← Book details Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 47

Sashe 40

Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta fisge hannun ta da qarfi tana kallon sa an fita d'in ina ruwan ka mecece matsalar ka dani, ni bani da wani auren ka akaina tuni na watsar dashi, baxan xauna da d'an iska marar mutunci ba, baxan cigaba da son ka ba nace bana son ka ko dole ne, ina da wanda nake so a yanxu mai tarbiya kuma shi xan au... tayi shiru sakamakon mari da sultan ya d'auke ta dashi sai da tayi kamar xata fad'i, shima fu'ad ransa a bace yake da hidaya yau.

Yace hidaya kin bani mamaki, sultan d'in kike gayawa haka, cikin xafin marin ga kwallah ta taru a idon ta take kallon sa an masa d'in shi waye, kada ka qara min magana ba ruwan ka dani ta juya tana kallon sultan tana fad'in ka mare ni.

Yace an mare ki d'in ko xaki rama ne ya fad'a yana matsowa cikin ta, ta soma matsawa daga baya tana fad'in nace bana son ka nace bana son ka kill me.. dai dai lokacin baffa ya fito jin kamar muryar hidaya ganin yanda sultan d'in ke tunkaro hidaya ya saka baffa shan gaban sa yana fad'in anan d'in ma fyade xaka mata kenan, ya juya yana kallon hidaya me yayi maki haka kike kuka.

Cikin kuka tace ya kifar da nonon baffa shine kuma ya mare ni, batare da tunanin komai ba baffa ya d'auke sultan d'in da mari yana fad'in bar qofar gidannan tun ban nakasa ma rayuwa ba banxa marar tarbiya wallahi ka qara sa mata hannu da sunan duka sai ka gamu da fushi na.

Cikin fusata sultan yace well ka rama marin da nayi ma a yanxu, xaka qara kuskure ne idan ka sake d'ora hannun ka a fuska ta da sunan duka saboda na daki matata, kuma wallahi hidaya ta sake fita haka sai nayi qarar ka kotu ita d'in matar aure ce kuma ka sani, ya dubi hidaya cikin bacin rai yana fad'in qofar gidan nan kika qara fitowa batare da ixini na ba Allah ya isa.

Baffa yace idan qofar gidannan ta kace sai ka hana mata fitowa, ko kuma idan kai d'an iska ne ka sake takowa qofar gidannan in gani.

Sultan yace sai naxo kuma gobe xan xo idan naxo ka kashe ni ko kuma ka nakasa rayuwata kamar yanda kace ai ba yanxu ne Karo na farko ba.

Baffa yace shikenan ga fili ga mai doki shege ka fasa, sultan xai yi magana fu'ad ya jasa a fusace ya saka shi a motar suka bar gurin, cike da bacin rai baffa yaja hannun hidaya suka shiga cikin gida.

Guy gsky wannan tsohon bashi da mutunci, fu'ad ya fad'a bayan ya hau babban titi, amma duk laifin na hidaya ne har ni take cewa na kyale ta, wannan small rat d'in duka tashin yaushe ce har ta isa ta min rashin kunya ma oh lallai.

Sultan kamar baxai yi magana ba sai kuma yace wai taya hidaya tana da ilimi ta sani sannan kuma tasan da aure akan ta xata fita ba mayafi ba kallabi akan ta sai wannan duwatsu nasu na iskanci, ta Saki gashi tana tafiya a hanya wannan wace rayuwa ce.

Fu'ad yace ni wlhy bangane ta da farko ba naga ko a gida mami bata bari su xauna gida ba hula akan su ballantana har su fita harabar gida da kai a sake, hidaya ta bani mamaki sai kace ba mai ilimi ba al'ada ai bai fi addini ba.

Shiru sultan yayi yana kallon waje xuciyar sa na masa quna.
2 days....

Da sallama ya isa falon mahaifin nasa jiki a sanyaye, aiman na xaune a qasan carpet yana cin farfesun naman d'awisu da yasa aka kawo masa daga sashen sarki.

Nesa kad'an dashi sultan ya xauna yana kallon sa fuska ba walwala yace daddy kayi haquri tuntuni na gane kuskure na baxan qara ba amma dan Allah kasa baki a dawo min da hidaya please.

Aiman ya dube sa kafin ya maida hankali ga cin naman da yake batare da yayi magana ba, ganin bai yi magana ba sultan ya cigaba da fad'in amana ta akaci a ranar daddy wani abu aka bani nasha, sai naji jikina yana canxawa to avoid doing something bad na tashi nace xan xo gida a wannan lokacin wallahi daddy ni ban san ya akayi ba ni dai na ganta kamar babba, ban san menayi ba a lokacin, daddy ka tambayi fu'ad
ko girlfriend bani da, bani da wadda nake so, am not into that, please daddy kayi haquri.

Merah ya qara kallon sa kamar baxai yi magana ba sai kuma ya tura masa plate d'in naman yana fad'in idan ci xaka yi gashi ka ci.

Sultan ya dube sa ya dubi naman, cikin bacin rai ya kau da shi gefe yana fad'in baxan ci ba, hidaya nake so kaje ka karbo min.

Aiman ya lumshe idanun sa yana fad'in baxan iya ba gaskiya bani na bata ba balle naje neman gyara kai da ka bata sai kaje da kanka, sultan xai yi magana aiman yayi saurin cewa get out please bana son damuwa.

Sultan ya tashi ya fice a fusace kamar ya saka ihu, aiman ya bishi da kallo sosai yana bashi tausayi yanda ya dawo cikin qanqanin lokaci kamar ba sultan ba, har wata rama yayi sosai ya lumshe idanun sa cike da tunani iri iri.

