← Book details Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 47

Sashe 18

Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aa ni baxan bashi auren salwa ba dan baxata ji dad'in xama da wannan miskilin yaron ba, baxai taba bata lokacin sa ba kasani, ina son tayi aure inda xata sami kwanciyar hankali fiye da xaman ta da sultan.

Yace hakane kuma, ko auren sa da hidaya na d'an wani lokaci ne ai in ba haka ba yaushe sultan ya isa aure.

Ni bana d'aukar wannan auren a matsayin aure, auren da babu biki ba komai, auren da babu wanda ya san dashi sai abokan arxiki da yan uwa, sannan auren da xai xama matacce na d'an wani lokaci.

Aiman yayi murmushi yana fad'in haka ne.

Mami wai hidaya baxata je skul ba yau?

Eh, ke kad'ai xaki je.

Meyasa Mami, nima baxan je ba.

A'a yasmeen, hidaya ba lafiya kinga ta tashi da xaxxabi yau, xuwa gobe idan ta sami lafiya xata je, idan kuma kika tsaya daddy xai maki allura ne idan xai yi mata.

Aa Mami xanje, ta juya tana kallon hidaya dake kwance a sofa cikin tausayi.

Sultan yaxo inda Afiya yana nuna mata hidaya da yatsa.

Mami.. hidaya... wasa
Tace yau babu wasa sultan, hidaya ba lafiya.

Yasmeen na gama breakfast ta d'auki food flask da jakarta ta fice da gudu.

Mami... hidaya... wasa
Ta riqo hannunsa ta kai a wuyanta ta langabe tana kallon sa cikin nuna masa ko xai fahimta, hidaya ciwo babu lafiya, yau babu wasa.

Yaje inda hidaya ya d'ora hannun sa a wuyanta xafi yaji rau ya juya yana kallon ta.

Mami.. hidaya..

Ciwo
Tace eh ciwo, ta had'o tea mai xafi ta qaraso falon ta miqawa hidaya, ta girgixa kanta ni baxan sha ba.

Kina son Golden morn, ta girgixa kanta tana hawaye, me kike so hidaya, Mami ni bana son komai idan nasha amai xai xo.

To ai baxaki xauna haka ba, tashi ki sha tea d'in sai kisha magani idan ba haka ba daddy allura xai maki daya tashi barci.

Hidaya ta tashi tana yarfe hannuwanta cikin kuka, Minkam miyida (ni bana so), sultan ya d'ago da sauri yana kallon ta, idanu ya tsura mata kamar mai son tuna wani abu.

Afiya ta subulce da dariya, tace yau kin tuna yaren naki kenan, to ni taya xan fahimce ki, kina so na baki da kaina.

Nan ma ta girgixa kanta, Afiya ta ajiye tea d'in tana fad'in bari na d'auko maganin tukunna ta juya ta fice.

Hidaya...

Sha
Tace ni bana sha ka kyale ni, sai yasa qafa ya shure tea d'in ya xube a gurin dai dai lokacin Afiya ta dawo d'auke da kwalin hollandia a hannunta.

Tashi kisha wannan tunda bakya son tea d'in, taja ta tsaya turus, waye ya xubar da tea d'in kuma.

Hidaya dake kwance tace nima ban sani ba, ko baa fad'a ba tasan baxai wuce aikin sultan ba
tunda hidaya bata sha ya xubar, taja tsaki tana fad'in tashi kisha kafin na saba maki yanxu dan dukan ki xanyi.

Ba dan taso ba ta tashi ta sha sosai saboda sanyi sanyi da take dashi yasa taji dad'in sha, tana ajiye wa sultan ya d'auka shima ya sha, Afiya ta bata magani tasha shima ya miqa hannun sa a bashi maganin yasha.

Tace baxan baka magani kasha kana lfy ba, ya qara miqa mata hannu yana yatsina fuska, sanin halin sa, sai ta dubo vitamin c aciki ta bashi, ya karba ya tura baki tare da korawa da ruwa yana bata fuska kamar yanda yaga hidaya tayi.

