← Book details Sartse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 39

Sashe 39

Sartse Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Cike da ™yama, ya janye ™afarsa da ™arfi daga kankamewar da na yi masa, wanda hakan ya sanya na kusan kifa fuskata da ™asa. Ya ja wani uban tsaki mai tsayi, ya dube ni da waWancan idanun nasa da suka riga suka zama tamkar na dabba mai cutarwa, sannan ya ce.

"Ke dallah malama, sake ni! Ubanki ma ai kin rasa shi kuma kin rayu, balle kuma ni da kika ganni da ha™oranki talatin da uku! Nana, na gaji da zama da ke... zama marar amfani da riba. Ke ba haihuwa za ki iya yi ba, ba za ki iya samar mini da ya ya ba, kuma ke ba karatu gare ki ba balle a ce za ki zama wata abar alfahari a nan gaba!"

Na daskare a wurin. Idanuna suka ™afe a kan kafaWarsa, wani irin masifaffen sanyi mai daskarar da jini ya ratsa daukacin gangar jikina. Nan take, wani irin sauti mai amo ˜uuuuuuu...! ya shiga ruri a cikin kunnuwana, yana toshe mini kowane sashi na jiyya.

Zuciyata ta fara wani irin juyi na takaici da nadama. Sardauna... Sardaunan da ya zama silar ajiye karatuna tun bayan gama Aji na Farko a jami'a, domin kawai ya ce kishina yake yi ba ya son maza su kalle ni, yau shi ne yake tsaye a gabana yana yi mini gorin rashin karatu? A daidai lokacin da abokan karatuna suke gab da shiga shekarar ™arshe ta kammalawa, yau ga ni nan daskare a ™asa, ina karSar kaskanci a matsayin jahila marar amfani.

"Hahahaha...! Ana bikin duniya, akan yi na ™iyama! Ga ki nan don Allah, shashasha da ba ta san darajar kanta ba. Miji zai sake ki, amma kina wani dur™usawa a ™asa kina masa magiya da kuka! Gaskiya Nana, ke jahila ce ta ™arshe, tabbas!"

Muryar Bilkisu, mai cike da dafin da ya fi na kowane maciji Sarna, ita ta dawo da ni daga wancan zancen zucin da nake yi.

Ina nan a dur™ushe, amma Wakin gaba Waya jiri yake mini, ganina yana neman gaba Waya ya canza launi ya koma ba™i. Hawaye masu zafi suka wanke mini fuska, amma saboda tsananin son Sardauna da ya riga ya zama jinin jikina, ban ji kunya ko tsoron sake kaskantar da kaina ba. Da ™yar, cikin rawar jiki da karkarwa, na sake rarrafawa a kan gwiwoyina zuwa daidai inda yake tsaye, na sake sa hannuna duka biyu na ™an™ame ™afarsa, muryata tana fita kaWan kaWan.

"Don Allah... don Allah Sardauna karka sake ni! Zan zauna da kai a kowane yanayi... ko da a haka ne. Ba zan nemi abinci ba, ba zan nemi abin sha ba, ba zan sake neman suttura ba! Ko magana ba zan rinka yi maka ba, ba zan sake takura maka ka kalle ni a matsayin mace ba... don Allah muddin dai ina cikin gidan nan da sunanka, zan jure kowane irin wula™anci...!"

Ya kalle ni na tsawon da™i™a guda, fuskar nan tasa babu alamar imani ko Wigon tausayi, ya ce.

"Nana, ba zan iya ci gaba da zama da ke a haka ba. Daman ™uruciyarki na aura, kuma a yanzu gashi ta riga ta tafi, kin rage daWi. Nana, ba ke nake so ba... ™uruciyarki nake so, kuma da ita nake son na rayu, ba da ke ba, Nana! Zan dai bar ki ki ci gaba da zama a Sangaren can na gidan, ba tare da rashin abinci, abin sha, ko suttura ba. Amma kuma babu wanda zai san na sake ki a duniyar nan... har abada!"

Na yi shiru, tabbas ina son Sardauna, so mai girma da zafi, son da ya riga ya zama jinin jikina. Idan har zan zauna a gidan nan ™ar™ashin ikonsa, to wallahi zan zauna, matu™ar dai ina numfashi a inuwar gidansa.

