← Book details Sartse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 39

Sashe 38

Sartse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To ina yi miki kishin da babu wata hallita da nake yi wa irin shi, abu mafi girma a zuciyata shine tsanar Turaki, to Nana kishin da nake yi miki ya zarci tsanar Turaki sau ba adadi a zuciyata.  

Na ji wani sabon shau™i ya lilluSe ni, kalaman sa kamar zuma suke malala a cikin jyjiyoyin jikina. Duk wata fargabar kishiya da nake ji ta gushe a wannan daren, na ji tamkar ni kaWai ce mace a duniya.

Don haka nake so ki kwantar da hankalinki, uwar gidana. Kewarki da zan rinka yi, ita ce zata ri™a addabar rayuwata a kowane minti. Babu wata mace da ta isa ta maye gurbinki.

A  cikin tsantsar daWin baki da zafafan kalaman Sardauna, na mika masa dukkan ragamar rayuwata, har ina jin cewa ko da duniya zata tashi, wannan mutumin Sardauna nawa ne ni kaWai.

***********

06:30pm

Zaune yake gefen gadon, ni kuma ina tsaye na gama sanya masa babbar rigarsa, haka hulal ma da kaina na yi masa karinta, ya fito fes kamar ango a daren aurenshi na farko. Duk wani jiri da ciwon kai da nake ji Wazu, yanzu babu shi. 

Muna nan zaune masu kawo amarya suka shigo, kallon kaina na yi a mudubi, na yi kyau na gaji da haWuwa, lace Wina dark blue ne da touch Win golden, ya yi matu™ar amsar jikina. Šikin doguwar rigar ya kwanta a jikina Was, na yi Waurina mai kyau na Wora ™aramin blue mayafi akaina ma zagayoshi ta ka faWa, kunnena da hannu Wankun zinare da Sardauna ya siya min ne. Sallama da na ji ana yi a Sangarena, ya sa na fita zuwa falon, iyayen amarya ne da ita amaryar. Cike da ladabi na tare su tare da basu mazauni. 

To Uwar gida ga amarya mun kawo miki, muna fatan zaku zauna lafiya da juna.  

Na yi murmushina na ko yaushe, sannan na ce.

Ni da Bilkisu kamar yan uwa muke, in sha Allahu babu abinda zai biyo baya sai Wimbin alheri, yar uwa barka da shigowa.  

Ma sha Allah, gaskiyya Nana munji daWi sosai na yadda kika karramamu, Allah Ya yi albarka.@ 

Amin na gode sosai.  

Daga haka suka mi™e nima na mi™e suka fice zuwa part Winta, na dawo na sameshi zaune gefen gadon. 

Amarya ta zo.  

Ina sonki Nana.  

Kallonshi na yi, a raina ina jin daWi. Me yafi wannan daWi? Mijinki yana ™ara aure amma babu abinda yake ce miki sai yana sonki. Shin a matan duniya akwai wacca tafi ni sa a kuwa? Ni Nanan Sardauna.

Ina sonka Sardauna, ina tare da kai komai runtsi komai wuya Sardauna, Allah Ya baka ikon yin adalci mijina.

Nana!  

Na am.  

Bilkisu ta ce min ba za ta iya girki a gawayi ba, amma na amince mata tunda daman kece kika zaSi yin amfani da shi, sannan ta ce ba zata rayu ba Ac, ba Iron, ba fridge ba, shima na amince mata, duba da adalaci ke baki saba da su ba, ita kuma ta saba, tun da a addini ma ance idan ka auri mace ka ba ta abinda take ciki a gida, ko wanda ya fishi, idan ba zaka iya ba kar ka aureta, shi ya sa Nana, ke kuma ko da na hanaki wannan Nana nasan na baki fin abinda yafi na gidanku ko?.  

Sardauna! Ni ba duk wani ™yale ™yalen duniya nake bu™ata ba a zama na da kai, Sardauna kai kawai nake so, kai nake bu™ata, kai ne zan rayu da shi Sardauna.  

