← Book details Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 47

Sashe 13

Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kusan magrib bayan su yasmeen sun dawo har lokacin hidaya bata tashi ba, Afiya ta saka mai aikin gidan ta dauke ta ayi mata wanka tare da wanke gashin kanta.

Sultan tare da mahaifin sa a toilet dama kullum shi yake masa wanka safe kafin ya fita aiki da dare idan ya dawo.

Yau yana tsaye yana ganin yanda sultan d'in ke yin komai da kansa inda yayi kuskure ya gyara masa, tabbas ba qaramin cigaba suke gani a tare dashi ba, ya fito d'akin nasa ya barsa ya qarasa wankan.

Yana xaune a d'akin tare da kayan barcin sa ya fito, juyawa yayi yana kallon sultan, ya salam ya fad'a kafin ya tashi da sauri ya nufe sa da towel ya d'aura masa a qugunsa, in banda ciwo yaushe sultan xai fito haka xigidir
wanda ko qirjinsa abu mai wuya ne kafin ka gani.

Yana tsaka da shirya sa fu'ad yayi sallama ya shigo d'akin, ya gaida mera yana kallon sultan.

Ya kira sunan sa, duk da bai amsa mashi ba ya juyo yana kallon sa, daddy kaga yau sultan har kallona yake yi fa.

Murmushi merah yayi kafin ya qarasa saka masa kayan yace da kanshi ma yayi wanka yau, Allah yana karba mana addu'ar mu.

Allah ya qara mashi lfy,
Amin cewar merah
Fu'ad ya shafi sumar sa yana kallon merah kafin yace daddy wata baquwa na gani a gidannan da glass ita d'in wacece kuma.

Meyasa kake tambaya? yayi shiru kafin yace kawai naga tana da kyau ne
Merah yace she is part of us yanxu itama ya'ta ce, marainiya ce ita.

Allah sarki fu'ad ya fad'a cikin shigar tausayi kafin ya juya ya bar d'akin.

Salwa qanwar fu'ad kusan sa'annin juna ne da amira 15years, tare suka xo da fu'ad tun da taga hidaya ta soma tambayar Afiya wannan wacece Mami, ina aka same ta, meyasa take xaune a gidan nan ina maman ta, ina ne gidan su.

Salwa bana son surutu kada ki dame ni.

Amira tayi caraf tace wai daddy ne ya kawo ta fa salwa, yana cewa she is part of us yanxu tsinto ta akayi fa.

Hidaya dake wasa da teddy tare da yasmeen ta dube ta cikin marairaice fuska tace, ni ba tsinto ni aka yi ba, baffana yaje ya barni xai dawo mu tafiyar mu.

Suka kyalkyace da dariya salwa tace bata iya hausa ba kinji yanda take mgn.

Amira tace wai a hakan ma ta iya ne sanda aka kawo ta ko shege bata ji a hausa sai da aka koya mata, English Ma baa mgnr shi, suka sake kecewa da dariya suna taba hannayensu.

Nan da nan hidaya ta soma hawaye, ta cire glass d'in ta tana share hawayen ta, yasmeen ta soma shafa kanta tana rarrashin ta irin na yara kafin tace ai kema salwa baki iya French ba keda amira ko ranar ni na koya maku yanda ake gaisuwa kuma baxan qara koya maku ba ko munje skul tunda kuka yiwa hidaya dariya.

Salwa ta tashi tana fad'in wallahi xan bige shegen bakin ki can't you call me Anty salwa dole sai kin kira sunana ba respect.

Amira tace she don't have respect for elders ta raina mu ne.

Yasmeen ta riqo hannun hidaya tana murgud'a bakin ta, tace ai kuma you don't have respect for your younger ones, in ba haka ba hidaya baquwar muce meyasa kuke mata dariya, and again naji kuna hirar yaya sultan da yaya fu'ad, ta nuna amira tana cewa ke kina son yaya fu'ad ko, ta nuna salwa tana fad'in ke kuma kina son yaya sultan ko, to duk basa son ku saboda baku da kirki and again ku ba types d'in su bane kuma sai na gayawa papa kullum xancen samari kuke.

Har ta juya xata fice amira ta fincikota tare da hidaya, tana qoqarin kai mata duka Afiya ta riqe hannun ta dai dai lokacin merah ya fito daga d'akin sultan.

Tace idan kika sake kika d'ora hannun ki akan yasmeen xan yi matuqar bata maki rai a gidannan maxa ku barmin falo kafin raina ya baci akan ku.

Yasmeen ta juya tana kallon merah, yauwa daddy kaga salwa da amira sun saka hidaya kuka, wai tsinto ta akayi suke cewa kuma suna mata dariya bata iya hausa da turanci ba.

Ya dubi hidaya kafin yace yasmeen kuje kuyi wasa a d'akin ki kinji, taja hannun ta suka bar falon ya dube su yana nuna su da yatsa.

Yace akan wannan yarinyar hidaya ku kiyaye ni, ban taba sa hannu na daki wani acikin ku ba amma akanta xan fara.

Amira ta fashe da kuka tana barin gidan gaba d'aya ta nufi gidan sarki, salwa ma tabi bayanta.

Da dare duk sun hallara dinning gurin cin abinci, hidaya sai xare ido take tana kallon kalolin abincin da aka jera kowa ya xabi wanda yake so yaci, ta rasa na xaba sai had'iyar yawu take.

Fu'ad sai kallon ta yake bai San dalilin da yasa yarinyar take birgeshi ba, musamman qaramin bakin ta kamar cokali baxai shiga ciki ba.

Hidaya ta dubi mera tana fad'in daddy ni me xanci, duk gurin kowa ya d'ago yana kallon ta.

Mera yace me kike son ci.

