← Book details Sartse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 39

Sashe 27

Sartse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nana, na yi miki al™warin duk tsanani dui wuya ba zan taSa rabuwa dake ba, ko da ke ce kika bu™aci haka, Nana wallahi ina yi miki kishin da bazan iya numfashi ba muddin na ga wani namiji a tare dake, ko da Wan gidanku ne, Nana a ™ar™ashin ikona zaki rayu, anan zaki mutu na yi mi™i al™warin hakan Nana." 

Duk wasu kalamam Sardauna daWi suke mim a rayuwa, babban buri na shine na rayu na kuma mutu a ™ar™ashin auren Sardauna. Yinin ranar bai fita ba sai dare, haka washe gari ma wai duk akan big Daddy, sai da ya kwana uki a gida sannan ya yanke shawarar zai fita, shima dai duk a tsorace yake. Ni kuma wani tausayinsa ne yake taSa min zuciya, Allah Ya gani bana son wani abu da zai dami mijina ko kaWan, bayan ya fita na yi ayyukana na kwanta bacci. 

*****

06:30pm

Yamma ce mai cike da sanyi, ina zaune a falo ina jiran dawowar Sardauna. Tun safe bayan ya fita na ji zuciyata tana bugawa, wani irin nauyi nake ji wanda na kasa fassara shi.  Ko da na yi bacci wani irin mafarki na yi marar daWi, amma abinda ya kwantar min da hankali shine ba Sardauna ba ne a mafarkin ni ce, ni kuma nasan ina zaune anan babu wani abu da zai sameni, duk da a mafarkin ganina na yi ina kuka a zaune a falon nan, amma yanayin kujeruj falon su sauya kuSa duk hotona na da suke falon babu su, nasan dai wannan duk mafarki ne. 

Ina zaune ina ta faman addu'a Allah Ya sa alherine, duk da al'amuran gidansu Sardaina sun dame ni sosai da sosai, gashi rabon Bilkisu da gidan nan an kwana biyu, sai dai ta waya da muke magana. Ina jin ™arar motarsa, na tashi da sauri don na tarbe shi kamar yadda na saba.

Ina buWe ™ofar, na gan shi tsaye, amma yanayin da na ganshi ya sanya na sandare a wajen. Sardauna ne, amma ba wannan Sardaunan mai takama da izza ba. Idanunsa sun yi jajir, fuskarsa ta kumbura alamar ya sha kuka, har lokacin hawaye suna zirara a kumatunsa.

Legendspen

08129553971

Legendspen

08129553971

*SARTSE*

-Amanar-Janafty-

*Sayyid Legendspen*

MAH/2026/001

Sadaukarwa.

RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA

(Mai Dambu) 

Shafi na ashirin.

    (20)

"Sardauna! Me ya faru? Me ya faru da kai?" Na faWa muryata tana rawa, hankalina ya gama tashi.

Bai ce mini komai ba, ya ™araso cikin falon ya zube a kan kujera, ya rufe fuskarsa a cikin tafin hannunsa, kuka yake yi mai taba zuciya, yana girgiza kai tamkar wanda aka yi wa rasuwa. Ban san lokacin da nima hawaye suka fara wanke mini fuska ba, na dur™usa a gabansa na kamo hannunsa.

"Don Allah Sardauna ka yi magana, ka tsoratar da ni. Ko wani ne ya rasu a gidan?"

Ya Wago idanunsa waWanda suka rine suka yi ja, ya kalle ni da wani irin tausayi, sannan ya fara magana cikin muryarsa wadda ta dashe sabida da kuka.

"Nana... gara ma mutuwa ta Wauke ni na huta da wannan mummunar kaddarar. Nana, Big Daddy da Hajiya sun sanya ni a gaba sun ce lallai sai na ™ara aure. Wai saboda har yanzu shiru ba ki samu juna biyu ba. Kuma matsalal daga gareki take Nana, su kuma ba za su iya jure  hakan ba, tun da ba asan zuwa lokacin da mahaifar taki za ta yi ™wari ba Nana, ina cikin damuwa gwanda mutuwa ta Waukeni da wannan abun."

