← Book details Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 47

Sashe 8

Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da qafafu ya soma tafiya, sauri sauri gudu gudu haka yake tafiyar tasa yana roqon Allah ya kawo wanda xai rage masa ko hanya ne kuwa.

Hidaya kuwa hankalinta yayi matuqar tashi tana ganin ba lafiya ba baffanta bai dawo ba har tsawon wannan lokacin, ta lalubi sandar ta, ta fito gidan ta soma tafiya batare da tasan inda ta nufa ba.

Sultan ya yatsine fuskarsa jin tsikar jikinsa na tashi, ga wata kasala da ta dirar masa lokaci d'aya, yanayin sautin kid'an dake tashi gurin da yanayin da yake jin jikinsa ya saka sa jin wani irin feelings, ya lumshe idanuwansa a hankali, tun da yake a rayuwar sa bai taba jin irin wannan abin ba, duk abinda yake ziyada na kallonsa tana murmushi plan d'in ta ya soma aiki, ta qaraso inda yake tana wata tafiya ta Jan hankali, tana qoqarin xama kusa da shi ya tashi wuf kamar wanda aka tsikara, ya dafe kansa saboda wani sarawa da yayi masa kai tsaye ya nufi qaseem yana duba agogon dake maqale a hannunsa, dare ya soma yi,
Guy bana jin dad'in jikina am going.

Qaseem yace meke damun ka, baxaka tsaya a yanka cake d'in da kai ba.

Sultan ya girgixa kansa yana yatsina fuska saboda wani abu da yake ji yana taso masa tun daga tafin qafafuwan sa har xuwa kansa.

Yace serious bana jin dad'i, granny ma ya kirani kayi haquri.

Qaseem yace ba komai, kabi hanya a sannu kaga dare ne.

Sultan yace kada ka damu xan kula ya basa hannu kafin ya juya ya bar gurin, kai tsaye motar fu'ad ya nufa dan yana tunanin yana ciki,
Yana tsaka da kiss d'in wata budurwa sultan ya buga motar kasancewar tinted ce ya saka baya ganin abinda ke faruwa.

Fu'ad ya sauke glass yana Jan tsaki had'e da kal
lon sultan fuska a d'aure irin ya katse masa jin dad'in sa.

Lafiya malam kake buga min mota haka.

Sultan ya kallesa kafin ya kalli budurwar dake xaune a motar, tsaki yaja yana fad'in fito xamu yi magana.

Yanayin sa ya saka fu'ad saukowa daga fushin da yake, ya fito daga motar yana kallon sultan yace menene?

Sultan ya xare glass d'in idanunsa yana kallon fu'ad, feelings nake ji, ban taba jin irin wannan abin ba.

Fu'ad ya kyalkyace da dariya yana fad'in ai baka isa ba baxaka fara ba k.....

Yayi shiru ganin yanda fararen idanun sultan suka dawo jawur ga kwalla ta taru a idanuwansa wanda ke tabbatar masa cewa bada wasa yake ba, ya riqo hannunsa yana fad'in.

Ko kasha wani abu ne sultan?

Sun bani drinks na sha, fu'ad yace bana tunanin akwai wani abu a drinks d'in gaskiya saboda nima nasha, da yawa ma nan gurin naga suna sha, ko dai wata ka gani ta rikitama tunani ne.

Xai yi magana sai ga ziyada taxo gurin tana wata tafiyar kissa, tana qarasowa ta kwanta qirjin sultan tana fad'in, ina buqatar ka.

Hakan da tayi yaji wani yarrr a jikinsa da sauri ya finciketa a jikinsa batare da tunanin komai ba ya d'auke fuskarta da Mari.

Fu'ad yayi xuru yana kallon ikon Allah dan ma xata taimaka masa daga halin da yake ciki miye laifin ta.

Ya nuna ta da yatsa, ni na maki kama da shashatattun maxa, ko kinga nayi kama da namijin da kowacce mace ke d'ora nauyinta akan qirjinsa, am warning you for the last time ko a hanya kika ganni kika yi gigin nuna kin sanni sai na wulaqantaki ballantana kiyi qoqarin sake had'a qaxamin jikin ki da nawa, baxan kyale ki ba is a promise sai na nuna maki ko ni waye a garin nan tunda kika taba jikina, ya juya ya fice a fusacce fu'ad ya bisa yana kiran sa amma bai saurare sa ba, kafin ya iso tuni ya buga motar sa ya bar gurin a tsiyace.

Tun fitowarsa ya rasa hanyar da xai bi tunda bai san kan qauyen ba, hanya biyu ce da ta rikitasa yayi tunanin acikin su wadda suka biyo ya kasa ganewa, ya dafe kansa saboda abinda yake ji ajikinsa kamar wanda yasha maganin qarfi, sai harbawa take yi da qarfi, ya matse qafafun sa yana bin hanyar da xuciyarsa ta kwadaita masa da bi, gudu yake sosai burin sa yaga ya fita qauyen lafiya.

Hidaya kuwa sai tafiya take batare da tasan inda ta nufa ba, da qarfi yaja burki ganin saura qiris ya bige ta, ya haske ta da hasken motar yana kallonta, yanayin da yake ciki idanunsa ke nuna masa wata babbar bafillatana kyakkyawar gaske, ya tsurawa lips d'inta idanu kafin ya kashe hasken fitilar motar ya fito.

Hidaya kuwa jin wani abu ya tsaya da qarfi a gabanta yasa ta tsaya cak, abinka da wanda baya gani Sam bata san an haske ta da fitilar motar ana kallon taba tsananin tsoro ya saka ta tsayuwa guri d'aya, jin alamun taku ana kusanto ta ya sa ta soma waige waige tana fad'in baffa.

