← Book details Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 47

Sashe 1

Sultan Merah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry
WordDocument
0Table
Data
[11/20, 10:25 AM]Ummi Tandama:
*SULTAN MERA*
Haske writers Association
Fertymerh Xarah
Phoenix
Wata sassanyar murya marar amo, wadda ke dauke da rashin kuxari ta yi sallama a dakin, ta amsar sallama tana kallon sa, sanye yake cikin shud'iyar shadda gexner wadda tayi matuqar fito da sirrin fuskar sa.
(kallo d'aya na yi masa na gane shi din jinin Aiman mera ne saboda tsananin kama da suke da juna)
SULTAN kenan mai shekara
goma kacal a duniya.

Duk wani fushi, bacin rai da ke cikin xuciyarshi sai yaji yana bacewa sanadiyar hada idanuwa da mahaifiyarshi Afiya.

A hankali ya qarasa shiga dakin tare da yiwa kansa maxauni a d'aya daga cikin kujerun da suka yiwa qayataccen falon qawanya.

'me ya same ka haka? ta tambaya cike da kulawa irin ta d'a da mahaifiyar sa.

Ya turo bakin sa tare da dauke kansa daga kallon ta,
Mami wai meyasa sai nayi kwallo ne, na gayamasa bana son
kwallo bata cikin tsarina a rayuwa, just look at me Mami dan Allah jikina yayi kama da na masu kwallo, meyasa Dad yaqi ya gane hakan?

Taja numfashi kadan tana kallon sa, meyasa kai kuma baka jin magana ne, sau nawa kake so nayi ma mgn akan wannan, miye aciki dan ka faranta ran mahaifin ka, kayi masa abinda yake so?

Ya qara tsuke qaramin bakin sa hade da yatsina fuskarsa, yana qoqarin tashi ta dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu.

Look sultan dole ne xakayi abinda mahaifin ka ya umurce ka dashi matuqar baka son raina ya baci akan ka, mahaifinka bai kasance mai bijirewa umarni iyayen sa ba, tun yana yaron sa ya taso da son kasancewa d'an kwallo amma mai martaba ya hana sa yana so ya xama cikakken likita domin yana sha'awar ace yau jinin sa mai ceton al'umma ne, sai ya xamana bashi da aiki ko lokacin wani abu idan ba kallon ball ba sai karatun sa, ya baiwa kallon ball muhimmanci fiye da tunanin ka wanda alokacin ko mace bata gabansa, ya kasa cika burin sa na xama d'an kwallo amma ya cika burin iyayen sa wanda albarkar hakan ke tare dashi har kake ganin sa a matsayin da yake yanxu, meyasa kai baxaka cika masa burin na sa ba.

Sultan ya dubi cikin dake jikin ta kafin ya motsa bakin sa da kyar yace, Mami ba gashi kina dauke da wani baby ba, ya bari idan kin haihu yaron ya cika masa burin sa amma ni ball baya cikin future plan d'ina, we have horses a gidan nan ni shine burina na xama d'an tseren doki.

Allah ya kyauta sultan amma baa nan gidan ba, footballer xaka xama ko kana so ko baka so final decision din mu kenan, ta gefen karatun ka xaka iya xabar fannin da kake so ka xama in your future.

Bai qara magana ba ya tashi xai fice ko me ya tuna ya juya yana kallonta kamar xai yi kuka.

Mami ban daina wannan mafarkin ba, yau ma nayi and again naga taurarin biyu suna kusanto junan su.

Ka cigaba da addua, nima Ina kan yi.

Ya juya ya fice ta bishi da kallo har ya bacewa ganin ta, ta rasa ma'anar wannan mafarkin da sultan keyi, wata takwas kenan da ya soma irin wannan mafarkin na taurari biyu, Allah kad'ai ya san me yake nufi da hakan.

