Sashe 4
Sartse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kicin na shiga na zuba mana abinci, na kawo mana falo jallop Win taliya da ta ji naman kaji za™wa za™wa, haka mu ka zauna muka ci, muna ci muna hira ko ba komai na ji matu™ar daWin zuwanta.
Bansan cewar ina zama kaWaici ba sai da tazo, bansan cewa zaman da nake ni kaWai ba, a ™untace nake ba sai da ta zo.
Muna tsaka da cin abincin aka yi sallar la'asar, hakam yasa muka gaggauta muka ci mu ka yi sallah, bayan mun idar ne Fauziyya ta ce.
"Gidanki ya yi kyau sosai, arzi™i da wadata faca-faca, sai dai ke din duk kina zaune babu wani kuzari kamar ba matar da take auren wanda take so ba?."
Murmushi na yi mata sanan na ce.
"Wanda nake so sama da komai ma a rayuwata, Fauziyya kinsan yanayin rayuwar auren, dole fa mace ta yi sanyi duk rawar jiki da kanta."
"Hakane kuma wallahi, to yanzu ya maganar wannan?"
Ta faWa tana nunan cikinta da ya tasa, na yi dariya sannan na ce.
"Yana hanya."
"Kun fa kawo shekara biyu da aure ko?"
Na gyaWa kai.
"Ikon Allah, kuma bai fara miki magana akai ba?"
"Bai fara ba gsky, ai yansan komai lokaci ne."
"Da gaskiyyarku shi ya sa fa auren mai ilimi wayayye yake da daWi, yanzu da irin mazajenmu timawan ™auye ne, ai da yanzu andame ki da magana, ko shi bai yi ba 'yan uwansa sai sunyi."
A raina na ce. "Gaskiyya dai kam." Dan ko da wasa Sardauna bai taSa yi mini maganar ciko ko haihuwa ba, ko zancen yara ma.
"Kinga har hudu da kwara, bara nazo na huce."
Fauziyya ta faWa tana mi™ewa, nima na mi™i mu ka nufi waje na rakata, ina dawo wa hankali na ya yi kan gugar Sardauna, ba shiri na shiga Wakin na dumbuzo kayan wajen Set goma na fito falo na jona dutsen gugar bayan na shimfiWa darduma na zauna na fara gugar.
Kusan awa Waya da fara gugar ya shigo cikin gidan, haka kwai na ji gabana yana faWuwa, duba da ko cikakken set bakwai bam goge masa ba, amma bayana ya ™age, gashi ban Wora masa girki ba. Jikina na rawa na kashe dutsen na mi™i na shiga kitchen.
Dame zanji kunna wuta? Ko tunanin abinda zan dafa masa? Ga kayansa da na bari a falo.
Ina jin ya shigo falon na fito da sauri tare da faWin.
"Barka da dawowa."
Wani mugun kallo na ga ya watsamin, mai Wauke da harara ya shige Wakinsa. Dum! Daram! Haka na ji gabana ya buga. A fili na furta.
"Innullahi wainna illahir raji'un."
Na nufi Wakim da ya shiga, yana zaune gefen gado ya haWe rai, fuskar kamar bai taSa murmushi ba.
"Sannu da zuwa dan Allah."
Na faWa bakina yana karkarwa.
"Mitchew."
Ya ja tsaki yana ™o™arin cire takalminsa, da sauri na ™araso na tsugunna zan kama takalmin ina faWin.
"Kawo na cire ma, wallahi kaina yake ciwo na kwanta, sai wajen huWu na tashi."
Wani kallon ya ™ara watsamin, sannan ya fara cire takalminsa, na kai hannu zan cire masa ya janye ™afarsa tare da ta™emim Wan yatsa. Na ™walla uwar ™ara tare da ri™e hannun da yake mini wani irin zugi kamar na sakawa ciwo gishiri. Yatsun da basu gama warkewa daga ™onuwar jiya ba, gashi sun sha taku.