Wani irin jiri na ji ya kwashe ni, na ji numfashina yana shirin Waukewa. Aure? Sardauna zai ™ara aure?

"Sun ce... sun ce idan ban yi ba, to za su cire ni daga cikin komai na gidan. Nana, na yi kuka, na ro™e su, na ce musu ke kaWai kika isa ki zama uwar 'ya'yana, ke kaWai nake so Nana ke  kaWai nasani a cikin duka matan duniya amma sun ™i saurare na. Wai ko dai na sake ki ko kuma na yarda na ™ara aure, idan lokacin da suka ba ni ya cika to za su aura mini wata ko wace."

Ya sake fashewa da wani sabon kukan, ya jawo ni ya rungume ni yana kuka a kafaWata, ni kuwa kamar mutun-Mutumi haka nake jina, ba na gane komai.

"Nana, ba zan iya rabuwa da ke ba, amma kuma ba zan iya saSa wa magabata na ba. Ina son ki Nana, amma kaddara tana shirin raba mana farin ciki."

Nima kukan nake yi kamar raina zai fita. Ganin yadda Sardauna yake zubar da hawaye saboda ni, ganin yadda yake nuna mini yana cikin matsanancin hali, sai na ji duk duniya ba ni da masoyi kamarsa. Na ji tausayinsa ya mamaye mini zuciya, har na manta da zafin kishin da yake shirin shiga rayuwata.

"Ka yi ha™uri Sardauna," 

na faWa cikin dasasshiyar murya. 

"Idan har hakan shi ne zai kawo maka kwanciyar hankali a gida, to ka bi maganar su. Ba na son ka shiga matsala da iyayenka saboda ni."

A daidai wannan lokacin, na lura da wani Wan gajeren murmushi da ya gifta a fuskarsa ba tare da na fuskanci ma'anarsa ba. Sai na ga ya Wago ya kalleni, ya sake murmushin. 

"Nana kina da hankali? Kinsan me kike cewa? Na je na yi auren haka kike cewa Nana wa zan aura, wa na sani? Kin taSa ganina da wata mace? Kin taSa kamani da wata mace? Nana ba kya kishina ne ko me?" 

Da sauri na girgiza kai sannan na ce. 

"A'a ba haka ba ne, amma ina ganin bamu da wata mafita a yanzu da ta kai hakan, babu ita dole ne mu yi biyayya, idan muna son kasancewa tare." 

Kuka ya sake fashewa da shi, tare da tashi ya shige cikin Waki. Yana tashi na bi bayanshi har zuwa cikin Wakin, nasan dole a yanzu ni zan tausashi Sardauna, tabbas yana cikin damuwa mai girma nina sani. Zama na yi akan gadon kamar yadda ya yi. 

"Kai daina tagumin nan dan Allah." 

"Hhhm! Nana idan banyi tagumi ba me zanyi? Ina da abun yi ne? Wai baki ji abinda na ce miki ba aure fa, aure suka ce na sake nan da two weeks ko zasu bani wacca suka ga dama kuma na sake ki." 

"Nasan sun yi fushine, amma ka bi komai a hankali nasan Hajiya za ta sake fahimta dan Allah."

"Nana kina nufin na je na yi musu wani bayani? Kina tunanin akwai abinda ban faWa musu ba? Nana kin raina girman soyayyarki a zuciyata ne?" 

"Ko kaWan ba haka nake nufi ba wallahi, ina nufin mu nutsu mu sami mafita a hankali." 

"Kina da mafita? Dan Allah Nana na faWa min." 

"A yanzu dai babu, amma dole na yi tunani na sami mafita domin matsalalka matsala ta ce." 

"Allah Ya bamu mafita Nana, ki yi ha™uri kin ji ko?" 

"Dame? Me ka yi min haka? Kai zan bawa ha™uri Sardauna." 