NIGERIA
Fitowar ta da kwarya a hannu yayi dai dai da shigowar dabbobin gidan, da sauri ta ajiye kwaryar wanda madarar shanu ce aciki ta qarasa garken nasu tana d'aure su d'aya bayan d'aya.

Tana cikin d'aurewa ya shigo gidan bakin sa dauke da sallama, yana riqe da wata qatuwar sanda a hannunsa tare da wata baqar Leda dake dauke da lemu da ayaba aciki.

Ta amsa sallamar tana kallon sa da murmushi,
Sannu da xuwa maigida.

Murmushi yayi yana ajiye kayan hannunsa ya qarasa inda take yana kama mata d'aure shanu dan baxata iya ita kad'ai ba suna da yawa.

Sun dauki tsawon mintuna kafin su gama d'aure su, suka dawo tsakar gidan suka xauna.

Bari na kawo maka ruwa mai gida, tayi qoqarin tashi ya dakatar da ita, kiyi xaman ki anjima xan sha (suna mgnr cikin rashin kwarewa a hausa kasancewar su Fulani asali )
Murmushi tayi ta gyara xamanta, ya janyo ledar gabanta ya Ciro ayaba da lemu d'aya d'aya ya dauka ya bata sauran yana fadin kici sosai Halimatu saboda cikin dake jikinki likita yace a riqa baki wannan.

Murmushi tayi batare da tayi magana ba ta janyo ayaba ta bare tana ci a hankali, ya tsura mata ido yana kallonta cikin tsananin so da birgewa, yana matuqar son matar sa kamar yanda take son sa take kula dashi, kawaici da kunyar ta suna birgeshi, yana tausaya mata musamman yanayin cikin nata dake matuqar bata wahala tunda ta same sa bata qara lfy ba, kullum da xaxxabi take kwana wataran ma duk abinda taci sai ta amayar dashi har xuwa lokacin nan da cikin yake cikin watan haihuwar sa.

Bayan ta gama cin ayabar ta dubesa da murmushi cikin harshen fulla tace kasan addu'ar me nayi mana yau dana yi sallah.

Ya girgixa kansa yana kallon ta da murmushi, ta shafa cikin kafin ta sunkuyar da kanta qasa cikin jin kunya tace nayi addua abinda ke cikin ciki ya kasance namiji ne saboda ya taimakeka xuwa daji da dabbobin nan.

Yayi murmushin da haqoran sa suka bayyana, yace nagode da wannan addua halimatu amma tunani na da naki ba d'aya ba ni Ina son mace kuma kullum ita nake addu'ar Allah ya bani mai kyau da kawaici kamar ki, mai haquri da sanyin hali irin naki.

Ta sa tafukkan hannunta biyu ta rufe fuskarta cikin matsinanci farin ciki, shima yana murmushi ya tashi yayi hanyar dakin sa.
[11/20, 10:25 AM]Ummi Tandama
*SULTAN MERA*
Haske writers Association
Fertymerh Xarah
Bayan wasu kwanaki.....

Safiyar yau ta tashi bata jin dad'in jikinta, komai ta na yin sa cikin dakewa da dauriya kada mai gidan ya lura tasan ba qaramin aikin sa bane ya fasa fita kiwo yau.

Ta xauna da kyar bayan ta ajiye masa kofin madara a gabansa, ya dube ta yana kallon yanda take yatsina fuska,
Lafia halimatu ko jikin ne?

Ta girgixa kanta da sauri tana kallonsa,
Ba jikin bane tashin xuciya nake ji kamar ko yaushe, baxan iya cin komai ba a yanxu sai xuwa anjima idan ta lafa.

Ya sauke numfashi cikin gamsuwa da bayanin ta, ya dauki kofin ya kai bakin sa had'e da lumshe idanuwansa.

Sai da yasha sosai kafin ya ajiye kofin, ni xan tafi halimatu, idan kinji jikin ya tsananta kije maqota kisa yaro yaje ya Kira ni, baxan je da nisa ba yau saboda yanayin jikin naki, dan Allah karki sa wasa ko kunya ki cutar da kanki kinji.