Mi™ewa na ga ya yi ya shige ban Waki abunsa, ya buga ™ofar hakan ya ™ara tabbatar mini da cewa yana cikim fushi mai tsanani.
"Wayyo Allahna."
Na faWa idanuna na zubar da hawayen da bana raWaWin da hannuna yake ba, na raWaWin fushin da mijina yake yi dani.
"Me ya sa na kasance haka? Me ya sa na kasance sakarar da batasan abinda take ba? Me ya sa na kasance butulu mai manta alheri? Mutumin da yake sona, amma na zaSi kullum na Sata masa rai? Tir dani! Tirr da halayena."
Abinda nake faWa a raina kenan, wani Sari daga zuciyata da yake matu™ar ™aunar Sardauna ya ce dani.
"Maza ki ™ara Sata masa rai da baza kije ki yi masa girki ba."
Kamar mahaukaciya sabuwar kamu haka na mi™e na fice zuwa kicin, idanuna na zubar da hawaye na fara ™o™arin kunna wuta, haya™i ya turni™e kicin Win, amma banaji bana gani.
Legendspen.
*SARTSE*
-Amanar-Janafty-
*Sayyid Legendspen*
MAH/2026/001
Sadaukarwa.
RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA
(Mai Dambu)
Shafi na uku
(03)
A gurguje cikin ™asa da minti ashirin na haWa cus-cus da mayar ganye, wacca sai da na kwashe tsawo minti na goma ina tunanin mai zan dafa, haka nake, a ko yaushe burina na ga na dafawa Sardauna abu na daban.
Albarkacin miyar ganyen da nagani a firiza ya gajarta mun tunanin da nake yi. Fuskarsa ka Wai na kalla na ji gabana ya faWi har na kusa yin tuntuSe. Ajiye masa plast Win abincin na yi akan dinning sannan na shiga Wakinsa na buWe ™aramin firinji dake Wakin na Wakko ruwan sanyi na fito dashi, daman anan kawai ake samun ruwan sanyi sai kuma firiza ya ce ita firiza sabida kar kaji kifi ko abinci ya lalace baya son asara, shi kuma na Wakinsa ™arami ne ba zai ja wuta ba.
Ko da na fito falon yana zaune kan dinning din ya fara zuba abincin, na ajiye masa ruwan da faWin.
"Kawo na zuba..."
Ya kuwa gallamin uwar harara, ba shiri na cika mai cikolin na yi baya, da idonsa ya kalli kayan da nake gogewa sannam ya Wauke kai.
Ba shiri na matsa daga wajen na dawo kan kayan na hau gogewa jikina yana Sari haka nake gugar.
Ina nan zaune ya gama cin abincin ya tashi ya shige Waki, ba shi ya fito ba sai da aka yi sallar isha, yana tafiya massallaci na kashe dutsen na tashi na Waura alwala na yi magariba na yi isha. Sannan na kwashe kayan da na goge na shiga Wakin na sanya su a sif, na sake Webu ragowar na dawo falon.
Sai da na yi nisa a gugar wajen ™arfe goma na dare sannan ya shigo, bai kalleni bare na sa ran zai mini magana ya huce Waki, haka nai ta guga ta har wajen ™arfe sha biyu da rabi na dare sannan na kamalla. Na Wauki kayan zan kai su Wakin sai jin ™ofa na yi a kulle, wani irin abu ya tsaya mini a raina, tabbas nasan na kai mijina bango har ya iya kullen ™ofa, tabbas ban kyauta ba, ban kyautawa kaina ba. Na daWe a falon sai wajen Waya sannan na shiga Wakina na kwanta, sai dai baccin da na yi ya kasance marar daWi kwata kwata.
A tsakanin karfe Waya zuwa biyar da rabi na dare, na farka ya kai sau shida.
Yau kam tun asuba na shiga kicin, na hau haWa masa abincim safe, cikin sa'a na kammala komai kafin ™arfe bakwai. Ina tsaka da jera masa dinning Win ya fito cikin shirinsa, kallo Waya ya yi min ya Wauke kai ya nufi ™ofa zai fita.