Murmushi Afiya tayi ta shafi kansa had'e da sumbatar sa a goshi tana fad'in Allah ya baka lfy, sai ya nuna mata hidaya dake kwance itama ayi mata, tayi wa hidaya ita, sai yayi dariya shima ya sunkuya yana yiwa hidaya,
Mai aiki taxo ta gyara gurin, Afiya ta xaunar da hidaya sai ta jingina da sofar, sultan kuwa ya shige jikinta sosai kamar xata gudu ta barshi, binni binni yayi mata kiss a goshi shi a hakan ma gani yake duk cikin wasa ne.

Me ya hana hidaya xuwa makaranta yau, merah ya fad'a yana qarasowa cikin falon
Sultan na ganin sa ya tashi ya nufesa da sauri yana nuna masa ita.

Daddy... hidaya.... ciwo.

Afiya tace iyye yau kuma harda daddy ake kira.

Ciwon me ya same ta, mera ya sake tambaya batare daya bi takan xancen sultan ba.

Xaxxabi ne ke damun ta, tasha magani yanxu, xai yi magana sultan ya riqo hannunsa yana jansa xuwa inda hidaya.

Daddy... hidaya..... ciwo... zo
Ya kai hannun merah jikin hidaya, xafin ya ragu akan d'axu.

Xaxxabi xai sauka tunda tasha magani kice yau xaa sha fama da sultan
Tayi dariya tana fad'in tun d'axu nake fama ai, harda maganin dana bata ya kafe sai na bashi yasha, yanxu yasan banbancin Mami da daddy tunda yaji suna fad'a kenan.

Aiman yayi dariya kawai batare da yayi magana ba.
*littafina na kud'i ne idan kana so ka biya*
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*
Haske writers Association
Fertymerh Xarah
Afiya d'auki hidaya ki shiga da ita d'akin su, baxata ji dad'in kwanciya anan ba.

Ta tashi ta d'auki hidaya, xumbur sultan ya miqe yana kallon ta kafin ya dubi mera yana fad'in.

Daddy...

Mami..

Hidaya...

Yace ba inda xata je da ita d'aki xata kaita, xo xauna nan ya nuna masa kusa dashi.

Sultan yaqi xama, ya bi bayan Afiya, ta shimfidar da hidaya akan gado shima ya hau gadon ya kwanta.

Mami..

Hidaya..

Kai sauko, barci xatayi, ya xaka xo ka hau gadon yara ko kunya baka ji.

Aiman dake shigowa yace ki kyaleshi mana, banda abinki sultan yasan wata kunya ne, duk abinda xai yi a gidannan naki kallo kawai ki kyale shi, ya ja hannun ta suka fice.

Ya kwanta yana fuskantar ta, idanun ta a lumshe barci take amma sama sama kasancewar yanayin jikinta, ya kai yatsansa yana taba lashes d'in ta dake jiqe da hawaye, ya kira sunan ta, batare da ta amsa ba ta bud'e idanuwan a hankali tana kallon sa murmushi yayi mata, hidaya... wasa.

Batare da tayi magana ba ta maida idanunta ta lumshe, hidaya... wasa ya qara fad'a yana qoqarin bud'e mata idanu da yatsa, ta juyar da kanta can gefe d'aya tana fad'in baxan yi ba ka kyale ni.

Ya koma ta can bangaren da take fuskanta had'e da soma girgixa ta, sai ta fashe da kuka ta diro daga saman gadon ta fito, shima da sauri ya biyo ta.

Aiman dake breakfast ya juyo yana kallon ta, menene kuma.

Baxai barni nayi barci ba sai munje wasa, aiman ya taso ya riqa hannun ta, d'akin ya maidata, ta hau gadon ta kwanta sultan na qoqarin sake hawa ya riqe shi.

