← Book details Sartse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 39

Sashe 2

Sartse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na Wauki Wayar nasa a plate Win da ya gama ci, na buWe plast Win miyar zan zuba sai dai fa sam babu miyar a ciki ya shanye, karo na farko cikin abubuwan da Sardauna yake yi mini na ji babu daWi, buWe plast Win da farfesun naman ragon yake ciki na yi shima dai babu.

 "Me ya faru haka?." 

Na tambayi kaina, dan nasan dai Sardauna bazai taSa cinye duka wa'yannan ba, dole wani wajen ya kai ko ya kai kitchen.

 "Ka kai ragowar kicin ne?." 

Na tambaye shi, muryata na rawa kamar wacca ta yi tsaren gudu, ko dayake ba shakka tsare na yi, domin na yi tsere da zuciyata kafin bakina ya iya fito da wanann tambayar.

 "Ban Wauke komai ba, ai aikin ne ko?." 

Zama na yi akan dinning Win, gaba Waya raina babu daWi na rasa abinda ke mini daWi. Muryar shi na juyo ya na cewa. 

"Me kike yi anan ne?." 

Na goge ™wallar da ta fito daga ido na ce. 

"Babu komai?." 

"To tawo nan mana." 

"Abincin zan ci." 

Na faWa ba tare da na taso Win ba. 

"Tom." 

Kawai ya faWa ya ci gaba da abinda yake, na tashi na shiga cikin kicin Win, ban masan me zan iya dafawa ba wanda zansa a cikina, ga yatsu na sai wani irin zugi suke yi mini kamar wacca na taSa attaruhu. 

Haka nagama zagaye na a cikin kicin Win na fito zuwa falo, na bude firij na Wakko biredi na dawo kan dining na haWa da ragowar romon farfesun naman na ci. 

Bayan na kammala na Wauke komai na kai kicin, na gyara wajen tsaf sannan na nufo shi zan zauna na huce gajiyar da take cin jikina. Sai dai ban kai ga ™arasowa ba idanuna suka sauka kan abinda yake yi, ya zuge zif Win Waya daga cikin fulallukan kujera yana fito da katifar ciki yana gutsirawa a hankali, kamar ™aramin yaro yana wasa, sai da na haWiye wani abu a raina sannan na ce.

"Sardauna! Kujerar kake yagawa fa?" 

Na fada ina kallon katifar da yake gutsirawa, gabana yana faWuwa ganin yadda yake Sarnatar da kayan gidan namu.

Kallona ya yi sannan ya kalli abinda ya watsar. 

 "To kin barni nan ni kaWai, ba dole na yi duk abinda zanyi ba dan ma banyi miki kuka ba." 

Murmushi na yi sannan na zauna kusa dashi da faWin.

"Abinci fa na ci."

Cuno baki ya yi kamar ™aramin yaro zaiyi kuka sannan ya ce. 

"To kuma sai ki bar mijin ki da yake sonki fiye da komai shi ka Wai, babu abokin ta ya shi zama." 

"To ai gani nan nazo." 

Na faWa ina shafa masa kai, ai kuwa ya kwanto akan cinyata. 

"Daman kaina ™ai™ayi yake, ki gyara mini." 

Ya faWa bayan ya kwanto, tare da  janyo wayarsa ya fara dannawa, wani irin nauyi na ji kamar an Woramin dutse, kamar da gangan ya sakar mini nauyinsa, na fara shafa masa kansa, ina jin dumin gashinsa a tafukan hannuna.

"'Nana."

Ya kira sunana a hankali, idonsa har yanzu yana kan wayarsa. 

"'Na ga yadda kika yi shiru Wazu da kika ga na cinye Gurasa, Ko dai kin fara gajiya ne da yi mini girki ne, ko gajiya da zama dani a cikin gidan? Rayuwar aure fa bauta da soyayya ne! Na Wauka kin fi kowa sanin cewa duk abin da yake nawa, naki ne... har da yunwar ki.'"