"Baka karya ba."
"Bazan karya ba, ai bakya sona Nana, kin gaji da yi mini biyayya, kin daina jin maganata."
Ya faWa yana tsareni da kaifaffun idanunsa, jikina yana Sari na fara cewa.
"Wallahi a'a ba haka ba ne."
"To ya ne? Har ™arya fa kika yi mini jiya, wai bacci kikayi, bayan ™awayen da na hanaki mu'amala dasu ne suka zo suka zuga ki. Nana dan ina sonki bazan juri abinda kike mini ba, kina ™askantar dani, kina nuna banda daraja banda mutunci. Nana a kaf faWin duniyar nan ko iyayen da suka haifeki basu kaini sonki ba, Nana kinsani, ina sonki, ina kyautata miki, ina baki duk wani ha™™inki, amma Nana me kike sakamini dashi? Mene abu Waya?"
Na yi shiru, gaba Waya jikina ya yi wani irin sanyi, wani sabon tausayin mijina ya lulluSe ni, a hankali na fara magana, idona cike da hawaye.
"Ka yi hakuri dan girman Allah, wallahi bazan sake ba, sai da na ce mata kar ta zo amma ta™i."
Sai yanzu na fara mamakin kaina, yadda aka yi na zama ma™aryaciya lokaci Waya, duk dan na faranta masa.
"To bance duka kike goge lambobi su ba?."
"Na goge fa, ai kana ganin wayar babu lambar kowa sai taka da ta 'yan gida, to idan suka kirani ne nake ganesu."
"Bani wayar."
Ya faWa yana takawo cikin falon, fuskarsa a haWe kamar zai dake ni, hannuna har karkarwa suke yayin da nake kokarin mika masa wayar, ya sa hannu ya fusgeta da ™arfinsa. Daidai lokacin sa™o ya shigo wayar ji kake. 'Wilim.' ™arar shigowarsa.
"Waya turu miki sa™o?."
Ya tambaye ni, cikin muryar kuka na ce.
"Nima bansani ba."
Wayar ya danna ya bude sa™on, ya ™ura ma wayar ido yana motsa baki, idanunsa na yawo akan sikirin Win wayar, wanda yake daidai da ™a™™arfan bugun da zuciyata ke yi.
"Mitcheww."
ya ja tsaki, ya danna maddanin gogewa ya goge sa™on.
"Ina so ki ciro mini layin nan yanzun nan."
Ya faWa yana mi™omini wayar, da rawar jiki na amsa na fara ™o™arin cire layin, yana kallona da idanunsa har na cire na mi™a masa, ya karSa ya sa a aljihu, kana ya zauna akan kujera, ya runtse idanunsa kusan mintina biyu sannan ya buWe su, ni dai ina tsugunne ina kallonsa, ™aunarsa da tausayinsa suna cika mini zuciya, ina son mijina,ina tausayinsa.
"Hon! Matso ki zauna."
Sassanayar muryarsa da tafi ruwan ™an™ara sanyi ta doki kunnunwana, ba shiri na mi™i na matso kusa da shi na zauna, ya sa hannuwansa ya kama nawa, a hankali ya fara matsa su.
"Nana, kin san me ya sa nake yin haka?"
Ya tambaya, muryarsa tana fitowa da wani irin sanyi mai ratsa zuciya. Ya kura mini ido, idanunsa da suke daidai da kwayar idona suka sanya na ji wani irin mugun tausayinsa.
"Domin ba na son kowa ya shiga tsakaninmu. Ke tawa ce ni kaWai, Nana. Idan kika bari waWancan kawayen naki da 'yan uwanki suka ci gaba da shigo miki da ra'ayoyinsu, za su lalata mana wannan kyakkyawar rayuwar da muke yi."
Na gyaWa kai, hawaye na wanke fuskata na ce.
"Na gane Hon. Nagode da kake kare ni, nagode da kake nuna mini gaskiya."