Rungumo ni ya yi jikinsa, sannan ya ce. 

Nana girmanki da kimarki a idona abune da bazasu taSa taSuwa ba, Nana zan iya ya™i da kowa akanki, Nana ina so a yadda kike yi min uziri a yanzu ki ci gaba da yimin har ™arshe Nana, ina sonki ina sonki ina sonki.  

Ina sonka nima sosai da sosai, yawwa gobe zanje asibiti akan ciwon kaina.  

Tom Nana, Allah Ya kaimu.  

Amin amin.  

˜arfe tara ta yi Nana bara na je wajen amarya, ki shiryawa zuwana, da akwai magana Nana.  

Tom Allah Ya tsare, amma ina kazar?  

Nana tana mota, yanzu zan shigo da ita, akwai taki akwai ta ta Nana.  

Tom Ango.  

Ya sa kai ya fice, ni kuma na zauna a gefen gado. Idan ace haka Sardauna zai nuna min soyayya, ya auri mata dubu mana, ni dai Allah Ya sallameni wallahi, na yi da ce da Sardauna, na yi da ce da miji na arzi™i, Allah Ya barmin Sardauna  na. Dan na yi imani Sardauna ya cika jarumin maza, ya cika miji, wai ni shin idan ban bautawa mijina na me zan masa, ni na daina zuwa wajen su Yaya Rumaisa, tun da na fuskanci kamar basu san me suke faWa ba, ina dalili ace wai biyayy zan masa ba bauta ba, Mitcheww.  

Na ja tsaki tare da tashi na fito falo, ina nan zaune har wajen goma Sardauna bai dawo ba, a raina na ce ko Sardauna ya je siyo kaza ya yi dare ne bai dawo ba? Ganin goma da kwata ya sa na Waga labule sai dai ga motarsa Nana. 

A a ina ya yi ne? Ko yana can wajen Bilkisun?  

Na faWa cike da mamaki, daidai lokacin kuma na ji sautin takunsa, komawa na yi na zauna akam kujera daidai lokacin kuma ya shigo. 

Nana!  

Na am.  

Ta so muje ko?  

Zuwa ina?  

Šakin Bilkisu mana? Ko kin manta.  

Na yi tunanin nan za ta zo.  

Na faWa ina mi™ewa. 

Ki kijiki ta zo ta yi miki me?

Bakomai.  

Yana gaba ina binsa a baya muka shiga Sangaren nata, ya ji kaya na alfarma, kina gani kinsan yar masu hali ce a gidan. Da sallama a bakina na shiga, tana zaune kamar ba amarya ba, ta mimmi™e tana danna waya, Waki ga Ac ga fanka abunta. 

Hajiya Bilkisu amarya.  

Na faWa ina washe baki da niyar zama akan kujera. 

Ke dakata! Kar ki kuskura ki zauna min akan kujera.  

Kallon ta na yi baki a sake, na kalli Sardauna da ya zauna yana danna waya. 

A tsaye zan zauna?  

Nana zauna a ™asa.  

Sardauna ya faWa, mamaki kamar ya kashe ni. 

Ki zauna Nana.  

Ba musu kamar umarnin ubangiji na zauna. 

Nana!  

Sardauna ya kira sunana, na Waga kai na kalleshi. 

Nana! Na gode da aura min mace mafi soyuwa a raina, na gode da aura min mace da nake son ta a zuciyata.

https://chat.whatsapp.com/FaQD2pS03r12pfKIb7jQMb?mode=gi_t

(Wannan shine sabon group Win mu)

*Munyi nisa a Arewapen, ta wannan link Win ko username Legendspen*

https://www.arewapen.com/book?id=69d7e87dfc259651b7635bff

*SARTSE*

-Amanar-Janafty-

*Sayyid Legendspen*

MAH/2026/001

Sadaukarwa.

RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA

(Mai Dambu)

Shafi na ashirin da tara.

    (29)

END OF BOOK ONE.

