Sashe 5
Sartse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Yauwa Nana. Don haka, tunda yanzu babu layin a wayar, babu wani abu da zai dinga raba miki hankali. Ina so ki maida hankalinki gaba daya a kaina da kuma wannan gidan. Kuma ina so yau ki goge sauran kayan da suka rage."
Ya sumbaci tafin hannuna, wanda har yanzu yake zugi saboda kunar jiya da kuma takewar da ya yi mini Wazo. Amma kalaman sa sun sanya na manta da raWaWin.
Na gyada masa kai cikin sauri na ce.
"Yanzu yanzu ma, kana fita zan ™arasa."
"Tashi ki je ki soma, ni kuma zan karya da kaina."
Na mi™e ina jin kamar an dora mini wani sabon nauyi, amma nauyin da nake ganinsa a matsayin Ladan Bautar Aure, da kuma tukwici ga soyayyar da ake nuna mini. Kai tsaye na shige Wakinsa na fito da ragowar kayan gaba Waya.
Ina tsaka da guguwar bayan fitar sardauna naji ana sallama, gabana har faWuwa yake yayin da na tashi zuwa buWe kofar. Ra'is!
"Ra'is lafiya?."
Na faWa baki na yana rawa, ya kalleni cike da bacin rai, sannan ya ce.
"Alhaji bashi da lafiya, ya ce yana son ganinki, yana son magana dake amma kin ™i, Yaya ta kira ki a waya kin ™i Wauka, anyi miki test message akan baba yana cikin halin jinya, amma kin gani baki ce komai ba, yanzu da safe an kiraki ma wayar akashe, sai kuma yanzu kika yi message a wayar mijinki kika wai ke ma baki da lafiya. Nana me yake damunki ne? Dan kinyi aure a gidan hali shine kika tsani 'yan uwanki?."
Tun da Ra'is yake magana ™irjina yake bugawa, duk wata kalma da yake faWa guda daya tamkar ana doramin dutse a kirjina ne, fuskata cike da hawaye na ce.
"Wallahi Ra'is ba haka ba ne, bansan Baba bashi da lafiya ba, kuma Sar...."
"Ta ina zaki san ba shi da lafiya, kin zaSi miji mai abun duniya akan 'yan uwanki da iyayenki, wallahi Nana kin bawa kowa kunya ciki hardani, wahala da Alhaji da Hajiya suka sha akan aurenki basu sha ta akan kowa ba, Nana kinsan tunda kika ajiye karatun da Alhaji ya ci buri akanki bai ™ara lafiya ba. Wallahi Nana daba dan Baba ya takura ba babu abinda zai kawo ni gidanki babu shi, kuma idan kinga dama ki je ki ganshi idan baki ga dama ba kar ki zo, amma ki kwana da sanin duk wani abu da yasami mahaifinmu ba zamu taSa yafe miki ba."
Yana faWin haka ya juya zai tafi, cikin muryar kuka na ce.
"Ra'is! Dan Allah tsaya."
Tsayawa ya yi ba tare da ya juyo ba, na tako inda yake sannan na ce.
"Dan Allah kira mini Alhajin, na yi magana da shi dan Allah."
Kallona ya yi sannan ya ce.
"Ki yi magana dashi? Kina nufin bazaki zo ba?."
"A'a Ra'is zan zo, amma dan Allah na fara jin muryarsa kafin nazo."
Murmushin takaici Ra'is ya yi sannan ya sa hannu a aljihu ya zaro wayarsa, ya danna kiran sannan ya mi™o mini. Hannuna har rawa yake yayin da na amshi wayar, ana Wagawa na fara magana.
"Ba..Baba!"
Na fada, daga can bangaren Yaya Radiya ta ce.
"Bara a mi™a masa."
"Yaya ki yi hakuri, wallahi bansan komai ba akai, wayar ta hannun Mijina."
"Mijinki kuma? Amma sa™on da kika turu dazu ai kece kika rubuta."