******

Washe gari Sardauna bai fita ko ina ba, yana gida gaba Waya babu abinda yake iya zuwa, ni ke ta Wawainiya da shi kamar ™aramin yaro, kuka kuwa ya yi yafi a ™irga. Gaba Waya bai bani wata dama da zan yi wani tunani ba, gashi a yadda ™wa™walwata ta toshe ina bu™atar isashen hutu kafin na yi tunani, nasan matsala ta babba ce amma har yanzu na™i yardarwa kaina matsalar babba ce, gani nake akan Sardauna komai zan iya yi. 

Sai wajen ™arfe biyar sannan ya shirya ya fita, bai daWe da fita ba na kira wayar Bilkisu, ina kira ta Wauka, cikin muryata dake cike da damuwa na fara magana.

"Sister kin daina zuwa kwata kwata, abubuwa duk sun caSe mini." 

"Ba haka ba ne Nana, nima ayyuka sunyi min yawa ga wata matsala da ta fara kunnomin kai a gida." 

"Ya salam, ni kaina abubuwam sunyi yawa daga gidansu Sardauna." 

"Nana tun da gidansu Sardauna ne ai da sau™i, nifa akan kaina nake magana, Nana kinsan Abbanmu ya bani sati Waya na fito da mijin aure ko ya auramin wani abokinsa, Nana dattijo ne ya kai kusan shekara 70, gashi kinsan ni babu wanda nake kulawa, Nana ina cikin damuwa." 

"Allah Sarki 'yar uwa, muma makamanciyar matsalalki muke fuskanta." 

"Bangane ba?" 

"Gidansu Sardauna sun matsa mishi akan ya ™ara aure." 

"Saboda me to?" 

"Rashin haihuwa mana." 

"Nana kika ce kin yi Sari har sau biyu, kuma kince mahaifarki ce ba ta yi ™an™anta ko?" 

"Hakane." 

"To ai zaki haihu Nana, ki yi musu bayani mana." 

"Bilkisu ba zaki gane ba, a yanzu dole Sardauna sai ya ™ara aure ko kuma ya sake ni." 

Na faWa ina fashewa da wani irin Kuka, bana son kalmar sakinan ko kaWan a rayuwata.

"Idan har haka ne mafita Nana ki amince masa, tun da kina son sa, kina son farin cikinsa, farin cikin iyayensa ai shine nashi, Nana ke kika ce kina son Sardauna sama da kowa sama sa komai, to ki nuna masa a wannan lokacin, ki nuna masa soyayya ki dage ki danne ki barshi ya yi auren." 

"To ai ba anan matsalal take ba." 

"Nana ga Momy nan mu yi magana anjima." 

Ta faWa tana kashe wayarta, bayan wayar ta mutu ta barni cikim tunani. 'Idan da gaske nake son Sardauna yanzu ne lokacin da zan nuna masa soyayyar ta hanayar ™arfafa masa gwiwa kenan? To amma Sardauna baya kula mata ba ruwansa.' 

Wani Sari daga zuciyata ya ce da ni. 'Ko a wajen aikinsa ba zai rasa ba, ko a 'yan uwansu.' 

'A 'yan uwansu fa?' Na tambayi kaina. 

'Kai a'a gaskiyya a gari kawai ya nema ya aura, zanyi ha™uri zanyi biyyaya in sha Allah.'

Wannan ita ce shawarar da na yanke akan Sardauna, ita ce mafita guda Waya da nake ganin za ta fiye mana daga ni har shi. Sai wajen ™arfe tara ya dawo, ina zaune a falo ya shigo. 

"Sannu da gida Honey." 

"Yawwa sannu da dawowa."  Na amsa masa, kasancewar ba shigar ofis ba ce yasa ban cire mai takalmi ko wani abu ba. 

"Ga abinci." 

"Honey ba ni da nutsuwar cin abinci, ni kaWai nasan abinda nake tun kara Honey, ni kaWai nasan abinda nake ji.Hon ina cikin damuwa, ina cikin tashin hankali, rayuwa ta yi min ba™i mutuncina yana watangarirya." 
Chapter 27 · 0% Book details