Sauko modibbo tunda baka ji, ka barta tayi barci mana, an gaya ma ana wasa idan babu lafiya, ya jasa suka fita ya rufe mata qofar.

Sultan yaja ya xauna bakin qofar d'akin, mera ya barshi ya koma dinning, Afiya na fitowa kallo d'aya tayi wa sultan sai da gabanta ya fad'i.

Yarima yaron nan kuka yake fa, kuka ya fad'a yana kallon sultan d'in, yana xaune a wurin sai hawaye yake.

Yace tunda ya fara ciwon nan bai taba kuka ba sai yau, just leave him he may regain something, kyale shi kawai yayi.

Ta juya ta bar falon, yana cin abincin nasa yana kallon sa, yana ganin yanda yake juya kan nasa yana dafewa, ya janyo wayarsa, dialing number Dr Patrick yayi wanda shine yayi wa sultan aikin kan a Riyadh.

Sun jima sosai akan waya suna magana kafin ya tsinke, tashi yayi ya nufi sultan d'in ya tsugunna gabansa tare da dafa sa.

Sultan, ya kira sunan sa.

Ya d'ago yana kallon sa,
Yace kukan me kake yi.

Yace hidaya,
Yace kana so na kai ka gun hidaya, ya gyad'a kansa yana kallon sa,
Yace xaka barta tayi barci baxaka dame ta ba?nan ma ya gyad'a kansa, aiman baya mamaki da sultan d'in na amsa masa likitansa ya tabbatar masa a yanxu kowane lokaci sultan d'in xai iya dawowa hayyacin sa.

Ya riqa hannun sa suka nufi d'akin, tuni tayi barci sultan ya nufe ta da sauri ya rungumeta tsam a jikinsa bayan ya hau gadon kamar xaa kwace masa ita, ya kalli mera sai dariya yake.

Daddy hidaya tana barci, kyam aiman yayi masa da idanu, me yaji sultan d'in na fad'a, kafin yayi wani yunquri sai ganin yayi ya kwanta tare da ita a jikinsa yana lumshe idanun sa.

Ikon Allah ya fad'a yana kallon su.

Yaya fu'ad d'axu driver ya d'auko mu skul muna hanyar dawowa na ganka ka wuce da wata a gaban motarka wacece ita?

Kallon ta yayi ta kafe shi da idanun ta kamar xata cinyeshi da kyar yace course mate ce.

Tace I see course mate, ta juya xata fice ya riqo hannunta da sauri.

Believe me Amira just course mate bayan wannan ba komai tsakanina da ita, lift ne kawai nayi mata.

Tace shikenan amma jiya da kaxo baka neme ni ba, na ganka da hidaya meyasa kake son xama da ita.

Yace hidaya itama qanwatace ai, me kike tunani?

Ta tabe bakinta kawai, yace meyasa keda salwa kuka tsangwami yarinyar nan me tayi maku.

Yaya mu fa ba abinda muke mata idan ta tsoka ne mune dai, amma tun daga ranar ai bamu sake mata komai ba.

Yace to shikenan amma ku daina mata abinda kuke mata itama qanwar kuce kamar yasmeen babu banbanci.

Amira ta tabe baki kawai batare da tayi magana ba.

Yau kam jikin hidaya da sauqi, ta murmure sai wasar ta take yi tare da jelar ta
A tsakiyar falo suka jera Teddy's d'in su, yasmeen ta soma rabawa, tace ga nawa ga naki ko.

Tace to ina na yaya sultan shima a raba dashi.

Aa baxaa raba dashi ba, ai shi namiji ne kuma yayi girma da wasar baby, ai shi xai riqa yo mana cefane kuma yana kai ya'yan mu School ko.

Hidaya tace eh fa kuma shi xai riqa mana girki tun da ai mu bamu iya ba.

Nan suka soma had'a kayan wasar suka raba ba dashi ba, sai ya tashi shima ya iya kai qara kamar yanda yaga suna yi, ya nufi Afiya.
Chapter 18 · 0% Book details