Sashe 6
Sartse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yaya Radiya tana da matu™ar sau™in kai, hakuri da kawar da kai akan abu, saSanin Yaya Rumaisa Al-jarabatu, sunan da kowa ke kiranta dashi, bata neman sauki a rayuwatar ko kaWan, rigima bata ta ba sai ta shiga ta yi kane kane, sai ka rantse ta tace. Yaya Ridwan kam, Wan kurma dinfa kenan. Babu ruwanshi da abunda ba a sashi ba, wanda aka sa shi mai sai ya yi kamar bai ji ba, sai ya yini a gidan amma bai ce da kowa ™ala ba, ko abokai ba shi da su kullum yana cikin daki, sai ya yini a daki bai fito ba idan ba massallaci ba. Ni kuma ina cikin wasu nauyin mutane da ba agane kansu, idan naso zanyi surutu sai na addabi kowa, idan kuwa banso ba buWe baki ma wahala yake mini, duk da cewa inda hakuri da kawar da kai, surutun nawa ma sai da yan gidanmu nake yi idan na ga damar, abun da ba asani ba dai bazan shiga ba, sannan kwata kwata ba na cikin nau in mutane marasa kunya, sannan duk abinda naga zai wahalal dani ina yi tattarashi gefe na watsar ko na tattara rayuwata na yi gaba. Haka ma Ra is bai da hayaniya shima ko kaWan duk cikinmu dai Yaya Rumaisa ce ta fita zakka, dan idan taso jarabarta kowa sai ya kula ta, Yaya Ridwan ne kawai ba ya kulata.
Kasancewar sunana Rawasiya yasa yan makarantar daren mu suke tsokanta, yau su ce Rawasiya, gobe Gabashiya, jibi har shami™antun sai su ce min, gaba daya na zama abar tsokana a unguwar, shi ya sa na tattara sunan na watsar na koma Nana, indai aka ce dani Rawasiya to a gidane ko yan uwa. Lokacin da na shiga FUD STAFF SCHOOL J S 1, idan yan ajinmu suka ji suna yayuna sai su yi ta tambayata me ya sa sunana bai fara daga Ra ba, amma na yayuna duka Ra, kasancewar dukkanmu muka shiga makatantar, Yaya Radiya da Rumaisa suna J s 3, Ridwan J s 2, ni kuma J s 1, Ra is ne kawai babu, sai na ce musu ni ba yar gidan ba ce. Wata rana da Yaya Rumaisa ta zo ajinnu ta ce da ni Rawasiya nan yan ajin suka Wauka Rawasiya shami™atin, amma da yake ban bada fuska ba akan sunan sai Nana yafi zama a bakin nasu. Sanda muka shiga Aji na biyu lokacin su Yaya Radiya sun shiga Siniya, a lokacin Yaya Ridwan ne kawai, yan matan makaranta tin daga yan ajinmu har na ajinsu kowacce sai ta zo ta ce dani tana son Yayana, kaf makarantar yafi kowa yawan masoya, ga halinshi na rashin son magana ya kara ja masa farin jini a makarantar. Lokacin da zan shiga Siniya ne lokacin da muka yi saukar Al-kur ani ni da Yaya Radiya, Yaya Rumaisa, Yaya Ridwan, ban da Ra is sabida mun yi masa nisa sosai a karatu mussaman na addini.
Alhaji yana da burin mu yi karatu me zurfi, amma Allah bai nufi hakan ba, domin yaya Radiya tana shiga Aji 3 na babbar sakandire, Yaya Hadi dan gidan babbar yayarsu Alhaji ya ce yana son aurenta, babu yadda Alhaji ya iya haka ya sa ya aminta, sabida bai isa ya tunkari Hajjansa da maganar yana so ta yi karatu ba, ko da wani ne a waje ya ce yana sonta bare kuma Yaya Hadi jikan da tafi so a rayuwarta.
Tabbas Hajjansu Alhaji macece mai mugun son zuciya da sabon abun duniya, an ce sanda Alhaji yana da arziki babu wanda take so sama da shi, amma tun da ya sami karayar arziki ta watsar dashi da iyalansa, ta kama wanda yake da shi, gashi ba ta wani cika son Hajiyarmu ba, har wani suna take kiranta dashi wai Fulanin tashi ko Fulanin jeji ne, ni ban wani sani ba, tun da ba cika shiga sha aninta na yi ba, domin nida Ra is ta tsanemu har ce mana take masu farar ™afa wai mune muka yi sanadiyar talaucewar Wanta, wani lokacin ma ta ce ubanmu idan tana jin tsiyarta.
Shi ya sa ma mu a famili mu ka zama ware, muna gefe sai ayi abubuwa nawa ba muje ba, wani ma bamu sani ba, wani ko mun sani ba zama bu, da idan ba muje ba Hajiya na ta kura mana daga baya kuma ta kyalemu, tunda da zuwan da rashin zuwan ba tsira zamuyi da zagi ba, har gwanda bamu je ba ma zagin a bayan idanun mu ne.
Allah Ya haWa jini Yaya Hadi Yaya Radiya tun da ita ma tana son abunta, ita ma Yaya Rumaisa ana haka saurayinta mai sunan Alhaji ya fito, ita ta turoshi ba ita ta turoshi ba Allah masani, dan da ya ce sai ta gama karatu amma rana tsaka ya sake maganar, hakan ya sa Alhaji ya amince zai aurar dasu tare da dora burinsa a kaina, ko ba komai ina da karancin shekaru a lokacin.
