← Book details Sartse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 39

Sashe 29

Sartse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na ga kin rame kamar bakya cin abinci?" 

Kallon jikina na yi, ni banga wata rama ba amma tabbas nasan a jikina ina jina falai falai kamar wata takarda. 

"Nana kamar ba kya cikin ni'imar aure, matar Ta Ambo ce a haka Nana?"

"Ba wata rama da na yi fa, kawai strees ne."

"Name?" 

"Abubuwan da suka dagule mana, komai ya rincaSe." 

"Nana ai komai yazo ™arshe ko? Komai zai yu sau™i tunda a yanzu za ayi auren kuma ai shikenan ko?" 

"Eyh shikenan in sha Allah." 

"Yawwa Nanaty, zan ci abinci." 

Tashi na yi ma nufi wajen dinnig Win, shi kuma yana biye da ni a baya, alkubus da miyar taushe ne na yi, ya zauna ya ci sosai nima kuma ya matsamin sai na ce, yadda ya ci haka na ce. Ko majalisar ma baije ba ya kwashe ne muka yi Waki, duk ranar da Sardauna ya Waukeni da kansa ina shan wahala har nagane, shi ya sa bana so ya Waukeni nafi son mu tafi ™afa da ™afa. 

Tun daga wannan lokaci Sardauna ya sani a wata duniyar ta daban, kullum aikina tunanin wace za ta da ce da Sardauna, dan ya zama dole na nema masa a ™asa da kwana ukun da ya ambata. ˜awayena Malaika ta yi aure tana kano, Fauziya ta yi aure, Amina Aminu ma ta yi aurenta daman su kenan, Yaya Radiya kuma Yayata ce babu aure a tsakaninsu, Anty Adiza kuma matar aure ce, ni kuma su kaWai ne mutanen da nasani, sai dai ko Bilkisu ita kuma aure ne ba ta so a yanzu. 

"Ni fa ina ganin can yaje danginsu ya nema, zai fi mana sau™i." 

Na faWa a fili kamar ina magana da wani ko wata, ko da ya dawo ma baiyi min maganar ba kuma nima bance komai ba, washe gari ma haka na yi ta faman tunani, sai gab da yamma na shirya naje gidan kitso wanda daman na tambayeshi, tun zuwana unguwar gidan kitson kawai nake zuwa shima sai na yi wata nawa banje ba. A hanya na yi ya kallon 'yan mata ko akwai wacce za ta da ce da Sardauna, amma bansamu ba. Haka a gidan kitson ina zaune ina kallon mutane sai hira suke, a Wauko gulmar waccan a sauke a Wauki ta waccan har layi yazo kaina ni dai ban tanka musu ba. 

"Baiwar Allah a wane gida kike?" 

Wata mata ta tambayeni. 

"Nan baya." 

"Ina ne baya ko ba anan kike ba?"

Wata daban ta yi tambayar.

"Eyh ina Takur Site C ne." 

"Eyh kam da dan nisa gaskiyya, amarya ce?" 

"A'a na shekara biyu." 

"Allah Sarki Allah Ya sanya alheri." 

"Amin." 

Na faWa daga nan ban sake ce musu komai ba har aka gama yi min na tashi na tafi, a raina na ce. 

"Ina fita zaku hau yi dani." 

Illai kuwa ko ™arasa fita ban yi ba na ji muryar wata ta ce. 

"Wai ita matan Takur sai wani shan ™amshi ake." 

Murmushi na yi na ™arasa ficewa ta, ba su san Wimbin damuwar dake damuna ba ne shi ya sa ma suke wannan zancen. 

Har na ™araso gidana ina kallon 'yan mata hanya sai dai Allah bai sa na ga wadda zata da ce da mijina ba, haka na dawo gida shiru. Nan dai na yanke shawarar tamnbayarshi na ji ko akwai wata yarinya da yake burgeshi haka, ko yake yawan ganinta. 

Banyi masa maganar adawowarsa ta farko ba, sai da ya dawo daga Majalisa sannan na ce. 