(˜arshen littafi na Waya)

Kamar saukar aradu haka na ji maganganun Sardauna suna dukan gangar jikina. Gaba Waya na ji duniyar ta yi mini tsit, kalaman sa suka baibaye mini tunani na, jiri na ji yana neman kwasata.

"Na gode Nana... na gode da kika share mini kukan zuciya ta hanyar aura min mace mafi soyuwa a raina. Na gode da kika cika mini burina na aurar min da matar da nake so a cikin zuciyata."

WaWannan kalaman na Sardauna su ne suka daki kunnena ta baya. Na ji tamkar an tsire min zuciya da mashi mai zafi. Na Wago raunanun idanuna da suka riga suka yi ja™aS da hawaye, suna mini wani irin zazzafan zafi, na kalli fuskarsa.

Fuskarsa daban da waccan da na sani a baya, Sardaunan Nana, babu sauran Wigon tausayi ko ™auna, sai tsantsar wula™anci da ya bayyana a cikinta. Na juya na kalli fuskar Bilkisu, wadda ke tsaye tana kallona tamkar tana kallon dabba.

A daidai lokacin, na fara kokawa da zuciyata ta ina ™o™arin ™aryata abun da kunnena ya ce ya ji. A raina na ce, 'Ba Sardauna na ba ne... mafarki nake yi... Sardaunana ba zai mini haka ba.'

Cikin ta™ama da jiji da kai, Bilkisu ta saki wata daddaWar dariya mai cike da ba™ar ba™antawa, ta kalle ni ta ce.

"Kanki ya Wauke wuta ko, Nana? Ke yarinya ce marar wayo, marar ilimi da tunani!"

"Bilkisu, yi shiru!"

Sardauna ya dakatar da ita. A lokacin, wani Wigon fatan alheri ya Warso a zuciyata. Na rin™a jiran abinda Sardauna zai ™ara cewa. A cikin raina addu a nake yi, 'Ya Allah... Allah Ka sa cewa zai yi ™arya take yi... Allah Ya sa cewa zai yi shi nawa ne.'

Amma sai na ga ya tako a hankali, ya tsaya daidai inda nake, ya zuba mini idanun sa da babu alamar tausayi a cikinsu, ya ce.

"Nana! Ba ke nake so ba. ˜uciyar jikinki kawai nake so... wadda na riga da na gama mallaka gaba Waya. Nana, ban taSa son na rayu da ke a matsayin macen da zan so ba, sai dai na rayu da ke a matsayin wadda zan killace ta, na hana ta kula kowa a duniya, saboda zazzafan kishin ki na ™addara da nake ji a rana, Nana."

Šum...!

Haka na ji kaina ya Wauki wani irin zafi, wani ba™in abu mai nauyi ya daki ™ar™ashin ™irgina, ya tare mini numfashi. Jikina gaba Waya ya daina aiki, ya saki tamkar gawa. Kafin na dawo cikin hayacina, muryar Bilkisu ta sake dukan kunne na.

Wani irin masifaffen jiri ne ya Webeni, na ji Wakin yana neman kayar da ni. Cikin tsananin razana da gigicewa,na lallaSa na dafa gefen kujerar da ke kusa da ni, jikina gaba Waya yana wani irin karkarwa kamar wacca za a zarewa rai, bakina yana Sari na fara faWin.

"Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un...! Don Allah... don girman Allah Sardauna karka sake ni! Don girman Allah karka yi mini haka!"

Cikin rashin tabbas da ™as™anci na zube a ™asa, na rarrafa ina jan gwiwoyina na matsa daidai wajen ™afafunsa, na sa hannuna duka biyu waWanda ke rawa tamkar ana jijigasu, na ™an™ame ™afarsa da ™arfi, hawaye masu zafi suka wanke mini fuska.

"Sardauna...! Sardauna ka yi wa Allah, ka yi wa Ma'aiki karka sake ni! Ina sonka... ina sonka da dukan rayuwata! Ban san yadda zan yi ba, ban san yadda zan rayu ba idan babu kai a rayuwata... Don Allah Sardauna, karka watsar da ni...!"
Chapter 38 · 0% Book details