← Book details Sartse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 39

Sashe 30

Sartse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana faWin haka ta katse kiranta, ni nama manta da halin faWa irin na ta har na kira ta, gashi ta zageni ta zage mijin nawa gaba Waya, ita daman bata da ha™uri ba abinda ta iya sai faWa a rayuwarta. 

Mitcheww.  

Na ja tsaki na kwanta akan kujera, banda rainin hankali irin Yaya Rumaisa mutumin da baya son auren ™arshe ma yaban zaSi shine za ta ce wai ya rabani da kowa shine zai ™ara aure. Duk sai da na yi danasanin kiranta, daman ita ba a fiya yin abun arzi™i a kwashe duka da ita ba, haka na yi ta faman Sacin rai har yamma, yau indomie na yi wa Sardauna dan ba abinda zan iya sabida wani irin ciwon kai da na tashi dashi bayan na kwanta da yamma. 

Fuskarsa babu yabo babu fallasa haka ya shigo cikin gidan. 

Sannu da zuwa. Bai amsa ba ya ajiye jakarsa, yanayin da nake ji ma bazan iya tashi na bishi ba, yanda ya shiga Wakin haka ya fito. 

Baki da lafiya ne?  

Jiri nake ji.

Sannu, bama ki yi girki ba kenan?

Na yi.

Bari na ci.  

Tom, akwai magana.  

An samu?

Na gyaWa masa kai.

FaWamin to.  

Ka fara cin abincin.  

A a faWan.  

Sai da na tashi zaune na ri™e hannunsa. 

Kasan dai bazan zaSa ma abinda zai cutar da ka ba, dan Allah ina son ka amshi zaSin da na yi maka da hannu biyu biyu, kuma kasa a ranka alheri ce a garemu duka.

Nana duk jikina ya yi sanyi, wace ki faWamin dan Allah.  

Bilkisu! Wannan ™awar ta wa ta kake Wan ganinta.  

Shiru ya yi sai kuma can ya ce. 

Wata fara haka?  

Eyh ita.  

Anya Nana?  

Dan Allah karka ce a a.  

Nana zan yi shawara.

Tom, amma da matsala guda fa?  

Kinji ko? Wace matsalal?  

Tana aiki.  

Wane kalal aiki kuma?  

Aikin Ofis, kuma ka ce ba zaka iya jure ganin matarka na cakuWuwa da maza ba, shine nake so dan Allah ka yi ha™uri ka barta.  

Nana sai na yi tunani gaskiyya, bari na ci abincin.  

Yana faWin haka ya tashi ya nufi dinning Win, da kanshi ya zuba ya ce kuma bai yi magana akan indomie Win ba, ko da yaga ban jindaWi ne? 

*********

Yau Sardauna bai fita majalisa ba, da na tambayeshi sai ya ce bani da lafiya dole ya yi jinyata kuma gashi yana son ya yi tunanin akan al amarin nan. Haka dai na yi bacci na barshi yana faman tunane tunane. 

Washe gari bayan munyi breakfast zai fita ya ce da ni.

Nana na yi tunani duba da yanayin da muke ciki na matsi Hajiya da Big Daddy na amince zan barta ta yi aikin na ta, amma gaskiyya bana so.  

Har cikin raina na ji daWi. 

Alhamdulillah, Allah Ya sa albarka, yanzu sai na yi mata magana nasan zata amince itama.  

Wannan ya rage naki.  

Ya faWa yana ficewa, ni kuma na koma kan kujera na zauna, na Wau wayata na fara kiran lambar Bilkisu, amma bata Wauka ba, gashi message Win na jiya ma ba ta dawo da amsa ba. Sake kiranta na yi har ta gama ™arar ta ba ta Wauka ba, haka na ajiye wayar da tunanin an jima zan sake kiranta idan ba ta kirani ba. Har yamma ba ta kirani ba kuma nasake kira ba ta Wauka ba, na yi ta addu ar Allah Ya sa lafiya dai. Da ddaddare na faWawa Sardauna na ce ya bani wayarsa na kira ta sai ya ce na sake kiranta dai. Ina kira kuwa ta Wauka. 

