← Book details Sartse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 39

Sashe 34

Sartse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mijina ba ya son fita, indai ba wani ™wa™waran uziri ba.  

Hhm, Me yaja miki Low Bp.  

Tun rasuwar Alhaji ne.  

Anty Adiza wayayyiya ce, tasan ta yadda zata kama mutum ta dole, wasu irin tambayoyi ta dinga watsomin har sai da na yi suSul da baka na ce da ita Sardauna ne zai ™ara aure, murmushi ta yi sannan ta ce. 

Nana kenan, bayan nan fa.

Babu komai Allah.  

Matsowa ta yi kusa dani ta kama hannu, ta fara magana cikim tausasawa.

Nana karki kasance sokuwa, karki kasance shashasha! Daga lokacin da miji ya fuskanci kin shashantar da kanki a kansa, zai mai dake marar amfani, zai mai da ke tsanin da zai taka ya hau kowane mataki, Nana ba a ce babu soyayya ba, ba a ce soyayya ga miji ™arya ba ce, amma Nana ki mutunta kanki, muma duka Nana ai muna son mazajenmu, so ba ™arami ba Nana, amma muna mutunta kanmu ta yadda suma zasu mutantamu, Nana babu mijin da ya isa ya zo sama da yan uwa ko iyaye, kowa matsayinsa daban. Ki farka daga wannan baccin da kike Nana, kisan idan kika tunkara karki zauna ki lalace a haka.  

Shikenan Anty Adiza, na gode sosai kuma in sha Allah zan gyara.  

Shikenan Nana Allah Ya sa gyara mana.  

Amin amin .  

Kalamanta duk sun shige ne ba ™arya, kuma a iya hasashen da na yi gaskiyya ta faWa min, amma ni har yanzu banga mafarkin da nake yi akan Sardauna ba, matsala Waya ce rashin zuwa gida kuma in sha Allah zan dinga zuwa.

Bata jira Sardauna ya dawo ba ta tafi sabida tabar yaronta a wajen masu aiki, ba ta daWe ta tafiya ba na sake gwada lambar Bilkisu amma ba ta tafiya. 

Allah Ka sa wannan baiwar taka tana lafiya.  

Na faWa a raina tare da ™udiri niyar idan Sardauna ya dawo zan tambayeshi, sannan na ce idan ya je ya haWani da ita.  Ba Sardauna ya shigo ba sai bayan magariba, shima a gurguje ya shigo ya shirya ya fita ko abinci bai ci ba, sai bayan goma ya sake dawowa, hannayen shi ri™e da leda da alama shopping ya yi. 

Nana ga wannan, Bilkisu ce ta ce akawo miki.  

KarSa na yi sannan na ce. 

An gode.  

Munje shopping ne, kinsan an sanya ranar aurenmu wata Waya, shine muka je siyayya.  

Kamar ansoka mini mashi haka na ji shigar maganarsa, amma sai na kauda kai tare da cewa. 

Allah Ya nuna mana.  

Amin Nana.  

Mi™ewa na yi da niyar shiga Waki na kwanta, Sardauna yasa hannu ya jawo ni kusa da shi, ya ri™e hannayena duka biyun da ™arfi, ri™on da ya yi min ya haifar min da nutsuwar dole, shi kuma ya zuba min idanuwansa waWanda suka riga canza launi zuwa yanayin tausayi da damuwa, sannan ya fara magana cikin muryar sa mai amo ta daWi. 

"Nana... kin san irin son da nake miki, kuma kin san cewa wannan lamarin ba zaSina ba ne, kaddara ce ta iyaye. Amma abin da ya fi komai burgeni ya haifar min da nutsuwar da ta bani damar sauke ha™™in da nake shirin Wauka shi ne yadda kika nuna min tsantsar girma da biyayya kika amince da wannan auren. Nana, wannan babban Aikin Lada ne kika Wauko wa kanki."

Ya gyara zama, ya ™ara matse hannuna.