Muryarta har cikin kwakwalwar kansa, ga wani bugun xuciya da yake ji kamar irin wanda yaji lokacin da xai fita asibiti, batare da tunanin komai ba ya riqo hannunta, ta soma kiciniyar kwacewa tana fad'in Ambo a Moi?(waye kai), ya fisgota yayi cikin jejin da ita hankalinsa a gushe dan bai san meke faruwa da shi ba.

Ta soma kuka sosai tana fad'in, Accam (ni ka kyale ni) baffa...

Baffa,Ko mi wadi ma or ko gadumami(me nayi ma)
Duk iya qoqarin ta na ganin ta ceci kanta ta kasa, kuka take sosai tana kiran baffanta, had'uwar numfashin su ya saka sultan rud'ewa abinda bai taba ji ba, bai san yanda xai yi ko xai fara ba qoqarin xare mata xanin jikinta kawai yake, abinda ke gudana acikin jinin jikinsa ya wuce his expectations to such an extent that lamarin yaxo wani limit d'in is beyond his capability to ignore.. he can't control himself duk da kuka da magiyar da yake ji daga gare ta.

Littafina na kud'i ne idan baka biya ba dan Allah kada ka karanta.
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*
Haske writers Association
Fertymerh Xarah
Bayan shud'ewar wasu lokutta, hayyacinsa ya dawo jikinsa, babu xato sai yaji wani kuka yaxo masa yana nanata innalillahi wa inna ilaihir raji'un,
Ya tsinci kansa a halin da bai taba tunanin xai kasance ba, menene yake aikatawa akan qanqanuwar yarinyar da bata san rayuwa ba, bata san menene duniyar da abinda ke cikin ta ba, wacece ita, me ya fito da ita a wannan lokacin? kafin ya farga daga tunanin da yake yaji saukar duka a tsakiyar kansa, ya dafe kan cikin axaba yana qoqarin tashi aka sake kai masa wani dukan mai xafi fiye dana farkon wanda yayi sanadiyar shudewar tunanin sa, bai san kansa ba, bai san ko shi waye ba, bai san me ya aikata a baya ba, bai san komai na rayuwa ba, bai san ko shi din mutum ne ko ba mutum ba baxai iya tuna komai na rayuwar sa ba, rayuwar sa ta dawo sabuwa tamkar jaririn da ya fad'o duniya a yanxu nan take ya fad'i gurin a sume cikin jini.

Baffa ya jefar da qatuwar sandar dake hannun sa ya qarasa da gudu inda hidaya take kwance, tunda yaje gida bai ganta ba ya fito neman ta hankali a tashe , a garin neman nata ne Allah ya saka ya jiyo muryarta tana kiran sunan sa har ya biyo sahun.

Ya tallabo ta da sauri yana kiran sunan ta,
Baffa ya saka min wani abu, akwai ciwo, fitsari yaqi xuwa baffa ka cire min.

Sai alokacin ya lura da babu xani a jikinta ballantana pant, da sauri ya saka hannu ya dafe gefen xuciyarsa danayi saurin bugawa, numfashin sa ya soma sama sama kamar yanda nata keyi.

Me hakan ke nufi hidaya, na kasa riqe amanar da halimatu ta bani kome, meyasa wannan rana taxo min a haka, waye shi wannan wanda ya cutar min dake, meyasa kika fito bayan na hana ki fitowa.

A gigice ya fashe da wani irin kuka mai ban tausayi, ya d'auki xanin ya rufe mata jiki dashi anan yaci karo da wani xobe mai kyau sai sheqi yake, ya boye xoben a aljihunsa kana ya d'auki hidaya da sauri ya nufi gida da ita.

Kud'in sa ya d'auka da ya tanadar saboda aikin idanun ta, lura da yayi kamar bata numfashi ya saka nashi numfashin soma sarqewa, da kyar ya d'auke ta ya goyata ya fito da ita.

Tafiya yake da ita batare da yasan inda yake jefa qafarsa ba addua yake Allah ya taimake sa ya kawo mota kamar yanda ya taimakesa dax'u.

Sai da yayi tafiya mai nisa kafin ya sami mota, da kyar mai motar ya yarda xai d'auke sa saboda dare yayi sosai.

Suna cikin motar ya sake rungumota xuwa jikinsa
Na kasa cika alqawarina na xamowa inuwa a rayuwar ki hidaya tunda wani har ya keta maki haddin ki, ki yafe min ni mai laifine a gareki da naje dake da hakan bata faru ba, da ban yi dare ba da hakan bata faru ba amma na d'auki wannan a matsayin qaddarar rayuwar mu daga ni har ke, baxan iya cigaba da rayuwa dake ba hidaya xuciyata ta kasa daurewa kamar yanda nayi alqawarin sama maki lafiyar idanu tabbas xan cika maki wannan alqawarin naki sai dai naki burin baxai cika ba na ganin baffan ki ko kasancewa tare dashi, ya fashe da wani irin kuka sosai yana qara rungumeta yayin da xuciyarsa tayi wani irin nauyi sosai.

Agogon dake office d'in ya buga qarfe d'aya dai dai na dare, ya rufe system d'in dake gabansa yana qoqarin tashi wayar sa ta d'auki ruri.

Yayi mamakin ganin kiran Afiya a wannan daren, ya d'auka da sauri.

Wai sultan baya gurin kane?

Na taba xama da sultan a irin wannan lokacin ne a asibiti.

Muryar ta na rawa tace wlhy baya gida bai dawo ba har yanxu, ga sarki can ya kasa kwanciya yana jiran dawowar sa, har da securities ya tura su nemo sa amma shiru har yanxu basu dawo ba alamar basu gansa ba, sultan bai taba kai qarfe tara na dare a waje ba ballantana yanxu one.
Chapter 8 · 0% Book details