← Book details Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 47

Sashe 6

Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Eh wanda aka kwatanta min kenan, ya riqa hannun ta suka fito daga gidan kana ya rufe suka tafi.
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*
Haske writers Association
Fertymerh Xarah
Kusan minti talatin da xuwan su office d'in amma Dr mera bai kula su ba, sai ta kan patients d'in sa yake.

Suna xaune, wata mata ta shigo tare da wata budurwa a bayanta, kallo d'aya xaka masu ka tabbatar kud'i sun xauna a gurin su tun daga yanayin suturar dake jikin su,
A hankali budurwar ke bin office d'in da kallo kafin ta sauke idanunta akan su fu'ad dake xaune, cikin murya qasa qasa ta dubi maman ta,
Wow, mom kinga wasu guys acan sun had'u wlhy, maman ta juya tana kallon su.

Yarima dake xaune caraf yaji abinda yarinyar ta fad'a ya maida hankalin sa gurin su sultan, abu suke kallo a waya Sam hankalin su Ma baya gurin.

Maman ta xauna tana murmushi sanin yarima, likitan tane sosai indai yana garin, sun san juna, cikin sakin fuska suka gaisa yake tambayar ta ko jikin ne,
Tace aa Hafsat na kawo, ya juya yana kallon yarinyar cikin d'aure fuska, yace meke damun ki.

Wata kunya da nauyi taji, ta saci kallon su sultan da har yanxu basu san da xaman ta a gurin ba kafin ta kalli mahaifiyarta, mom ki gayamasa da kanki ni baxan iya ba.

Murmushi matar tayi kafin ta soma yiwa Aiman bayanin yanda tayi mata bayani kafin su xo.

Kai tsaye yace infection ne ke damun ta,
Infection d'in da suka ji an kira ne ya saka su d'agowa suna kallon mutanen dake xaune a gurin aiman.

Dr yace Hajiya kuje da ita gurin Dr iman ko Dr fulani ki gayamasu ni na turo ki, idan yarinyar tana discharging duk ki fad'a masu.

Yayi hakan ne saboda su sultan dake gurin.

Suka tashi, Hafsat ta kasa daurewa ta dube su cikin murmushi tace hey... tana d'aga masu hannu.

Sultan ya dauke kansa kamar bai gani ba, fu'ad kuwa murmushi yayi ya d'aga hannu har xaiyi magana suka had'a ido da yarima yayi saurin mai da hannun yana washe baki.

Matar har xata fita ta juya tana kallon mera, tace Dr waye yaron ka acikin su da nake jin labari,
Batare da ya nuna mata ko d'aya daga cikin su ba, yace duka ya'ya nane kuma jinina.

Cikin rashin fahimta tace su d'in twins ne, amma akace yaron ka d'aya ne dake Phoenix.

Cikin qaguwa da tambayar nata dan da ba dan ita bace baxai kula ta ba ya nuna mata fu'ad yace wannan ne firstborn nawa shi na fara gani kafin wannan, ya nuna mata sultan yace shi kuma yaron sister d'ina ce Rumaisa kinga duka jinina ne babu banbanci,
Hakane kam masha Allah, kyawawa dasu, Allah ya inganta rayuwar su.

Yace amin, suka fice.

Dad wane ciwo ne infection kuma yaji muryar fu'ad na jefo masa tambayar.

Daga sultan har mera kallon sa suke kafin yace meyasa kake tambaya.

Ba komai saboda mu kiyaye da ciwon ne muma kada mu kamu da cutar ko ba haka ba sultan ya fad'a yana kallonsa.

Sultan yayi saurin gyad'a kansa yana murmushin yaqe cike da haushin fu'ad.

Mera yace wannan ciwon mata sun fi kamuwa dashi kuma mafi akasarin ciwon rashin tsabta ne a gurin.

Gurin ina?

Suka tambaya lokaci d'aya suna xaro idanun su cike da mamaki.

Kallon su yayi cike mamaki sai kuma yaja dogon tsaki yace ba wannan na kira ku ba, sultan nan da 2wks ka shirya xaka koma Phoenix lokacin resuming School d'in ka yayi beside ma an kira ni akwai wasar da xaku gudanar tare da yan Germany.

Wani tsalle sultan yayi cike da farin ciki kafin ya xagaya ya rungume mera, thank you dad, I so much love you, wannan qasar kamar akan qaya nake.

Murmushi kawai mera yayi kafin yace kuna iya tafiya ina da ayyuka a gabana yanxu.

Suna fitowa fu'ad ya dubi sultan yana fad'in man sai wani nishad'i kake ni fa yarinyar nan ta min kyau sosai amma abinda ban fahimta ba duk gayun nan nata ace bata da tsabta, wane guri ne a jikinta wanda bata kula dashi.

Mtsew sultan yaja tsaki yana fad'in ni fa saboda ya xama dole ne nake yawo da kai wlhy amma Sam baka da class, qaseem ma ya fika wlhy, you are not my type.

Kai fa sai ana maganar mutunci ka sako rainin hankali aciki, wannan yarinyar ce bata had'u ba, You are blind, idan dama taxo maka kayi amfani da wannan lokacin kafin damar ta subulce maka.

Sultan yace idan damar ta subulce Ma xaa iya siyen ta matuqar kud'i suna magana, maxa nifa har yanxu ban yarda akwai abinda kud'i baxai iya siya ba cos ban taba neman abu ko na saka abu a raina ban same shi sanda nake so ba, har yanxu ban ga kalar macen da nake so xata burgeni ba.

