← Book details Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 47

Sashe 14

Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tace ni Mami baxan je ba kaina yana ciwo sosai.

Ciwon kai baxai hana ki xuwa skul ba haquri xakiyi kinji babyna, jibi ai babu skul Saturday ne.

Amma ni Mami gobe baxan je da wannan takalmin ba, ni bana son su, hidaya tayi caraf tace ni ina so yasmeen xaki bani.

Yasmeen ta girgixa kanta tana fad'in ai daddy xai siya maki naki sabo idan xaa kaiki skul d'in mu.

Hidaya tayi murmushi batare da tayi magana ba.

Bayan mai kula da yasmeen tayi masu wanka, ta saka masu kayan barci suka nufi d'akin su domin kwanciya.

Hidaya tace wannan gadon naki ne ina na amira.

Yasmeen tace itama nata yana d'akin ta, daddy yace xaa sa miki naki gadon acan.

Hidaya tayi murmushi tana fad'in irin naki nake so akwai dad'in hawa gashi mai kyau, wanda muke kwanciya nida baffana bai yi laushin wannan ba.

Yasmeen ta dube ta itama da murmushi a fuskar ta tace kada ki damu yanxu komai iri d'aya xaa riqa mana inji daddy, yace mu twins ne dukkan mu muna da kyau.

Wannan kuma menene shi?

Duvet ne ki shiga ciki yanxu Mami xata xo ta mana addua kullum haka take mana da dare.

Basu dad'e da kwanciya ba sai ga Afiya ta shigo d'akin, kallon su take kafin ta nufi yasmeen, cikin dariya yasmeen ta miqa mata tafukan hannunta duka biyu, Afiya na karantowa itama tana maimaitawa kafin ta tofa mata ta shafa a jikinta da sauri.

Ta dubi hidaya tace kema ki kawo hannun ki Mami xata maki addu'a.

Hidaya ta girgixa kanta tana fad'in ni na iya baffana ya koya min idan kina so xan koya maki ba sai Mami taxo tana miki kullum ba.

Afiya ta xuba mata idanuwa cikin mamaki kafin tace karanta naji tukunna, hidaya ta karanto mata, ta jinjina kanta cikin mamaki batayi tunanin mutanen qauye kuma fulani xasu sami ilimi haka ba, mutumin qauye da ake kira jahilai saboda rashin neman ilimi... tunanin ta ya katse jin yasmeen ta sumbace ta a goshi tana fad'in gudnyt Mami, ita ma ta maida mata tana fad'in night sweetheart, bata san dalili ba sai kawai ta tsinci kanta tana sumbatar goshin hidaya kamar yanda tayi wa yasmeen, sai da ta gyara masu kwanciya kafin ta bar d'akin.

Washe gari a gaggauce suka yi breakfast suka fice har hidaya saboda xaa mata interview na shiga School d'in.

Ko da Afiya taje da breakfast d'in sultan qin karba yayi ya tsurawa qofar d'akin ido kamar mai jiran wani ya shigo.

Tayi juyin duniya yaqi karba, tayi yanda taga hidaya nayi masa yaqi karba, tasha kusan sau nawa amma ko ya kula ta sai ta kira wayar merah tana gaya masa.

Yace baxai sha ba sai tare da hidaya ki kyale shi kawai.

Na kyale shi fa yarima sai ya xauna da yunwa har xuwa lokacin da xasu dawo.

Yace a'a ko drip da kika ga na cire masa da asuba yana d'auke da sinadarin abinci sultan baxai ji yunwa ba, ki kwantar da hankalin ki, taja numfashi kafin ta katse kiran.

Da gudu suka shigo falon suna dariya,
Mami...

Mami mun dawo, hidaya ta xube tsakiyar falon ta kwanta cikin gajiya yayin da yasmeen ta nufi d'akin Afiya da gudu, amira kuwa ta nufi nata d'akin.

Basu jima da dawowa ba merah ya dawo daga asibiti saboda shirin xuwa massallacin jumma'a, su yasmeen sun yi wanka sun shirya cikin kayan su na gida.

Tun da ta dawo bata ganshi ba, haka kawai take son ganin sa wanda bata san dalili ba, ta matsa kusa da Afiya dake had'awa merah abinci cikin sanyin murya tace Mami ina abokina?

Afiya ta d'an dube ta kafin tace kar na qara jin kin kira wani namiji abokin ki shi ba aboki bane yaya sultan xaki kira shi kamar yanda kika ji su amira suna fad'a.

Hidaya ta jinjina kai cikin gamsuwa kafin tace ni ina so naganshi, yau bamu yi wasa ba.

Kije ki gani idan ya fito daga wanka, amma kiyi hankali kada yayi maki rauni kuma duk abinda yayi maki kada kice xaki rama kinji.

Hidaya ta nufi d'akin da gudu, tana shiga d'akin yana fitowa toilet daga wanka xigidir kamar yanda yake yi.

Da gudu ta bar d'akin cikin tashin hankali taci karo da yasmeen.

Tace menene haka hidaya,
Maciji nagani a d'akin yaya sultan.

Yasmeen tace qarya kike mu bamu da maciji a gidannan da har xai shiga d'akin yaya, ba jiya na nuna maki maciji a TV ba.

Shine yasmeen na ganshi a qafafun yayanki kuma shi bai ji tsoron sa ba.

Yasmeen ta rud'e ta soma kiran Mami da daddy, aikuwa da gudu suka fito.

Hidaya tace taga maciji a d'akin yaya sultan wai, ta soma yarfe hannu tana kuka, ganin yanda yasmeen keyi ya saka hidaya tunanin wannan abin babba ne kuma mai cutarwa dama tana jin lbr maciji jiya ta ganshi a TV yau kuma ta ganshi xahiri.