Nana ki yi ha™uri, yau na yi busy da yawa wallahi, ina ta ganin kiranki ban sami zama ba.

Ayyah ba komai Bilkisu, ya gida ya aikin?  

Alhamdullilah, ya mai gidan?

Lafiya ™alau, na ce ya ake ciki da maganar Abban naku an da ce kuwa?  

Tun da ya ™aramin sati Waya bamu sake maganar ba, kuma kamar naga sa™onki ko? Kince kin sami mafita?  

Eyh Bilkisu na samu wacca nake ganin za ta yi amfani wa ni dake.  

Nana ai matsalal mu ba ta da ala™a da juna.  

Eyh Bilkisu sai dai kamanceceniya, Abbanku ya matsa miki, nima Hajiyar Sardauna ta matsa me zai hana Bilkisu mu haWu a rufawa juna asiri, ki auri Mijina.  

Nana kina da hankali? Kinsan abinda kike faWa kuwa? Na auri mijinki Sardauna?  

Is for the best Bilkisu Please.

Nana bazan iya ba, a yadda kike son mijinki na shiga ciki? Ki rufan asiri Nana.  

Bilkisu ke ce last hope Wina, aure na ma tangarWa yake ki taimaka.  

Lallai Nana, dan Allah ina so ki a ranki bamu taSa wannan maganar ba dan Allah.  

Tana gama faWin haka ta kashe wayar, na kalli Sardauna da yake zaune yana sauroro. 

Nana akawai wata bayan ita?  

Na girgiza kai sannan na ce. 

Ita kaWai ce.  

Nana to ya za ayi?  

Ita Win dai, nasan za ta fahimta in sha Allah.  

Nana banga alama ba, ki na ji ta ce yadda kike son mijinki ba za ta iya shiga tsakaninku ba.  

Hhhm, idan ba ta shiga ba rasa ka zanyi gaba Waya.

Nana ki daina wannan tunanin ba zaki taSa rasani ba, Nana a yadda nake jin ki a rayuwata idan babu ke nima ai babu ni.  

Nima nasan ba zan rasa ka ba, amma biyayya ga iyaye dole ce idan muna neman albarka a rayuwa.  

Nana bari na je gidan Hajiya na gara kiranta yanzu.  

Tom Allah Ya tsare hanya.  

Amin Ya Allah.  

Ya faWa yana tashi, yana fita na sake kiranta a waya amma bata Wauka ba, message na hau rubuta mata. 

Salam, Bilkisu dan Allah ki fahimceni, ina so ki aure mijina Sardauna sabida ki tsira daga auren dole da zaayi miki, shima ya tsira daga auren dolen da za ayi masa ki fahimta dan Allah.  

Na tura mata amma har Sardauna ya dawo ba ta yi min reply ba, washe gari da safe ma na sake tura mata wani amma shima ba ta ce dani komai ba. 

Honey ya kuka yi da yarinyar?  

Kallonsa na yi sannan na ci gaba da haWa mai tea Win, sai da na gama sannan na ce. 

Ba ta sake cewa komai ba, amma dai zan ™o™arta zan sake magana da ita.  

Shikenan Nana, nasan zaki iya, Allah Ya yi miki albarka.  

Amin Amin.  

Bayan mun kammala breakfast ya tafi, na dawo na ci gaba da kiran wayar Bilkisu amma bata Wauka ba, ganin ba zata Wauka ba na shiga fito da wankin kayan Sardauna na hau yi, da ™arfi nake dirza kayan sabida ina son su fita su yi haske yanda zai ji daWi, sai wajen la asar na gama wankin na shanya su s abun shanyar mun na bayan kitchen, ina dawo na ga missed call Win Bilkisu, jikina har Sari yake na Wau wayar na kira ta, ina kira ta Wauka, cikin rawar baki na fara magana. 

Bilkisu!  

Na am Nana.  

Bilkisu kinga messages Wina?  

