← Book details Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 47

Sashe 45

Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace eh mana had'a ruwan wankan tukunna ina xuwa, ya fita bai jima ba ya dawo da towel daure a jikinsa, ta dube sa cikin fad'uwar gaba tana fad'in shine kuma ka cire kayan, yace da kaya kika taba ganin anyi wanka, towel d'in ma cire shi xanyi ai kema kayan jikin ki dole xaki cire.

Ta bata fuska tana qoqarin fita daga toilet d'in ni gaskiya baxan yi ba, ya riqo hannun ta yana fad'in amma ai kince kin yarda tunda xamu kashe hasken toilet d'in
baxaki ganni ba nima baxan ganki ba please hidaya, ta tunxure baki tana fad'in to kashe hasken ka rufe idanun ka, yayi murmushi yana fad'in an gama your Highness, itama murmushi tayi tana kallon sa cikin langabewa.
(Fans da son jin kwab kowa yana son jin ya akayi wankan to bara kuji ba
A tare suka fito kowane daure da towel, kome ya basu dariya sai dariya suke dai dai lokacin aiman ya shigo d'akin cikin shirin sa na fita office, kallo d'aya yayi masu ya d'auke kansa ashe yarinyar tana nan Afiya take ta neman ta tun d'axu.

Da sauri hidaya tayi baya ta shige toilet d'in cike da jin matsinanciyar kunya, ko wane kallo daddy ke mata yanxu, sultan ma cikin jin nauyi ya qarasa yana gaida shi, aiman ya miqa masa wata takarda yana fad'in hannu xaka sa kan filin da kace ka baiwa baffa, dalilin yasa na naxo na kawo ma dan ina sauri xan fita, sultan ya karbi takardar yana kallon sa, daddy yanxu xan yi na baka ne ko kuma xan kawo ma anjima ne,
Aiman yace idan xan bari ka kawo anjima menene amfanin xuwa na anan da baxan jira har anjima ba, ina so na bada aikin a fara ne, sultan ya karbi biro hannun sa yayi signing kafin ya bashi yana Shafa gefen fuskar sa, kallonsa aiman yayi kafin ya juya ya bar d'akin batare da yayi magana ba, da kyar ya samu ta fito daga toilet d'in idanun ta jagab da hawaye, ba shiri ya soma rarrashi yana dariya.

Cikin qanqanin lokaci suka shirya suka fito falon hannun su sarqe dana juna, Afiya ta fara ganin su perfect match ta fad'a a xuciyar ta, ba qaramin dacewa suka yi da junan su ba sai yau ta hango hakan, suna had'a ido da Afiya hidaya tayi saurin janye hannun ta daga riqon da yayi mata, Afiya ta d'auke kanta gefe kamar bata gansu ba su yasmeen kuwa sai suka soma iyye, lallai ma yarinyar nan sai yanxu kike fitowa, hararar ta tayi kafin ta juya tana kallon mamee tana gaidata, shima sultan ya gaidata su biyu suka xauna dinning yin breakfast kasancewar kowa ya gama su kad'ai ne suka rage ba su yi ba.

Bayan wasu kwanaki komai ya canxa a wurin baffa ya dawo kamar ba shi ba cikin qanqanin lokaci ya nemi mata bafillatana budurwa da taimakon sultan aka sanya masu lokacin aure.

Da farko hidaya bata so ba sai daga baya kuma ta Saki jiki.

A satin duk kafafen yada labarai na Radio, talabijin da jaridu na garin basu da miuhimmin labari sai na yada labaran gayyatar daurin auren jikokin Sarki El'ameen Merah da Pres.

Ahmed Abbas d'an qasa (wato president mahaifin Afiya da aliyu)wanda al'ummar garin baxa su taba mantawa da wannan daurin auren ba.

Bayan kwana biyu sai ga lefe na gani na fad'a daga gurin el'mustapha na ya'yan sa, akwati goma goma cike da kayan alfarma masu tsadar gaske, da farko aiman bai so akayi lefen ba amma ganin yanda el'mustapha ya kafe yasa ya amince, yasmeen da hidaya kuwa suma aliyu yayi masu komai kamar yanda aka yi wa su amira akwati goma, Masha Allah kayan kam sai san barka.

Auren baffa aka fara yi, suka sha shagalin su amarya Nafisa ta tare anan birni inda sultan ya basu gida flat mai kyaun gaske.

Asabar d'in qarshen watan nuwamba dubban jamaa cikin garin abuja da wajen ta
suka shaida daurin auren Fu'ad Aliyu d'an qasa da Yasmeen Aiman Merah, Aryan El'mustapha Muneer da Ameera Aiman Merah sai Arham El'mustapha Muneer da Salwa Aliyu d'an qasa akan sadaki mafi qanqanta.

Anan Aliyu ya tashi yayi bayanin Auren El'ameen Aiman Merah (Sultan) da Hidaya Ma'awiya ga mutanen da basu san da auren ba, sai dai an boye ainihi dalilin auren wanda labarin qarya aliyu ya shirya masu a lokacin.

Angwaye suka xarce gidan tsohon shugaban qasa inda ammi ta tanadar masu walima da xaa yi, Afiya kuwa iyayen mata ita da rumaisa sai faman shirin matan suke.

Afiya hidima ta sha ta kam, gidan sarki a cike yake taf ba masaka tsinke, musamman da manya manyan abokanta suka fara sauka gidan da suka taso daga wata uwa duniya a waje, ga matan manyan abokan Aiman suma baa bar su baya ba.