Yaya Radiya ta fada, ban kai ga bata amsa ba ta sake cewa.
"Ga Alhajin."
"Alhaji ina kwana, Ya jikin naka?."
Na faWa cikin rawar murya.
"Rawasiya kina lafiya?."
Ya tambaya muryarshi cike da alamun rashin lafiya, wani abu ya tsaya min a rai, yana cikin halin rashin lafiya amma tambaya ta yake ina lafiya?
Ina son Sardauna sosai, amma tabbas bai kai ko rabin soyayyar da nake yi wa Alhaji ba.
"Alhaji lafiya kalau, ya jikin naka?"
"Nana yaushe zaki zo?"
"Baba anjima zan zo, yana dawowa zan faWa masa ko da daddare ne sai nazo, ko gobe da safe."
"Toh shikenan! Ubangiji Ya yi miki albarka."
"Amin Baba, Allah Ya baka lafiya."
"Amin amin Nana."
Ya faWa yana mikawa Yaya Radiya wayar.
"Nana ki samu ki shigo dan Allah."
Yaya Radiya ta fada, duk jikina ya yi sanyi na ce.
"In sha Allah Yaya." Daga nan na katse kiran na bawa Ra'is wayarsa, ya kaWa kai zai tafi.
"Ra'is, baka shigo ba! Baka sha ko ruwa ba."
Murmushi ya yi sannan ya ce.
"A'a ba komai, zan wuce kawai sai kinzo."
Yana faWin haka ya fice, ni kuma na koma Waki na zauna kan kujera, kamar wacca aka haskawa majigi haka rayuwata ta baya ta shiga tariyo wa a idanuna.
******
Asalin labarina.
Da farko sunana Rawasiya Alqasim Babuga wacca kowa ya sani da Nana, sunan da na zaSawa kaina kenan, tun ta sowa ta ni macece marar son hananiya ko kaWan, bana son abun da zai dame ni a rayuwa ko ya ne, abun da nasa a gabana shi nake yi, shi nake so.
Mahaifina Alhaji Alqasim sannanne a anguwarmu dama gari gaba daya, kasancewarsa dan siyasa mai a™idar ri™au. Sannan Wan kwangila ne da yake da kamfaninsa wanda yake karbar ayyukan daga 'yan siyasa da ma sauran mutanen gari.
Mahafiyyata Sailuba haifaffiyar jihar Adamawa yola ce, irin kyawawan fulanin nan ne na Yola, a lokacin da mahaifina yake tashin aikin kwangila da kuma siyasarsa Allah Ya haWashi da ita, bayan shimfiWa kyakyawar soyayya kuma suka yi aure, inda mahaifina ya dawo da ita unguwar Federal Low-cost dake dutsen jihar jigawa. Unguwa mai kyau da daWin zama, unguwar da ta kasance ta masu matsakaicin hali, akwai manyan gidaje da kuma ™ananan, akwai hada™ar masu kuWi da talakawa.
Zaman tsarkakkiyar soyayya ya ginu tsakanin Mammanmu da Abbanmu da muke kira da Alhaji da Hajiya, tun haihuwarsu ta farko Alhaji ya zo da wani tsari, babbar Yayarmu sunanta Radiya, bayan yan shekaru aka sake haifi wata aka saka mata Rumaisa, bayan ita kuma sai namiji da aka sa masa Ridwan, a lokacin Alhajinmu yana tsaka da siyasa da samun kudi ya dau™esu gaba Waya suka sauke farali, a lokacin ina ciki sai bayan sun dawo da aka haifeni inda aka samin Rawasiya, ban kai shekara ba dukkanmu Alhaji ya kwashe mu zuwa aikin Hajji, wanda bayan dawowarmu daga aikin Hajji karyar arziki ta sami mahaifina.