"Nana, yanzu an riga da an sa rana, komai ya fara Waukan harama, kuma hausawa sunce aski idan yazo ™arshe yafi ™ai™ayi. Ina so ki sani, ShaiWan ba zai bar ki ba. Zai rin™a hura miki wutar kishi a zuciya don ya rusa miki ladan da kika fara nema. Kar ki bari ShaiWan ya yi nasara a kanki. Ki duba yadda kika jure har zuwa yanzu, don Allah Nana ki daure ki ™arasa wannan jihadin da kika fara."

Ya Wanyi shiru kamar mai tunani, sannan ya ci gaba.

"Idan aka kawo matar nan, ina so ki nuna mata cewa ke mace ce ta gari, uwar gida mai daraja. Ina so ki sanya ta ta yi miki biyayya kamar yadda kike mini, amma ta hanyar nuna mata ke ce babba. Ki zama uwa a gare ta, ki koya mata yadda ake girmama ni. Idan kika yi hakan, Nana, kin gama mallakar zuciyata har abada, kuma kin tabbatar wa duniya cewa ke ba mace ba ce irin ta sauran mata masu kishin hauka."

"Ina so ki nuna mata girmana da darajata a gidan nan, ta yadda ita ma za ta bi sawun ki wajen yi mini hidima. Ta hakan ne kishi ba zai taSa samun gurbin zama a tsakaninku ba. Nana, shin za ki iya yi mini wannan alfarma ta ™arshe? Ki zama jagora a gare ta, ki kuma kare ladanki daga sharrin ShaiWan?"

Wani irin sanyi na ji ya ratsa zuciyata, soyayya da tausayin Sardauna suka sake lulluSe Sargo da fatar jikina, cike da tausasawa nima na fara magana.

In sha Allah Sardauna, ni zan kasance mai biyayya da tausayawa a gareka har ™arshen numfashina, Sardauna na yi niyar ya™i da kowanne irin sheWani da zai zo ya shiga rayuwata, zan yi ha™uri zan zauna da amaryar ko da ba ta son zama da ni, zan nuna mata girmanka da soyayyarka.

Ya sa hannu ya rungumo ni jikinsa, sannan ya ce. 

Na gode Nanata, Allah Ya yi miki albarka.  

Na amsa da amin, ina rugume da shi. Ban sami damar yi masa maganar rashin Waukan wayata da Bilkisu take ba, tun da gashi har abu ta bada akawo min. Tun daga wannan rana bansake bari sheWan ya samin wani tunani na kishi ba ko wani abu mai kama da hakan, shirye shiryen biki suna ta ™aratowa, Sardauna ya yi matu™ar busy abubuwa kawai yake shiryawa na auren, lefe akwati set uku ya yi mata, ni kuma ya yi min set Waya. Ranar da aka kai kayan gidansu Bilkisu ya kama Waurin auren saura sati biyu cif, amma shagulgulan bikin sauran kwama takwas afara a yadda Sardauna yake faWan. Har da wasu Events da za ayi a Abuja ma, Waurin auren ma acan zaayi sabida Bilkisu na da yan uwa acan, ni dai nawa na yi fatan alheri ne kawai. 

Lokacin da bikin ya rage saura kwanaki biyu a fara Sardauna ya umarce ni da na je gida na faWawa su Hajiya, idan zan iya ma na kwana Waya acan. Na ji daWi sosai sabida ina son na zaga yan uwa da na daWe bangani ba, duk da ya ja kunnena sosai akan kar na faWi wasu abubuwan. 

Da kanshi ya kaini har gida, bayan ya shiga sun gaisa da Hajiya sannan ya tafi, gidan bakowa sai Hajiya Yaya Radiya tana makaranta, Ra is da Yaya Ridwan ma haka, yaran Yaya Radiya ma sun tafi makaranta. Hakan ya bamu damar zantawa da Hajiya sosai da sosai, har na faWa mata auren da zaiyi, sai dai na Soye mata cewar Bilkisu ™awata ce, na ce a familyn Winsu take, ta yi aure ne ya mutu. 