Na haWiye miyau me Waci da ya tsaya mini a ma™wogaro, na yi ™o™arin yin murmushi duk da raWaWin da yatsuna suke mini na ™unar da na yi Wazu na ce. 

"'Haba Sardauna! Kai fa mijina ne, ni kuma matarka ce mai ™aunarka, ai na ji daWi ma da ka cinye abincin, hakan na nufin girkin ya yi daWi kuma hakane burina."

Ya Waga idonsa ya kalle ni, wani kallo mai wuyar fassara sannan ya ce. 

"Yauwa. Domin idan kika fara ™orafi a kan abinci, zan fara tunanin ko ni Win ne ba kya so... ko kuwa kin fara manta yadda iyayenki su ka gaya miki yadda mace ta gari take zama da mijinta?" 

˜arar wayata ne ya katse mini maganar da na yi niyar yi, na kai hannu zan Wauka amma Sardauna ya riga ni.

 "Wake kiranki a daren nan?"

Murmushi na yi sannan na ce. 

"Bansaniba wallahi, amma bani na Waga." 

Sardauna bai ba ni wayar ba, sai ma juyawa da ya yi ya fuskanci allon wayar, hasken ya haska kwayar idonsa da ta canza launi lokaci guda. Ya dade yana kallon sunan dake kan allon wayar kafin ya dago ya kalle ni, wani irin kallo nasa da yake mini wanda ni kaina bana gane me yake nufi dashi, sai kuma ya saki wani irin murmushi kana ya ce. 

"Daga gida ne..." 

Ya fada muryarsa na rawa kaWan. 

 "Radiya ce." 

Ya kama sunan babbar Yayarmu kai tsaye, sannan ya ce.

"Me take nema gunki a wannan lokacin?"

Ban kai ga ba shi amsa ba, ya danna maSallin kin amsa kiran (Reject). Ya ajiye wayar a kan kirjinsa, ya kara gyara kwanciyarsa a cinyata yana kallon silin din dakin.

"Ita ta™i zaman aure, tana so ta hanaki kula da miji ko bawa mijinki lokacinki. Nana, kin san ina son ki ko? Kuma kin san ba na son kowa ya shiga tsakaninmu. Wannan gidan namu ne mu biyu, duk wanda zai kawo mana rarrabuwa, ko da kuwa danginki ne, to ba ya son mu."

Wani irin nauyi na ji ya ™ara danne ni, ba nauyin Sardauna ba, nauyin kalaman da ya jefo mini ne. Ya kama hannuna da ya kone dazu, ya matse shi a hankali sannan ya ce. 

"Gobe me zamu karya dashi? Ni bana son cin biredi abinci nake son ci very special, ba irin wanda muka saba ci ba." 

Na yi murmushi muryata na rawa sannan na ce. 

"Tom Mijina na me kake so?." 

"ZaSi yana wajenki, amma dai abu na daban, ko zan sami Vento cake wanda zan fita dashi ofis?." 

Na gyaWa kai sannan na ce. 

"Zaka samu mana."

Bansan ashe ™walla ta fito daga idona ba, sai ji na yi ya kai hannu gefen idona ya goge hawayen da yatsansa, sannan ya kai yatsan bakinsa ya WanWana. 

"Hawayenki suna da WanWanon gishiri, Nana. Kada ki sake kuka... domin kukan mace a gidan miji, alama ce ta rashin godiya ga Allah ko kuma raina kulawar da miji yake ba ta."

Washe gari.

Gaba Waya jikina babu daWi haka na tashi, bayan na yi sallar asuba na shiga kicin, ba tare da sanin ainahin abu na daban da Sardauna yake maganarsa ba. Sai da na ™arewa kicin Win kallon sannan basira ta faWo mini, na tsugunna gaban kurfoti bayan na zuba gawaye na fara ™o™arin kunna wuta, sai dai da na kunna hutar iska take kaWe ta, abu kamar wasa na kusa minti sha biyar a gaban huta amma ta™i kunnuwa. 

