← Book details Sartse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 39

Sashe 19

Sartse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hawayene suka fara zubowa daga cikin idanuna masu Wumi, gaba Waya na rasa abinda ke mim daWi, me ma ya sa suka zo, me ya sa Yaya Ridwan zai dake shi?. 

"Ba zamu sake zuwar ma gida ba, duk da cewa 'yar uwarmu na cikin gidan." 

Yaya Radiya ta faWa tana ficewa, Ra'is da Yaya Ridwan suka bi bayanta, nima na bisu da gudu ina faWin.

"Yaya ku tsaya dan girman Allah." 

Amma babu wanda ya jiyo cikinsu, haka suka kaWa kai suka tafi su ka barni ina faman zubar da hawaye. Ko da na dawo falon Sardauna baya nan

, ban kuma nemeshi ba na shige Waki na hau kiran layinsu amma babu wanda ya Wauka, har wajen ™arfe goma babu Sardauna babu alamunshi, haka na kwanta bacci.

Washe gari da safe ban iya ta shi da wuri ba, sabida ban samu bacci da wuri ba, karar bugun ™ofar da ake yi min ce ta tashe ni. 

"Hon! BuWe ™ofa." 

˜afafuna na sauke daga kan gadon sannan na nufi ™ofar na buWe, ban ko kalleshi ba na yi hanyar ban Waki. 

"Ina zaki?" 

"Wanke fuska zan yi." 

"Okay ki yi sauri." 

Bayan na wanke fuskar na Waura alwala na fito, kasancewar lokacin bana sallah ya ™ara ba ni damar mimi™ewa ina baccin. 

"Zo.. ina da wani abu na baza ta." 

Ya faWa yana kama hannuna muka fito falo. 

"Muje mu fara breakfast to." 

Ya faWa yana nuna min wajen dinning, da mamaki na kalli wajen sannan na ce. 

"Waye ya yi girkin?"

"Hon ai na iya girki sosai, muje ki ji." 

Na nufi dinning Win, ya ja min kujera na zauna ya shiga zuba min, gasashen biride da ™wai sai kuma shayin Na'a na'a. Komai ya yi daWi sosai haka na ci ina mamakin yadda aka yi duk zaman nan Sardauna bai taSa ce min ya iya girki ba. 

Ina cikin ci ya tashi. "Hon ina zuwa." Ya faWa tare da barin wajen, kusan minti uku sannan ya dawo hannun sa ri™e da wani ™aramin kwali mai kyau. 

"Hon, canki mene anan?" 

Na yi murmushi sannan na ce. 

"Mene?" 

"Kin bani gari?"

"Uhm na baka." 

Aikuwa ya buWe kwalin, kyakyawar sar™a ta bayyana wacca aka yi ta da zinare sai she™i take. 

"Hon naki ne." 

"Wow, na gode." 

Na faWa bakina ya kasa rufuwa, Wauka ya yi ya gwada min a wuyan, aikuwa ta yi kyau ta hau Was da ita kamat a wuyan nawa aka ™era ta. 

"Na gode." 

Na sake faWa. 

"Akwai wani ta so."

Ya faWa yana kama hannuna. 

"Hau na goyaki." 

Ya faWa yana sunkuyawa, aikuwa na hau ya Waukeni zuwa waje, bai sauke ni na  sai a harabar gidan. 

"Kinga." 

Ya faWa yana nuna min wata ash Win mota.

"Wow ta yi kyau wata ka sake siya." 

"Eyh, amma wa ke, ta kice Hon." 

"Ni.. tawa?" 

Na faWa cike da ruWewa, ban taSa hango kaina da mota ba a rayuwata, amma sai ga shi yau Sardauna ya bani, kai ina son Sardauna. 

"Ko ba kya so?" 

Na yi murmushi, sannan na ce. 

"Na gode mijina, na gode Allah Ya biya ka da aljanna, Allah Ya ™ara maka arzi™i duniya da lahira." 

"Amin Honey, na gode da soyayyarki a gareni, na gode sosai da sosai, muje ciki mu yi magana." 

"Tom." 