Yana fitowa ya sami yasmeen a falo tana xaman jiran sa, fitowar sa yasa ta tashi tana fad'in yaya tun d'axu na shirya dan Allah kaje dani naga hidaya.

Duk da yana cikin halin bacin rai bai hanashi yi mata alama da ta biyo shi ba, da sauri kuwa ta bi bayan sa cike da murna.

Yasmeen sai kallon qaramin qauyen take, ko a mafarki bata taba tunanin xata xo irin wannan qauyen ba, lallai hidaya kamar baa nan ta fito ba.

Tare suka nufi cikin gidan baffa na shirin fita hidaya na tsaye tana bashi saqon abinda take so ya siyo mata daga birni, tana ganin yasmeen ta buga uban tsalle taje da gudu ta rungume ta.

Oh sis I miss you so much, hidaya ta fad'a tare da kaiwa yasmeen peck a kumatu, sultan dake tsaye yaji kamar shine tayi wa haka, yasmeen sai murmushi take ta dubi baffa ta gaidashi, fuska ba walwala yake amsa mata hidaya Ma bata ji dad'in yanda yayi ba, taja hannun yasmeen suka nufi cikin d'akin.

Sultan na qoqarin bin su baffa ya tsaida shi yana fad'in.

Kai malam miye haka, rashin kunya da tarbiya xaka nuna min na shiga d'aki batare da ixini ba.

Sultan yace kayi haquri baffa nayi tunanin komai ya wuce a yanxu.

Tunanin ka kenan ba abinda ya canxa, tukunna ma banyi ma kashedi da karka qara xuwa qofar gidan nan ba, uban me ya dawo da kai.

Sultan ya dube sa yana fad'in baffa ka saba xagin mahaifina nayi haquri bana tanka ma amma yau tare nake da qanwata idan taji kana xagin mahaifin ta tunanin ka ya xata ji bayan nata mahaifin ko da wasa bai taba xagin mahaifin hidaya ba.

Dallah malam rufa min baki, fitar min daga gida kada nayi ma rashin mutunci.

Sultan ya d'aga kai yana kallon gidan kafin ya girgixa kansa batare da yayi magana ba ya juya ya fice.

Yasmeen ta dubi hidaya da ta ajiye mata ruwa da madara tana fad'in, sis rayuwa tafe take da destiny Kala Kala kin manta da yaya sultan kin bude sabuwar rayuwar da ta bani mamaki ko ni bakya tunawa da ni ko?ta fad'a tana qarewa d'akin kallo.

Hidaya tace haka dai kike gani ni na isa na manta dake kice Allah kin tuba
Ni ba wannan ba maganar yaya sultan nake maki nasan kina sonsa yana son ki amma meyasa kin kasa duba masa, meyasa baxa Ku tallafi juna, ku baiwa xuciyoyin ku abinda suke so ba, yaya sultan yayi kuskure ya Kuma gane kuskuren sa yayi Nadama mai suna Nadama amma har yau hidaya kin kasa karban tuban sa meyasa?

Murmushi hidaya tayi tana Kallonta Wanda iyakacinsa fatar bakin ta saboda nauyin ta da take ji a yanxu,
'tace na karbi tuban sa yasmeen, wata qila dai iyakar xaman kenan babu saura tund....tayi saurin katseta cikin tashin hankali.

Ke fa banxa ce wani sa'in baki san rarrashi ba sai baqar kafuwa, wai meyasa kike hakane tunanin ki yaya sultan baya gayamin duk wulaqanci da kike masa, tell me hidaya did my blood brother deserve duk wannan abin da kike masa.

Hidaya tayi shiru cikin dabircewa sanin halin yasmeen tace nidai kiyi haquri.

Tsaki yasmeen ta ja ta tashi xata fita daga d'akin tana fad'in babu ranar xuwa na kenan kuma baxaki qara ganin qafana a wannan qauyen naku ba nayi tunanin babu abinda xan nema a duniyar nan kiqi min shi.

Hidaya tayi saurin riqa hannun ta tana fad'in kiyi haquri shikenan naji please amma ni ba yanxu xan koma ba ta fad'a kawai saboda ganin yanda yasmeen d'in ta d'auki xafi.

Ko da yasmeen xata tafi da taxo rakata kallo d'aya tayi masa ta d'auke kanta, ya shiga motar cikin mamaki hali irin na hidaya ko bata mishi magana dan komai ba ai ta gaida shi a matsayin sa na mijin ta.

Wasa wasa tun daga lokacin kullum sai sultan yaxo gidan amma baffa yaqi bud'e masa ya hana shi ganin hidaya.

Yau ma kamar kullum yayi magiya yayi roqo amma fafur baffa yaqi bud'e masa qofar gidan, yana xaune kan motar sa ya xubawa gidan ido tunani yayi idan fa bai nuna wa wannan tsohon nima kafuwa ne dani ba kamar sa baxai bani matata ba, ya diro daga saman motar da qarfi ya buga qofar kusan sau hud'u sai gata ya ballata kamar wancan lokacin, hidaya tana ganin shigowar sa tayi cikin daki da gudu baffa kuwa kallon ikon Allah yake shi kam a rayuwa bai taba ganin ja'irin yaro ba kamar sultan.

Yace wannan karon sai ka biya kud'in wannan qofar da ka balla kuma xanyi qarar kane ga hukuma domin su yi min iyaka da kai.
Chapter 40 · 0% Book details