← Book details Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 47

Sashe 26

Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya kasa samun nutsuwar xuciyar sa a yanxu, bashi da aiki sai na tunanin ta, idan ya rumtse idanuwan sa ita yake hangowa, mafarkin sa duk akan suna wasa ko wanka tare, wannan halin ko in kula da take nuna wa a yanxu idan ya kira waya taki karba ya dame sa, yana son jin muryarta ko yaya ne, gashi mafarkin tauraruwar sa ya dawo masa a yanxu.

Ya rasa tunanin sa akan qanqanuwar yarinyar da bata fara sanin kanta ba, yarinyar da tasha fama dashi lokacin da yake cikin lalura, ta sadaukar da farin cikin ta domin ta bashi farin ciki a tasa rayuwar, ko meyasa ya damu da yarinyar a yanxu?

Bata da wani abu attractive da xai d'auki hankalin wani d'a namiji ta fannin sura yarinyace sharkaf, balle yace wani abu na jikinta ya jawo hankalinsa gare ta,
Ya lumshe idanun sa yana shafa sumar kansa a hankali, meyasa ya damu da hidaya fiye da kowa da komai a duniya?meyasa yake qalubantar xuciyarsa kullum akan ta?yana referring ko wanne motion na xuciyarsa
akan ta da soyayya, ya d'auki duk wani motsin da xuciyar sa da gangar jikin sa keyi akan ta da cewa yana sonta, he can feel the feelings a yanxu, tabbas yana SON HIDAYA.
*idan baka biya ba kada ka karanta, idan kana so kayi magana, 08169334980*
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*
Haske writers Association
Fertymerh Xarah
Hidaya meyasa kika xauna baki je airport mun raka yaya sultan ba, yasmeen ta fad'a tana kallon ta.

Hidaya ta dauke kanta gefe had'e da tunxuro baki, bana son ina ganin sa.

Yasmeen tace ai yanxu ma ya tafiyar shi shikenan munji dad'i mu riqa wasar mu.

Hidaya ta gyad'a kai tana murmushi.

Tun tafiyar sultan sai ta xama wata irin sukuku ba kuxari, ta saba da sultan, matuqar sabo kuwa.

Idan ta tuna yanda suke wasa, suke cin abinci tare, kwanciya tare, guje gujen da suke yi da kuma canxawar da yayi mata na lokaci d'aya wanda tana d'aukar hakan a matsayin fushi ne yake da ita mai tsanani tun lokacin da ta ture sa daga gado.

Ya shiga ranta fiye da tunanin mai karatu, yau sati d'aya da tafiyar sa amma har yau kewar shi ba ta sake ta ba, walwala ta ragu, farin cikinta ya taqaita.

Wannan hidaya ta yanxu ba waccan hidayar da kuka sani mai surutu bace, mai kaxar kaxar da son wasa, wadda da wuya kaga fushi akan fuskarta sabanin farin ciki, wannan hidayar ta xama ma'abociyar tunani da rashin walwala ko yaushe, yaushe baffan ta xai dawo ya d'auke ta daga gidan nan gabaki d'aya ta huta, yaushe baffa xai dawo ya xama abokin wasar ta na koda yaushe kamar daga farko babu kyama da hantara, babu fushi ko tsawa kome xata yi masa kuwa.

Ta goge wasu hawaye dake sintiri a kumatun ta, ta tuna wani lokaci sun fito xasu je School suna qoqarin shiga mota sai ga sultan shima yaxo shiga mota.

Amira tace yaya sultan ina xaka je School fa xamu je, yasmeen taje ta riqa hannunsa tana fad'in baxa muje da kai School ba kayi girma babu mai irin girman ka acan.

Sultan ya fisge hannun sa ya nufi hidaya yana fad'in hidaya wasa wasa wasa.

Tace ni baxanyi wasa yanxu ba, makaranta xanje kaima kaje gida kayi wasa idan mun dawo xamuyi da yasmeen kaima sai muyi da kai.

Sultan ya girgixa kansa yana make kafada cikin rashin yarda kamar yanda yaga suna yi idan basu son abu ko basa son yi, suna haka sai ga merah ya fito cikin shirin sa na xuwa asibiti, kallon su yayi yanda suka yi cirko cirko har yanxu basu je ba.

Yace lafiya me kuke jira, ina driver na ku.

Yace gani yallabai, su nake jira har yanxu ranka shi dad'e.

Hidaya tayi caraf tace daddy ba wai yaya sultan bane shi sai ya bimu munje School tare, ai mun gayamasa ya xauna gida ya jira mu kafin mu dawo xamuyi wasa dashi.

Mera ya riqa hannun sultan yana fad'in, school xasu je baka ga uniform a jikin su ba, banda rigima irin ta ka fita aka saba yi da kai ne, xo muje inda Mami sai kuyi wasa tare, sultan yaja ya tsaya sai ga hawaye ya soma yi wannan dalilin ya saka hidaya xuwa ta riqa hannun sa tana kallon mera.

Daddy ni xanje dashi sai mu xauna a seat d'aya.

Yasmeen tace wlhy baxa muje dashi ba, ai friends namu dariya xasu mana mun xo da yayan mu class d'aya.

Salwa tace gsky daddy baxaa je dashi ba, teachers d'in ma baxasu yarda ya shiga class ba yayi girma.

Amira ta gyad'a masa kai cikin tabbatar wa itama bata bada goyon bayan aje da shi ba.

Hidaya tace ni baxan je School na barshi yana kuka ba, idan baxaa je dashi ba nima baxan je ba.