"Na yi tunani a iya matan da nasani, amma kafin nan kai babu wata yarinya da ka sani ko kake ganin tana da hankali." 

"Nana bayan ke bansan kowa ba."

"Ko a wajen aikinku, ko a family?"

"Nana bayan ke bansan kowa ba." 

"Ka na ji, ko a unguwarku da kuna ™anana?" 

"Nana unguwar da na taso ba irin Yalwawa ba ce, Unguwa ce da ba ruwan kowa da kowa, unguwa ce ta masu arzi™i babu talaka ko Waya a unguwar dan haka babu 'yar wanda nasani Nana, ba kamar ku ba cike da yara wani gidan na cin wani gidan, yara su shiga wancan gidan su fita wancan, mu duk ba haka muke ba."

A maganar sai na ji kamar gori, na yi mishi murmushin ya™e sannan na ce. 

"Ba haka nake nufi ba ranka ya daWe, irin ko a makaranta haka?" 

"Nana, zaki yi min ko bazaki yi ba? Idan bazaki yi ba just tell me, ba sai kina haWani da ™azamar rayuwa marar daraja ba, rayuwata ba irin wannan ba ce Nana. Ina ga har yanzu bakisan su waye Familyn mu ba Nana."

"Ka yi ha™uri, baka fahimce ni ba." 

"A'a ba wani ban fahimce ki ba Nana." 

"Ka yi ha™uri." 

Ta shi ya yi ya shige Waki ba tare da ya ce dani ko ™ala ba. 'Oh ni yau me yake damun Sardauna ne?.' Na tambayi kaina a zuci. 

Washe gari ma haka ya tashi yana faman cicin magani ko breakfast ma cewa ya yi wai ba zai ci ba. 

"Dan Allah me ya faru?" 

"Nana kinfi kowa sanin duk abinda ya faru."

"Bansan sani ba, bansan wani abu da ya faru wanda yasa ka canja baki Waya."

"Hhm! Nana sai na fito fili na faWa miki cewar ki nemo min aure?"

"Ai akan wannan maganar muke kai kuma ina kan dubawa." 

"Su wa kika duba?" 

"Duk cikin ™awayena kowacca ta yi aure." 

"Duka babu marar aure kenan?" 

"A na kusa dai babu, shi ya sa nake so kara faWa tunanina don bincikawa." 

"Nana yau ne fa ranar ta ™arshe da Hajiya ta bani." 

"Nasani kuma in sha Allah yau komai ™are." 

"Nana ki yi duk abinda kike tunanin zaki iya, dan Allah." 

"In sha Allah, to muje ka yi breakfast Win." 

Muka nufi dinning Win, muna cikin breakfast Win Sardauna ya ce. 

"Nana! Ko zan samu ki wanken kayana ko guda biyu ne, na ji daWin wancan da kika yi min." 

'Ashe Sardauna ya kula na yi masa wanki? Amma ko a ido bai taSa nuna min ba, ko da yake gashi yanzu ya faWa.' Murmushi na yi masa sannan na ce. 

"Babu damuwa, ko ban yi yau zanyi gobe."

"Me ya sa sai gobe."

"Idan ba mafita na samu akan wannan maganar ba bani da nutsuwar da zan iya yin wankin da zai burgeka ya yi maka kyau." 

"To shikenan, Allah Ya yi miki albarka Nanaty." 

"Amin amin." 

Tin fitar Sardauna nake tunanin inda za a sami mafitar ™arshe, kwatsam Bilkisu ta kirani a waya, bayan na Waga muka gaisa na ce da ita. 

"Ya Abban naku?" 

"Nana ya ™aramin one week Wazu, na ji daWi sosai wallahi Nana zan duba yanzu duk wanda yazo zan bashi fuska." 

"Ma sha Allah Bilkisu, Allah Ya kawo na gari."

"Amin Nana, na gode miki da nuna kulawa, zan je ofis mu yi magana anjima." 