Yaya Ridwan ne ya fara dawowa, amma bai nuna ko ya ganni ba, ya shige Waki sai kuma Yaya Radiya, ita ce ma muka tattauna muka yi hira sosai, sai Ra is da ya dawo. Da daddare Sardauna ya kirani na ce da shi zan kwana anan Win, ya kashe wayarsa na tare da ya ce min komai ba. 

Washe gari na je gidan Yaya Rumaisa, ta yi mamakin ganina a gidan nata dan tun da na yi aure bai fi sau biyu na je ba, shima duk kafin rasuwar Alhaji ne, amma tun da Alhaji ya rasu banje ba. Muna cikin hira ta ce dani. 

Shashasha, wannan yarinyar ce zaki ce mijinki ba sonta yake ba tuntuni?  

Ta faWa tana nuna min hoton Sardauna da Bilkisu a cikin mota wanda Bilkisun ta Wauka da kanta, na yi murmushi sannan na ce. 

Yaya ai sun amshi ™addara ne, sabida dukkansu ™addararsu iri Waya ce, amma aina kika sami hotonan?  

Nana baki da hankali, a yanzu babu wasu couples da suke trending a social media kamarsu. ko wane shafi kika duba hoton su nr, mutane suna ta posting suna cewa Sardauna Ta ambo, ya sami matar da yake so, wasu a comment sai ™are miki zagi suke, har da masu cewa yar mitsiyata.

Hhm Yaya Wannan tunanin su ne, tun da dai muna zaune da mijina lafiya ai shikenan, duk abinda mutane zasu ce su yi ta faWa,ni dai ina son mijina shima yana sona, ba shikenan ba.  

Ke Nana kalle ni, wallahi Allah Sardauna baya sonki, ke ni yanzu na fahimci Sardauna auren manufa ya yi dake.  

Legendspen

08129553971

*SARTSE*

-Amanar-Janafty-

*Sayyid Legendspen*

MAH/2026/001

Sadaukarwa.

RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA

(Mai Dambu) 

Shafi na ashirin da shida.

    (26)

Yaya bana son irin wannan maganar, ai daman na san kwata kwata ba kya son Sardauna.  

Na faWa a fusace.

Ke dalla malama rufe min baki kafin na yi ™asa ™asa dake anan, rashin kunya zaki yi min akan Sardaunan?  

Ni ba rashin kunya zan miki ba, amma kema kinsan ai abinda kika faWa bai kamata ba, miji na ne fa.

Au mijinki ko? To mene amfanin aure irin na Sardauna?  

Yaya wai mene haka?  

Duka na zaki yi Nana? Duka na zaki yi?  

Ta faWa tana mi™ewa, ganin tashin hankalin na ta ya yi yawa na mi™e da cewa. 

Ni kinga tafiya ta.  

Har n kai gab da ™ofa ta kira sunana. 

Nana!  

Na juyo na kalleta, ta yi min alama da hannu sannan ta ce. 

Zo.

Dawowa na yi na zauna, itama ta zauna kusan minti biyar  Yaya Rumaisa ta gyara zama, ta dubi ni, wadda idanuna suka yi jawur saboda ri™on da ta yi min kaWai ya karyan zuciya da kuma fargabar abinda zata ce min. Ta nisa, sannan ta ™ara kama hannun na ta matse shi sosai, cikin muryar tausasawa ta fara magana.

"Nana, ki nutsu kar kice zaki yi kuka ki saurare ni da kyau. Rayuwa ba soyayya ce kawai ba, kuma zaman gidan miji ba hauka ba ne. Ina kallon yadda kika lallace akan Sardauna, kina neman mayar da shi tamkar abin bautarki. To ki buWe kunnenki ki ji; Iyaye daban, Miji daban."
Chapter 34 · 0% Book details