A tare mera da Afiya suka nufi d'akin, sultan na xaune bakin gado kansa a sunkuye suka soma dube dube d'akin kamar masu neman wani abu.

Kome mera ya tuna sai kuma ya dubi sultan dake xaune ya ganshi ba kaya a jiki, nan take ya fahimci abinda yaran ke magana akai ya dauko towel da sauri ya rufa masa baya so ko kad'an Afiya ta fahimci wani abu.

Afiya jeki kawai ki bar yaran can da shirmen su babu wani maciji anan gidan ma, ba dan taso ba ta fita, da kansa ya shirya sultan ko yayi masa fad'a tabbas baxai fahimci abinda yake nufi ba, merah ya riqo hannun sa suka fito.

Hidaya taja baya tana kallon sa, yasmeen Ma ta matsa duk suka xuba mashi idanuwa domin hidaya ta bata labarin yanda taga abin a jikinsa har suna maganar anjima xasu je su labe ta nunawa yasmeen ta gani.

Yana ganin hidaya ya nufe ta da sauri, ita kuwa tayi cikin falo da gudu tana fad'in,
Ni bana son xama da kai kuma, ka daina bibiyata kada wannan macijin ya cije ni.
*littafina na kud'i ne idan baka biya ba dan Allah kada ka karanta*
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: SULTAN MERAH*
Haske writers Association
Fertymerh Xarah
Afiya tayi saurin riqo hannun sa tana kallonsa,
Na rasa dalili har yau da kake son xama da hidaya fiye da kowa a gidannan, duk wahalar da nake yi akan ka, ni mamin ka ce fa sultan.

Sultan ya fisge hannun sa daga gare ta yana waige waigen neman hidaya wadda tuni ta fice daga falon ma.

D'akin sa ya nufa batare da ya qara waiwayen ta ba, merah bai yi magana ba sanin ko yayi mata bayani baxata taba fahimta ba.

Bayan wata uku...

Hidaya an xama yar gida sosai ta saba da kowa na gidan musamman yanxu da tafi shaquwa da sultan sosai, komai bata iya yi sai tare dashi, wasa tare suci abinci tare, idan hidaya bata gidan taje skul haka xai xauna falo yana jiran dawowar ta tamkar wani maraye, har xuwa lokacin bai taba magana ba, bai taba nuna yana so ko yana sha'awar abu ba kamar hidaya,
Hidaya kuwa acikin watannin nan kacal da tayi fatarta ta qara haske, hausa yanxu a bakin ta kamar bahaushiyar gaske, turancin Ma kad'an kad'an tana fisga bata da matsala a yanxu kamar amira da salwa da suka d'ora mata karan tsana a gidan, idan suna gidan bata da walwala ko sukuni duk hanyar da xasu bi su sanyata kuka sai sun bi.

Da dare bayan sun gama cin abinci suna falon duk sun xube littafan su hidaya da yasmeen suna assignment suna kallon wani series na India.

Sultan na gefen hidaya xaune kamar xai cinye ta, merah yake koya masu assignment d'in yayin da Afiya ke xaune kawai ta tsura masu idanu.

Kuskuren da yasmeen tayi ya saka merah dukan ta da biro a goshi, hidaya ta soma dariya sultan na ganin haka shima ya soma dariya.

Yasmeen ta tunxure baki tana kallon Afiya, Mami kin gansu ko,
Kyale su ki cigaba da abinda kike, bata qara kallon su ba ta cigaba da rubutun da take, the same mistake da hidaya tayi merah yasa biro ya bigi goshin ta aikuwa babu xato yaji saukar bugu shima a nashi goshin, sultan ne da wannan aikin ya fad'a yana kallon yanda yake huci akan sa.

Me nake gani haka, daddy ka daka sultan, na shiga uku yaushe xaka dawo cikin hankalin ka ne, Afiya ta fad'a cikin damuwa.

Sultan bai masan me take fad'a ba yana can yana taba inda merah ya bigi hidaya, ta janye hannunsa tana tunxuro bakin ta,
Ni ka kyale ni munyi fad'a tunda kake dukan daddy.

Aiman bai kula su ba ya cigaba da abinda yake dan sultan ya dake sa ba wani abu bane akan patient d'in dake jifan sa da duk abinda yaxo kansu masu irin lalurar sultan, bai ga abin damuwa anan ba akwai wadanda suka fi sultan hauka kuma ya xauna yayi jinyar su balle d'an cikin sa.

Sun gama assignment d'in suka maida hankalin su gun kallo, taurarin film d'in ke kissing junan su, yasmeen tace Mami a saka mana MBC 3 ai kince mu daina kallon wannan babu kyau.

Hidaya tace meyasa babu kyau, haka ne fa kawai, ta sumbaci yasmeen a kumatu da sauri tana dariya.

Mera ya canxa channel d'in, yasmeen ta maida wa hidaya sumbatar da tayi mata a kumatu, sultan na gani ya miqowa aiman fuskarsa shima yayi masa, aikuwa mera yayi masa cikin murmushi, sai ya miqawa hidaya fuskar sa itama ta mishi.

Cikin dariya tace ni baxan yi ma ba, ai kayi babba kuma kai ba mace ba amma mu a skul idan mutum yayi qoqari class ai anty tana yi masa a goshi ko yasmeen.

Yasmeen ta gyad'a kai da sauri tace hakane ai ranar nima tayi min kingani, ni xan yiwa yaya, yasmeen taje gabansa tayi masa tana dariya, hidaya kema kixo ki masa.

Tace ni baxan masa ba, ai kinsan muna fad'a dashi ya bigi daddy da biro.
Chapter 14 · 0% Book details