Bayan ta kashe wayar kawai tunanin haWa ta da Sardauna ya faWomin. 

"Zaman Sardauna da Bilkisu zai yi Waya kuwa? Tsakanina da Bilkisu akwai fahimtar juna, akwai soyayya to amma Sardauna fa?" 

Legendspen

08129553971.

*SARTSE*

-Amanar-Janafty-

*Sayyid Legendspen*

MAH/2026/001

Sadaukarwa.

RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA

(Mai Dambu) 

Shafi na ashirin da biyu.

    (22)

Sardauna baya son karatu? Bilkisu har aiki take yi, shin Bilkisu za ta iya barin aikinta sabida Sardauna, ko kuwa Sardauna zai iya ha™ura ta yi aiki, ya ce kuma yana da kishi ba zai iya jurar matan shi na yawo a titi ba suna cakuWuwa da maza, amma tabbas Bilkisu za ta dace da zamanmu a wannan ™adamin, tun da itama mahaifinta ya bata lokaci kamar yadda Hajiyar Sardauna da Big Daddy suka ba shi?  

To Nana hakan ba matsala? Na ji wani Sari na zuciyata ya faWa a fili kamar wani daga wajene ya faWa. Sardauna yana sona, kuma Bilkisu tana sa ilimi zata zauna da ni da Sardauna lafiya, ni bani da wata matsala indai Sardauna na nan kuma yana kallona a matsayin mata ina ™ar™ashen inuwar aurensa.  

Waya ta na Wauka na kira Bilkisu amma ba ta Wauka ba, ™ila bata ™arasa ofis ba sai kawai na tura mata text. 

Bilkisu dan Allah ki kirani, akwai mafitar da nake tunani wacca za ta kawo ™arshen komai in sha Allah.  

Na tura mata tare da emoji na kuka da na ro™o, ina turawa na nemi lambar Yaya Rumaisa dan tabbas sai na sanar da wani nawa. Bugu Waya ta Wauka tare da faWin. 

Manya yau a gari?

Ina wuni Yaya?  

Lafiya ™alau Nana, ya gidan?

Alhamdullah Yaya, dan Allah wata magana zan faWa miki amma bana son Hajiya ko wani ya sani.  

Wace magana ce haka Nana?  

Ki yi min al™wari dan Allah.

Nana ya za ayi na yi al™wari akan abinda bansani ba?

Dan Allah ki yi min, ba wani abu ba ne na cutarwa kawai labari zan baki.

Shikenan Nana na yi miki.  

Na sauke ajiyar zuciya sannan na ce. 

Zan ™arawa Sardauna aure.  

Bangane abinda kike nufi ba.  

Yaya a gidansu aka bashi zaSi guda biyu, tun da ni bana haihuwa mahaifata ba ta gama ™wari ba ko ya sake ni su aura masa wata ko kuma ya ™ara aure.  

Ke bana son rashin hankali, uban waye ya ce miki ba kya haihuwa?  

Ta faWa cikin jarababbiyar muryarta.

Munje asibiti sabida na yi Sari har sau biyu, shine aka ce ba ta yi ™wari ba.  

To da zai sake auren shine ke zaki ™ara masa?  

Yaya ya bani zaSi ne akan na nema masa matar.  

Wannan shine kuskure na biyu da zaki yi a rayuwarki da Sardauna, na farko kin zaSi miji sama da kowa, sai da ya raba ki da yan uwanki da duk wasu mutane a kusa dake shine zai ™ara aure? Nana wai uban me kike sha?  

Yaya Umarni ne daga gida, shi ya sa ma ya bani damar zaSa masa wadda zai aura.  

Lallai Nana mahaukaciya ce ke? Dan mun yi al™warin bazamu sake shiga al amuran gidanki ba, amma dai sai na zo har gidan na ci ubanki na ci uban mijin, banza marar hankali wace yarinyar kika zaSa masa?  

Wata ma™wafciyar mu ce.

Jaka! Nana bansan ki lalace ba sai yanzu.  
Chapter 29 · 0% Book details