Cikin qanqanin lokaci aka gama shirya su, ba qaramin kyau suka yi ba cikin fararen dogayen riguna masu kama da wedding gown, duk acikin su hud'u amira tafi su kyau nesa ba kusa ba sai kamannin ta da sultan suka fito sosai a ranar wanda kallo daya xaka mata ka tabbatar da hakan.

Cikin mota aka sanya su aka nufi gidan da su, sanda suka iso mutane birjik a qofar gate d'in suna jiran isowar su sosai sun ji dad'in yanda ake tarbon su bama kamar hidaya da take ganin baa nuna mata banbanci da su komai tare ake masu.

Suna shiga gidan idanun maxajen akan su kowane yana so yaga tashi yana so ya san wacece tafi kyau a ciki, matar arham amira tafi kyau kam amma saboda son xuciya irin nasu sai kowa ya soma qiyasta tashi tafi kowace kyau a xuciyar sa.

Angayen suma suna sanye da lallausan yadi mai shara shara fari Sol wanda har kana iya hango fararen vest d'in su, kowane yaje ya riqo hannun matar shi suka nemi guri a inda aka tanadar masu suka xauna.

Ba qaramin kyau suka yi ba hatta qawayen amaren sai da suka yana, sun raxana da bayyanar wad'annan zaratan maza ma'abota haiba da kamala, bama kamar sultan acikin su sak kamar Aiman mera sanda yake ganiyar quruciyar sa, wannan ji da kai, wannan taqama da ji da sarauta duk ya tattaro su ya dawo da su a yau musamman daya lura kowacce mace ta kalle sa sai ta furta wow.

Game aka fara akan salwa da amira su xo kowacce daga cikin su ta fitar da mijin ta acikin twins d'in, aikuwa nan kowacce ido ya raina fata Aryan da arham basu da banbanci ga kaya iri daya komai iri d'aya har hasken fata ma.

Wani tunani amira tayi sai tayi wa salwa rad'a a kunne, lokaci daya suka Saki murmushi wato amira tana gane su ta girman jiki, d'aya yafi d'aya jiki kad'an, nan take kowacce ta nuna mijinta aka d'auki tafi,
Sai yasmeen aka xo kanta tare da rufe idanunta da jan kyalle aka jera mata su akan ta xabi nata mijin fu'ad, a bisa rashin sani sai ta nufi sultan fu'ad na gani yayi saurin taro ta hakan kuwa ya baiwa mutane dariya sosai, da aka xo kan hidaya kuwa bayan an rufe nata idanun shiru tayi tana tafiya kad'an kad'an a gefen su duk da tana cikin fargaba, har ta wuce sultan sai kuma ta dawo da sauri dalilin qamshin turaren sa, a tare suka rungume juna aka d'auki sowa da tabi wurin.

Bayan an kammala walima suka nufi cikin gida amaren maxan na waje, sultan yana kan motar sa, fuskar nan tasa a murtuqe cikin baqin glass duk dai saboda matan da suka xo masa magana wurin ya fi a qirga, xuwan hanifa ne ya sa ya saki fuskarsa ba laifi,
Tace ai bro tunda nayi tattaki naxo auren ka har Nigeria kai ma sai kaxo aure na har Cameron ko baka so.

Yace ai dole ne kuma tare da hidaya xamu xo bikin sis, yaushe ne auren?

Tace February ne,
Yace ashe ma an kusa,
Ta gyad'a kai tana murmushi kafin tace yaya matar ka ta had'u qarama da ita mai kyau,
Yayi murmushi yana fad'in ke dai ki fad'i gaskiya nasan halin ku keda su amira ai,
Wallahi da gaske fa yaya,
Hidaya da ta fito tana nemansa ya bata waya tana son kiran baffa taji ko matar shi xata xo d'in kamar yanda suka yi magana taja turus ta tsaya cike da tashin hankali ganin sultan d'in nata tare da wata suna dariya, kamar ance ya d'ago kuwa suka had'a ido da ita, yanayin ta yasa yaji gaban sa ya fad'i, kafin ya diro daga motar tuni ta juya ta koma a ganin ta wannan toxarci ne ace ranar bikin auren ta mijin ta yana fira da wata.

Hanifa ta dube sa tana fad'in lafiya yaya?

Yace ba komai ina xuwa, ya bi hidaya.

Hidaya na shiga d'akin da suke before abokan su amira suka dube su suna fad'in amaryar yayan ku ma tana da kyau very young and fresh, salwa tayi carab tace but duk aciki shi kad'ai ne ya auri bare kowa yana da alaqa da jinin sarauta amma banda ita, hidaya ta kalle ta sai kuma ta d'auke kanta tana barin d'akin, yasmeen tace wannan rayuwa da kike da ita bata da kyau ke kike kallon ta bare mu a gurin mu ba bare bace koma bare ce a hakan aka ganta akace ana so har aka xabe ta tana bare aka bar masu jinin sarauta, tayi tsaki ta fice, amira tace meyasa xaki ce ita bare ce ko ba komai a gidan mu ta tashi kuma yayan mu take aure, ta dubi friends d'in tana fad'in hidaya is our cousin ku kyale salwa tana jin haushi ne saboda yaya sultan bai aure ta ba ya auri hidaya, aikuwa nan take d'akin ya d'auki dariya, salwa kuwa ranta ya baci sosai.
Chapter 45 · 0% Book details