← Book details Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 47

Sashe 36

Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baffa yace guda hud'u ne,
Aiman yace ka kawo min hidaya da awarwaro uku a hannun ta, biyu a d'ayan hannun ta, d'aya a hannu ta guda, ina d'ayan ya shiga.

Baffa ya girgixa kansa cikin tunani yace ban sani ba kuma ban lura daga yaushe d'ayan ya fita daga hannun ta ba,
Aiman yace fine, lokacin da ka kawo min hidaya kafin na karbe ta tabbas naga wayar sultan a gaban aljihun ka, ban kawo cewa wayar sa bace a lokacin beside ma hankalina duka yana gida matata ta kirani a waya sultan baya gida a wannan daren.

Na karbi hidaya da amanar ta a gurin ka na juya na barka a gurin da cewa nurses su kula da kai, Dr Fulani bata qasar a yanxu ta d'auki annual leave da itace xata bada shaida a yanxu cewa akan idanunta ka bar asibitin da qafafun ka haka ta gayamin, dalilin ka na guduwa ka bar yar'ka ban sani ba amma na dad'e ina mamakin haka, sanin kana raye yasa ban taba gayawa hidaya baffanta ya mutu ba sai dai nace xai xo kace xaka xo kuma nasan dama xaka xo tunda gashi ka xo d'in,
An kawo sultan baya numfashi kuma a maballin aninin rigar sa na sami wannan d'ayan awarwaron ya maqale sai dai ya katse wanda rabin duwatsun duk sun xube, na d'auki awarwaron naje na gwada dana hannu hidaya duk iri d'aya ne, kuma hidaya tana qamshin turaren sultan, idan sultan ne yayi wa hidaya fyade kenan kaine wanda ya illata masa rayuwa, you make my son disabled, ya dawo bashi da wani amfani ya xauna tamkar jaririn goye komai sai an nuna masa an koya masa, wannan mahaifin yaron da ka nakasawa d'a shi ka baiwa amanar taka y'ar kuma ya riqe ta da hannu biyu batare da hantara ko tsangwama a gidannan ba, na kula da ita na bata sutura na bata ci da sha na bata ilimi da duk wani abin jin dad'i na rayuwa dai dai da rana d'aya ban taba banbanta ta da abinda na haifa ba, na nema mata lafiya da kud'in jiki na batare da ko kwandala acikin kud'in ka ba bayan nasan mahaifin tane
sanadiyar lalata rayuwar tawa d'an, ina da iko a qasarnan tsab xan iya saka a nemo min kai a duk inda kake fad'in qasar nan kuma ina da hanya da dama da xanbi na gano asali da yan uwan hidaya duk banyi ba, koda sarki yace xai saka ayi bincike a wannan qauyen ni na hana a ranar saboda na riga da nasan komai wanda babu wanda ya sani, daga baya naje na gayawa sarki komai akan abinda sultan yayi wa hidaya da dalilin da ya saka nake son riqe ta kuma na aura masa ita, da ba dan sarki yasan da maganar fyaden ba babu ta yanda xai amince da sultan yayi aure a wannan shekarun nasa, na dannewa xuciyata na boye wanda ko matata bata da masaniya akan wannan na sani komai daren dadewa xaka nemi hidaya xaka kawo kanka.

Na dage da tursasawa matata amincewa da auren hidaya saboda shi kad'ai xanyi na ceci tata rayuwar daga quncin da xata fad'a duk ta auri wani namijin daban, sultan shine yayi mata fyade kuma shine ya cancanci xama da ita, nayi masa uxuri a lokacin saboda nasan wannan fyaden shine na farko a garesa daga yanda yayi amfani da ita, bayan samun lafiyar sa na tambaye shi meya faru a wajen party yace ba komai, na qara tambayar sa fu'ad ya gayamin ya fita daga gurin bai da lafiya meya faru daga lokacin still ya kafe akan ba komai kuma sai na barshi kar na qarfafa bincike na akan sa nasan with time gaskiya xata yi halin ta, kana aibata tarbiyar sultan ga y'ar ka nan itama ta nuna min kalar nata tarbiya ta hanyar d'aukar hannu ta mari babba batare da nuna kawaicin ta a gurin mahaifiyar sa ko kuma ni ba, xaka iya d'aukar hidaya ku tafi shikenan, duk sanda ka ke son takardar sakin hidaya xaka iya xuwa ka karba.

Baffa ya d'auki sadakin ya ajiye masu anan yana fad'in auren da ban yarda dashi ba bana so baxan karbi sadaki ba,ya cire xoben hannun sa ya jefa ma sultan yana fad'in waya kuma na siyar na kashe kud'in,
ya d'auki nasa kud'in ya riqa hannun ta yana fad'in xo muje, cikin kuka ta juya tana kallon mera,
Daddy dan Allah kayi haquri, aiman yace ki bi mahaifin ki ya fimu son ki, ta juya tabi baffa batare da tayi magana ba.

Sultan ya yunqura xai bi su Afiya ta riqo sa tana fad'in, kyale su dama an xauna an tsara wannan drammer ne saboda aci xarafin ka, tsawon shekara biyar suna tsara wannan game d'in aka cutar da xuciyar ka ta hanyar saka maka soyayyar wannan marar tarbiyar, ni na yarda da kai nasan babu wata hanya ta mace da kasani baxaka iya ma kowa fyade ba.