Fu'ad ya tabe baki ya shiga mota, shima sultan ya shiga ya tada suka fita, suna fita napep d'in su baffa na sako kai cikin asibitin, sultan yaja wani birki yana dafe qirjinsa, fu'ad ya dube sa da sauri yana fad'in lafiya meya raxana ka haka?

Yace nima ban sani ba haka kawai naji fad'uwar gaba kamar xuciyata xata fad'o.

Baffa yana riqe da hannun hidaya suka nufi cikin asibitin, hidaya sai tafiya take tana tsalle yau ta shiga mota har kusan Kala biyu, yau gata a birni cikin asibiti xaa gyara mata idanuwanta taga baffanta.

Baffa yace ki nutsu hidaya kada kiji ciwo.

Sun jima sosai a gurin har sun soma gajiya da xama kafin axo kansu, aka kira sunan su suka tashi suka nufi office d'in.

Suna shiga duk suka qame jikin su lokaci d'aya saboda wani sanyi da qamshi daya ratsa jikin su.

Baffa sanyi nake ji nan ina ne muka shigo.

Wai sunce d'akin duba likitane hidaya nima naji wannan sanyin.

Duk abinda suke mera na kallon su sai dai baya jin me suke fad'a, yanayin su ya nuna Sanyi suke ji dalilin a.c, kallon su yake qasa da sama cikin shigar su ta fulani ko meke damun wadannan mutanen oho.

Ka xauna anan, ya nuna wa baffa gurin da xai xauna, ita kuma ta xauna anan, baffa ya girgixa kansa ya d'auki hidaya ya d'ora a qafafun sa yana fad'in,
Bar ta anan likita wannan sanyin xai cutar da ita idan bata ji d'umin jikina ba.

Murmushi kawai mera yayi jin yanayin hausar tashi da babu kwarewa aciki.

Yace menene matsalar ya fad'a yana bud'a file d'in nata.

Baffa yace makauniya ce likita bata gani ka taimaka likita a gyara mata idanun ta.

Mera ya d'ago da sauri yana kallon ta, yanayin idanunta baxaka taba tunanin suna da matsala wai bata gani ba, Allah mai iko wannan kyakkyawar yarinya haka amma ta rasa idanu,
Yace yaushe matsalar rashin gani ta same ta.

Baffa yace ni ban gane me kake nufi ba likita,
Aiman ya d'auki wayar sa ya kira Dr fulani, bata jima ba sai gata taxo, ya nuna mata su,
Mutanen ku ne, bana gane nasu basu gane nawa can you help?

Tayi murmushi tana jinjina kanta tana kallon su, ki tambaye shi matsalar idanun nata yaushe ta fara ko a hakan aka haifeta.

Fulani ta juya harshen ta tana tambayar sa,"Baba famtinam ko fe'i be ko damata mo"
baffa yaji dad'i sosai ya soma yi mata bayanin komai, kafin ya juya yana kallon hidaya yace kinji wata yar'uwar mu ko hidaya kina cewa baxakiyi karatu ba, ita wannan d'in fa likita ce.

Fulani tayi murmushi ta juya tana kallon mera kafin ta soma yi masa bayani, mera ya yamutsa fuska jin suna maganar kamar ruwan naquda ne acikin idanun nata,
Yace Amiotic fluids doesn't causes blindness
But there are Congenital anomaly that causes blindness,And in the physiology of Liquor is only meant to lubricates and cushion the baby while in utero, ki duba idanun sosai ya fad'a yana bud'a idanun hidaya d'in, babu wata alama dake nuna ruwan naquda a wannan idanun, wannan inheritance ne.

Kamar ya likita, fulani ta tambaya tana kallonsa, bani da ilimi ta gefen idanu cos ba fannina bane amma yau ina so nasan wani abu game da hakan.

Mera yaja numfashi kafin yace Which type of eye disease are inherited?

More than 60 percent of cases of blindness among infant are caused by inherited eye disease such as congenital (present at birth) cataracts, congenital glaucoma, retinal degeneration, optic atrophy and eye malformation.

Kin fahimci me nake magana, ta gyad'a kai tana qara kallon hidaya,
Ya cigaba da fad'in in adults, glaucoma and age related macular degeneration are two of the leading causes of blindness, and both appear to be inherited in a large portion of cases.

Tace amma likita idanun nata kana ganin xasu gani kuwa?

Yes of course me xai hana, they need good clinic to provide early diagnosis and effective treatment for complications of inherited eye disorders.

Your ophthalmologist pediatrician geneticist or family doctor may refer you or your child to the center for specialized evaluation, testing and diagnosis if a genetic eye disease is suspected.

Ta sauke numfashi tana kallon baffa, tace Neddo man larai tobe huwi more ( yarinyar xata gani idan an mata aiki).

Hidaya ta diro tana tsalle cikin farin ciki kafin ta qanqame mahaifin nata tana dariya sosai wadda ya jima baiji irin ta daga gurin ta ba.

Tace amma kud'in aikin yana da tsada sosai baba dan xai kai million biyu haka.

Cak baffa ya tsaya yana kallonta yayin da xuciyar sa ke bugawa ina yaga wannan kud'in, ya dubi merah dake kallon su yace likita ayi haquri a rage mana wani abu, mu ba masu kud'i bane, babu komai.

Haka kawai mera yaji yana son taimaka masu bai san dalili ba ko dan yarinyar ta kasance marainiya ne?
Chapter 6 · 0% Book details