sallamar ba.

Yaya sultan sannu da hutawa.

Yauwa ya fad'a kansa akan sabuwar dalleliyar wayar dake hannunsa yana chatting.

Shikenan yaya sultan idan kaje sai kuma nan da 5years xaka dawo.

Sai akayi me? ta girgixa kanta tana fad'in ba komai amma xanyi kewar ka sosai.

Yace to naji, excuse me pls.

Tace please yaya sultan ko sau d'aya ne ka bari muyi hira mana, meyasa kake nuna min kamar baka san na damu da kai ba.

Ya d'ago yana kallon ta, ban gayamiki karki sake min wata magana da ta shafi soyayya ba, ni sa'an ki ne, dan baki da kunya kin raina ni har kike turomin kina sona harda kalaman soyayya ma, ni nayi maki kama da shashashan namiji ne da xai xauna bashi da aikin yi sai akan mace, xan gayawa papa abinda kike aikatawa as your age waya sani ma kafin ni kinyi bibiyar maxa da yawa su so ki, big lunatic get out pls.

Wani qololon baqin ciki ya taso ya tokare qirjinta, ita yake gayawa kalamai masu xafi haka harda kiran ta lunatic, meyasa shi da Mami sun kasa fahimtar tane har suke mata kallon mai bibiyar maxa saboda su so ta, dama laifine idan mace taga namiji tace tana so, kallon sa tayi tana fad'in am.. ya katse ta cikin tsawa xaki fita ne ko sai naxo na same ki gurin, ta juya ta fice a fusacce idanunta cike da kwalla.

Yasmeen ce ke kai da kawowa a falon ita kad'ai tana wasa, hidaya na kwance tana kallon ta, kwanakinnan duk haka take xama babu walwala ko sukuni a tare da ita, xuciya da gangar jiki sun saba tarayya da abokinta ba qaramin abu xai saka ta manta shi lokaci d'aya ba kamar yanda yake hantara da nuna mata kyama a yanxu ba, ta ga yasmeen ko kad'an bata damu dashi ba ko meyasa, saboda kawai ta ture shi yake ta fushi da ita haka xata bashi haquri tace baxata qara ba yaxo suci gaba da rayuwar su suna wasa tare.

Meke damun ki hidaya duk kin canxa kwana biyu d'innan ko baki da lafiya ne?

Sai ta girgixa kanta hawaye na xubowa daga idanuwan ta.

Afiya tace to menene harda kuka, kunyi fad'a da yasmeen ne ko su amira sun qara dukan ki.

Nan ma ta girgixa kanta kafin tace yaya sultan baxai xo muyi wasa ba.

Tace baxai xo ba hidaya, ki manta dashi ki Saki jikin ki kamar farko ga yasmeen ta ishe ki wasa, sultan d'in da kika sani before wannan bashi bane, bana gayamiki lokacin bashi da lafiya bane shiyasa, yanxu kuma ya sami lafiya baxai taba xama acikin ku yayi wasa ba ki manta dashi kamar yanda kika ga yasmeen tayi.

Tace to yaushe kuma xaiyi wata ras
hin lafiya.

Afiya tace har abada insha Allah wannan cutar baxata qara dawo masa ba ko wani jinin sa, nace ki manta dashi ai ko.

Sai ga hawaye sharrr, tasa hannu tana gogewa Afiya taji tausayin ta sosai, yaro da sabo sai ta soma rarrashin ta, lokaci yayi da aiman ya kamata yayi mgn akan raba auren yaran tunda an sami abinda ake so, tasan ko banxa dama sultan baxai taba son hidaya ba.

Qamshin turaren da taji ya saka ta d'agowa da sauri, idanunta sai a cikin nasa, ta taso da sauri ta nufe sa tana share hawayen fuskarta tace kayi haquri baxan qara ture ka ba.

Ya tsura mata idanu cikin takaici kafin yace ke wane irin naci ne dake haka, are you stupid?

Hidaya ta girgixa kanta, yace idan kika qara gani na kika nuna kin sanni sai na tattakaki a gidan nan.

Ta langabar da kanta tana kallonsa tace shikenan baxan qara yi ma magana ba, amma ka gayamin wannan turaren a ina ka same shi.

Cikin takaici da bacin rai yace gidan uban ki na sato, ta nuna sa da yatsa tana fad'in kenan.. kenan kai ne ka mari baffana?

Kashe shi nayi, waye baffan naki, me yake dashi gayamin wane mulki ko muqami yake dashi a qasar nan.

Waye baffana nima ban sani ba amma idan ya dawo ya tabbatar min da kaine ka mare sa nima baxan barka ba sai na mare ka sai nayi ma wulaqanci irin yanda kayi masa, ta juya xata fice cikin bacin rai ya fincikota tana juyowa ya d'auke ta da mari sai da glass d'inta ya fita idonta, ya jefar da ita qasa kamar kayan wanki, a tsorace Afiya tayi kanta cikin tashin hankali duk abinda yake aiman na tsaye yana kallon sa tuntuni ya dad'e da shigowa, juyowar da xaiyi shima ya d'auke shi da mari karo na farko a rayuwar sa.

Cikin rud'ani da mamaki yake kallon mahaifin nasa kada dan ya daki wannan banxar ne ya mare sa.

Da yatsa ya nuna masa ita yace daddy saboda wannan?
Chapter 22 · 0% Book details