Nagani Nana, ni bansan abinda zance miki ba shi ya sa ma ban miki reply ba, kina magana kamar wata yar ™waya.  

Hhm Bilkisu ba zaki gane ba ne, amma dan Allah ki taimaka, ki taimakeni ki taimaki mijina.  

Nana babu wata hanyar taimako da zan ia yi miki bayan wannan? Gaskiyya wannan abun yafi ™arfina, ki barni da matsalal Abbana kawai.  

Bilkisu dan Allah ki biyo ta gidana mu yi magana.

Nana bana jin zan sake zuwa gidanki, tun abinda kike son ™ullamin kenan? Ace na zo gidanki na aure miki miji, duniya ta yi ta zagina.

Haba Bilkisu ya zaki ce haka? Dan Allah kizo ko ba zaki aureshi ba nasan akwai shawarar da zaki ban.  

Shiru ta Wanyi na yan mintina sannan ta ce. 

Shikenan, bari na zo yanzu.  

Tom Bilkisu na gode sosai.

Sai na zo.

Ta faWa tana kashe wayar, na koma na zauna. A halin da Bilkisu take ciki na yi tunanin zata amshi wannan tayin hannu biyu biyu? Ko dan mafita da take nema, amma ta™i! Lallai Bilkisu ta cika mutuniyar arzi™i.  

Ta shi na yi na duba kayan Sardauna dana wanke, na fara kawahe waWanda suka bushe na shiga dasu ciki, ina fitowa itama ta shigo Wakin, ban bari ta zauna ba na fara mata magana. 

Haba Bilkisu, ahalin da kike ciki na yi tunanin wannan mafita ce a garemu duka?  

Nana mafita ce mana, amma da ace wani ne ba mijinki ba, Nana da wane ido zan kalli duniya? Da wani ido zan kalli mutane zan kalli makwafta, zan kalli yan uwanki, ace ina ™awarki na zo na auri mijinki, zagin da zan sha Nana ba ™arami ba ne, Nana tsinuwa zan sha a bakin jama a, ta yanda babu yadda zaayi na kare kaina, tun da gani a gidan naki, Nana a dinga duba ana saran gatari.  

Bilkisu mu zauna. Na faWa ina kama mata hannu, zaman ta yi sannan na ce. 

Ina ruwanmu da surutun wani? Waye zai sani? Waye zai san mi dake ™awayene, Bilkisu ko sun sani mene a ciki? Ba dai mu muna zaune ba, nasani Bilkisu zaki zauna tare dani cikin aminci, mu kula da mijinmu, to ina ruwanmu da zancen mutane? Su yi ta yi kar su daina.  

Idan ke kunnenki zai iya jurewa, to ni nawa ba zai ya jurewa ba. Nana bakisan mene bakin mutane ba, idan suka sa ka agaba wallahi duk wata albarka dai ka nemeta ka rasa, Nana idan ke kin fahimta ina yan uwanki zasu fahimta?  

Kishiya ce fa Bilkisu! Kuma ba Kaina farau ba ko karau? Mijina ne kaWai ya taSa ™ara aure?  

Hannuna ta kama sannan ta ce. 

Nana, ki yi ha™uri abar wannan maganar, kamar zata fi amfani Nana, idan duk na ce na ji nagani shi mijin naki fa? Yana sona? Zai soni? Zaman alfama Nana bazan iya ba dan Allah.  

Salamu alaikun.  

Muyar Sarauna ta ratsa Wakin, ban maji ko warn Winsa ba, kawai sallamarsa na ji.  

Sannu da zuwa.  

Yawwa sannu.  

Sannu da zuwa.  

Bilkisu ta faWa kanta yana ™asa. 

Yawwa sannu. Yana amsawa ya shige cikin Wakin, bai ™ara sa shigewa ba Bilkisu ta mi™e tare da faWin. 

Nana, zan tafi.  

Bilkisu bamu gama magana ba.  

Nana ni dai nagama yanke hukuncina.  
Chapter 30 · 0% Book details