← Book details Sartse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 39

Sashe 10

Sartse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gabana ne ya faWi, maganarsu Malaika ta fito da suke cewa yafi ™arfina, a Royal family suke aure ko ya yan manya. 

Nana wannan ba matsala ba ne, ni zanyi ™o™ari da gida kema ina so ki yi ko™ari anaku gidan ki tabbatar Abbanku ya ce zai miki aure.  

Shiru na yi gaba Waya jikina ya yi sanyi, ta ina zan fara tunkarar Abba da zancen ya yi min aure? 

Kinyi shiru, wannam fa aiki ne babba muka Wauka Nana, kina sona ina sonki, kuma kowa akwai matsala a Sangarensa, naki Sangaren ba yanzu za su yi miki aure ba, nawa Sangaren ya yan masu kuWi suke su.  

Yanzu ni ta ina zan fara, wannan aikin babbane.

Na faWa kamar zanyi kuka. 

Ta ina da zan fara, look Nana idan bakya sona ne ki fito ki faWan.  

Ina sonka mana.  

Banga alama ba.  

Ya faWa tare da kaWa kai zai fice. 

Ka yi ha™uri dan Allah, zan yi musu magana Allah.

Banza ya yi ya sa kai ya fice. 

Shikenan na sake Sata masa rai.  

Na faWa tare da juyowa idanuna suka faWa cikin na Yaya Ridwan, yana tsaye yana kallona. 

Legendspen

08129553971

129*SARTSE*

-Amanar-Janafty-

*Sayyid Legendspen*

MAH/2026/001

Sadaukarwa.

RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA

(Mai Dambu) 

Shafi na bakwai

    (07)

A hankali na shiga takawa zuwa cikin gidan, yana tsaye yana kallona har na shige, kamar daga sama na ji muryarsa. 

Wane wannan?  

Shiru na yi bance ko ™ala ba, a fusace ya sake magana. 

Ba dake nake ba?  

Bakina na rawa na ce. 

Saurayina ne?  

Ya yi dariya sannan ya ce. 

Ba shine Sardauna ba? Fahad Ta ambo.  

Fahad Ta ambo.  

Na faWa kaina a ™asa. 

Nana.  

Ya kira sunana amma yanzu muryarshi a hankali, na Wago kai na kalleshi. 

Zo nan?  

Ya faWa yana nuna kusa dashi, kamar mai ciwon jiki haka na taka na je. 

Kinsan waye shi? Su Win masu kuWi ne sosai kuma kinsan duk irin waWan nan masu kuWin ba wani kirki ba ne dasu, kaWan ne masu mutunci.  

Nasani.  

Na faWa a hankali, ya kalleni sannan ya ce. 

Nana ki sani kefa macece, rayuwarki tana da daraja ga iyayenki da yan uwanki, ba wai dan baku da kuWi yana nufin ku Win baku da daraja ba, nasani muna cikin wani zamani wanda duk mai wani abu shine mutum, amma duk da haka kada ka ta Sa bari darajarka ta ragu ko ki nuna baki da ita, karki ta Sa sa wa ranki alfarma zai yi miki ko yake yi miki, ke macece kuma mai daraja. Dan haka ka da nasake ganin abinda ya faru yanzu ya faru.

Yana faWin haka ya shige Waki, ya barni ina faman tunani, me ya gani? Me yake magana akai?. 

Abu kamar wasa Fahad shiru, sati Waya sati biyu, idan na kirashi a wayar Hajiya ba ya Wagawa, ta Malaika kam daman ya ja min kunne ya ce a wayar Hajiya kawai ya lamunce na kirashi. 

Sai da aka yi sati uku baya Waga wayata kuma ba ya kirana, duk na bi na damu kuma na yi al™warin zanyi masa biyayya akan komai ya sani, tun da harshi ya Wauki jahadin yi wa iyayensa magana akan yana son auren wacca ba ta kai ba, ni to me ya sa bazanyi ba. 

Wata ranar laraba da yamma ina zaune a Waki na Wauki wayar Hajiya na sake gwada lambarsa, ina kira ya katse ya kirani. Na ji wani mugun daWi a raina, ina Wagawa ya ce da ni. 

Ina bayan gidanku.  

Ba shiri na mi™i na zura hijabi na yi waje, Hajiya na tsakar gida tana kaWa miya na ce da ita. 

Zani gidansu Amina.  

Da yamman nan?  

Eyh.

Ina faWin haka na fice zuwa bayan layi, yana jingine jikin farar motarsa, yana sanye da light blue Win shadda, ina ganin fuskarsa na ji wani sanyi ya mamaye zuciyata, wata irin nutsuwa ta shigeni, duk wata fargabar da nake ji ta tafi. 

Yanzu ma kin daina damuwa idan ban nemeki ba.

Ya faWa yana ™are min kallo. 

Waya faWa ma, wallahi na damu sosai da sosai.

Ban yarda ba, gashinan har wata ™iba kika yi.

˜iba kuma?  

Eyh, ya maganar mu? Me kika yanke?  

Zanyi magana da Alhaji ta yadda zai fahimta.  

Good girl.  

Ya faWa yana buWe motarsa, ya Wauko leda ya mi™amin. Hannu nasa na amsa sannan na ce. 

Na mene?  

Naki ne, na yi magana da Daddy ya amince amma Mom ce abun sai addu a.  

Wani irin tausayinsa na ji ya ratsani, nasan irin wannan abun tabbas da wahala. 

Allah Ya sa ta amince itama.  

Nana na sha wahala akan lamarinki, sai na ji kamar zan ha™ura sai na ji bazan iya ba, amma ke  babu ruwanki Sata min rai kawai kike, maimakon ki nuna sakayyar soyayya amma naga babu abinda kike so sai Sacin raina.  