A lokacin ina da wata goma sha Waya a duniya, wannan lamarin ya afku, inda mahaifina da alhalina suka shiga matsanancin tashin hankali na rayuwa, duk arzikin mahaifina ya kare a yadda nasamu labari wani lokacin gidanmu suna iya kwana ba tare da suncu abinci ba, ana haka mahaifiyata ta shawaraci Alhaji da ya sayar da gidansa na Federal low-cost ya nemi wani karamin mu koma can ragowar kudin ya sa su a kasuwa, haka kuwa aka yi mahaifina ya siyar da gidansa na Federal Low-cost ya nemi matsakaicin gida a unguwar Yelwawa, inda suka dawo nan, gida mai dauke da dakuna uku, Na Alhaji (Baba) daban, na Hajiya (Umma) daban, Yaya Radiya da Yaya Rumaisa daya, shi kuma Yaya Ridwan tun da shine karami yana kwana dakin Hajiya, ni kuma ina karama. Daga Amana Academy makaranta mai zaman kanta aka dawo da yan gidanmu zuwa Government Day School Yelwawa, canji rayuwa ya yi wa gidanmu ™awanya, ni kam basan duk dadin da aka sha ba lokacin da Alhaji yake Alhaji bare nasan yadda aka shiga lokacin da ya dawo Hajijiya, wannan ya sanya Alhaji yake matukar so da tausayina, kasancewar gatan da yayuna suka samu a lokacin da suke kamar ni bansame shi ba, Alhaji ya fara zuwa kasuwar Laraba da take ci Mako Mako yana siyar da kayan abinci, sauran ranakun kuma yake zama a shagon da ya bude shima na awon kayan abinci a gida.
Legendspen
08129553971
*SARTSE*
-Amanar-Janafty-
*Sayyid Legendspen*
MAH/2026/001
Sadaukarwa.
RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA
(Mai Dambu)
Shafi na huWu
(04)
Shekarata uku a duniya, Hajiya ta sake samun ciki wanda shine cikin autanmu Ra is a zuwa wannan lokacin Alhaji ya fara samun rufin asiri, duk wani ci da suttura na masu rufin asiri baya gagararmu, haka karatu babu wanda bamayi, na zamani da na addini, bayan haihuwar Ra is sai Alhaji Yasa aka shigo da shagon waje zuwa cikin gida, bayan ya sami wani babban shago a bakin titi, tabbas ance haihuwar Ra is ta zo da alheri sosai domin akwai wasu cikin yaran da Alhaji yake biyawa kudin karatu da yan bu™atun rayuwa lokacin da yake amsa sunan Alhaji, wani cikinsu mai suna Isah Nadabo da ya zama babban mutum shine ya siyawa Alhaji Shagon a bakin titi, bayan ya cika masa shi da kayan siyarwa, sannan wani kuma ya cika mana gida da kayan abinci.
Tun daga lokacin haihuwar Ra is bamu sake zama da rashi ba a gidan, muna zaune cikin rufin asirin ubangiji, haka kuma muna samun tsayayyiyar tarbiya daga wajen mahaifiyarmu Hajiya, domin Hajiya macece mai tsayawa kan tarbiyar yara. A bangaren kyau, dukkanmu irin kyawunta mu ka yi mussaman mu matan da mu ka yi har farinta, Yaya Ridwan da Ra is da suka dan dakko duhun Alhaji, sai suka fi mu kyau ma, sabida ba suyi duhu dilik ba, sannan ba suyi haske fatau ba, sun yi black beauty ne, ko na ce Brown, ga sumarsu irin ta fulani, wacca duk muka Webo daga Hajiya, dan mu matan ma babu wacca gashinta bai kai gadon baya ba, kasancewar nafi su Yaya Rumaisa ™an™anta sai akafi ganin kyawuna akansu, kuma ni kaWai ce na yo dara dara idanu irin na Alhaji, shi ya sa aka fi ganin kyawuna akansu. Sai da fa duk gidan kowa ya kwana da sanin cewa Yaya Ridwan yafi kowa kyau dan shi kama yake da larabawan Dubai.