Ta gyad'a kai tana murmushin qarfin hali, tana qoqarin tashi ta raka sa taji ya riqo ta,
Yace na yafe yau ki kwanta ki huta, xan biya ma na turo maki yakumbo ta xauna dake.

Nagode sosai Allah ya dawo da kai lafia.

Amin...

Ya shafi kanta yana fadin Allah ya miki albarka, ya barmin ke har qarshen rayuwata ina son kasancewa dake cikin farin ciki, ina matuqar son ki halimatu, ya sumbaci goshinta cikin wani yanayi.

Ta lumshe idanunta tana murmushin da ya bayyana fararen haqoran ta, suna had'a ido tayi saurin sanya tafin hannuwanta ta rufe fuskar ta cikin jin kunya, murmushi kawai yayi sanin halin ta ya tashi ya fice.

Ta bisa da kallo cikin so da qaunar kasancewa da shi a koda yaushe, kafin ta fara tuno bayan ta.

Asalin su...

A gurguje pls
Malam Ard'o shine sunan mahaifin halimatu yaya ne a gurin mahaifin Ma'awiya (mijin halimatu).

Akwai shaquwa da yarda sosai tsakanin iyayen nasu, lokacin da Halima ta isa aure aka so aurar da ita ga wani Habibu yaron hakimin garin ne, kasancewar mutanen garin sun San ba yaron kirki bane sai mahaifin ma'awiya da halimatu suka bijirewa auren wanda ba qaramin matsala yaso ya janyo masu a garin ba.

Akwai shaquwa mai tsanani tsakanin ma'awiya da Halima irin na yaya da qanwar sa wanda iyayen suka yi tunanin soyayya
ce tsakanin su wannan dalilin ya saka iyayen qudirin had'a su aure.

Tun daga lokacin da suka ji wannan labari shaquwar su ta qara tsananta, halimatu yarinyace kyakkyawa mai matuqar kunya sosai, tana da son wasa da raha, tana da haquri ba kasafai kake ganin bacin ran ta ba, tana da kau da kai akan abinda bai shafe ta ba ko acikin abokanta yam'mata sabanin ma'awiya da idan kaga dariyar sa tabbas yana tare da halimatu ne, ba wani babba bane sosai shekarunsa 25 kacal a duniya halimatu na da 17.

Bayan saka bikin su ne mahaifin halimatu ya soma rashin lafiya wanda bai jima ba Allah yayi masa cikawa dama mahafiyar ta, ta jima da rasuwa.

Kafin mutuwarsa ya dauki duka dukiyarsa ya damqawa ma'awiya da cewa ya kula masa da halimatu batare da cin amanar ta ba.

Ma'awiya ya karbi amanar da hannu biyu, duka shanu da sauran dabbobin dake gidan mafi akasarin su duk na halimatu ne, yana kula da su sosai kamar yanda ya daukarwa mahaifin ta da mahaifin sa alqawarin haka.

Tun bayan auren su musu bai taba had'a su ba, suna xaune cike da so da qaunar juna, har Allah ya kawo wannan cikin da take dauke dashi tana watan haihuwar ta.

Jin ciwon ya lafa mata ta tashi da kyar ta fito tsakar gida dai dai da shigowar ma'awiya, tayi masa kallon mamaki tana fadin
Lafia maigida ka dawo yanxu,
Naje ban sami yakumbo ba, taje birni wurin sana'ar ta shine hankalina ya kasa kwanciya da yanayin ki na dawo na qara duba ki.

Murmushi tayi tana kallonsa, tace ai na gayama ba abinda ke damuna kuma yanxu kaga shaidar hakan, dan Allah ka kwantar da hankalin ka.

Taya hankalina xai iya kwanciya bayan nasan yanayin da kike ciki.
Chapter 1 · 0% Book details