Mi™ewa na yi na nufi kan gas Wina yau kawai zanyi girki akansa, ina kunnawa na Wora tea kafin na Wakko fulawa na shiga kwaSa Fanke, amma wannan mai attaruhu da albasa da maggi ne a ciki, banda tabbaci amma nasan Sardauna bai taSa cin wannan ba, nima na ko yi sarrafa fulawane a wajen Anty Hadiza matar Isah Nadabo dake ita 'yar kano ce kuma a kanon ma ™wararriya ce a harkar sarrafa fulawa. Bayan kwaSa na rufe shi na shiga juye tea din a flask sannan na Wakko kasko na Wora akan gas Win na zuba mai. 

Ina ™o™arin fara saka fanke a cikin mai ya shigo kicin Win, har ™asa na tsugunna ina gaida shi kamar zan yi masa sujjada.

"Ina kwana, an tashi lafiya?." 

Kallona ya yi sai kawai na ji ya ce.

"Me yasa baki da tausayi ne Nana, me yasa imaninki yake raguwa a ko da yaushe?." 

Gabana yashiga faWuwa, ™irjina ya fara dukan uku uku, bansan tausayin da ya kaini kunna gas ba, duk da ba wani amfani nake dashi ba, sai na yi sati biyu banyi girki akai ba, hasali ma shi ke amfanin da shi wajen dafa ruwan wanka, ko tea idan yana sauri. 

"Ka yi hakuri dan Allah, gawayin ne ya™i kamawa gaba Waya, na kusa minti goma ina kunnawa amma ya™i kamawa." 

"Mitchewww." 

Ya ja wani uban tsaki, sannam ya ce. 

"Minti goma kacal? Ba zaki iya minti goma wajen kunnawa hutar da zaki yi wa mijinki girki ba? Nana bansan yaushe rashin imaninki ya kai haka ba, tabbas 'yan uwnaki zawara suna fara Woraki a turbar da suka bi suka kashe aurensu." 

Hawaye na ji ya fara gangaro mini daga ido, cikin sanyi murya na ce. 

"Ka yi hakuri dan Allah, nasan kana son fita da wuri kar na Sata maka lokaci, amma in sha Allahu bazan sake amfani dashi ba har Abada." 

Na faWa muryata na rawa, alamun kuka ya fara cin ™arfi na. 

"Kuka kuma? Nana me yasa kike son azabtar da zuciyata da hawayenki ne? Nifa mijinki ne mai sonki fiye da komai a duniya, Nana kawai ina guje miki bin hanyar da 'yan uwnaki suka bi."

Shiru na yi bance komai ba, sai shasha™ar kuka da nake yi. 

"Nana! Goge hawayen nan ki ci gaba da abinda kike amma bana son almubazaranci, kinsan yadda rayuwa ta yi tsada, ko da yake ba sai na faWa miki ba, gidanku ka Wai ya isheki ishara." 

Legendspen

08129553981

*SARTSE*

-Amanar-Janafty-

*Sayyid Legendspen*

MAH/2026/001

Sadaukarwa.

RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA

(Mai Dambu) 

Shafi na biyu

    (02)

Goge hawayen na shiga yi, na rasa me yake mini daWi, Allah Ya gani ina mugun so da ™aunar mijina, kamae yadda shima na tabbatar yana sona, to me zai sa na tsaya akan gas ina Sata masa rai. Tashi na yi na je na kashe Gas Win sannan na ce. 

"Ka yi hakuri dan Allah, idan ban tausaya maka ba wazan tausayawa a duniya? Wa nake dashi da zan zo bayan kai?" 

"Nana ai naga alamun kamar ana son shiga tsakanin mu a hure miki kunne." 

Ya faWa fuskarsa Wauke da murmushin da nake kallo a matsayin soyayya mai girma, sannan ya ™ara cewa. 

"Nana ina son na nemi alfarma a wajenki guda Waya." 

Na gyaWa masa kai sannan na ce. 

"Ina sauraronka." 
Chapter 2 · 0% Book details