Mera yace duk kuxo na kaiku a mota na, I will talk to the principal, duk suka fito a motar ba dan sun so ba, hidaya kuwa farin ciki kamar me xata je da abokin wasar ta School.

Mera da kansa yayi wa principal d'in bayanin ciwon sultan, ya roqi alfarma a barshi na yau kawai.

Hidaya taja hannun sa sai farin ciki take banda harara babu abinda salwa da amira suke binta da shi.

Aikuwa suna shiga class aka soma kallon su, yasmeen ta nufi seat d'in ta, ta xauna hidaya kuwa taja hannun sa xuwa nata seat, kowane seat a class d'in na xaman mutum d'aya ne, each student per seat
haka tsarin skul d'in yake, sai ta xauna kad'an ta matsa mashi shima ya xauna yana bin class d'in da kallo.

Ranar littafan ta haka yabi duk yayi ta xane akan su, wasu kuma ya keta idan ta bige shi ya rama, sai dariya yasmeen ke masu, da aka tashi breakfast yaran suka xagaye shi.

Hidaya wannan yayan ki ne, tace eh, amma yana da kyau sosai, shi bashi da skul ne, meyasa kika xo dashi class d'in mu, shi baya magana ne, kurma ne shi, hidaya yayan ki dolo ne, meyasa yake abu irin na yara, shine tambayoyin da yan class da friends nata ke mata.

Da aka tashi breakfast ta riqo sa suka fito inda suke cin abinci suka nufa, abincin ta tare suka ci kasancewar baa saka dashi ba nata kawai sai duk basu qoshi ba,
Hidaya abinci babu...

Tace ai duk kaine ka cinye min nawa gashi nima ban qoshi ba, meyasa baka ce a baka naka kaxo dashi ba.

Yayi shiru yana kallon ta, ta soma tattara kayan tana had'awa sai ga yasmeen ta xo da nata abinci.

Hidaya kun cinye naku ne.

Tace eh kuma bamu qoshi ba.

Yasmeen tace gwai waya ce ki bari ya biyo ki, gashi ya cinye maki abinci ni kuma yau tare da farida xan yi breakfast tunda kika xo baki kira ni munyi tare ba.

Hidaya tayi shiru batayi magana ba, yasmeen tace kije inda su amira su bada nasu a bashi mana, hidaya ta girgixa kanta tana Jan hannun sa ta dube sa, ka gani kayi haquri idan mun je gida sai muci wani abinci yanxu babu nima ban qoshi ba.

Hidaya abinci in ci ya fad'a kamar yana son yayi kuka, ta xaunar dashi inda yasmeen ba dan ta so ba, sai ta nufi block nasu amira, sai gasu sun fito suna tafe suna dariya ko me suke ma dariyar oho.

Anty amira ta kira sunan ta, ta juyo tana mata wani kallo, menene me ya kawo ki block namu.

Tace yaya sultan ne ya cinye min abinci kuma bai qoshi ba.

To me kike so nayi, uban wa yace kixo dashi ba sai da muka ce a'a kika nace ba maxa kije ki bamu wuri cewar salwa.

Amira tace a'a yaya sultan ne fa, shikenan sai mu barshi da yunwa, aa wlhy, xo karbi nawa kije dashi kuma wlhy kika barmin food flask a skul sai na maki shegen duka ke xaki je gida da ita.

Hidaya taje karba salwa ta mata wani uban rankwashi mai shegen xafi, amira ma sai da ta dangware ta kafin ta bata, jikin ta na rawa ta karba ta juya tana hawaye saboda taji xafin sa, tana xuwa ta share hawayen nata da sauri kafin ta bashi abinci ya soma ci.

Hidaya xo ya fad'a yana kallon ta tare da nuna mata su ci abincin tare, ta girgixa kanta, kallon ta yasmeen tayi sai taga kamar tayi kuka, tace hala sun dake ki ne?

Hidaya ta gyad'a kai tana qoqarin had'iye kukan da yaxo mata, ki barsu da Allah xo muci wannan.

Bayan sun dawo gida suka cire uniform nasu suka cigaba da wasa, tun daga lokacin idan xasu je School da boye suke xuwa batare da sun bari ya sani ba, kafin ya tashi sun gama shirin su sun yi breakfast sun fice a gurguje, idan ya tashi ya fito bai same su ba yayi ta rigima kuma daga baya sai ya daina damuwa ko ya fito bai same su ba, idan ma yana nan xasu je sai ya raka hidaya da yasmeen har mota yana masu kiss a kumatu suna yi masa
bye bye wannan abin ba qaramin qona ran amira da salwa yake ba.

Ta numfasa bayan ta dawo daga tunanin da take, ire iren wannan tunanin ke sakata xama wata iri babu kuxari ko da yaushe a tare da ita sai na kewar sultan, ko yaushe xai dawo suci gaba da wasar da suke yi before oho.

A makaranta ba ta tsinana komai sai tunanin sultan da al'amuranshi, tare da tuna abubuwan da suka gudana a tsakanin su masu qara saka mata kewar shi, bata note bata maida hankali gurin teacher idan ana masu darasi kullum sai an dake ta wanda yasmeen ko kad'an bata jin dad'in sauyin hidaya a yanxu, tayi tambaya tayi rarrashi irin nasu na yara duk a banxa.

Da aka xo jarabawa ta kwaso na talatin, yasmeen tayi na uku, amira na d'aya dama can tana da qoqari sosai da kaifin basira idan bata d'auko na d'aya ba xata d'auko na biyu, sai salwa da tayi na biyar.
Chapter 26 · 0% Book details