Sultan ya fad'a jikin ta yana fad'in help me mamee ina son hidaya, ki dawo min da ita daddy baxai taimaka min ba.

Afiya tace taya xai taimaka ma bayan dashi aka had'a baki domin a cutar da kai, shekara biyar an rasa wanda yayi fyaden sai yau kuma ace kai, Allah ya saka ma.

Aiman murmushi yayi yana kallon su.....
#TeamAiman
#TeamBaffa
*littafina na kud'i ne kada ka karanta baka biya ba xaka bada haqqi inda baka da ikon biya, idan kana so kayi magana ta wannan number 08169334980*
[11/20, 10:24 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*
*littafina na kud'i ne kada ka karanta baka biya ba xaka bada haqqi inda baka da ikon biya, idan kana so kayi magana ta wannan number 08169334980*
Dariya kake tunda ka barsu sun tafi, halin da yaron ka xai shiga ko a jikin ka?

Yasmeen ta fashe da kuka ta bar falon da gudu haka amira ma jiki a sanyaye ta bar sashen nasu.

Aiman ya dube ta yana fad'in saboda me xan hana su tafiya, fyade fa yayi wa yar sa, rasa budurcin yarinyar nan ba abinda baki ce ba a gidannan ba irin maganar da baki fad'a ba yaron ki baxai auri mace ba Virgin ba ashe yaron naki shine ya d'auke mata budurcin baki da labari, wannan dalilin yasa na kafe akan lallai sai na aurawa sultan hidaya, meyasa a lokacin baki qarfafa
sai kinji dalilin auren sultan da hidaya ba duk na xo maki da mgnr a tunanin ki yarinya kamar hidaya ta isa ta kula da sultan ne, tasan yanda xata kula da kanta ballantana wani sultan, me tasani a rayuwa balle wani aure, nayi maki wasa da hankali saboda sanin halin ki nace warkuwar sultan tana tare da hidaya kuma banyi qarya ba itace sanadi, taya sultan xai cuci yarinya kamar wannan sannan ya tafi a banxa, ni na tursasa masa son hidaya da kaina gashi nan ki tambaye shi, tun bayan xuwan sa Phoenix bai qara mgn akan hidaya ba idan xai yi magana da kowa kuwa a gidannan lura da haka ya saka na fara tura mashi pics d'in ta tare da yasmeen ko kuma nata ita kad'ai, sannan ina qara tuna masa wahala da yarinyar tayi domin sa, sannu sannu sai ya fara magana akan hidaya baxai tambaye ni ita ba sai dai ya tambayi yasmeen, sanda yaxo yace min yana son hidaya ni na qarfafa mashi akan yaje ya nemi soyayyar ta ina so ta amince mashi kinsan dalilina na yin haka saboda ina son sultan ya san rayuwa, yasan akwai da babu, yasan abu xai iya xama naka ko kuma sabanin haka, yasan daraja da qimar mutum ko waye shi, ya san qunci da xafin rayuwa ya kuma san akwai abinda qarfin iko ko kud'i baxa su baka a rayuwa ba, duka wad'annan sultan bai san su ba, abinda kawai ya sani xai sami duk abinda yake so kowane lokaci idan ya nemi hakan sannan shi talaka bashi da wata qima a idanun sa komai girman sa da tsufan sa, can you imagine kamar sultan ya d'aga hannu ya mari wannan dattijon saboda mota, motar banxa, wannan ba tarbiya ta bace wannan rainon gimbiya Afiya ne da ta gudu da shi.

Sultan ya dube sa yana fad'in amma daddy kaine kace xaka tsayamin akan ko me nake so...

Aiman yace ban gayama idan na sami sa hannun ka a mai batawa hidaya ba xaka gamu da fushina, ban gayama haka ba last time, sannan ranar da ka farfado ban tambaye ka me ya faru a wannan qauyen ba kace ba komai, da a lokacin baka boye min ba ka gayamin gaskiya xan san ta yanda xan bullowa al'amarin kafin a kawo wannan lokacin.

Amma daddy ni baka ji meyasa na aikata hakan ba....

Aiman ya katse sa yana fad'in I don't care na sani yanxu ka riqe sanin ka ko ka gayawa mahaifiyar ka, kai kama aikata ne mahaifiyar ka taqi yarda da hakan saboda idanuwan ta sun rufe da soyayyar ka ta kasa gano kuskuren ka, ni nan qage aka min ta tattara kayan ta da kai ta gudu abinta, bata damu da halin da xata saka iyayen ta ko kuma mijinta ba, taje ta baka wannan tarbiya kaxo ka aikata laifin da kaima taka matar ta guje ka kamar yanda mahaifiyar ka tamin so yanxu itama xata dandana taji wannan xafin ya yake,
yanxu lokaci yayi ka fuskanci rayuwa kaje ka nemi yafiya da soyayya a Karo na biyu gurin hidaya I wish you all the best, xan yi murna idan hidaya ta amince Ma amma ni ba hannu na acikin wannan al'amari yanxu.
Chapter 36 · 0% Book details