Saki nawa za a rubuta?

Muryar Bilkisu ta katse mini tunani, tana tambayarsa cikin isa.

Šaya.

Šaya kuma?

Ta tambaya a gatsine, cike da rashin gamsuwa. Shi kuma ya dube ta, ya ba ta amsa a tsawace tamkar zai rufeta da duka.

Eyh Waya! Ki rubuta: Ni Fahad Ta ambo (Sardauna) na saki Nana saki Waya.

Ba musu ta Wauki biron ta rubuta. Ni kam wani irin ba™in abu mai Waci na ji ya tsaya mini a wuya, ya toshe mini ™ofofin numfashi. Saki mafi ™as™anci da walakanci a rayuwar mace, shi ne kishiyarki ta rubuta miki saki da hannunta! Ni Nana na shiga uku! Rayuwata ta gama lalacewa!

Nuna mata ta gani!

Sardauna ya ba ta umarni cikin ko-in-kula.

Ta sa takardar daidai saitin fuskata, ta nuna mini rubutun da ya wargaza mini dukkan sauran darajata. Sannan ya kalli takardar, ya ce.

To yaga, saboda ba na so kowa ya gani.

Ba musu Bilkisu ta cire takardar, ta yaga ta guntu-guntu ta watso min a fuskata tamkar almajira.

A tashi a tafi!

Ba shiri na yun™ura zan mi™e, sai dai kafin gwiwoyina su Wauki nauyin jikina, na ji Wakin gaba Waya ya kife da ni. Wani duhu mai nauyi ya lullube idanuna, na zube a kasa sumamma...

********

Šum... Wum... Wum...!

Haka nake jin kaina yana mini wani irin duka kamar an buga guduma. A hankali na fara

˜o™arin buWe idona, amma wani zazzafan raWaWi ya sara mini a tsakiyar kaina ya sanya na sake rufe idon da sauri, ina dafe gashin kaina. Muryoyin mutane na jiyo a kaina sama sama.

Dr. Na ima, zan bar wannan case Win a hannunki don Allah. Referral ne daga wajen wani abokina, to ba ya ™asar a yanzu, ki kula da ita sosai.

Ni fuskar patient Win tamkar na sani, amma bari ta tashi tukunna.

Sai da na kwashe kusan mintuna talatin ina nishi, sannan na iya buWe idona gaba Waya. A hankali na sauke su a kan kyakkyawar fuskar Dr. Na ima Da™ayyawa, wadda ke sanye da farar rigar likitoci tana duba wani file.

Mrs. Ta ambo, is that you?

Na gyaWa mata kai a hankali, hawaye guda Waya mai zafi ya fito daga gefen idona. Ta taso kusa da ni, ta zauna a gefen gadon asibitin.

Duk abin da nake fada miki a baya, ba kya ji ko? Ki godewa Allah da yasa yanzu BP Win ya dawo daidai, amma kina da babbar damuwa a ranki.

Na girgiza kaina na kasa cewa uffan, bakina ya yi mini nauyi tamkar an daure shi. Ta zuba mini idanu na tsawon dakika, sai can kuma ta ce.

Kin kyauta abin da kika yi wa mahaifarki? Na shan abubuwan da za su hana ki daukar ciki?

"Ban gane abin da kika fada ba fa..."

Na fada cikin kiWima, kaina ya sake Waukar wani irin sabon jiri. Ji nake yi kamar akan garwashin wuta nake kwance ba a kan gadon asibiti ba.

"Abin da kika shuka da hannunki ne ya dawo miki yanzu.

Ta faWa tana yi mini wani irin kallo na zargi da takaici.

"Wallahi ban gane abin da kike nufi ba! Abin da na sani, rayuwata ban taSa shan wani abu da zai hana ni Waukar ciki ba! Hasali ma akwai wani likita da nake zuwa wajensa tun can baya, kullum yana duba ni yana ce mini mahaifata ta fara ™wari, kuma bai taSa yi mini irin wannan zancen ba!"

"Uhm... shi wane ne wannan likitan?"

"Sunansa Dakta Šan Adala... kuma abokin miji na ne."