Ba mu dade da yin biki sauka ba aka sanya ranar aurensu duka su biyun, dan Hajja ta ce babu amfanin karatun da zasu yi. Haka ya sa aka sanya auren nasu, sai dai duk wannan balo™o™on da ta yi da aka tashi bikin babu kobo da ta bayar duk Alhaji ne da kudinsa ya yi, sai kuma yaransa da yake tare da shi Isah Nadabo har wannan lokacin, wanda ya siya maa shago a bakin titi ya cika masa shi da kaya, shine ya dauki nauyin yin kayan daki na duka su biyun.
Haka aka zo lokacin biki Alhaji da Hajiya sunyi hidima dai gwargwado, hidimar da babu wanda ya yi tunanin zasu iya irinta, dan bayan angama biki ma sai da Hajja ta kira Alhaji ta ce wai aina ya sami kudi, sai ya ce da ita yan uwan Hajiya ne suka yi, maimakon ta gode musu ko ta yaba musu sai ta hau aibatasu, wai basu dauke ta da daraja ba da bazasu kawo gudumawa wajenta ba sai dai su ba wa yarsu, abu kamar wasa sa ga Hajjan a gidanmu ta zo ta yi wa Hajiya tas, sannan kuma wai tafito da ragowar gudumawar sai dai Hajiya ta ce jiya ta haWe komai anyiwa Yaya da Radiya da Rumaisa gara an kai musu, abu kamar shafar iska sai ga Hajja a gidan Yaya Rumaisa ba ta je gidan Yaya Radiya ba sabida tasan jikanta ne zai ci komai, sa ta je gidan Yaya Rumaisa, haka ta dinga jidar kayan garar abun haushi a gaban dangin mijin Yaya Rumaisa, har da kukanta sai sune suka rarrashe ta bayan Hajjan ta tafi.
A da Alhaji baya Soyewa Hajja komai amma yau da gobe tafi karfin wasa, a hankali ya gane Hajja ba ta yi dashi dan ba zai ce ba ta kaunarsa ba tun da babu uwar da zata haifi Wa ta ce ba ta son shi, shi ya sa ya boye mata Isah Nadabo, mutumin da ya taimaka masa wanda ya rike amana ya dawo yana sakawa Alhaji da fin abinda ya yi masa, dan tsaf Hajja zata sa shi a gaba yakirashi ta kuma sa shi ya bata ma™udan kudaden da ba lallai gobe ya sake tun karar Alhaji, kuma ta dinga i™irarin tsine masa idan ya™i, a haka ma duk sati sai ta aika an amsar mata shinkafa da wake har dasu mai da maggi da kudi a shagon nasa, wani lokacin ma sai ta zo da kanta tai ta jidar indomi da madara, wani abun ma bata san shi ba kawai mugun hali ne, dan akwai lokacin da ta dauki Izel na wanke bandaki ta tafi dashi ta dauka abun sha ne ta sha, dakyar ta mi™e dan ta yi jinyar wajem wata biyu, maimakon ta yi hankali sai ta ce ita yanzu ta fara. Haka take rufe ido ta yi ta jidar kaya duk sanda tazo, akwai ma lokacin da ta fado daga kan kanta, dake shagon akewaye yake anyi gini tsakanin inda kayan suke da inda mutane zasu tsaya, sai da fridge da kayan ruwa sune daga waje, shagon yana da girma da fadi, to garin haurowa ta tsallaka ciki ne ta dawo kasa ta fadi, nan ma sai da ta yi jinya, amma dake matar nan babu Allah a ranta sai ta ci gaba da zuwa. A kullum burina shine na yi karatu mai zurfi, na zama wata ko da a iya Dutse ne, na taimaki iyayena da yan uwana, ina son ganin na yi wa Alhaji wani abu da zai ji dadinshi a rayuwa, mahaifina da mahaifiyata suna da buri akaina na ganin cewa na yi karatun boko mai zurfi, kuma ni kaina haka sabida na fahimci idan banyi karatu mai zurfi ba, babu inda zani.
Haka rayuwa take ta tafiya, yau fari gobe ba™i. Yayuna suna gidan aurensu kuma kowacce babu abinda zamu ce da Allah sai godiya, dan kowacce da ka ganta zaka san tana cikin rufin asiri, a hankali rayuwa tana gangarawa inan da burin na karatu mai zurfi, sai dai bansan me kaddara ta tsara mini ba.
09:30pm.
Zaune muke a tsakar gida ana dan taSa hira, ni da Hajiya da Ra is, ko na ce Hajiya da Ra is da ni da ido kawai nake binsu, bansan me ke damauna ba amma gaba Waya tun yamma banajin daWi, gaba Waya ji na nake wata sukuku. Yaya Ridwan kam yana can daki yana faman game, dan yanzu game ya siya da ake yi a tv da wani abu na rikewa a hannu wai shi Handle, in ji Ra is.
Alhaji ya shigo bakinsa dauke da sallama, da sauri na mi™e ina faWin.
Sannu da zuwa, babanmu.
Ya sakar mini murmushi sannan ya ce.
Yawwa.
Bayan ya zauna ne Ra is da Hajiya suka yi masa sannu da zuwa, Hajiya ta mi™e Wakko masa abinci, Ra is da Hajiya Aminan juna ne, ko da yaushe tare zaki gansu, dan Ra is ina ga ko a waje baida wasu abokan kirki, kullum suna zaune da Hajiyya hirar su ba ta ™arewa, karasa me suke cewa, yanzun ma tare suka nufi kitchen din Wauko ma Alhaji abinci.
Bayan Alhaji ya gama cin abincine ya ce.
Rawasiya ga sa™onki.