Tace ni duka ma xan iya cinyewa.

Fu'ad ya fashe da dariya yayin da su salwa suke binta da kallon mamaki.

Merah ya dubi amira da tayi kicin kicin da fuska yace amira serve her irin abincin yasmeen xaki ci ko, ta gyad'a kai tana murmushi.

Kamar ta d'ora hannu aka ta buga ihu saboda haushi, ta xuba mata abincin kad'an bakin ta a tunxure.

Hidaya ta dubi merah tana fad'in daddy ni wannan baxai ishe ni ba, batare da ya kalli amira ba yace ki saka mata wanda xai ishe ta, amira ta loda mata abincin da tasan baxata iya cinyewa ba kafin ta xauna a fusacce, fu'ad kallo d'aya yayi mata ya d'auke kansa daga gare ta.

Yasmeen ta dubi hidaya tana cewa duk wannan abincin xaki iya cinye sa hidaya
Hidaya ta washe baki tana fad'in e mana, tayi loma d'aya kafin ta dubi merah, daddy wannan abincin akwai dad'i.

Salwa taja guntun tsaki a hankali tana fad'in wannan shegiyar yarinyar da surutun tsiya t... tayi shiru sakamakon bige mata baki da fu'ad yayi duk gurin ba wanda ya lura, ta tunxuro baki tana qoqarin maida hawayen dake son xubo mata saboda taji xafin dukan.

Kallon kowa gurin tayi d'aya bayan d'aya kafin ta juya tana kallon Afiya.

Mami ina wannan yaron naki da baya lafiya shi baxai xo yaci abinci bane.

Ke wa kike cewa yaro, yaya sultan kike cewa yaro, amira ta fad'a cikin bacin rai.

Hidaya ta murgud'a baki tana fad'in ni da Mami nake magana ba dake ba.

Afiya tayi shiru tana sauraren qarfin hali irin na yarinyar.

Merah yace karki damu hidaya kici abincin ki, idan Mami ta gama cin nata xata bashi daga baya.

Ni baxan ci wannan abincin batare da shi ba, shikenan saboda bashi da lafiya sai ayi masa wayo sai kun cinye abincin sai ku bashi ragi, to baxai ci ragin kowa anan ba, ni xanci nawa tare dashi, ta tashi da plate d'in abincin ta, ta nufi d'akin sultan da taga an shiga dashi dax'u, duk suka bi ta da kallo.

Xaune kawai yake bakin gado ya tsurawa carpet idanu kamar mai son gano wani abu akai,
Kaxo ka xauna anan kowa yana can yana cin abinci, gaka lafiyar ka qalau amma ake d'ora ma ciwo idan gaskiya ne baka da lafiya meyasa baka kwanta ka lullube anyi maka allura ba kuma ai naga ko amai baka yi.

Sultan bai masan tana yi ba, taja tsaki tana fad'in qila kurma ne kai baka ji shiyasa ayi ta magana baka amsawa inaji wannan dalilin ya saka ake cewa baka lafiya, ta riqo hannun sa.

Ya daqo da sauri yana kallon ta, ganin plate d'in abinci dake hannunta ya saka shi tasowa ya biyo ta, haka suka fita tana riqe da hannunsa.

Duk falon kallon mamaki ake mata bama kamar mera, anan qasan carpet suka xauna idan taci shima yaci.

Sosai xafin hidaya da Afiya keji ya soma saukowa har tana ji a ranta hidaya tana birgeta.

Duk abinda hidaya tayi sai sultan yayi, sai da suka kusa cinyewa ta tabbata ta qoshi ta d'auki spoon d'in ta, ta buga mashi a goshi.

Aiman idanun sa na kansu yace ban hana ki dukan sa ba.

Tace ai shine ya soma dukana dax'u, cup ya.... tayi shiru sakamakon jin duka da tayi a goshinta kwal, shima ya rama.

Aikuwa amira da salwa suka fashe da dariya sosai cikin farin ciki.

Hidaya ta tashi dafe da goshinta tana kuka.
*littafina na kud'i ne idan baka biya ba dan Allah kada ka karanta
*[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama:
*SULTAN MERAH*
Haske writers Association
Fertymerh Xarah
Ni wallahi baxan yarda ba sai na rama,
Ganin yanda ta dafe goshinta ya saka shima sultan dafe nasa goshin yana kallon ta.

Afiya tace ke meyasa bakya jine idan kika kuskura kika qara dukan sa kema dukan ki xanyi.

Ta soma hawaye sosai taje ta xauna, merah ya cigaba da cin abincin sa, sultan yaje ya xauna kusa da ita, ta matsa da sauri tana share hawayen fuskarta, shima ya matso, ta qara matsawa shima ya matsa, cikin kuka take kallon Afiya.

Ki cewa yaron ki ya daina matsowa kusa dani tunda na kyale shi.

Murmushi Afiya tayi a ranta cewa take oh wannan yarinya wace iri ce.

Salwa tace lallai ma dan kin samu har ya xauna kusa dake da sanda yake cikin hayyacin sa ne ke kin isa ki tsaya qofar d'akin sa ballantana ki xauna kusa dashi, kin raina yaya sultan ne.

Amira ta tabe baki tana tashi daga dinning idan kin gama ki same ni d'aki na kece mai bakin magana ta fice salwa ma ta tashi tabi bayanta.

Fu'ad kam hankalinsa na gun chatting d'in da yake yana cin abincin sa cikin kwanciyar hankali.

Merah kuwa tashi yayi bayan ya gama ya qaraso cikin falon, hannun sultan ya riqo ya fita sashen dashi xuwa inda sarki.

Mami ni gobe baxan je skul ba.

Me xai hana maki xuwa yasmeen.
Chapter 13 · 0% Book details