Na faWa tare da binshi ciki, ya zauna akan kujera ya jawo ni kusa da shi, ya kura min idanu cike da wani irin tausayi na mussaman, ya fara magana cikin sanyin muryar tamkar mai shirin yin kuka. 

"Nana, kin san me ya sa nake yin dukkan waWannan abubuwan? Kin san dalilin da ya sa nake ™o™arin killace ki? Saboda Kishi ne, Nana. Kishinki nake yi fiye da yadda kike tunani. Duk lokacin da kika fita kika tafi wannan karatun na wahala, zuciyata ba ta samun natsuwa. Ina ganin kamar kowane namiji da kika bi ta gabansa, kallon sha'awa yake miki. Ba zan iya jure ganin wani namiji ya kalli kyakkyawar fuskarki ba, ko ya ji muryarki."

Ya sauke numfashi, ya Wago ya kalleni tare da matse hannuna dake cikin nasa. 

"Wannan karatun na nan... Nana, wahala kike sha a banza. Kalle ki, yadda kika rame, yadda kika fita a hayyacinki saboda shiriritar malaman nan da ba sa ma san abin da suke koyarwa. Nana nasan ba kya gane komai, lokacinki kawainkike Satarwa, ni kuma bana son naga kina shan wahala. Shin darajar matar Sardauna Ta Ambo ita ce ta ri™a bin layin motar haya ko ta ri™a shiga aji ana cakuWawa da ita? A'a, Nana. Matsayinki ya fi haka."

Ya kamo hannuna ya Waura a kan saitin zuciyarsa, sannan ya cigaba

"Nana, kalle ni cikin idanuwa na. Kin ga wannan motar? kin ga wannan zinaren? Duk ba komai ba ne a wurina idan aka kwatanta da darajarki. Ina son ki zama sarauniyar da ba ta taka ™asa, sarauniyar da duniya za ta kalla ta san tana ™ar™ashin inuwar Sardauna Ta ambo. Nana a yanzu ina so na baki umarni, umarnin da nake son ki bi, ki je ki sami Alhaji. Ki gaya masa cikin lallashi cewa kin fasa wannan karatun na wahala. Ba wai kin daina ba ne, a'a ki gaya masa cewa ni Sardauna zan tafi ™arin karatu a Turai, kuma na yanke shawarar tafiya da ke can. A can za ki yi karatu a manyan makarantun duniya, inda ba za ki sha rana ba, ba za ki fuskanci cin mutuncin malamai ba. Ba zaki yi karatu a wahala ba, can ne ya dace da matsayin matar Sardauna. Amma yanzu, kin daina Sata lokaci a nan. Ki gaya masa kin gaji da wannan, kin fi son ki huta kafin mu tsallaka can ™asar waje."

"Nana, kina tunanin zan yaudare ki ne? Ni ne fa masoyinki. Idan ba ki bi maganata ba, za mu rasa wannan damar ta tafiya can tare, Nana ki amince da ni, sama da kowa, dan babu mai ™aunarki kamar ni."

Legendspen

08129553971

*SARTSE*

-Amanar-Janafty-

*Sayyid Legendspen*

MAH/2026/001

Sadaukarwa.

RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA

(Mai Dambu) 

Shafi na sha huWu.

    (14) 

Na yi shiru har ya kammala, tabbas komai Sardauna yake faWan gaskiyya ne, bai taSa yi min ™arya ba, kuma nasan bazai yaudareni ba, tun da da zai yaudareni ai da bai aure ni ba. Na buWe baki yi zan yi magana wayarsa ta fara ringing, ya Waga yana faWin. 

Sister Memah, ya sauka?  

Da ke wayar tana handsfree na ji ta ce da shi. 

Yeah! Kuma yana zama maganarku kai da Turaki ya fara, an sanar da shi faWan da kuka yi last time a company, ya ce duka yana nemanku.

My god! Big Daddy akwai faWa yanzu shikenan zan kira anjima thanks you.  

Ya faWa tare da kashe wayar, sannan ya juyo ya kalleni. 

Ina saurarenki.