A tsorace na ce. 

Ya zaayi naso Sacin ranka?  

Gashi ina gani.  

Da irin waWannan abubuwan Fahad ya dinga amfani yana cusa min tausayinsa da wata iriyar soyayyarsa mai girma, wanda a kullum gani nake yana shan wahala a kaina, sai da fa na kasa tarar Alhaji ko Hajiya da maganar, duk son da nakewa Fahad bana jin ya kai tausayin da nake yi wa Alhaji ba. 

Shi kuma a kullum faWa min irin tashin hankali da suke yi da mahaifiyarsa da yan uwansa a kaina, har cewa ya yi dani ya daina shiga sabgar sister Winshi, a ranar na yanke shawarar tunkarar Alhaji akan maganar. 

09:15pm. 

Alhaji na zaune a Wakinsa ya bayan ya yi wanka yana sauraren radio na shigo cikin Wakin. 

Barka da hutawa Alhaji.  

Nana barka dai, akwai abinda kike bu™ata ne? Ko kin shirya sanar dani damuwar da na ce tana damunki kike Soyewa.

GyaWa kai na yi sannan na fara magana cikin rawar baki. 

Alhaji daman.. daman wani ne..  

Alhaji irin mutanen nan ne masu sauraron mutane, zai iya kwashe awa guda yana saurarenka ba zai katse ka ba, sannan kuma ba zai yanke ma hukuncin ba har sai ka kammala. 

Wani ne.. tun da daWewa ya ce wai yana so ya turo iyayensa wajenka.  

Murmushi Alhaji ya yi sannan ya ce. 

Su yi mini me?  

Wai yana sona zai aureni, kuma na faWa masa kai bazaka aurar dani ba sai na yi karatu me zurfi na zama maaikaciya, ya ce wai ya ji ya gani zai barni na yi karatu duk wani waje da nake so.  

Shi Win waye?  

Sunansa Fahad Ta ambo.  

Wani murmushi Alhaji ya ™arayi sannan ya ce. 

To ke me kika yanke, auren ko karatu Nana?  

Na yi shiru na rasa me zance. Allah Ya sani ina son Fahad ina tausayin halin da yake ciki a kaina, kuma bana son rasa shi, sannan kuma ina son cika burin mahaifina, amma kuma abu guda Waya da nake gani shine auren tun da Fahad zai barni na ci gaba da karatuna, domin a maganar mu ta ™arshe da shi ya ce da ni. 

Idan kika ga zai™i sai ki faWa masa ni zan barki ki ci gaba da karatun naki.  

Nana  

Alhaji ya kira suna na. 

Na baki kwana biyu kije ki yi shawara, duk hukuncin da kika yanke zan amsa tare da nawa sharaWin akai.  

Na gode Alhaji.  

Na faWa tare da tashi na fice, ko da na shiga Waki na kwanta abubuwa suka yi ta faWomin a rai, na sa™a wancan na kwance wancan. 

Kalli su Yaya Radiya, da Rumaisa sunyi aure kuma suna cikin rufin asiri, ga Rumaisa nan ma ta koma makaranta tana karantar harkar lafiya, ke me kike jira zaki zauna wani zama idan kika gama karatun girma ya kama ki tsaf sai ki rasa mijin auren.  

Zancen zucin da na wayi gari da shi kenan, haka na yi ta abubuwa komai sukuku, dan ma yanzu ba makaranta muke zuwa ba WAEC zamu fara nan da sati biyu, shi ya sa bamu cika wani zuwa ba. Bayan Alhaji ya fita na shirya na lallaSa Hajiya akan ina son zuwa gidan Yaya Rumaisa da Yaya Radiya duka a rana Waya. 

Wai me zakije ki yi musu duka su biyun a rana Waya?

Hajiya ta tambaya cike da mamaki, ganin tana neman hanane ya sa na ce. 

Alhaji ne fa ya ce na je dukkansu mu yi magana dasu.  

KuWi ta Wauka ta bani tare da cewa. 

Kuma karki yi yamma.  

Ta gidan Yaya Rumaisa na fara, tun da shi yafi nisa, akan gidan Yaya Radiya. Shi ya sa na fara zuwa gidan Yaya Rumaisa, yanayin da na sameta ya yi matu™ar burgeni, ta yi ™iba abunta duk da karatun da take yi ga yaranta kyawawa guda biyu Afra da Affan.

Bayan mun gaisa ne na kalleta sannan na ce. 

Yaya shawara nazo nema wajenki.  

Ina saurarenki.  

Sai da na Wan yi jim sannan na ce. 

Nasami Miji kuma dagaske aure na yake so ya yi, sannan ya yi min al™warin bari na na ci gaba da karatu da nuna masa Alhaji yana son karatun.  

Rawasiya, kinyi magana da Alhaji.  

Na yi, shi ya ce na yi shawara.  

Yaya Rumaisa ta gyara zama, ta kalli ni cikin idanu tare da kamo hannuna, sannan ta numfasa ta fara magana cike da nutsuwa. 

Nana zan gaya miki abubuwan da suke cikin aure na daWi da rashin daWi, idan na faWa miki sai ki yi tunani da kanki, ki ga wanne kika zaSa.  

Tom Yaya.  

Nana, aure ba kawai canza gida ba ne ko samun wanda zai ri™a lura da ke. Aure ibada ne, kuma makaranta ce da ba a yaye Walibi har sai mutuwa ta raba. Idan kika ga mace a cikin jin daWin gidam aure, to dole akwai matakan da ta bi waWanda suka kai ta ga wannan matsayin jindaWin. Nana abinda zaki fara sani a farkom farko shine, mene ne Aure kuma yaya Rayuwarsa take?
Chapter 10 · 0% Book details