Fuskar Dr. Na ima ta canza gaba daya, ta matso da fuskarta tana kalleni, "Kina nufin da kanki ba ki taSa shan wani abu ba da zai hana ki Waukar ciki ba, wanda gashi yanzu ya haifar miki da mummunar lalacewar mahaifa? Kuma wannan lalacewar tuntuni ta faru, ba yanzu ba."

"Wallahi-Allah ban taSa sha ba! Ban taSa sani ba!"

Na fada ina kuka, kaina yana wani irin juya mini, jiri yana Wibana duk da cewa a zaune nake.

Hannuna ta kama ta dam™e shi da ™arfi, sannan ta ce.

Mrs. Ta ambo, ki nutsu... ki saurare ni da kyau."

Kallonta na yi, babbar mace wadda na san tabbas ta haife ni, ta haife har Yayatama.

"To..."

Na fada ina saurarenta da dukkan guntuwar nutsuwar da ke tare da ni.

"Mijinki... ya kuke da shi? Ina nufin yanayin zamantakewar aurenku na cikin gida?"

Sai da na goge hawayen idona da gefen rigata sannan na ce.

Komai daidai yake... yana nuna mini soyayya ta daban."

"Bai taSa nuna miki bacin rai ko damuwa a kan rashin haihuwa ba?"

"Eyh... bai taSa ba. Shi da abokinsa Dakta Šan Adala ma sune kusan kullum suke kwantar mini da hankali, suke ce mini lokaci ne bai yi ba. Sai dai daga baya-bayan nan ne ya fara nuna damuwa a fili, har abin ya kai shi ga ™ara aure."

"Hhmm... auren soyayya kuka yi ko na haWin gida?"

Ta tambaya tana girgiza kai. Sai da na kalleta da kyau sannan na ce.

Na soyayya ne."

"To akwai babbar matsala gaskiya! Tabbas, ko da saninki ko akasin haka, amma an daWe ana baki kwayar da ke hana Waukar ciki, kuma da alamu kin daWe kina amfani da ita a asirce har aka kai ga wannan matakin na cewa mahaifarki ta mutu!"

Wani muguwan shock ne ya daki zuciyata...! Dakta Šan Adala? Magungunan da yake ba ni yana cewa na "Kwarin Mahaifa" ne? Sardauna ne ke karbo mini?

Kafin na gama hada wannan mummunan lissafin a kwakwalwata, aka buWe ™ofar Wakin asibitin Sardauna ya shigo, fuskarsa Wauke da wani irin murmushi. A hankali ya tako cikin Wakin tamkar babu abin da ya faru. Dr. Na ima na ganinsa ta mi™e tsaye, ta dube shi cikin Sacin rai ta ce.

Idan ka gama da ita, meet me in my office.

Okay, ya amsa mata cikin ko-in-kula, ita kuma ta fice ta ja musu kofar.

Šakin ya rage daga ni sai shi. Ya tsaya daidai saitin gadon, ya zuba mini idanunsa da na daWe ina bai wa amana.

Nana... kallon me kike mini?

Wata irin azabbariyar tsana, mai Waci da zafi, ita na ji ta dirga ta mamaye kowane sashi na zuciyata a lokaci guda. Tsanarsa ta daki jinin jikina.

Ya duka daidai fuskata, ya rage murya yadda ni kaWai zan ji, ya ce.

Nana, kin sami labarin abin da na yi wa mahaifarki ko? To ba iya wannan ba... ki sa rai da shirin ganin abubuwa da yawa nan gaba Nana, waWanda ma ba lallai kanki da rayuwarki su iya daukansu ba!

KARSHE EN LITTTAFI NA FARKO

END OF BOOK ONE.

Jama a wannan bakomai ba ne illa shimfiWa, littafi na Waya ya shimfiWa mana hanyar da zamu kwarara doguwar tafiya. Ga dai Sardauna ya saki Nana, shin zata zauna a gidan ko tafiya zatayi? Ga kuma Turaki a gefe. Ku hanzarta ku biya kuWinku ku karanta, na tabbatar muku babu nadama a cikin wannan tafiyar.

*Littafin Sartse na kuWi ne 700 a whatsapp ake posting, ku tura kuWin karatu ta wannan acc Win 8104743474 opay Hafsat muhammad lawan, shaidar biya ko tuntuSa ta wannan lambar.*

08129553971
Chapter 39 · 0% Book details