A hankali na fara magana, cike kulawa da soyayya. 

Na yarda da kai Sardauna, na yarda baza ka taSar cutar da ni ba, na baka ragamar rayuwata gaba Waya, zan yi amfani da ™arfina da lokacina wajen sama maka farin ciki, zanje na sami Alhajin.  

Ban ™arasa ba na ji ya rungumo ni jikinsa, tare da faWin. 

Good girl, tare zamuje umara this year in sha Allah, i love you Nana.  

Love you More Hon.  

Daga nan muka shiga lamarin soyayya, yinin ranar Sardauna kamar zai mayar da ni ciki, haka yake kula da ni, ko girki ba mu yi ba fita muka yi muka ci daga nan muka biya shopping duka a sabuwar motata, har ya fara nuna yadda ake tu™i. 

Gaba Waya na manta da wani abu ya faru jiya tsakanin Sardauna da yan gidanmu, hankalina yana kan mijina ban nemesu ba, suma basu nemeni ba. Haka kusan sati guda sannan Sardauna ya ce da ni gobe zan je gidan. 

******

Shi ya sauke ni, amma bai shiga gidan ba ya tafi ya ce da ni idan ya dawo zai shigo,  shiga ta gidan na tarar da Yaya Ridwan zai fito. 

Ina yini?

Lafiya.

Ya amsa bai ko kalleni ba, haka na shiga gidan jikina ba ™wari, Hajiya ce a tsakar gidan tana ganina ta washe baki da faWin. 

Zuwa ba sanarwa.  

Na dur™usa kasa na ce. 

Hajiya ina yini?  

Lafiya ™alau Nana, ya gida da me gidan

Lafiya ™alau Hajiya.  

Na amsa tare da shigewa cikin falonta, sai bayan na zauna ne na ce. 

Hajiya ina Yaya Radiya, da Ra is?

Radiya ta je makaranta wai za ta yi screening, Ra is kuma yanzu na aiki shi siyo salat, baki ga Ridwan ba ne?  

Mun gaisa Hajiya, kinsan halinsa.  

Murmushi ta yi tare da faWin. 

Bari na sauke miyar nan.  

Ina nan zaune Ra is ya shigo daga siyo salat, bai nuna mamakin ganina ba kuma bai nuna Sacin rai ba, bayan mun gaisa Hajiya ta zuba mana abinci muka ci abinci, bayan Hajiya ta tashi ne Ra is ya ce. 

Ya zancen makarantar?  

Bawani labari Ra is a yanzu har an fara jarrabawar zango na farko ma, na zo ne kawai na faWawa Alhaji na ji abinda zai ce.  

Allah Ya kyauta.  

Me ya faru?  

Hajiya da ta shigo ta faWa. 

Mijinta je ya hanata komawa makaranta, gashi har an fara jarrabawa.  

Innullahi wa inna illahir raji un, garin ya? Me ya faru?  

Wallahi Hajiya haka kawai, har Yaya Ridwan ya masa magana da Yaya Radiya ™arshe ya yi mana rashin arzi™i.

Hajiya Yaya Ridwan fa fasa masa baki ya yi.  

Na faWa kamar zanyi kuka, da mamaki ta kalleni. 

A yaushe a ka yi haka?  

An kwana biyu.  

Amma babu labari.  

Ai ni na yi tunanin ma sun faWa muku, ni kuma gudun Sacin ran Alhaji yasa mana na ja baya da zuwa.  

Amma bai kyauta ba, to yana da wani dalili ne?  

Eyh Hajiya, yana da dalilinsa mai ™arfi ma, kuma ya ce da ni ™arshen shekara zamu tafi turai, zai sama mini wata makarantar acan.  

Tom Allah yasa, yawwa Nana ina fatan dai ba haWa baki kukayi da mijinki ba, kika sha wani abu da zai hanaki Waukan ciki ba ko? Abun shiru ya yi yawa.  

Eyh Hajiya ba abinda nake sha, nama je asibiti an bani magani ina sha.  

To Allah Ya duba lamarin.  
Chapter 19 · 0% Book details